NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 25 of 26

ga buhun suga da buhun shinkafa, suka ce daga mahaifin Amiru shi ma yana nan zuwa gobe, sannan Amiru ya ce, ayi masu gaisuwa kamin dare yana nan zuwa yau. Inna Tambai ta yi hanzarin sauke abinci sannan ta zubawa bakin Kano. Sai da suka yi Sallah sannan suka kara bada hakuri suka Kano, suna yabon Hadiza akan lalle Amiru zai mori mata ga kyau ga addini sannan ga natsuwa. Tsakanin ta da kowanne bako ya shigo gaisuwa a natse cikin mutunci sai ta juya bisa karatu wani dan karamin kur'ani da ta ssyo a Madina. Idan har ta yi magana mai tsawo, to da Inna Tambai ne, ko ana bukatar wani abu. Rasuwar Baba Kado ta kama alhamis ne, saboda haka a lokacin da Yusuf ya sanar wa Amiru a waya yana shaida masa Hadiza ta yi waya tana sanar da shi mutuwar Babanta, gaba dayansu mutuwar ta bugi zukatansu, domin a gaskiya Yusuf, koda bai san kowacece Hadizan ba, ya tausaya mata a bisa yanayin sautin muryarta, sai ta dawo mai da tunanin ta shi mutuwan mahaifin, tabbas babu abinda ya fi mutuwa ciwo, radadinta a zuci duk yadda dan adam yaso ya bayyana bai iyawa, sai dai ran da a kai ma ka, sai ka ji abinda kowa yaji. Saboda haka, sai Yusuf ya rinka ba Amiru hakuri har ya ce, "ina fatan zaka shigo jirgin Abuja don mu raka ka Malunfashi wajen ta'aziya;" Amiru na so ya ce masa "ai a Bakori ne" amma sam maganar ta kasa fita bakinsa saboka juyayin tsohon Hadiza sai dai kawai yace; "To ina nan zuwa." Falanke ma da ya ji tafiya ce wajen kauyensu sai ya ce, "yallabai zan biku", suka ce "Bissimillah!" A ranar jumma'a suka baro Abuja. A motar Amiru su uku ne da Yusuf da wani direban kanfaninsu sai wata galleliyar motar Yusuf da ya shigo da ita kwanan nan daga Hong-Kong su Falanke ne da wani abokin su da direban Yusuf. Sun iso Zariya ne Amiru ke cewa ina fatan ka zuba komi da komi a sabon gidanka na Bakori dòmin ina ganin 60 anan zan zauna har sai an yi sadakar bakwai, kasan mahaifin Hadiza mutumin Bakori ne." Yusuf ya juyo ya dube shi ya ce, "amma ce min ka yi yar Kaduna ce, iyayenta ne a Malunfashi;" Amiru ya ce, "kai labarin Hadiza na da tsawo. Ainihin mahaifinta ma dan Bakori ne, uwarta ina jin aure ne ya kai ta Malunfashi koko yar malunfashin ce, shi ne ban gane ba, idan de mun je gidan, kila kai ka gane tunda dan gari ne." Shi ma kan shi Yusuf sai labarin ya dan rikice masa ko me yasa, oho! Suna isowa Bakori gidan Yusuf yana a bakin hanya ya ce, "ga fa gida Amiru mu tsaya mu aje kayanmu tukun?" Amiru ya ce, "haba mu dai fara isa gidansu Hadiza, ka san kuwa ban san wannan shi ne gidan ka ba? domin kwanan baya mun zo nan Bakori da Hadiza har ta ke cewa, kai amma gidan nan ya birge ni, na ce mata, ai dole ya baki sha'awa domin irin wannan gidan a kauye?" Yusuf da Amiru su kai dariya. Me kuma zai faru, kwatancen da Amiru ke yi ta inda suke bi duk hanyar gidan Malam Kado ce, har aka isa kofar gidan.Yusuf ya amince gidan Baba Kado ne, ya dora kan shi cikin tafukan hannunsa, nan da nan idanunsa suka yi jajur sai kwalla shar, da ya tabbatar dai Baba Kado ne ya rasu. Mutuwar ta bugi Yusuf tamakar yadda ta bugi Hadiza domin har ga Allah Yusuf yana son Malam Kado kamar yadda Kado ke son Yusuf. Su Malam Tukur ne da Malam Iliyasu da sauran dattawan gari ke zaune a zaure, suka zauna suna juyayi. Malam Tukur ya ce, "Yusufa ashe ka ji mutuwar?" Yusuf ya ce, “E to". Sai kawai ya kara fashewa da kuka da ya tuno yau shekara daya kenan rabban sa da zuwa wajen Baba Kado suka mike za su shiga cikin gida, a bisa hanya ne Amiru ke cewa, "ashe ka ga ne Baban?" Yusuf ya ce, "Wallahi Amiru, ina son tsohon nan tamkar mahaifina." Suna shiga dakin da Inna Tambai ta ja su, wato inda Hadiza ta ke, anan ne kuma Yusuf ya kara zubewa da ya sha wani mamakin da ya ga Hadiza. Itama Hadiza ta dubi Yusuf ta juya ta maida kallonta 6.1 akan Amiru sannan ta sadda kai hawaye shar suka rinka fita. Koma mai Hadiza ta canza, babu tantama yasan wannan Dijensa ce, itace Amiru zai aura, lalle wannan abu da daure kai. To amma abin mamaki daya ne anan, me yasa ako yaushe yazo Bakori mahaifiyar sa Gwoggo Halima ta ke damunsa da fadan ya yi aure, bayan ta san Hadiza na nan bata yi aure ba amma ta ki gaya masa? Ya kawad da wannan tunanin ya daga kai ya dubi Dije tabbas itace. Mutuwar Baba Kado ta dawo ma da Yusuf da mutuwar mahaifinsa danya. Hadiza ta daga kai tace, "Amiru kana nan ko har sai lahadi idan an yi sadakar uku?" Ya dube ta yace, "ina nan ma har sai an yi sadakar bakwai, saboda ina ma da masauki gidan wannan abokin nawa da na ke gaya ma ki Yusuf." 62 DANDANO DAGA LITTAFI NA UKU Bayan an yi sadakar uku ta marigayi Alhaji Kado ran lahadi kenan, Amiru na can gidan su Hadiza sai ya dawo gidan Yusuf don ya dan kwanta yà huta, me zai faru? Yusuf ne a dakin da ya zauna ne Amiru yayi masauki duk ya yi dai dai da kayan Amiru, ga hotunan Hadiza nan kaca-kacă, sannan yana ta bincike masa takardu. Amiru ya tsaya bakin kofa yana kallon ikon Allah, yayin da Yusuf ya yi kasake na rashin gaskiya. Na lok
🏠