NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 26

wari." A ranar litinin da daddare kwana a kai Gwoggo Halima da Malan Tukur na yi ma Yusuf huduba suna cewa, "Don 16 Allah Maitama kada ka kuskura shaidan ya rinjayi zuciyarka ka canza akidarka domin yanzu za ka tsincí kan ka ne a wani matsayi na daban. Haka nan ko wane mataki Ubangiji ya kai ka, ka tabbata kana girmama na gaba da kai, sannan ban da danne hakkin na kasa da kai ban da danne hakkin al'umma ka tabbata akwai ranar da za ka tsaya gaban Sarki Allah ka yi bayanin yadda ka gudanar da al'amuranka.” Magana ta karshe itace "Don Allah Maitama idan ka sami aiki, sannan ka mallaki mahallinka to ka zo gida ka duba mata 'yar mutunci ka aura domin darajar da namiji bata cika sai da iyali." A nan ne fa Yusuf ya yi sunkui da kai, an ya zai iya mallakar mace a duniya? Kwata-kwata ya dawo rakiyar mata, domin kamar shi wai Fa'iza bata son shi to menene abin mannewa sai wata ta so shi? Shima a ra'ayinsa ya sallama kaunar ko wacce irin diya mace a duniya. Karfe goma sha biyu na rana ya isa ofishin Alhaji Yahaya, zuciyarsa ta raunana ganin irin tsananin tsaron da ake yi akan Alhaji Yahaya, arizikinsa daya ya nuna katin Alhajin sannan aka bar shi ya shiga. Aikin ya samu na wani shaharararren kanfanin 'yan kasa da hadin gwiwar nasara jar fata. Mamaki ya kama Yusuf bai taba zaton zai iya samun hanyar wani ba wanda ke aiki a wannan kanfanin amma yau albarkacin Malan Tukur ga shi an dauke shi aiki a kanfanin. Wasa-wasa wata daya juriyar aikin Yusuf yasa manyamanyan daraktoci na kanfanin sun san da Yusuf sani ko ba na wasa ba, irin sanin da ya jawo Yusuf jikinsu, domin ko tsakar dare Yusuf na tare da su ana gudanar da aiki, wanda ba ko wanne ma'aiki zai iya ba, wannan ta ba su damar fara fita da Yusuf kasashen waje. A ranar wata asabat da yamma direban kanfaninsu Yusuf na janye da shi a motar kanfani sai ya ga abokinsa Amiru cikin wata galleliyar motarsa, ya umurci direba da cewa ya tsayar da Amiru. Amiru ya fito a lokaci guda Yusuf ya fito daga gidan baya. Amiru yace, "Kai mutumin daga ina! Yaya na gan ka 17 haka kamar bakon wani baindiye?" Yusuf ya kama kafadar Amiru ya janye shi gefe daya yace, "Ai ni bana sai hamdala. Amiru na sami aiki daya da daya anan Abuja, yanzu kai a ina ka ke ne?" Amiru ya ce, "Ba ni Kano ba ni Legos amma na fi zama nan Abuja. Ni ke tafiyar da yawancin kasuwancin mahaifinmu ina fatan za ka zo gidana mu zauna anan Abuja". Yusuf yace "Ai ni ma sun ba ni gida yanzu haka har na dauko wannan uban rigimar don ya debe min kewa wato Falanke tela, yana nan na manna mai daki daga jikin gidana ya fara dinki, a kullum shagon baka rasa jama'a ana sokonci." Amiru yayi dariya ya се, "Ка сe kai gidanka gidan hira ne, inda su Falanke su ke ai wajen raha ne, Insha Allah nan zan mayas gidan hira ta, yau din nan ina nan zuwa." KASHI NA SHIDDA Bayan shekara shidda da rabuwar Dije da Yusufa, bari mu ji yadda Dije ta samu shekara shidda a gidan mahaifiyarta Amina. To Amina dai bata da wata diya mace baya ga Dije domin kimanin maza biyar cif ta haifa a gidan Malan Isa, to dawowar Dije hannunta wannan sai ta bata wata dama ta nunawa Dije gatanci da so na kasancewarta diya mace tilo a gare ta, duk wata 'yar atanfar zamani ko yadin zamani wanda bai fi karfinta ba za'a ganshi a gindin Dije, yayin da ita kuma Dije ta mayas da zancen káratun'ta ne kadai matsala a rayiwarta. Farkon jarabawarta ta zo na bakwai, amma a fannin lissafi itace ta zo na daya, domin Dije na ganin beken wa`anda ke cewa lissafi na da wuya ita a ganinta duk rashin natsuwa ne, a ranar da malaminsu ke yaba mata cewa tana daya daga cikin 'ya'ya matan da ya taba gani wadda ta iya lissafi, nan ne tunanin Yusuf ya bijiro mata a dakin Inna Tambai yana koyar da ita wasu darussa, amma da suka zo kan lissafi, sai ya lura ta na so ta kure shi domin shi ma ba gwanin ba ne wajen lissafi, ya ce, "Da mamaki yadda ki ka iya lissafi haka har kin so ki kima" Ta yi 18 zarce murmushi tace, "Ba haka ba ne abinda ke faruwa mutane ne sun yi ma lissafi mummunar fahinta, har ya zamanto wani ma bai taba tsayawa ya koya sai kawai yace, "Bana yin lissafi shegen wuya ne da shi". Yusuf ya yi kasake maganan Dije ta yanke shi, domin ya san akwai abokansa da dama wa'anda ba su shiga aji lokacin darasin lissafi zamanin yana sakandire wai su ba su ganewa. Tace, "Ni ko ka ga duk aiki babu wanda na ke fahinta irin lissafi". Yusuf yace, "ko ba ki fadi min ba ni na- san haka, sai dai na ba wani labari. Ina alfahari da samun mace mai natsuwa da fahintar abinda ba kowa ne ke iya fahinta ba." Suka hada ido ita da shi suka yi murmushi. Nan da nan Dije ta yi ajiyar zuciya ashe duk karya Yusuf ke mata, ba haka take ba a zuciyarsa? Abinda ya fi daurewa Dije kai shi ne me yasa tun farko Yusuf bai muzanta halittarta ba sai daga karshe? Ita dai ta san akwai wani abu da Allah ke nufi akan ta da Yusuf amma dalilin Yusuf ba dalili ba ne. Sai da Dije ta sami watana bakwai cif a Malunfashi bata je Bakori ba, a w
🏠