lumshe ido
kamar bai ji abinda ta ce ba, zuwa can yace "Wallahi kuwa".
Ya mike ya nufi dakinsa yace ma gwoggo a cikin ledojin
nan a duba akwai busasshen kifi a dauke a gyara kada ya
lalace.
Kwana biyu da dawowar Yusuf duk ya fita
kamannunsa domin mugun zazzabi da damuwa ta sakar
masa, tun Gwoggo Halima nayi masa dariya ta dawo abu
ya dame ta. Aka diba aka ce kila maleria din sa ce ta dawo
likita yace, sam ya auna jinin babu maleria, to ai fa sai
gwoggo da malan Tukur suka shiga neman masa maganin
gargajiya, kamar na shawara da basir saboda irin sambatun
da aka ji yana yi a hankali Malan Tukur ya lura duk ciwon
da ake tunanin yana damun Yusufa ba su ne ba, sai kawai
ya koma rokon Allah wanda a kullun yana rubutawa Yusufa
Bissimillah kafa dari babu daya sannan addu'ar (Ya Hayyu
Ya Kayyum bi Rahamatika Astagfirillah) ta zamanto abin
ambaton Yusuf a kodayaushe, cikin ikon Allah wannan su
ne sanadiyar warkewar Yusuf tas, ya murje ya roki gafarar
mahaifiyarsa.
Yusuf ya fid do takardunsa ya shiga neman alkı lunyulungu kamar karamar hukuma da ma'aikatar karamar
hukuma da maʼaikatar ilmi ko za'a dauke shi malamin
makaranta, har dai gidan redio Katsina ya leka amma shiru
ka ke ji.
Babu dare babu rana ya rungume Malan Tukur tamkar
yadda zai rungume mahaifinsa a kullun yana ta dibar karatu
da nasihohi da dabarun zaman duniya, idan har baya tare
da Malan to yana shagon Falanke tela yana hira.
14
Falanke tela kamar yadda su Yusuta kan krasa
sunansa na gaskiya Sha'aibu, aminin Yusuf ne tun suna
yara, illa dai kawai Falanke bai yi ilmin zamani ba kamar su
Yusufa. Falanke mutun ne mai ban dariya ga barkwanci
don haka tunda ya fara sana'ar dinkin keke a kullun shagonsa
cike ya ke da samari ana hira ana ban dariya yanzu haka
Yusuf sai ya kai karfe dayan dare a shagon Falanke suna
hirarsu, wani zubin har Yusuf ya amshi maballi ya rinka
taimaka masu.
Kamar kullun yau jumma'a da la'asar sakaliya Yusuf
ya shiga shagon Falanke sai yace, "Falanke za ni gidan
Malan Tukur akwai wata addu'a da na ke koyo ina son na
gama daukar ta a yau ko za mu tare ne, daga can sai na
raka ka Funtua sayen zaren dinki?", Falanke yace "Wannan
zance na ka Yusuf shine abin yi, daman yau kuiyar dinkin
nan na ke yi".
Suna zaune gaban Malan Tukur yana baiwa Yusuf
karatu, duk sha'awa ta kama Falanke, ya rinka raya ma
zucıyarsa lalle shi ma zai dawo daukar karatu wannan
dunıyar shirme ce kawai.
Mota irin ta daga wane sai su wane ke iya shigar ta
a kasar nan ta danno kai ta shigo zuwa kofar gidan Malan
Tukur, gaba daya su Yusuf suka raja'a wajen kallon wannan
galleliyar motar tamkar gajimari.
Direban ya fito da sauri ya bude mai motar mota.
mota. Alhaji Yahaya ya fito cikin kyakyawar shiga kai kace domin shi aka kera wannan mota.
Yusuf da Falanke suka rusuna suka gayas da Alhaji Yahaya yayin da Malan Tukur ya mike suka shiga dakin
zaure shi da Alhaji Yahaya domin su gana, kimanin shekara
goma sha takwas kenan Alhaji Yahaya na zuwa wajan Malan
akan wasu bukatansa na duniya. Alhaji Yahaya babban ma'aikaci a Abuja, haifaffan garin Katsina ne, kusan Alhaji Yahaya na daya daga cikin manyan ma'aikatan da Katsina
ke takama da su a matsayin`ya yanta.
Sun jima suna zantawa da Malan aka bukatar da ta
15
kawo shi. Malan yace, "Kamar kullunı hana son ka ji komi
Insha Allah za mu kai kukanmu wajjen Ubangiji, abinda kuma
duk ya zartas mu dauka shi ne mafi alhairi a pare mu".
Alhaji Yahaya ya yi murmushi zuciyarsa ta yi mai dadi don
haka ya ke zuwa wajen Malan domin malan mutun ne mai
dayanta Allah.
Malan Tukur yace "Alhaji akwai wani taimako da na
ke nema a wejenka ina fatan za'a taimaka min idan har an
ga abin bai fi karfinku ba". Alhaji yace "Haba Malan kа
fada mana". Malan yace "yaro gare ni ga shi nan waje ya
kammalo karatunsa na jami'a amma mun nemi aiki mun
rasa, shi ne zaka taimaka ka samar masa aiki". Alhaji yace
"A kira shi Malan"; Malan ya kwallawa Yusuf kira.
Alhaji yace, "Ina takardan imakarantar taka?" Yusuf
gabansa ya fara bal bal, duk farin ciki ya mamaye shi tabbas
ya san batun aikin sa ne kuma babu abinda zai hana irin su
Alhaji samar masa.
Yace "Ranka shi dade su na nan". Ya dubi Malan ya
ce "Baba suna cikin takardun ka na zaure bari na je na
kawo" nan da nan Yusuf ya milka takardu hannunsa na
rawa.
Alhaji Yahaya ya duba takardun Yusuf da kyau ya
kada kai yace, "Bapu komi Malan ai yaron ya yi abinda ko
wacce ma'ikata ke so, zan iya samar masa aiki a ko ina,
amma ba dole ne sai aikin gwamnati ba ko na kamfani ne
masu zaman kan su zan samar masa".
Yusuf ya karkatar da kai cikin murmushi yace, "Godiya
nake ranka shi dade".
Alhaji ya fid do katinsa mai adireshinsa na gida da na
ofis ya baiwa Yusuf yace ka same ni Abuja ran talata mai
zuwa.
Yusuf ya fito shi da Falanke suna ta murna da zumudi,
Falanke yace, "Don Allah Yusuf idan Abuja aka aje ka nima
ka yi min hanya na koma can da zama an ce sana'ar dinki
tafi ci a can". Yusuf yace, "Insha Allah na yi maka alka