ar gona yaddiisl
je sai dai aka maido shi gida barin jikinsa ya shanye." ed em irla
Karfe shidda na yamma Hadiza da Saminu sun iso gud
asibitin Funtua, hankalinta ya kara tashi yadda ta ga bakin Alhaji Kado ya jirkice tayi kuka ta yi kuka har sai da ta san vavix
kuka ba zai mata maganin komi ba sannan ta hakura. Tana erda
nan zauna tare da su Malan Iliyasu can wajen karfe tara nalauek
dare sai ga suInna Tambai, anan suka dawo da wani sabon
kukan.stnores s вnenлu ly usb st awuat ly et aslulleo isa
Inna Tambai ta lallashi Dije suka tafi Bakori ta kwanaA
a can amma asuba na yi ta dawo Funtua gani take ta yisogal
kamar zarta iske ya mutus sy syhams haао ву вyhsb ly вy ise
Misalin karfe daya da rabi na rana Armiru ya iso yace
mata ya yi waya ne Kaduna matar Baba Garba ta ke sanar 00 61
masa garabinda ya faru shi ma daga Abuja ya ke. Tace,
"Wallahi ciwon Baba kuma ya tashi". Amiru ya ce, "Dama yayi masa kárfi haka?" Tace, E' yace, "Amma Hadiza ya
dace mu kai shi wata asibitin da tafi.wannan". Tace, "in dai
law
sbud
cayill
57 82
on samu ne na fi son A.B.U. Zariya". Yace, "A to barı mu
ja mu ga likitan wannan asibitin ko?" Suka jora zuwa
ofishin likita suka yi masa bayanin bukatarsu ya dauko katin
Alhaji Kado ya duba sannan ya rubuta takarda wadda za'a
kai can A.B.U. Zariya.
Ya debe su a motorsa sai Zariya sai da ya tabbatas
an duba Alhaji an bashi gado sun shiga yi masa abinda
ya dace, sannan yace Hadiza ta zo ya kai ta G.R.A gidan
abokinsa da safe sun kawo ta shi kuma ya wuce Kaduna.
Kimanin kwana biyar haka Amiru ya rinka jele hanyar
Zariya har sai da ya ga sirikinsa ya fara gane mutane, sanna
kuma kullun zai ga Hadiza ta rungume shi tana ba shi
abinci. Sai hankalin Amiru ya kwanta ya ci gaba da harkan
kasunwancinsa. Da zai tafi Lagos sai ya bar wa Hadiza
cellular din sa ya ce "idan akwai wata damuwa ki yi min
waya, da zarar na sauka Lagos zan sanar da ke lambar
wayan daki na, haka nan ga ta ofis din mu na Kano da
Abuja ga kuma na abokina Yusuf shi ma yana aiki ne a
Abuja sannan ga ta mahaifina!" Hadiza ta bude ido ta се,
"lah ba na iya yi ma Baba waya," ya ce, "haba Hadiza ashe,
shi ma ba Babanki ba ne, in dai ki na cikin damuwa, ki
buga mashi."
Ta raka shi har gindin mota, tana yi masa Allah ya
kiyaye, hanya, ya ce, "kin tabbata dai wa'annan kudin sun
ishe ku?" ta ce, "Haba Amiru sai kace wadda zata sai rai,
yaushe zamu kashe wa'annan kudade."
Tana zaune kusa da Babanta tana bashi ruwan lemo
sai cellular ta yi tsuwa, ta dauka ta yi kunnenta a zatonta
ko Amiru ne, sai ta je an ce, "Ina Amiru" ta ce, "ya je
Legos?" aka ce, "wa ke magana?" ta ce "matarsa ce Hadiza"
sai ya yi dariya ya ce, "Ran amariya ya dade, idan ya bugo
ace ina san magana da shi abokinsa ne Yusuf daga Abuja;"
ta ce "zan sanar da shi, sai anjima."
Alhaji Kado ya rinka badardarawa maganarsa guragura
wai menene kuma wannan? Hadiza ta yi mai bayani. Ya
bude baki numa alamun yana mamaki. ita da su Malam
Iliyasu suka rinka yi mai dariya..
58
Ana ta murna sauki na ta samuwa, daga Legos Amiru
ya yi mata waya ya ce, "yau dai sauran kwana ashinrin da
biyar bikinmu. Ubangiji Allah ya ba Baba lafiya don mi ji
dadin shagali." Hadiza ta ce, "amin" ya ce, "ki gaida min
Baba, sai na zo gobe."
Da azuhur bayan su Malam lliya sun yi mai alwala
sun kawo dutse ya yi sallah. Kafin ya kwanta, sai shakuwa
har idonsa na kafewa. Nan da nan Hadiza ta ruga kiran
likita, suna isowa tana rike da hannun likita. Likita na duba
Alhaji Kado, amma i.na, babu Abdulkadir, ya amsa kiran
sarki Allah.
Hadiza ta yi waya dakin Amiru amma shiru ba'a dauka
ba, ta yi ofis din su nan ma ana ta surutu bisa layin, kwatsam
idonta ya fada bisa lambar Yusuf. Ta na yi bugu daya,
Yusuf din ne ya dauka, ta ce, "don Allah ka nemi Amiru ka
sanar da shi sirikinşa ya rasu yanzu a nan Zariya." Kafin
Yusuf ya yi wata tambaya, ta kife layi. Tana sharan hawaye
a fice zuwa bakin titi, ta nęmo masu motar haya wadda
zata dauki gawar Alhaji Kado.
Kafin mangarib har an kai shi makwancinsa, ya bar
su Hadiza da juyayin rashinsa da sauran rigingimun duniya
wa'anda ba su karewa sai in irin wannan ta afku.
Ana sallar mangarib, yaya Amina da mijinta suka
iso amma ita anan zata zauna har sai an yi sadakar uku.
Kashegari Hadiza da Inna Tambai suka gyara dakin
marigayi Kado suka shinfida dardumarsa inda za su rinka
zama kenan. Ita da yaya Amina da Inna Tambai da mutanen
da suka zo masu ta'aziyá, koda yake inna Tambai bata ga
ta zama ba domin Hadiza ta bayas da kudi an yanka rago
sannan an sawa buhun shinkafa ta ce a dafa saboda zuwan
baki na nesa.
Aiko misalin sha biyun rana sai ga motoci biyu ta
maza da mata daga Kano iyayen Amiru. Inna Tambai ta yi
murna da shawarar Hadiza da suka gyara dakin marigayi
da ina za su saka wa'annan kosasun mutane? domin dakin
su Ankudi, zaman shi sai ka daure.
lyayen Amiru har da daron sinasir da daron waina
59
da na shinkafa suka zo suka ce a baiwa jama'a sadaka,
sannan kuma