ddu'a.
A babban bankin C.B.N Rilwan ya samarwa Hadiza
da Hadiza aikin hidimar kasa na Kaduna. Suka zauna a
gidan Baba Garba cikin Anguwan Sarki shi ma Baba Garba
kani ne wajen su Rilwan yana aiki a matatar mai.
Bai fi wata uku ba kacal su kammala hidimar kasa a
wani lokaci sun je Jos hutun kwana uku da yamma Mama
Binta ta duba firij din ta na kicin ta ga bata da kayan salad
sai ta kwallawa su Hadiza kira. Hadizan Bakori ce ta fito a
guje tace,`Ga ni mama'. Mama tace, `Ina daya Hadizan?"
Yar Bakori tace, "Tana wanka, kin san Dr.Sani ya yi waya
daga Legos yace ga shi nan zuwa". Mama ta yi murmushi
tace, "Shiririta ni dauki makullin karamar mota ki yi sauri ki
sawo min kayan salad da alayyahu don Allah maza ki kawo min."
Hadizan Bakori ta fito sanye cikin kyakyawar shiga
ta yane kanta da wani gyale na zamani ta fito tana sulbi ta
nufi inda ake aje motoci, ta shiga ta tayas. Maigadi ya dage
mata koía ta fita da sauri.
Daga can gefe su Rilwan ne da abokansa suke hira,
a cikinsu har da babban bako Mai Martaba Hakimin wani
gari ne a can cikin jihar Katsina, shi ma kusa ne a gwamnatin tarayya amma samun sarauta da tara dinbin dukiya ya sa
37
ya yi sallama da siki ya rungumi sarautar da yan kanfanonin
da ya kafa. Wannan mutun shine yallabai Mamud, idonsa
fes akan Hadizan Bakori, ya tambayi Rilwan "shin wai ina
ku ka sami waccan yarinyar ne dazun na ganta ta gitta ita
da Hadizan gidan nan yanzu kuma ta fita da motar gidan?"
Rilwan yayi dariya ya bashi cikakken bayanin Hadiza,
yallaba Mamud yace, `Idan haka ne ko ina son ta zan ko
aure ta'. Rilwan ya kara dariya yace, "Sarkin hadama kana
nufin ka yi mata uku?" Yace, "shi ne me, ba basarake na ke
ba?"
Rilwan yace "Na yi zaton sarautar`yan boko a ke".
Mamud yace, " Yan bokon yanzuai ba sa anfani da
turancinsu wajen tara mata, sai`yan bokon da waton na
zamanin 1960". Rilwan yace, "To ni sai na ce Allah ya
bada sa'a ai ba na hana yallabai diya ta ba."
Can muna iya kiran lokacin karfe tara saura`yan
mintoci na dare dn karamin yaron Mama Binta yayi sallama
dakin su Hadiza yace, "Anti Hadiza Baba yace ki yanka
lemo ki kai falon baki". Ta mike da sauri ta yi abinda aka
umurceta.
Ta yi sallama ta shiga sai Yallabai Mamud kadai zaune
a falon, zata aje a bisa tebir yace "Kawo min nan gaba na,
ke ce Hadizan Bakori?" Ta dube shi a tsakiyar fuskarsa
tace, "E ni ce, a kira Hadizan Jos ne?" Ya kyaikyale da
dariya yace "Amma fa wannan lakani na ku da ban sha'awa
ya ke, sai dai Hadizan Bakori na ke son magana da ita".
Hadiza tace, To' ta nemi waje ta zauna.
Ya shiga tambayarta labarin yadda a kai ta zo jami`ar
Jos ta bashi bayani, sannan ya nemi jin labarin iyayenta
duk ta gaya masa, ya dan fito daga cikin kujerar ya tsura
mata ido yace, "Hadiza a yau na ganki na kuma yaba da
abinda na gani don haka ina gayyatanki da ki zama ivalina?"
Tamkar ruwa ya ci Hadiza ita ko me yasa rayuwa ke latsa ta
ne irin haka? Ita dai ta san ba kowa bace illa talaka likis
wadda bata a bakin komi gidan. Ubanta na son ta yi aure
fiye da zaton dan adam ko don ta farantawa Baba Kado rai
to amma me yasa take cin karo da mazan da bata so?
38
Tabbas babu abin ki wajen Mamud sai dai kawai ba irin
rayuwar da ta ke son samu bane a gidansa domin tuni ta
sha jin labarin gidan sa wajen Hadizan Jos.
Gidan Mamud babu abinda bai mallakawa wa` annan
mata na shi guda biyu ba, to amma babu zaman lafiya;
bala'in kishi suke yi tamkar su halaka junansu, ashahadu a
wuyansu an ce akwai dan amaryar da ya rasu ana kyautata
zaton uwargidan ta kasheshi don kada ya girma ya gaji
Mamud.
Yallabai yace, "Ba ki ban amsa ba Hadiza". Ta dawo
daga tunanin rayuwar gidansa ta ce, "Ka ba ni lokaci zan yi
tunani". Yace, "Ban dai yi maki ba kenan, kila na yi ma ki
tsufa?" Ta yi mai wal da 'yan kyawawan hakoranta ta сe,
"Lah wallahi babu zancen tsufa, ka san komi yana son a yi
nazari". Sai ya ji Hadiza ta kara shiga mai cikin rai, wannan
fara'ar da ta yi tabbas tana son shi sai ya ce ya amince.
Mama Binta tace "To Hadizan Bakori ya kamata dai
ki kwantarwa da mahaifinki rai inda duk ake son samun
miji yallabai Mamud ya kai miji sai dai kuma idan akwai
wani kudirin a ranki". Hadiza ta ce, "A gaskiya Mama ina
ni, ina fitinar matansa wallahi ban iya wa". Mama Binta ta
'sha mur tace, "Kina nufin shi ma watsa maganar ta shi za
ki yi? Karyarki ta sha karya in don maganar matansa na yi
mai wannan maganar ya ce ba gida daya zai aje ku ba, su
suna can inda suke a Katsina amma fa ba za ki yi aiki ba."
Yar Bakori ta daure rai ta shiga tunanin abinda zai je
ya komo a kanta, ita kan gaskiya ba za ta cuci kanta ba ta
auri gidan da ake bala'i kiri-kiri, yadda duk Mama Binta ta uya Hadiza ta ki amincewa, domin a san ran Mama Binta
ayi bikinsu gaba daya nan da wata uku idan sun kammala hidimar kasa.
Kashegarin da su Hadiza za su koma Kaduna tare da
Mamud a kai tafiyar motar su Mamud na gaba ta su Hadiza
na baya har su ka isa gidan Baba Garba.
Mamud ya kebe Hadizan Bakori y