allah suka kebe da Amiru yana tambayansa,
labarin Fa`iza. Yusuf ya yi murmushi yace, "Wallahi yanzu
ma hidiman ta na zo yi anan Kano." Amiru ya yi shiru yace,
"Baka dai dauki shawarar da na ba ka ba kenan a wasika
ta?" Yusuf yayi murmushi. Amiru yace, "Ni dai murna ta
daya da baka batawa yarinyar nan `yar kauyenku rayiwa
ba". Yusuf yace, "Wai Hadiza? Na ji ance ma sun mayas da
ta hannun kakanninta can wani kauye kusa da Dabai ina
jin sun samar mata wani mijin ne a can. Ni abinda ke damuna
yanzu shi ne Fa`iza ta shirya kasaitaccen bikin zagayowar
ranar haihuwarta to shi ne nake son na dan nuna tawa
murnar."
Amiru yayi murmushi ya ce, "me ka ke so ka bata?
Allah yasa bukatar bata fi karfi na ba. Yusuf yace, "kada
ka damu da karfi na zo domin akwai wasu. kudi da a kai
man biyan bashi tun zamanin mahaifinmu na da rai
ranci kudin to shi ne zan yi anfani da nawa, ga su nan a
jaka dubu talatin ne."
Amiru ya zaro ido yace, `Yusuf yaushe ka canza
halinka ban sani ba? To wallahi bari na baka labari idan
kana zaton wa`annan 'yan kudin zai shawo maka kan Fa`iza
kana shirmene, domin ina da kanne mata a gidan nan ina
kuma kallon hidimar da samari ke masu amma wannan ko
kallo bai ishe su ba, saboda duk abinda kake takamar za ka
bata akwai dubun su a gidansu. Ban hana ka neman Fa'iza
ba illa ina baka shawara idan zata so ka ta so Yusuf amma
bana tsammanin kamar 'yar gidan Alhaji Abba na Zariya
har kudi za su iya rudar ta.'
Wannan maganganu na Amiru kamar ba da Yusur ya
ke ba, shi fa ya riga ya yi niyya babu mai hana shi, dole
Amiru ya raka shi kasuwa, ya yi sayayya, ya sai ma kansa
wasu tsadaddun boyel kala da fari sol da mai ruwan bula
yadi biyar biyar zai yi doguwar riga da wando sannan wan
takalmi sawu ciki suma masu kyan gaske farare.
Gimbiya kuwa ya sai mata leshi mai tsada mai ruwan
bula da wata agogo Civic da zoben zinari ya nade su a iril
takardar nan ta nade sakon girmamawa.
A Kano ya kwana biyu aka kammala masa dınkunan
sa. Amiru yace, `Baba zai aike ni Legos wallahi da na halatcı
wannan biki na Faiza, ko don in ga wannan Faizar'. Yusuf
yayi dariya yace "Na gode Amiru Insha Allah kaine na farko
da zan fara aiko ma da hotunan mu na wajen bikin."
Yusuf ya yi kokari su je tare da Awal amma Awal din
ya ki, yace "Wannan sai manya, ba irin bikinmu ba ne. da
dai Wasila 'yar nan Zariya ce dole na je rakiyarta ba yadda
zan yi."
Yusuf ya cake cikin farin boyel ga takalma wa anda
2
suka dace da su yan zamani ya zuba, ya zuba kyautar da
zai ba Fa`iza a wata farar leda ita kanta ledar naira dari ya
saye ta, ya hau mashin ya nufi wani studion daukar hoto
ya dauki daya daga cikin yaran mai hoto aka tsadance akan
dubu daya da dari takwas yace duk motsin da Fa iza ta yi
ya dauke ta amma kada ya dauketa da wani namiji idan ba
shi ba.
A masaukin baki na Alhaji Abba Zariya anan akai
wannan biki. Guri kam ya cika ya batse da samari da 'yan
mata, na haraban gidan domin a haraban aka yi.
Fa'iza da babbar kawarta Shatu suna falo sun gama
shiryawa, sai Fa'iza ta je bakin taga ta tsaya ta yane labule
ta dubi dan adam din da suka taru albarkacinta ko wanne
yaci kwalliya kamar ran sallah. Ta ce `zo nan Shatu ki yi
kallo'. Shatu ta isa inda Fa'iza take ta dafa kafadar ta tana
kallon jama'a. Shatu tace, Wai ke fa'iza yanzu yaya zaki
yi da duk samarinki ne da ki ka hada su anan?' Fa'iza ta yi
dariya tace, `Na yi haka ne don kowa ya san matsayinsa,
zan nuna masu Isma'il kadai na ke so wanda ya ga zai iya
ci gaba da wahala ruwansa'. Shatu ta yi ajiyar zuciya tace
Kina hangen Bello ga shi can kamar zai tashi sama don
shan kamshi?' Fa'iza ta ce, bar ni da shi yau zai zan matsayinsa.'
Yusuf ya harde hannayensa a kirji yana ta dan
shawaginsa can Shatu ta hango shi tace, `Fa'iza wancan
fa mai farin boyel?' Tace `shi ne Yusuf wanda na ke ba ki
labari ina dariya, ni wallahi yaron dariya ya ke ba ni an yi
masa baiko saboda ni yasa aka warware.'
Shatu ta yi shiru ta tsurawa Yusuf ido, sannan ta
nisa, ba tare da ta dauke idonta daga kan Yusuf ba ta ce, "Kin san wani abu kuwa?" Fa'iza tace "kaman me fa?"
Shatu tace, "Yusuf din can ba fa karamin namiji ba ne, ina
tabbatas maki duk mazan da ke gurin nan babu mai kwarjininsa da zatinsa, ke ki dube shi a hankali in da duk ya gitta sai kin ga kamar yafi kowa girma da kyau, ina so ki lura nan gaba idan yaron nan ya kammala jami'a ya sami aikin da zai huta ina tsoronsa da 'yan mata domin sai yayi 3
da gaske. Allah ya dawo min da Tijjani na lafiya daga Canada
sai kin ga kamar su shi 'da Yusufe vet5
Fa'iza ta jima tana kallon Yusuf ko daya bai cikin
'yankayanta, bai bata sha'awa amma maganar Shatu kuab aA
san gaskiya ne. rom dub aory wA hab ab syeb uduq
Tace, Don Allah Shatu ki dan taimake ni kivinganta sb sY
masa jin dadin bikin nan domin na san saboda ni, ya ciwosd irie
bashin boyel din can ko kuma ya aro?" Suka kyalkyale da
dariya. Fa'iza da Shatu suka keta fili suka fito sai walkiyaw
gimbiyar take yi, tafe take tana gaisaw