za
ta je Jos. Ya yi mashi kwatancen gidansu na Kaduna.
Suna aje waya ya latsa wayar gidan Yaya Garba, wani
yaro ya dauka yana jin an ce Hadiza a ke son magana da ita sai
ya ce mata, "Anti Hadiza ga Baba Amiru". Ta je da saurí ta dauki
waya ta ce, "Na yi hushi angona, haka mu ka yi da kai saboda
Allah Amiru?" Yadda Hadiza ta rausayar da murya ta tsumar da
Yusuf amma a lokaci guda kishi ya dirar masa wai Haidizansa ke
ma Amiru magana mai dadi irin wannan? Kamar ya aje amma
kuma bai iyawa, ya ce, "Ba Amiru ba ne, Yusuf ne. Kina lafiya?"
Ta ja tsaki ta aje wayar.
Hadiza na sauraron aiken Amiru ne domin ya yi mata
alkawarin turo direba zai kai ta wajen taron sunan Hadizan Jos,
to amma shiru a zaton ta shi ne ya yo waya ta dauka da niyyar
ta yi masa tsiya sai ta ji Yusuf, to bayan ta dawo ta zauna sai
kuma Amirun ya yo wayar ya na bata hakuri akan ta yi hakuri
tafiya sai gobe, domin ya samu ya kammala `yan hidimomin
gabansa ne don haka shi ne zai kai ta ba direba ba.
Yusuf ya je ofis a washegari, ya rinka duba fayal-fayal
don ganin irin ayyukan da ke gabansu, a kalla akwai zuwa Legos
don shigar da wasu takardun kwangila da aka ba kanfaninsu na
sa wutar lantarki a garin Zariya, haka nan akwai zirga-zirgar
zuwa Kaduna kamar sau biyu a satin nan shi ma ana bukatar
kula da kwangilar hanyoyin da kanfanin su ke yi, akwai son akai
ma gwamnan jihar Kaduna wasu takardu don sa hannu suma na
sabon shigar aiki ne.
Yusuf ya ja birki daga nan ya ce, "Yauwa". Maganar zuwа Kadunan nan ita tafi damunsa domin wata dama ce da zai samu
ta kusantar Hadiza ba tare da aikinsa ya raunana ba, ya mike ya
nufi ofis din Shugaban kanfanin, ya gayas da shi bayan ya yi sallama. Yusuf ya shiga nuna mai mahimmancin kasancewarsa
a Kaduna na tsawon lokaci don ya samu ya gudanar da wa`annan
ayyukan da suka taso. Shugaba ya duba a tsanake sannan ya ce,
"A lalle kam, bayan wannan ma akwai wata takarda da ta iso a
21
daga Kaduna za` a zauna mitin da gidan gwamnatin da
kamfaninmu a sati mai zuwa don haka ina ganin kai ya dace ka
wakilci kamfaninmu, saboda haka duk sauran maganar shiryeshiryen maganar kudaden tafiya sai ka sami Yakubu
akawuntanmu sai in ce sai mun ji waya ko kuma ince sai Allah
ya dawo da kai lafiya". Yusuf ya ce, "zan yo wayar domin ta
yiwu wani abun ya taso daga baya."
Ya isa gida ya yi sallama da su Falanke ya kara jaddada
ma Falanke cewa kada a kara barin wata 'yar iska ta shigo mai
gida. Falanke ya ce, "Haba Yallabai tun yaushe wannan ta
kwaranye mu dai addu'ar mu Allah Ya bamu Hadiza a matsayin
matar sunna". Yusuf aka yi murrmushi aka сe "To Amin, mun
tafi farautar aure sai mun dawo."
A gidan Baba Garba babu kowa daga Hadiza sai mai aiki
sai ko mai gadi yana can bakin get. Hadiza ta ci kwalliya amma
a saukake kwalliyar matafiyi yadda ba zata wahala ba, jefi-jefi
ta kan dan dubi agogon hannunta ta na zargin Amiru da son ya ja
masu tafiyar dare.
Yusuf ya isa gidan Baba Garba ya rubuta ma Hadiza wasu
"yan maganganu na rokon arzikin son ya ganta, maigadi ya kai
mata wasika har gabanta ya fadi a zaton ta ko Amiru ne ya kara
aikowa yana bada hakuri, to sai tagaYusuf ya rubuto ta ja tsaki
ta tsaida maigadi ta rubuta masa amsa kamar haka
Yusuf
Ni Hadiza yanzu na manyanta a halin yanzu a gani na
kuma wannan zamani na da zan sarrafa al'amurana na zabin
aurena saboda haka ya dace na auri mutumin da bana so?
Maigadi ya mika ma Yusuf takarda wani daci ya daki
zuciyar sa, wai shi ko maye ne bai kyale yarinyar nan ne? Tabbbas
ya san ya yi nacin son Fa'iza to amma itå Fa'iza bata nuna masa
masifar kiyayya irin haka; nan da nan idanunsa suka yi jajur ya
rinka ganin duhu har shi maigadin, yayin da ita kuma Hadiza
tana can tsaye gindin taga tana kallon irin halin da Yusuf ya
shiga da ta ga ya shiga motarsa ta saki labulen ta dan rintse
22
idonta ta ja tsaki ta ce,`shit kawai'. Ta kwanta bisa gado ta
rinka tuno irin son da ta nuna masa a da anan ma ta kara tsanarsa.
Yusuf na kokarin fidda motarsa daga gidan Baba Garba
yayin da Amiru ke kokarin cinna tasa motar ciki, suka rinka huci
na jirı zafin dayansu yayin da shi Amiru na jin zafin me ke kawo
shi wajen Hadiza idan ba yana samun fuskar Hadizan ba ne?
Yayin da shi Yusuf yana jin zafin wai kan wannan Hadiza ke
muzanta shi? Tunda Hadiza ta shiga motar Amiru taga canjecanje da dama, ranta ya bata ganin da yai ma Yusuf ne, don
haka itama sai ta share shi ta daure ta ta fuskar.
Sun sami kimanin tafiyar awa daya da rabi, kafin Amiru
ya dan juyo ya dubi Hadiza ya ce, "yaya kina son wani abu mu
tsaya nan garin?" Hadiza kanta a sunkuye ta yi tagumi bata
tsinka masa ba sai akwai ta girgiza kanta nuna alamuna'a, ta
kara takurewa jikin taga, to anan ne kuma abinda rai ke so sai
Amiru ya dan rikice ya yi yakace dama bai bullo ma Hadiza da
hushi ba, ai fa sai ya shiga rarrashi, na tsawon lokaci amma bai
shawo kan Hadiza ba.
Amiru ya ce, "Amma a gaskiya Hadiza kin bani mamaki
ca nike idan duniya da gaskiya nine da hushi, ki d