cikin jikinsu, to na
yadda shi dai Yusuf yana da maitar, kin ga wasikar da na rubuta
masa kuwa ina nuna masa a shagube bana son sa amma wai
kin ji mayen ya biyo ni har Jos, to ba zai ganni ba, ya gaji da
zamansa ya tafi, Hadizan Jos ta ce, "Tafdijam! Ai wallahi sai
mun je Yusuf din da na ke ji kamar na je har gaban mahaifiyar sa
na ci mutuncinsa ace yau ga shi a gidanmu ba zan je na fada
mai maganganu ba wannan shi ne kuma karya!"
Murna da dadi suka kama Hadizan Bakori domin ta sami
mai yi mata maganin Yusuf yadda zai daina zuwa gareta. Suka
shirya don zuwa falo, abin mamaki har Mama Binta ta shirya
masa abinci an kai masa ya ma gama cì, shi ma direbansa yana
can waje an kai masa.
Hadizan Jos ce a gaba yayin da Hadiza ke bayan ta
rungume da Fatima an nade ta cikin tawul amma idonta biyu.
Ya amsa sallamar Hadizan Jos yana mai murmushi ya сe "Kar
dai ace min ke ce mai jegon, lalle godiya ta tabbata ga Sarkin
halitta da ya sauke ki lafiya ga ki tangaran-kamar ruwan sama,
wannan ina baki shawara kanwata idan kin tashi komawa gidan
Dr. Sani sai ya baki sabon sadaki domin na sabon amarci". Haba
nan da nan `yar Jos ta kyalkyale da dariya ta ce, “To na amince
kai ne mai amsar mani tunda kai ne yayana" Ya mike ya nufi
Hadizan Bakori ya cę, "Masha Allah bebin kenan? ya amsa cike
da murmushi ya koma ya zauna ya dade yana kallon Fatima ya
sha mur ya ce, "A duniya yauşhe rabon da na ga jariri ma
kyau irin wannan? Ya Allah! Ya Allah!! Ya Allah!!! Ka ba ni irin
wannan kyakkyawar jaririyar nan da wata tara!"`Yar jos ta
kyalkyale da dariya ta ce, "ka san ko abinda ka ke fadi, nan da
wata tara fa ka ce! Don Allah ka kara watanni". Ya kara zubaw
26
aririyar ido ya ce "Ai ni idan ma zata rayu ban ki ba a haifar
min ko nan da wata biyar ne kanwata". Ya kai fuskarsa daidai
kumatun Fatima yana sumbatarta ya dago ya dubi su Hadiza da
Hadiza ya ce, "Kin gama ma Dr. Sani komi Hadiza". Hadizan Jos
da Yusuf suka kyalkyale da dariya tace, "Ashe haka kake,
gaskiya ba ka da dama". Suka shiga yi ma juna bayanan
anguwarsu a can Abuja Yusuf ya fara kwatanta mata gidansa
ya ce ya san kanfanin Dr. Sani amma bai san gidansa ba.Yar
Jos ta ce "Ni ma na gane naka gidan inda teloli suke, wa` anda
sun fi yin'aikin hannu, na taba raka Dr. amma na zauna cikin
mota domin maza sun fi yawa a wajen". Yusuf ya yi dariya ya
ce,."Yes, kin gano gidana kenan." Tunda suka shigo falo Hadizan
Jos ta canzawa `yar Bakori yayin da`yar Bakori ta sha mur
tana ta hararar`yar Jos akan ta daina yi ma Yusuf dariya ta
shiga zaginsa kawai.
Fatima ta shiga rigima tana dan korafin kuka, Yusuf ya yi
galala yana dubar su Hadiza ya ce, "To kun ga fa inda za ai rikici
da ni ban san yadda ake rarrashin jariri ba, domin sai na ga
tamkar zan matse shi". Ya mike ya nufi Hadizan Bakori da
Fatima ya mika mata, ya ce, “Ga ta Gimbiya". Yana murmushi
yayin da ita ta sha bula, sai ta rungume Fatima a kirjin ta tana
riritata nan da nan ta yi shiru, sai Hadizan Jos ta mike ta ce, "ina
zuwa, bari na kawo mata ruwa na canzó mata hula kila wannan
ta yi mata nauyi."
Bayan tafiyarta an yi `yan mintoci Yusuf na kallon Hadiza
da Fatima babu abinda ya ke yi sai addu` a Allah ya bashi Dije ta
haifar masa kamar Fatima.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ranki shi dade, ina gajiya? Ta dago kai ta galla masa harara ta ce, "Wai me ya kawo ka nan,
ba ka ga abinda na rubuta ma ba ne?" Ya yi dariya yace, "Oh
yes! Na ga ni mana, ai shi yasa na zo don muyi shawara, ina fa
zan yadda ina matsayin yayanki ki auri wanda ba kya so?"
Anan kuma ya saki layin wasa ya sha mur ya ce, "Don Allah
don Annabi Hadiza kin galabaitar da ni, kin wahalad da ni, na
27
azabtu na shiga halin da ban taba zatun diya mace zata sáka ni
ba, duk a dalilin dan kuskure kalilan, ki yi hakuri (anan sai ya
mike ya isa gabanta ya durkusa gwiwa bibbiyu) yana afi da
hannuwa yana hada ta da girman Allah, ga kwalla taf da idonsa
itama Hadiza anan taji jikinta ya yi sanyi karara, ta tuno irin
matsayin Yusuf a gidansu yadda mahaifiyarsa da kannansa ke ji
da shi, amma a yau gashi tsugunne gabanta yana kuka yana
mai rokonta.
Idonta ya kada ya yi jajur ta dubi Yusuf ta ce, "Wallahi
Yusuf ban rike ka da komi ba, domin ai ka so ni lokacin da na ke
shan wahala Allah ne bai yi aurenmu ba sai dai a gaskiya wallahi
ka ji na rantse bana iya fasa auren Amiru a wannan lokacin".
Har yanzu Yusuf na tsugunne ya ce "Hadiza don ba kya so na
kin fi son Amiru ko?" sai kawai Hadiza ta sami kan ta tana jin
tausayin Yusuf amma kuma tace mashi, “E to„ba wai bana son
ka ba ne, ai kai ma na so ka a lokacin da na so ka din, yanzu
kam gaskiya Amiru na ke so". Wasu kwalla suka sake taruwa a
idon Yusuf ya fiddo hankicinsa ya goge idonsa ya yin da kwayar
idon ta yi jajur, a daidai nan ne Hadizan Jos ta iso da niyyar kawo
ma diyarta ruwa amma ganin Yusuf na tsugunne a gaban
Hadiza vana kuka, sai ta ja da baya ta koma daki.
Yusuf ya koma ya zauna dirshan a gaban Hadiza sai gugar
kwalla