NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 20 of 26

akori. Hadiza ta cika `ya hazika, jarima kamar namiji domin sai kace ta taba zuwa aikin Hajji komi ita jke ma ubanta, idan masallaci za su tana nan rike da shi, idan wajen cin abin ci ne mai kyau ta ke zuwa tana sai mashi. Hadiza bata mantawa suna dawafi tana makale da kafadar mahaifinta sun isa dai dai indararan rahama ta ji Baba Kado na sheka mata albarka tare da rokon Allah ya baiwa Dije mijin kwarai, itama a lokacin tana rokon Allah ya gajarce mata wannan zama ya kawo mata mijinta, jin abinda mahaifinta ke fada sai ta ji idonta ya cika da kwalla taf domin tausayinsa. To haka dai aikin hajjin su Baba Kado da Hadiza ya kasance, bayan an sauka arfat an kammala da jifar shedan da dawafil ifada sai Hadiza ta dauki Baba Kado suka shiga tsarabe-tsarabe, ita kam ta sawo akwatuna uku da kaya a 47 a ciki sai abin hannun zinari guda hudu da sarkan zinari cikakken saiti, to sauran sayayyar fa duk na'urorin kicin ne, idan ta yi aure ta zuba a kicin dinta. Baba Kado yace, "Wai Dije wa'annan injinan na mene ne? tace, "Baba akwai na hada biredi a kuma gasa cikin `yan mintoci haka nan akwai na daka nama ayi danquu nama akwai na daka sakwara akwai ma wanda zai fere maka dankali duk cikin dan kankanin lokaci, wannan tukunyan kuwa zata iya dafa kafar sa ko kan rago cikin 'yan mintoci." Malam ya dafe baki yace, "ke Dije ba ko karya suke ma ku ba dan dai ku yi masu ciniki ne?" Tace, "Haba Baba duk muna anfani da irin su gidan Baba Rilwan." Tafiya ta yi kyau domin su Alhaji Kado an dawo gida lafiya, a kullun zauren nan na shi shake ya ke da dattawa kaman su Malam lliyasu, Alhaji Kado ne zaune bisa wata sabuwan darduma ya zuba jallabiya fara sol mai dogon hannu ya dora rawani da kanbun wuya, da gani dai ka ga sabon Alhaji, ba su komi sai sauraren Alhaji Kado yana bada labarin kasa mai alfarma. Malan lliyasu ya ce, "to Alhaji yaya ciwon ka fa, ina ta yi maka zullumi kada ciwon nan ya hana ka sukuni?" Alhaji Kado ya ce, "abin mamaki, sam bai taso min ba, in ban da sau daya a Madina muna shirin barin ta, ai ko sai ciwon kai ya taso min nan da nan Hajiya Dije ta kai ni asibitin larabawa kada ka so kaga irin magungunan da suka hada min yanzu haka ina nan da su cikin jaka, cikin ikon Allah dan lokaci kadan na nemi ciwo na rasa, na tambayi Hajiya Dije ko nawa ta biya? tace min ai su can kasan magani kyauta ne, ko aikin tiyata za a yi ma mutun duk a kyauta ne." To haka dai Alhaji Kado ya kasance, yayin da Hadiza ta adana saye-sayen aurenta a karkashin gadon Inna Tambai ta sallami kowa da tsarabarsa sannan ta zarce Malunfashi ta ba su tasu, ta kwana bakwai a can tana baccin gajiya kafin ta koma Kaduna. Abuja ma kwananta daya wajen Hadizan Jos, a Jos ne bata samu kwana ba domin tana son ta dawo Kaduna da wuri ta gama shiriya-shiriyan ta kaman su gyaran gashi AR a salun zuwa kai sabbin dinkunanta domin washekare zata koma aiki saboda aikin na su ne babu isasshen hutu. KASHI NA GOMA SHA DAYA Yau kimanin wata daya kenan da `yan kwanaki da dawo war su Hadiza daga kasa mai tsarki, karfe goma sha daya na safe tana zaure bakin aikinta, Asabe wata `yar kabilar ibira ta zo wajen Hadiza ta zauna tace, "kai Hajiya Hadizz kowa idan ya je aikin Hajji yana yin baki amma ke sai kyau naga kin kara." Hadiza ta yi murmushi tace, "ke ko ga ni fa ga Babana me zai dame ni?" Suka bushe da dariya Hadiza tace, "Hala baki da aiki ne ko ki ka bar mazauninki?" Asabe tace, "Wannan ofis din za'a rasa aiki na dai zo ne na shaida maki muna da walimar suna ran asabat din nan a gidanmu." Hadiza tace, "Idan har ba zani Malunfashi ba insha Allah za ki ganni." Daga bayansu aka rinka yi masu sallama Asabe ta juya ta dubi mai magana suka amsa masa. "AMIRU NE” ya ce, "Asabe na je mazauniki ban iske ki ba aka ce min kina nan." Asabe ta mike da sauri tace, "lah har ka įso, yaya kaga manaja?" Yace, "har akawuntan ma na gani mun gama da su, komi ya kammala", tace, "yayi kyau" Duk maganar da su ke da Asabe yana satan kallon Hadiza, daga karshe ya kara gayas da ita itama ta gáyas da shi cikin nuna damuwa, sannan ya yi mata sallama suka fita tare da Asabe zuwa gindin motarsa, tace, "yaushene tafiya Japan din?" yace, "Ban fidda rana ba amma dai ban wuce sati daya yace, wai Asabe na tambayeki mana", ta kara matsawa kusa da shi tace, "me ya faru?" Yace, "Don Allah wannan yarinyar matar aure ce?" Tace "lah Hadiza bata taba aure ba." Ya ce, "kina ganin idan na ce ina son ta zata yadda ta aure ni?" Asabe tace, "E to babu ruwan ta dai da kowa, amma kila mijin ne bai zo ba." Amiru ya ce, "yanzu ga ni na zo" Suka kyalkyale da dariya, yace, "kina da wayanta ta gida?" Tace, "E amma ban rike da ka ba sai dai ga ta ofis." Ta fada masa yace yi mani kwatancen gidansu 49 anan ma Asabe ta yi masa yace, "ki taya ni addu'a Allah ya ba ni sa'ar Hadiza" Ta yi danya ta ce, 'To amin'. Ta koma wajen Hadiza a guje tana murna, tace "Albishir Hadiza sai kin ba ni goro." Hadiza dai sai dariya ko da Asabe bata gaya mata ba ta s
🏠