NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 15 of 26

a lokaci guda ya je ya yi maki irin wannan cin mutuncin a gaban Inna Tambai mata mai mutunci da ita? Wai ko dai tabin hankali ya same shi iyayen ba su gane ba? Amma ni yanzu ina ganin mai kyau kamar ki a fadin jami`armu? Kin san Allah wani lokaci har tunani na ke yi na ce ko mutumin kauye zan aura domin ni sai na ga mutanen kauye kun fi mu kyau". Hadizan Bakori ta cе, 341 "Ina son ki ko don seli ki mai suman." Hadizan Jos tace Ya Ubangiji Allah ka hada ni da wannan Yusuf sai na rama maki wulakancin da ya yi maki, shi din me? Don Allah ba ki ji labarin inda ya ke yanzu ni ko ne mabuta masa na zage shi tas, wai ke don Allah wace irin zuciya gareki da har kika kyale shi, ai idan nice har gaban Gwoggo Halima zan same shi na wanke shi tas." Hadizan Bakori ta ce, "Wallahi ban kara jin labarinsa ba. Tun tamba yar da na yi ma Babana a hutuna na farko da na ba ki labari amma ran da mu ka je Bakori na hada ki da inna Tambai ki sha labarin inda ya ke clomin ta sani sai dai ina tabbatar maki idan don ni za ki yi nnasa tsiya don Allah ki bari domin idan na yi haka ban gode wa Allah kenan ba a bisa baiwar da ya yi min, lalle na san na shiga fitinu a dalilin shakuwa da kaunar da na ke ma Yusuf, amma kuma canjin rayiwar da na rinka samu a dalilin rashin aurensa sai ta zamar min kwanciyar hankali da daukakar rayuwa." "A gaskiya na san na so Yusuf amma na san ina kara son shi ne saboda zan bar azabar gidanmu na sami yancin kaina to irin rayuwar da na samu a gidan mahaifiyata da ci gaban makaranta ta sai suka gusar min da Yusuf a raina, sai kuma Allah ya kara yi min wata daukaka ta basirata wadda a dalilin ta na zo wannan gida, kin ga na sami ci gaban rayiwa, domin rayuwa ma a wannan gida makaranta ce, yanzu dubi ko na'urorin da ke kicin idan ba dalilinBaba Isa ba yaushe zan zo nan har na san su? Ki tuna fa ki ga yadda gidan mahaifina yake to yau y shi na zo gidan da zan kwaba kek ko burodi cikin minti goma a injin sannan na gasa cikin yan mintoci, da sauran girke-girke, haka nan yau ni Hadiza Dije na iya tuka mota bayan mahaifina keke gare shi? Kin san Allah ba na jin haushin Yusuf da rashin aurena domin ko da zan sami irin wannan rayuwar a gidan sa karshenta zan sha wuya can gaba, domin na lura namijin zara ne. Kin ga ran da ya sami dadin raina min wayau zai yi yace zai auro `yar duniya kamar shi su ci duniya yace ni yar kauye ce, domin sai yanzu na ke tsanar tsarin rayuwarsa cika son komi na `yan duniya ni kuma a lokacin rashin ye 35 wayau sai na rinka biye masa wai don kada ya kira ni bakauya. Suka yi shiru na dan lokaci can Hadizan Jos tace, "Kai! Ni kam Allah ya hada ni da Yusuf na fada masa magana domin wanda Allah ya ba mata mai hali irin na ki ya gama mallakar komi a rayuwa amma don tsageranci irin nasa zai ma Baba Kado haka, a gaskiya Hadiza akwai yarinyar da Babanta ke son ta kamar ki?" Hadizan Bakori ta kyalkyale da dariya tace,`Kin ji sokoncin naki ba, ba ga ki ba da Baba Rilwan ba?" "Yar Jos tace, "Wai ba kya jin yadda ake kwafdata da zagi wani lokacin?" Hadiza tace, "Ai ba kya ji ne kamar wata yar bebi, kyan ki Dr. Sani ya nemi bulala, idan mun kai mashi ke". Ta kyaikyale da dariya tace "Sai ya nemi bulala biyu kenan." * Abba Abba ya hakura ya sakawa Hadiza Abdulkadir ko a ranar da suke sallamar ban kwana, wato a rannan zai koma Bauchi mahaifarsa ya kammala jami'ar Jos. Suna tsaye ya dafe hannunsa jikin dalbejiya yayin da ita kuma Hadizan ta mikar da dogon hannunta tana tsinko ganyen dalbejiya, ya yi gyaran murya, yace, "Hadiza na ji sakonki wajen Hadizan Jos amma ni ban dangana ba ina tabbatas maki wata ran sai kin yi da nasanin kin amincewa da ni, amma dai ga adireshina nan da nambar talfon din gidanmu ina saurarenki ako dayaushe, zan yi zaman jiranki ko nan da shekara nawa ne, har zuwa ranar da ki ka janye sarautar haranta ta soyayya a tsakaninmu". Ta yi murmushi tace, "Ni kam na fi daukar kauna ta yanuwantaka da mahimmanci fiye da kaunar soyayya wadda ke karewa balle a zamanin nan namu mai cike da rudin kwadayi." Abba yace, "Kwadayi kamar yaya?" Tace "E mana yanzu za ka kulla soyayya da mutun dan lokaci kadan zaı iya barinka a dalilin ya ga wadda ta fi ka, kyau, ko ta fi ka kudi da dai sauransu duk me ke kawo haka in ba kwadai ba? Abba yace, "Haka ne amma ni ina daukar wannen 36 dama can ba soyayya bace ta gaskiya ta riya ce, amma kuma wani lokacin skwai fa kaddara". KASHI NA TARA A kullun dai su Hadiza suka ziyarci mahaifinta a Bakori ba shi da wata magana irin ta, "Wai Dije yaushe za ai aure ner" Ta kance, "Wallahi Baba da zarar na sami mijin zan kawo maka shi da kai na ni kai na ina son na yi auren saboda danmiwar da na lura kana nunawa haka nan kuma ganin yanzu ni ce babba a gidan nan". To irin wa'annan kalaman na Dije ta samu ta danne zuciyar Malan Kado daga zancen aurenta sai ya rinka tausaya mata yana ganin kamar da gaske bata sami mijin ba ne, ya yi alkawari a ransa zai daina damunta da magana ya shiga yawaita yi mata a
🏠