NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 11 of 37

uba tsakanina da Yusuf? Amma kin hada mu kina gara mu kamar wasu 'yan yara, ai ni a zato na bai kamata ki rinka sauraron kowa ba, bama Yusuf kadai ba, haba Hadiza dlarajar da Allah ya yi wa mahaifinki kin fi karfin haka ya kamata ace duk wata hulda da wani namiji kin jingine ta." Hadiza ta ce, "zaka iya rantsewa akan yau Yusuf ya gan ni?" Amiru duk nauyin Hadiza ya lullube shi ta kara cewa "ka tabbatas tunda na tsayar da zancenka na sake kula wani da namiji? Duk shirmen Yusuf me ka ji ance nayi nuna alamun zubar da mutuncina? Dan Allah Amiru idan za'a zarge mu a rinka jiran ana kama mu dumu-dumu amma ban da zargi, domin ni dai ma'aikaciya ce idan mun fara samun irin haka kaga ba karamar matsala zargi zai haifar mana ba a rayiwar aurenmu. Amiru ya ce, "To don Allah wannan ta shige haka nan, 23 wallahi sanin halin Yusuf na yi shegen mutum ne, duk abinda ya kallafa rai yana so sai yaga bayan sa. Hadiza ta juyo ta dubi Amiru ta ce, "Ba dai komi ba me ya hana shi auren wadda ya mutu yana ciwon so Fa'iza?" Amiru ya ce, " ai lokacin da shirmen kuriciya bai kai munzalin da dabararsa zata mallaka masa komi ba". Hadiza ta ce, "gaskiya ban yadda da kai ba anan ai idan mutum jarumin namiji ne ya dace ace da kuriciyarsa ya nuna kwazo ya amshe ma wa'anda suka fi shi mata." Amiru ya janye hannunsa daya daga kan sitiyarin mota ya shafa kansa ya ce, "Ai shi kuma aure ba haka ba ne Hadiza na Allah ne yadda duk ba ki tsammani haka yake faruwa, yanzu ba gashi da can da Yusuf zaku yi aure amma Allah bai yi ba, a wancan zamani babu irin lallashin da ban yi masa ba akan kada ya kyale ki amma ya ki, cikin ikon Allah sai gashi Allah ya hada mu zamu yi aure." Hadiza ta shayar da Amiru mamaki ta ce, "tsakaninka da Allah idan ka ganni a zamanin da Yusuf ya ki aure na zaka iya aure na?" Amiru ya ce, "menene na wannan tambayar?" Ta ce, "haka dai na tambaya don Allah fada mani?" Ya ce, "sanin gaibu sai Allah! Suka yi shiru cikin motar kowanne da tunaninsa, tabbas Amiru ya tuna hotunan Hadiza tana 'yar shekara shabiyar wanda Yusuf ya taba nuna masa ko kusa bai taba tsammanin za`a sami sambaleliyar mace ba kamar wannan. Da yamma likis suka isa gidan Baba Rilwan gida kam ya fara cika da`yan suna na murnar diyar da Hadizan Jos ta haifa gobe ta ke suna. Amiru ya ce, "To Hadiza ki gayas man da maijegon sai na zo da yamma ni zani in nemi masaukin kwana. Ta ce, "To sannu o, Allah huta gajiya". Ya dube ta su kai murmushi, abinda ya fi damun Amiru shi ne Hadiza sai kodewa ta ke yi ta rame ta yi fari fat abinda da ya dauka rasuwar mahaifinta ne, to amma ya san matsalolin Hadiza sun fi karfin kidaya sai du'ae kawai. Ranar suna aka radawa jaririya sunan Mama Binta wato Fatima. To Hadiza ta sami kanta cikin rashin hutu ranar suna Ja 24 washegarin suna domin duk kawayensu ita ke kula da su haka nan Dr Sani ya dora mata nauyin yawancin hidimomin sa da kula da jama'arsa. Saboda haka ma ko da Amiru ya zo ranar suna a tsaitsaye ya ga Hadiza da mai jego amma sun karrama shi ta fannin abincin suna da kayan kwalan na suna, su kai sallama ya ce zai tafi Lagos sai kuma bayan sati biyu su hadu a Kaduna. Kashegarin suna Hadiza ta shiga kintsa ma mai jego kayanta da ta samu suna kara tantancewa. Maijego ta roki Hadiza don Allah ta kara kwana kafin ta wuce Kaduna, itama Hadizan ta amince domin rudanin da ke kanta duk ya sukurkutar da ita, tun tana daukar Yusuf wawa bata da lokacin sa shirme ya ke, to yanzu ko al'amarin sa ya fara tayas da hankalinta, don haka ne ma ta yanke shawarar idan ta koma Kaduna zata shirya ta je Bakori ta yi ma Inna Tambai bayani don ta je ta yi ma Gwoggo Halima magana saboda a tsawata masa ya fita hanyarta. Yusuf a Kaduna yana ci gaba da gudanar da ayyukan ofis din su, kullun ya sami sukunin tunanin Hadiza babu abinda ya fi bata masa rai irin wasikar da ta rubuta masa, anya Hadiza ta iya tabbataswa kanta cewa bata son shi? Ya nemo takardar ya kara karantawa ya-yi mata kyakkyawar nazari sai ya ga ma ashe shirme ya ke yì, wannan takarda na bukatar a kara tattaunawa. Da yamma ya shirya ya nufi gidan Baba Garba don ya ga Hadiza. Maigadi ya ce ai ta je Jos bata dawo ba, Yusuf ya nemi ganin matar gidan, aka shigar da shi falo ta tabbatas masa Hadiza na can Jos suma yau suka dawo. Ya ce, "Ita fa sai yaushe?" Ta ce, "Ba na iya cewa domin na je maijegon na cewa ta kwana biyu a can". Yusuf ya yi shiru sannan ya ce, "Don Allah a yi min kwatancen gidan Baba Rilwan". Ta ce, "idan ka je Jos ka san dai jami'ar Jos ba boye take ba, kana isa get gidajen Malaman zaka iya hangen wani sabon gida zaboda ba su fi wata biyu a cikin sa ba, to nan ne gidan Baba Rilwan." 25 Karfe sha daya da `yan dakoki Yusuf ya sauka gidan Rilwan shi da direban Kanfaninsu, su Hadiza sun koma daki kanan sun raka Dr Sani zai koma Abuju, Mama Binta ta aiko wai su je falon baki ga Yusuf can na san ganin su. Hadizan Bakori ta dafe kirji ta dubi `yar Jos ta ce, “Ke da gaske ne fa wasu mutanen suna da maita a
🏠