a, sannan
ta subuls jakarte daga kafada tare da takardun da ke
hannunta ta shige daki ta aje ta fada kewaye ta yi alwala ta
fito ta vi sallar mangariba sannan ta koma falo ta nemi
gefen kalet ta zauna tare da hade kafafunta.
Amina ta juya a fusace ta dubetta ta ce "Munafukar
banza munafukar wofi, kin je kin shiryawa ubanki karyar
da ki ka saba, shi kuma don rashin tunani ya hau kai, to
Allah ya ba ku sa`a tunda ba mu da mutunci ba mu da
daraja a idónku ai ban ga anfanin zamanki ba anan, domin
Rilwan da Isa da Garba duk daya ne sai ki koma can gidan
ubanki ki karaci sakarcin ki." Nan da nan Garba ya dakatar
da ita yace, "Haba! Haba!! Yaya Amina menene na gorin
gida? Mu mun fid da tsammanin Hadiza ta rike `ya yanmu,
idan ta rike kanınanta ai mu ta yi mawa, ban ji dadin wannan
magana taki bia, don Allah idan rai ya baci a san abinda ya
dace a fadi."
Duk wannan bai sa Amina ta saurara da bala'i ba
haka nan sam bata amince da zamanta ba, sai dai ta koma
can Bakori har sai da Garba ya yi ma Rilwan waya yayi ma
Amina fada sannan ta dan sausauta amma da sharadin
kada Hadiza ta sake zuwa wajenta a Malunfashi.
Hadiza ta yi kuka ta yi kuka kamar ranta zai fita ta
kwana tana rokon Amina amma kemerme Amina ta ki janye
hushin ta.
A kodayaushe tana kokarin rubuta mata wasiku na
neman gafara amma dai babu amsa. A wata jumma'a ta
shirya taje ta yi kwana biyu a Malunfashi, babu dai maganar
arziki a tsakaninsu sai dai akwai banbanci tunda ta gaisheta
ta amsa. Lokacin da zata koma Kaduna ta shirya tsab,
kkarsierita maza suka daukar mata kavanta ta durkusa gaban Amina tace, "Don Allah don annabi Yaya ki yi hakuri, kin ga
abin rai, ina iya yin hatsari a yau na mutu ga shi ki na hushi
da ni, me zan ce ma Ubangijina?" Amina ta yi jigum zuciyarta
s natsu tace, "Tashi ki tafi Allah ya tsare, na hakura." 45
KASHI NA GOMA
Tana zaune bisa tebir din ta aiki ya cukume mata
wayar da ke gefenta na dama tayi kara ta dauka, sai ta ji
ashe shugabansu ne gaba daya nan da nan ta kara kwantar
da murya alamar biyayya ya ce, yana son ganinta yanzu
yanzu. Ta shiga ofis din Yallabai ta tsaya cikin girmamawa
sai da ya umurce ta da ta zauna sannan ta zauna, yace, "А
sashen ofishin da ki ke wato (Banking Office) a koyaushe
daga ofishin gwamnati akan baiwa wannan ofis alfarmar
kujerar Makka to a cikin sa'a wannan shekarar kujerar а
hannunki ta fada."
Hadiza Abdulkadir yarinya mai cike da sa'a ta yi luu
da idanu kamar zata some don murna sai dariya kawai, ta
rasa bakin magana, duk irin kalmar da ta furta sai ta ga
kamar bata yi daidai ba.
A wannan dare ta rasa yadda za ta yi ta runtse ido,
ga murna ga tunanin Mahaifinta Baba Kado saboda tun
tana yarinya babu bukatar Malan Kado irin yaje dakin Allah, domin bata mantawa ko labari ya ji ance ga wani za shi
aikin hajji sai ya yi kokari ya je gidansa ya roki alfarma
cewa don Allah in ya je ya roka masu suma Allah ya kirasu
su je wannan waje to ita yanzu yaya za ta yi ta tafi ta bar
mahaifinta? A gaskiya bata iyawa duk inda zata ci rance
insha Allah ita ko za ta cu su tafi tare.
Kashegari tana isa ofis abinda ta fara yi shi ne cekin
din kudinta na ajiya tabbas tana da kudi da za su kai shi
amma babu guzurin kirki ita kuma bata son ta kai shi ya
shiga matsala, ga shi yana da lalurar rashin lafiya a tare da
shi. Sai ta yi ma Hadizan Jos waya ta gaya mata zancen
tafiyarta, ta yi mata murna tace ita ba don ciki ba da sun je,
sai Hadizan Bakori tace, "Matar Dakta taimako na ke so."
Tace, "tunda ki ka hadani da rabin raina za ki samu fadı na
ji." Tace, "wallahi tafiyar nan ce bana son yi ba tare da
Babana ba, to amma kudina basu kai ba shi ne na ke neman
rance, in Allah ya dawo da mu lafiya na amshi ariyas dina
zan maido ma ki." Ta ce, "Gaskiya kin kyauta fadi min ko
46
abinda ki ke so da nambar akwatun ki na banki insha Allah
gobe suna iske ki." Hadiza ta fadi mata.
Ta shirya ta je Bakori tace, "Baba ka shirya za aima
hoto zan tafi da shi domin na biya maka kudin kujerar Makka
ni kuma gwamnati ta ba ni a wajen aikina."
Malan Kado ya saki casbahar da ke hannunsa yа се
"Ke Dije! Kin san abinda kike fadi kuwa?" Tace, "Baba amma
ai kun fi karfin na ja ku da wasa."
Malan ya sadda kai kasa kwalla ta fara taruwa masá.
Hadiza tace, "Haba Baba ai tsakanina da kai sai addu`a,
babu zancen kuka anan."
Yace, "Bań ni Dije wai yau ke ce kika biya min zuwE
Makka? Ni ko idan ban yi kukan dadi ba me zan yi?"
Bayan ta kammala da Bakori sai ta zárce Malunfashi
ta sanarwa da Yaya Amina. Amina ta yi murmushi ta ce,
"To yanzu ke da kina da aure ai da tafiyar ta ku tafi armashi."
Hadiza ta dubi uwar a kunyace tace, "kai Yaya in Allah ya
yarda zan yi auren ne." Tace, "Ke dai ki ka sani."
Duk shirye-shirye sai da Hadiza ta kammala masu,
da lokacin tashinsu ya yi ta je Bakori da miotar ofis din su ta
dauko Babanta, su Malan Iliyasu da Inna Tambai kamar za
su lashe Dije har Kaduna sukai masu rakiya sai da suka ga
tashin su sannan suka koma B