annan hutun ganin ita ta zo na daya
a makaranta sannan kuma ta shiga aji biyar a lokacin saura
wata tara ta kammala karatun sakandire. Yaya Amina kamar yadda`ya`yanta ke kiranta itama Dijen Yaya take kiranta
sai ta umurce ta akan ta shirya ta je ta gano mahaifinta da
su Gwoggo Tambaya.
Da la'asar ta sauka garin Bakori ta sha lullubi da bakin gyale yayin da take daure da wata atanpa 'yar Japan
mai tsantsa ruwan bula da baki, an dinka riga da zani da kallabi na atanpar, takalmanta sukol ta yi shar da ita, 'yan matanci da kuriciya ke ta fita jikinta kai kace sarauniyar 'yan mata ce ta wannan zamanin. A kafadar ta tana rataye da wata bakan jaka mai cin kimanin zani da riga kaman kala shidda. Tana ta wuce jama'ar da ta sani suka santa
amma abin mamakin Dije kowanne ya kan dauke mata kai
nuna alamar bai gane ta ba.
Dai.dai kwanar shiga lungun gidansu ta ci karo da Shafa mai kosai dauke da kwaryar wakenta zata nika injin. 19
Dije cikin fara'a tace, "Sannu mai kosai". Shafa ta kara
dafe kwaryar wakenta, tana ma Diya kallon tsoro tace,
"Yawwa sannu 'yan mata daga ina ki ke yarinya?" Dije ta yi
dariya tace, "Mai kosai ni ce Dije diyar Baba Kado fa!" Mai
kosai ta bude baki tace, "Iko ya tabbata wajen Sarki Allah.
Yanzu Dije ke ce kika murje haka? Kai duniya idan mutun
bai mutu ba bai gama kallon abin al'ajabi ba, ke ko Dije ina
kike aure haka?" Dije ta yi dariya tace, "Mai kosai ban yi
aure ba, ina hannun innata ina makaranta."
Mai kosai ta tsaya galala tana mamakin canzawar
Dije yayin da Dijen ta shige ta bar ta nan tsaye cikin mamaki.
Malan Kado na kishingide bisa tabarma a kofar gidansa, ya
dawo kasuwar Dayi ya gaji likis, yana ta kallace-kallacen
yaran anguwa, sai ya hangi galleliyar budurwa ta nufo
gidansa, zuciyarsa ta bashi ko Dije ce, amma wata zuciyar
ta rinka raya masa yaushe Dije ta kai girman wannan
budurwar da wayewarta? Illa kawai murmushinta da irin
kallon ta sun kamanta masa irin na Dije.
Ya mike ya zauna sosai ta iso gare shi ta ce, "Sannu
da hutawa Baba". Ya ce, "Ni fa na ce wannan Dije ce amma
canzawar da ki ka yi gaba daya ta hana na amincewa
zuciyata, keDije! Ke ce haka?" Tana cike da dariya tace,
"Nice Baba".
Ta durkusa bakin zaure ta fara gaishe shi yayin da ya
rinka amsawa baki bude, ya ce, "Ban taba zaton za ki yi
girma kamar jikin mahaifiyarki ba! Masha Allah tubarkallah,
Sannu da hanya, ya su Aminar da kannanki?" Ta amsa
"lafiya lau. Baba sunce duk suna gaidaku."
Yace "Shiga cikin gida ni ma gani nan shigowa". Tа
mike ta shiga. Ta cimma su Sabura da Ankudi ana nan
kamar yadda ta bar su, babu cikakkar tsabta kamar yaya
Amina. Ta yi ma Allah godiya da ya raba ta da rayiwa irin ta
su Ankudi, babu tsabta babu kamun kai balle uwa uba kula
da ibadar Allah, amma wajen yaya Amina dole ne ka'ida
wankan nan ayi shi sau biyu a rana, sallah da zuwa Islamiya
kuwa da ladan ya yi kiran sallah ne, kowa ya nemi butar
alwala, sannan babu hali karami ya raina na gaban shi,
20
idan bako ya yi sallama ya shigo gaba daya yaran gidan
za` a tarbe shi da sannu da zuwa a kuma gaishe shi, sannan
a ba shi guri ba'a zama inda manya suke. Tabbas Dije ta
sami kanta cikin canji kala-kala wanda ta ji dadin hakan.
Su Ankudi da Sabura da yaransu ko wanne ya yi wal
da ido yana kallon Dije, Duk da kishi ya turnikesu amma
babu mai kuzarin iya cin zarafinta kamar da, a dole kowacce
a dakale ta ce "Maraba da Dije". Ta ce "yauwa sannunku
gwoggo mun same ku lafiya?" Suka ce, "lafiya lau". Ta
sami kujera 'yan tsugunne ta zauna, me Ankudi ta gani,
oho, ta debo ruwa a kwano ta mika wa Dije. Dije ta amsa
cikin fara'a tana sha sannan Ankudin ta sake cewa, "zai fi
kyau ki shiga da jakarki zuwa dakina ko na Sabura bai dace
ki aje a tsakar gida ba."
Wannan ma ya kara baiwa Dije mamaki ta mike ta
shigar da jakarta hatta gyalenta ma sai ta aje ta fito ta
zauna ta na kiran kannanta.
Bayan ta yi sallar issha'i taci tuwo tace, "Baba zani
gidan Gwoggo Tambaya na gaisheta" Ya ce "To, kice ina
gaisheta, amma fa kada ki kwana a can ki dawo nan gida".
Ta ce "Lah Baba yanzu zan dawo ai nima ina son mu yi hira
da kai". Ya yi murmushi dadi ya lullube shi domin yau ji ya
ke duniyar ta yi masa tas, a dalilin ganin Dije, yana son Dije
son da ya ke jin zai iya bada fansar ransa akan ya kubutas
da ran Dije.
Haka itama Dije tana son Amina innarta sannan tana
jin dadin zama da ita, ko yanayin canjin jikin Dije ka duba
ka san tana jin dadin zama da uwarta, amma abin mamaki
son da Dije ke ma Malan Kado cikin kashi goma kashi biyu
zata iya baiwa uwarta Amina, tana son Babanta fiye da
son da ta ke ma uwarta, yayin da ita Amina tafi son Dije a
duk cikin 'ya'yanta.
Dije ta yi sallama "Salamu Alaikum". Inna Tambai ta
amsa sallamar Dije sannan Dijen tasa hannu ta yane labulen
dakin su kai ido nudu da Inna. Inna ta fid do ido ta sa
hannu ta dafe habar baki tace, "D-I-J-E!" Dije ta fada cikin
dakin da sauri ta zube kan tabarma ta dora hannayenta
21
Inna Tambai tana kyalkyatar dariya.