an itace rana ta farko da ya fara jin kunya da
cewa wai yana son Fa'iza da aure. Ya yi karfin hali ya daga
kai yana kallon mutanen da ke kai da komowa a kofar gidan
su Fa'iza, babu wanda ya damu da shi tamkar dama bakon
Malan Inusa ne ba wai na diyar gidan ba. Mota da mutun biyu a gidan baya direba na janye 'da su, suka iso gidansu Fa'iza, nan da nan kowa da kowa ya maida hankalinsa a
kan wa`annan baki hatta Malan Inusa ya mike ya nufi wajen
su, yayin da ya ke tafiya ne ya ke cema Yusuf "Ina jin ma yallabai ne Shehu angon Fa'iza".
*
Yusuf ya mike a hankali ya tari yana tanagal - tangal,
a haka ya rinka tafiya a kalla ya yi tafiyar awa biyu cif a
kasa, can hanyar Hanwa low coast ya mike ya sami wani
tsaunin dutse ya haye ya yi zaune.
Ga abinda ya rinka fadi: "Fa'iza ba ki cuce ni ba,
babu wanda ya ingiza ni cikin wannan wahalar sai ni kai na
Yusuf sai ko kaddara" Ya yi shiru sannan ya ci gaba, "To
wai minene laifin Fa'iza anan? Idan ma Allah ya isa na yi
mata lalle zata dawo kai na in ga bala'i, na rasa Fa'iza na
rasa rayiwata, ina son Fa'iza a yau na yadda Fa iza bata so
na. Why?"
Abinda Yusuf dai bai da labari shi ne, a lokacin da
mahaifin Fa`iza ya ce lokaci yayi su ba shi mijin da suka
zaba, babu tantama Ismail Fa'iza ta fiddo, anan take
mahaifinta yace, "Fa'iza idan dai ni zan ba ki shawara ki
dauka Isma'il ba mijin aure ba ne, domon na yi iya bincike
na banji gaskiyar sana'arsa ba, saboda haka idan aure za ki
yi na tsoron Allah, ki kiyayi Isma'il". Ana cikin haka ne, a
wata rana sun je filin jirgi rakiyar Baban su Allah ya dora
idon Shehu dan gwamna na wannan zamanin akan Fa'iza.
Alhaji Abba yayi binciken da musulunci ya kayyade
aure ya fada akan Shehu.
Yusuf ya yi kuka daga karshe yace, "A yau babu
Fa'iza, babu Dije tana can gidan wani mijin". Amma rashin
Dije alhairi ne domin ita ma ya san ba wani son shi take yi
ba, auren kawai take so ayi mata.
Ya duba agogon hannunsa karfe goma da rabi na
dare, ya mike ya nufi gidan su Awal, a kalla hankalinsa ya
dawo jikinsa ya fada a fili "THE GAME IS OVER!" Tafiya
yake har ya ga ji likis, gajiyar ta fara tambayarsa, ya rinka
jin kamar ya watsar da kayan da ke hannunsa wato dai
tsarabar Fa'iza amma kuma ya bai wa kan sa shawara gara
ya jure ya rike ya kai ma su Sarai kada asarar ta yi mai
yawa.
Ya isa gidansu Awal karfe daya saura na dare, abin
mamaki Awal na zaune a zaure yace "Awal lafiya baka
kwanta ba?" Ya ce "Ina zan kwanta na yi bako ya bace a
gari, don Allah ina ka je Yusuf?" yace "Bar ni kawa Awal ba
ni ruwan sanyl na sha."
Ya kawo masa ruwa har da damammar hura a kwano,
12
Yusuf ya sha nan da nan idanunsa suka kara kadawa su kai
jawur.
Yace, "Yanzu nan saboda Allah Awal ka san an daura
auren Fa'iza?" Awal yace, "kai yanzu din nan a yadda ka zo
kana ta faman rawar jiki ko na shekara ina fada ma an
daura wa Fa'iza aure yaushe za ka yadda da ni? To ai garama
dai da hakan ta faru, wallahi Yusuf baka jin magana haka
kawai da rana tsaka ka canza halayyarka, ni wallahi cikin
sha'anin nan mahaifiyarka kadai na fi jin tausayi, bayan irin
kuncin da ka saka ta na jama'ar gari sai kuma yadda ka
rinka mai da kan ka dan karya saboda Fa'iza. Shi ne, ka yi
ma Allah Subahanahu godiya da bai makareka da auren
Fa'iza ba, sannan ka roki mahaifiyar gafara a bisa karyace
- karyacen da ka rinka yi mata". Yusuf ya dafe kan shi
"Don Allah Awal zan sami panadol na sha kai na tamkar
ana fasa kwakwa". Awal ya mike ya bude wata jaka ya
mika masa panadol.
Yusuf yana jin Awal na ta sharara bacci yayin da shi
komi ya yi mai zafi daga zuciyarsa har kwakwalwar kan sa,
ya rinka jin shin a duniya akwai wanda ya taba shiga kunci
irin na shi? domin shi dai yanzu bai ga kamar Fa'iza ba a
duniya son ta ya ke, son da bai iya misiltawa dan adam
yayin da ya san shi da Fa'iza har abada, to wannan kalmar
ce ke wahalad da shi.
Da safe ya dibarwa Awal tsarabar da ya yi ma
mutanen gidansu. Awal yayi godiya ya dubi Yusuf yace,
"Ka tabbata za ka iya tafiya Bakorin nan ko dai mu je na
raka ka asibiti, ka ko ga yadda yanayin jikinka ya canza?"
Yusuf yace, "Babu komi zan lallaba, ai gida za ni" Awal
ya ce, "Shi kenan mu je na raka ka tasha."
Ya isa gida, Salmanu na zaune cikin shagonsu, wasu
yara na sayen Omo da magi mai tauraro, ya hango Yusuf
na sauka bisa dan acaba da wani dan acaban ya labto kayan Yusuf nan da nan Salmanu ya sallami yara ya nufi wajen Yusuf, yana yi masa barka da`zuwa tare da amsan kaya yana shiga da su cikin gida. Rabon da Yusuf ya ga fara'ar Gwoggo Halima tun zamanin yana neman Dije sai
13
ko yau tamkar zata kama shi ta rungume.
Ya sami tabarma ya kishingida da ganinsa ba sai ka
tambaya ba ka san yana tattare da matsaloli Gwoggo ta
kama aje masa abinci a gabansa amma ban da ruwa babu
abinda ya taba.
Ya fara tambayar jama'ar gida kamar kannansa da su
Malan aka tabbatas masa kowa lafiya. Gwoggo tana
murmushi tace, "Sai kuma mu ka ga Fa'iza da wani ana
hidimar daurin aure ba da kai ba?" Yusuf ya