ya ke mata, ya ce, "ina son na ga Mama ta nan gidan".
Hadiza ta mike da sauri ta fita, daman zaman ya gallabe ta,
yaya zai tasa ta ya rinka yi mata kuka ita lokacin da ta yi nata
kukan rashinsa yana ina? Ba yana can ya sami Fa`iza ba, to
itama yanzu ta sami Amiru don haka kada ya matsa mata.
Ta sanarwa da Mama sakon Yusuf sannan ta cimma Hadiza
a daki ta kwantar da Fatima ta koma inda Hadiza ke kwance ta
zauna, ta dubi`yar Jos tace, "A gaskiya kin ba ni kunya wai
duk bakinki da irin tsiwarki amma wai ki ka kasa ce wa Yusuf
komi sai ma wani gatanci da ya samu wanda ban ga Amiru na ya
samu ba". Hadiza ta tashi zaune 'ki vi hakuri, ni kai na nayi
mamakin yadda na yi ma Yusuf, saboda na tsane shi a bisa
28
labarin da ki ka bani, to amma ina shiga falo yadda na gan shi sai
na ji duk na sare domin kwarjininsa da barkwancinsa ya fi karfin
a yi mai wulakanci. Na san a da Yusuf ya yi laifi to amma yanzu
Hadiza ki tausaya masa, ki duba fa har tsugunnawa ya yi bisa
gwiwowinsa yana kuka? Haba! Hadiza ai namiii irin su Yusuf
komi su kai idan har $un gane kurensu sai a yafe masu haka nan,
wallahi yadda ya tsugunna a gabanki ba don kuka ya ke yi ba ni
kam yau da na dauke ku hoto da sauran fim din Fatima, kin ga
irin kyan da ku ka yi kuwa? Kai Hadiza ke da Yusuf Allah ya yi
ajiyarsa!"
Hadizan Bakori ta daga kai ta dube ta ta ce, "kina da
hankali kuwa? Kin manta an tsaida min miji Amiru?" Hadiza ta
ce, "Na fi kowa sani, amma in gaskiya ta zo a fade ta, haka nan
kuma sau nawa ake sa rana a warware wani lokacin ma ana
gobe za'a kai amarya gidan miji ake canza mijin" Hadiza ta cе,
"Tunda ba'a yi akan ki ba, insha Allah ba za`a yi akai na ba, su
Fatima ga su can gidan Amiru".
Suka dade suna kallon juna sannan suka kyalkyale da dariya.
Hadizan Jos ta ce, "Tafdijam! Ina ganin Bakatsine ba na auren
Bakano, sadda duk miji zai saka hulà sai dai kiga (birki kunne)
haka nan za su ranbadawa idanunsu kwalli bajau wa ya aike ni!"
Hadizan Bakori ta dingi dariya har tana kwantawa ta ce, "Wai ya
ake sa hula birki kunne kuma Hadiza?" Ta ce, "Idan Amiru ya zo
ki dube shi tsab za ki gani, amma kin hada da su Yusuf gogaggun
Katsina idan an saka hular nan a murza ta sai ta kusa danganewa
da gira, ke komi na Bakatsine fa daban ya ke, idan har an sami
tsantsar Bakatsine za ki same shi da daddadan lafazi mai tsima
jiki da kashe kwanya sannan ga kyan iya shirya lafazi yadda zai
shigi bil adam, sai kuma wata baiwa da Allah ya yi ma su na
kamun kai, wanda shi ne ya haifar da wata ilhama ta kwarjini na
musamman a gare su, to kin ji dalilin da yasa Katsinawa su ka yi
zarra, amma fa ba su danne `yan Bauchi ba domin suma sun
hada yawancin abinda Katsinawa suka tara, ko kin san duk
Nigeria ba wanda ya kai jama'ar Bauchi da Katsina mulki irin na
29
Kuma sun iya domin irirn jininsu kenan.
Hadizan Bakori ta ce, "kai Hadiza da dai Dr Sani ba dan
Katsina ba ne, sai na ce ya ba ni da bakin ki, to Allah ya taimakeshi
ya fito daga jiharku ta Katsinan. Ni kam ina kin Yusuf ne a
dalilin ina ganinsa a namiiin zara irin su ne a kullun suka hango
abun sha'awa jikin wata za su bar ka zuwa gare ta"..
Ina son kuma ki fahinci abu daya a wajen Kanawa kamar
yadda ki ka fahinci Katsinawa wato a duk kabilar arewa babu
masu ladabi da biyayya da sanin ilmin Islama kamar 'ya'yan Kano
daga nan sai`ya`yan Maiduguri, in da duk Bakano ya ke yana
girmama na gabansa, haka nan bai iya saba maganar iyayensa
ko yaya take, sannan za ki same su cikakkun mutane masu
sana`ar gado tun suna `yan kanana, amma kin hada da yaranmu
na jihar Katsina yawancinsu sun faye girman kai da nuna isar
ba a isa ba, da sauransu, to kin ji abinda ke ba ni sha' awa da
halayyar kanawa.
A can falo kuma Yusuf ya yi zaman dirshan bisa kafet
gaban Mama Binta ya fi awa daya yana kashe ta da lafazinsa
masu dadin sauraro, ya ce, "Wallahi Mama ina tausayin kaina
ina tausayin Hadiza domin yadda na ke sonta itama ni kadai take
so, to kin ga na kyale ta ta cutu akan wani jin kai da kunya?"
Mama ta ce, "E to sai na yadda da kai anan domin zurfin cikin
Hadiza yawa ne da shi, duk yadda ka ke da ita da wuya ka san
abinda take so ko wanda bata so, haka nan mu dai tunda muke
da ita a gidan nan ba mu san ko me ke bata ran Hadiza ba."
Yusuf ya gyara zama ya ce, “To kin san Allah daya ne
Mama, duk duniya daga ni sai Baba Kado wato mahaifinta muka
san cikin Hadiza da bai dinta, yanzu idan da yana da rai tabbas
ya san tafi so na fiye da Amiru babu tantama ba zai tsaya
sauraronta ba zai umurtai ni na ci gaba da shirye-shiryen biki,
yanzu haka idan zan aika na kira ta zata zo, illa dai zata rinka
fada min maganganun wulakanci amma idan na dubi kwayar
idonta wani zubin zan ga ba har cikin zuciyarta take min ba, sai
dai saboda jin dacin abinda na yi mata, na kuma tabbatas idan da
30
ni ne aka sa mana rana babu yadda za ai ta fito wajen wani idan
ya kira ta."
Mama ta ce, "Lalle Yusuf dole ne ka nace domin ba a san
rabo ba, ni dai shawarar da zan baka