boda ya yi kudi don kudi amma yana can ya
budewa kadangarun bariki kunne, iyakar su da shi ya aiko
masu da kudi amma shi yana can yana shagalinsa, yanzu
wannan ne abin saurare?"
Hadizan Jos daga can gefe tace "A'a Yaya ku
daina wannan maganar ko ni na isa shaida Hadiza bata
jiran Yusuf."
Amina tace "To ta fadi mana uban da take jira yaya
zata mai da mutane wawaye?"
To iyakar fada na iyaye Amina da, Mama Binta sun yi
ma Hadiza amma zuciyar Hadiza ko gezau.
Tsana da kananan maganganu babu wanda Hadiza
bata samu ba a lokacin bikin Hadizan Jos, kowanne ya
tsinci kansa cikin jin dadi a zamanin bikin amma ban da
yar Bakori. Wani karin bacin rai ma shi ne a lokacin bikin
kusan Mamud anan ya tare yana lallashin Hadiza wanda
har ya sa Rilwan ma ya tsoma baki ya rinka lallashin Hadiza
wannan shi ya kara tayas da ran Amina. Wai Dijen da ba
kowan kowa ba za'a zauna ana lallashi bayan da can an ba 42
wani yaro mara kwabo yace bai so amma a yau tana yi ma
mai hannu da shuni yanga. Bayan ta koma Malunfashi Amina
ta shirya ta je Bakori gidan Inna Tambai ta sa mijin Inna
Tambai ya nemo mata Malan Kado ta sanar da shi halin da
Dije ta ke, shi kan shi bai ji dadin labarin ba, hankalinsa da
na Tambaya ya tashi suna al`ajabin me ya sami wannan
yarinva. Tambaya tace, "Malan ko dai tun farkon yarinyar
nan su Ankudi sun yi mata asiri ne abin fa da ban tsoro,
yanzu idan ka tara`yan mata dari akwai mai kyan diyarmu
Dije! amma ace wai bata yi aure ba har yanzu kai Malan da
sake."
Amina tace, "kada ku zargi kowa isgilanci ne irin na
dan yau, ai ni yanzu wannan yarinyar har tsoro take ba ni,
na yi fadan na yi amma ko gezau, sai shegen kukan tsiya?"
Malan Kado yace, "yanzu yaushe zata zo nan Bakori?" Tace,
"Na ji tana cewa dai zata zo cikin satin nan idan ta sami
hutun kwana biyu ka san ta fara aiki anan Kaduna inda tayi
hidimar kasa sun dauketa aiki."
Malan Kado yace, "Wa'annan mutane suna fa da
mutunci sun kama ta sun rungume ai bai dace ayi masu
haka ba." Tambaya da Amina suka ce, "Sabo fa da Allah!"
Yace, "Ku ban ni da ita zata zo ta same ni in Allah ya yarda
karshen watan nan za'a daura masu aure."
Ta sha ado da wata doguwar riga mai kamar alkyabba
ta yane kanta da gyale mahadin rigar kai da ka ganta ka
san girman jami` a ne, domin ilimi ne ke bugun kyau yayin
da kyau ya gogu da jin dadin rayuwar gidan masu da shi,
kai da ganin launin fatar`yan yatsunta ka san sun murzu
da shafar mai mai gyara launin fata."
Tana rataye da`yar jaka a kafada yayin da dandako
ya ke gabanta dauke da akwati don karami na zamani, ta doshi gidan Inna Tambai, Hadiza Abdulkadir kenan. Suna shiga gidan Inna ta amshi akwatinta ta balle jaka ta mikawa
yaro naira goma sabuwa fil. Inna Tambai tace, "Eye ka ga fa mutanen banki!"
Sai da mangariba Baba Kado ya iso wajen bakuwar
tashi suka hadu shi da Inna Tambai inda suka shiga ba nan 43
su ke fita ba, ita dai kanta a sunkuye lalle bata da mafita
sai wajen Allah domin wanda take sa ran samun jin sanyi
shi ma bayan su ya ke.
Tace, "Baba ka duba matsala ta don Allah da kyau
wallahi wallahi na yi kokari na ga zan iya auren wannan
mutumin ko don saboda kai ma amma na ka sa, dalilina
daya ne Baba shi ne iyalen sa." Ta fayyace masa labarin
irin zaman matan Mamud kaf sannan ta kara da cewa, "to
Baba wai shin ko ya aje ni gidana daban ai dai zaman matar
shi na ke wata ran dole ne mu hadu kuma idan mutun mai
mugun abu ne ai ko ba gida daya kuke ba sai ya sami
hanyar da zai tsangwameka, ni kam Baba na sha wuya a
zamanin kuriciyata bana son na kara fuskantar irin wannan
matsalar ko kuma dan da zan haifa. A gidan Mamud fa har
dan amaryar ake zargin uwargidan ta baiwa guba yaci ya
mutu sabada masifar kishi yanzu Baba ina mu ina irin
wannan rayuwar? Ka yi hakuri Baba.insha Allah aurena ya
kusa domin ina ji a jikina."
Malan Kado ya dubi Tambai yace, "idan haka ne ke ai
Dije tafi mu gaskiya." Tambaya ta ce lalle mu bamu san
tarihin gidansa ba, ina fa dalili za mu kai yarinya cikin fitina
balle kishinmu na mata yanzu suna jin ya aje ta gidanta
daban za su dirar mata."
Malan Kado ya aiki Inna tambai Malunfashi akan ta
baiwa Amina hakuri a kyale zancen Mamud, ita ko Hadiza
ta koma fagen aikin ta a kaduna tana zaune abinta cikin jin
dadi a gidan Baba Garba a kullun kwanan duniya sun kashe
fiye da awa suna hira da Hadiza daga Abuja maganar dai
kenan "Wallahi yar Bakori ki yi aure ashe babu abinda ya fi
aure dadi idan ka sami masu halin kirki kamar irin su Dr.
Sani." To irin wannan labarin na `yar Jos ya kan tayas da
hankalin Hadiza har ta ji kamar ta yi ma Abba Abba waya
akan ya zo su yi aure amma kuma babu sha`awa wadda
zata haifar masu da jin dadi auren." Yau ma laraba aiki ya
kacame masu don haka bata sami dawowa gida ba sai gab
da sallar mangariba, me zai faru ta cimma a falo, ita da
Baba Garba da matar Baba Garba tace, Lah! Yaya sannu
44
da zuwa saukar yaushe?' Kallo ma bata ishi Amina ba balle
ta tsinka mata, ta gayas da su Garba da matars