shi ne tunda ka fahinceta a
hakan, to sai ka koma can Bakorinku ka nemi daurin bakin su
Inna Tambai da aminan Babanta domin sanin kan ka ne, a duniya
Hadiza bata da uwa kuma aminiyar shawara bayan Inna Tambai,
sannan kuma tafi son Babanta fiye da komi na duniya, idan ka
sami amincewarsu ina gánin za su shawo maka kan Hadiza."
Yanzu a duniya Yusuf ji yake bai da masoya irin Saminu da
Hadizan Jos da Mama Binta. A ran nan ya koma Kaduna kashegari
ya yi ayyukan kanfaninsu da dama ya yi sa` a daya daga cikin
wa`anda ke da alhakin mallakar kanfanin ya na nan ya je Kaduna,
ya yaba da aikin da Yusuf ya gudanar har ya nemi Yusuf da ya zo
gidansa da yamma, gaban Yusuf ya fadi ras domin a niyyar Yusuf
so ya ke da yamma ya nufi Bakori ya kashe su Inna Tambai da
Baba lliya da dadin bakinsa, amma sai ya tuna aikinsa na gaba
da komi, idan babu aikin nan matar ma tsanarka ta ke. Ya cimma
uban gidansa da karfe tara daidai na dare sun yi rubúce-rubuce
har zuwa karfe biyun dare akan kanfaninsu. To a lokacin ne
Yallabai ya lura ba haka Yusuf ya ke ba akwai dai wani abu a
kalkashin ransa, yana tambayar Yusuf bai tsaya wani kawaici
ba ya warware mai irin damuwar da ke cin sa a rai, nan da nan
Yusuf ya fara kawo kwalla ya ce, "Yallabai ni na san na yi
kuskurena amma yarinyar nan ta ki hakura, ga shi abin haushi
wai abokina na kut da kut zata aura."
Yallabai ya yi shiru tausayin Yusuf ya kama shi balle ma
da yaron ya nuna mai shi maraya ne, duk zuri`arsu a kan shi aka
rataya, sai ya ce ma Yusuf "To kai ba ka dan sakarma iyayenta
31
kudi ne ko kamar abokin na ka?" Yusuf yace, "Inal Yallabai ai
wa'annan sun fi karfin a rude su da ku". Yallabai ya yi dariya
yace "kai wawa ne ba ka san halin kanawa ba kenan. Bari na
baka wani guntun labari: akwai wani bakano za shi England neman auren baturiya fara kal, sai abokansa suka ce masa 'wai wai Alhaji ka rufa mana asiri, kai da ba ka jin turanci ita kuma bata jin hausa? Ka dai ci gaba da auro filanin mata kyawawa', sai Alhaji ya yi dariya ya sa hannu aljihu ya fid do takardar 'yar wazobia wata naira hamsin ya daga masu ita yace, 'kun ga wannan, to babu yaren da ba ta ji a duniya, sai dai idan baka da ita'. Yusuf da Alhaji suka bushe da dariya.
Yallabai yace, "Gobe zani gida Katsina sai ka shiriya zan tsaya Bakori na ga iyayen ita yarinyar wa anda su ke da karfi
akan maganar, sai ka shirya da wuri karfe takwas na safe." Yusuf ji yake kamar an ce an bashi Hadiza dan murnar
Yallabai zai sa baki a al'amarin. Karfe goma sha daya na safe suka isa gidan Inna Tambai. Yusuf ne ya fara shiga ya firgita
Inna da cewa ta yi manya-manyan shinfidu ga shugabansu nan gaba daya ya zo ganinta, ai ko Inna ta rude har wata darduma ta shinfida bisa tabarma.
Sun jima ana gaisawa yawancin gaisuwar a bisa matuwar
Baba Kado. Sannan Yallabai ya gangaro bisa zancen Hadiza shi
dai Yusuf na gefe ya takure, (manya na magana).
Yace, "To Inna Tambai ai ina ganin da kai da kaya duk mallakar
wuya ne, ki tuna fa ke mai nemarwa Yusuf aure ce, bayan
kuskuren da yayi domin ko ita takun Ubangiji na iya jarabar ta da
irin hakan, shin ashe idan da ta yi wani aure sannan ta fito ta zo
tace a duniya kuma babu wanada take so sai Yusuf ashe
mahaifiyarsa bata isa ta tursasa Yusuf ba akan ya yi hakuri ya
auro Hadiza, domin kamar kanwa ce a gare shi? Dole ne kuma
ya aureta ba zai ki ba domin kuskuren aure ba inda ba a yin sa.
Amma yanzu inna kuna kallon Hadiza kun kyale ta zata bar
dan uwanta akan wani kuskure kalilan na kuriciya?" Inna Tambai
nan da nan ta ga gaskiyarsu anan, domin ta sha ganin yarinya ta
32
ki mijin sai daga baya, a dawo a neme shl bayan ta yi aure ta hayayyafa, kuma a rnatsawa namijin dole ya aura hakanan bayan
a da can babu irin wulakancin da bata yi mai ba. Yallabai ya katse tunaninta yace "Wannan Amiru ba fa halin sa kuka sani ba, bayan Yusuf tun yana cikin ciki kun san halinsa. Don Allah ki natsu ki sami lokaci ki yi ma Hadiza nasiha irin taku ta manya".
Inna Tambai tace, "Ranka shi dade wannan zance na ka fa
abun dubawa ne, na yi ma alkawari zan yi iyakar kokarina, sai
dai kuma idan haka Allah Ya kaddaro, to sai Yusuf yasa hakuri"
Yallabai ya ji vwani irin sanyi domin babu wanda bai son ya
nemi alfarma a ki yi masa, to anyi mai alkawari yace Yusuf ya
dauko mai jaka cikin mota. Yusuf ya fita da sauri ya kawo jaka
ya tsugunn yaba shi, ya bude ya fiddo bandir din 'yan wazobia
sabbi fil na dubu as hirin ya baiwa Yusuf yace ya mikawa Inna Tambai.
Inna ta bude hannaye tace, "kai Yusuf ina zan kai
wa annan kudi ku bar su kawai". Ya yi dariya yace, "Haba Inna
ku amsa, karamin aikin Yallabai kenan idan ki ka ji babban sai ki rike baki."
Sun isa gidan Malan Iliya motar Yusuf ce gaba ta Yallabai
na biye, sun kuma ci sa'a Malam din na gida. Bayan an gama
gaisawa Yusuf ya gabatar da Yallabai kamar yadda ya gabatar
da shi wajen Inna Tambai, shi kuma Yallabai ya shiga kurunta
matsayin Malam Iliya a wajen Baba Kado, ya nuna masa shi kadai zai iya lankwasa Hadiza