NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 17 of 26

ana ci gaba da kokarin shigar da kansa amma abisa dukkan alamu bai samu fuskarta ba, ya kawo kudi dubu ashirin ya bata, da farko 39 an ta ki amsa amma sai ta yi tunanin don ta raba shi da wa'annan kudi har wani abu ne a wajensa? Sai ta amsa ta yi godiya. Ko sisi bata taba ba ta adana a banki ma`ajiyar kudinta. A wannan dare kwana sukai zance daya na Mamud Hadiza da Hadiza. Bayan sati daya Mamud ya sake dawo wa Kadina wajen Hadiza har ya shaida mata idan zai koma Katsina zai biya ta Bakori ya gaida Malan Kado Sannan ya shiga Malunfashi ya gaisa da su yaya Amina. Hadiza dai bata ce masa komi ba domin a ganinta ta kai matsayin a bar ta ta zabin mijin aurenta da kan ta, saboda ta wuce zamanin auren dole. A ranar da yaje Bakori tamkar an yi ma Malan Kado gafara kowa ya gan shi ya san yana cikin murna, domin Allah ya kawo masa mijin Dije miji kuma na fada aji ako ina cikin fadin kasar nan, lalle Allah na amsar addu`o` in bayinsa in dai sun roke shi, wai yau kamar Dijen da ake muzantawa gidan sa itace babban mutun irin Yallabai Mamud ke tsananin so da aure? Baba Kado ya je masallaci ya yi nafila raka'a biyu yana ma Ubangiji godiya. a A Malunfashi ma gidan Yaya Amina bayan tafiyar su yallabai Mamud, maigidanta Malan Isa ya shigo suka zauna a daki suka zubawa kudin da ya ba su ido, Amina tace, "Yanzu Malan duk fadin jihar nan ta mu wanene bai da labarin wannan mutumi da kyawawan halayensa?" Malan Isa yace "Ke maganar jaharmu kadai ki ke yi, gaba daya kasar za ki ce, a gaskiya wannan yarinya ba karamar sa`a gare ta ba a rayuwa sai kawai ki shirya ki je can Jos din ki ji yadda aka tsayar da ranar bikin waccan Hadizan sai a zo aje Bakori a samu a daidaita ayi masu biki rana daya kamar yadda shi Alhaji Mamud din ya bukata". Amina ta sadda kai tace, "Ai ni Malan tsakanina da zuri arku bani da kalmar godiya sai addu`ar fatan alhairi kawai, duk abinda za ai ma yaro sanadiyar arziki sun yi ma wannan yarinya ko `ya`yan da muka haifa da kai iyakar dai zumunci kenan." Ya ce, "Wannan duk ba wanı abu bane 40 mu dai fatanmu Allah ya daidaita Dije da wannan bawan Allah yasa itace sanadiyar zaman lafiyar gidansa domin na san aminin Rilwan ne ba tun yau ba." Amina bata tsaida ranar tafiya Jos ba tana ta yan kintse-kin tsenta a tsanake, yayin da hankalin yallabai Mamud ya jirkita ya dimauce bai ganin kyan wata diya mace face Hadiza a kullun yana bisa hanyar Kaduna yana kuma dankara mata iyayen kudi ita kam Hadiza tana adanawa a banki. Suna kammala hidimar kasa shugabansu na wajen aiki yayi mata alkawarin sun dauke ta aiki, saboda haka wannan ya fi komi farinciki wajen Hadiza domin tana tunanin yadda zarmanta zai kasance a Malunfashi kafin ta sami aiki domin tana ganin bata iya zama Jos babu Hadizan Jos kuma Mama Binta na so ta auri Mamud. Suna isa Jos komi ya kacame na shirye-shiryen bikin Hadizan Jos da Dr. Sani inda zai aje ta Abuja wato inda ya ke zaune kenan da kanfaninsa. Kusan a wannan lokacin kowa ya azazzalawa `yar Bakori ganin ta sami miji mai son ta. Yaya Amina ta iso, sai da ta turke Hadiza a gaban Mama Binta sannan ta ji wannan danyen labari wai bata son Mamud, kafin Hadiza ta ankara har idanun Amina sun juye tamkar an watsa mata barkono tace, "Tafdijam! Ai ba ki isa ba dan ubanki, tun yaushe na ke jin labari kina samun samari kina basarwa, to wannan kam tunda ya nuna kauna babu abinda zai sa a fasa." Hadiza ta bata rai ta dan muskuta tace, "Ni wallahi Yaya bana aurensa, tunda na ce bana iya rayuwar iyalan sa, ban ga dalilin da zai sa ku tada hankalinku ba." Amina ta harzuka zuciya ta zo mata wuya, ta ce, "To sai ki fada mana wanda kike so tunda mu ba mu isa ba." Tace, "Ni a yanzu ba ni da kowa a dai kara min lokaci." Hadizan Jos na zaune can gefe daya ta yi tagumi tana jin badakalar da ke faruwa akan Hadizan Bakori, ita kanta ta dan tsani Hadizan Bakori anan domin bata son taurin kai iri wannan, tunda tace babu tsana tsakaninta da Mamud me zai hana ta hakura da yadda iyayen ta ke so? 41 ita kuma wadda ake abun don kanta ta kakure ta na, ts shakar kuka. Mama Binta tace, `A gaskiya Hadiza ki baiwa kan ki shawara wannan ba zancen bata rai ba ne har ayi kuka, zancen gaskiya ne randa ka rasa mai fada maka gaskiya ka shiga uku, ki jure kawai ayi maku bikinku hankulanmu su kwanta, ba kya tausayin tsohonki? Wallahi Mamud yace da suka je gaishe shi kamar ya hade su don murna, amma kuma ace duk ke kadai ki watsa farin cikin kowa?' Wasu hawayen suka taho a guje da ta ji an anbato Malan Kado, tasa hannu ta goge ta murje hancinta ta ce, *Insha Allah zan yi masa bayani zai fahinceni." Amina ta ja tsaki tace, "Zancen banza me ke gareki wanda za ki fadi mashi, to ko wannan dan iskan yaro Yusufa ki ke zaman jira?" Hadiza ta yi war da idanu bakinta a bude, itama `yar Jos ta bude bakin suna mamakin maganar Yaya Amina. Yaya Amina ta cigaba da cewa, "Idan shi kike kunata kina da wahala, domin uwar da ta haifeshi ma ance yanzu kuka take da shi, sa
🏠