ย  ย  NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 14 of 26

auka a cikin makarantar nan ganin ba ku kula kowa sai ni. To a gaskiya ni aski ya zo gaban goshi domin`yan kwanaki ya rage min na kammala karatuna kamar yadda kika sani, to amma wani abu ke damu na sai dai an hana ni na amayas da shi". Ya yi siru anan. Hadizan Jos tace, "Waye ya hana ka ka amayas?" Ya ce "Wanda abin ya shafa"; Tace, "Wa ke nan?" Yace, "ะ gaskiya son Hadizan Bakori na ke, so kuma irin na wanda zai tabbata ga aure amma ta ki ba ni hanya na fada mata shi ne na ke son ki taimaka min." Ta yi murmushi tace, "Haba kamar ba namiji ba, me zai hana ka nunawa Hadiza bukatarka a zahiri ai ina ganin kun yi shakuwar da ba za ka iya rufe mata komi ba". Yace, "Haka ne Hadiza, wallahi wayon tsiya ne da ita yadda duk na so na sako batun soyayya sai ta ki kamar wadda soyayya ta wahalad!" `Yar Jos ta yi dariya tace, "Shirmen Hadiza ne kawai wadda bata da lokacin samari yaushe har soyayya zata wahtalad, ka ban ni da ita zan yi mata magana komi kenan zan sanar da kai."`Yar Jos bata nemi yi ma `yar Bakori zancen Abba Abba ba sai da daddare bayan sun kulle kofa sun yi shirin bacci Hadizan Jos ta ki kashe lantarki, saiyar Bakori ta juyo ta dube ta tace, "Yaya ki ka zauna ba ki kashe mana, wuta ba, na yi zaton mun kare hirar yau 32 bacci za mu yi?"`Yar Jos tace, "Haka ne yau magana ce gare ni ina son mu yi zancen aure, ba kullun maganar karatu ba sai kace da karatu zamu lahira". Hadizan Bakori ta kyalkyale da dariya ta ce "Baki da lafiva Hadiza, da wa za ki maganar auren? Ba dai ni ba mara miji Ki bari in kin sami`yar uwarki mai samari sai ku yi".` Yar Jos tace, "Insha Allah ba kya kara ganina da saurayi ko ki ji na dauki wayar wani sai ta wanda zan aura, a gaskiya na yanke shawara na tsaida miji".`Yar Bakori tace, "Wai Dr. Sani?" Ta ce, "Insha Allah shi zan auraโ€. Yar Bakori tace, Yanzu me sunan ba kya tsoron matarsa?" `Yar Jos tace "Ban ga abin tsoro ba wajen mace `yar uwata, auren mai mata ba wani abu ba ne illa mu `yan zamani da mu ke neman mu canfa abun, ki tuna fa addininnu da al'adarmu sun amince mana da aje mace hudu matsawar zaka iya baiwa kowacce hakkinta. To sanin kan ki ne Dr. Sani a shirye ya ke ya mallaka min gidana kaman yadda zai mallakawa uwargidansa na ta, to sai kuma me? Tana aikin asibiti yayin da shi kuma ya ke aiki a kamfaninsa na kashin kan shi, ni ma yace a kanfaninsa zan yi aiki idan na gama. karatu." Hadizan Bakori ta yi ajiyar zuciya tace, "Ke shikenan kun gama tsara rayiwarku?" Tace, "E saura ta ki, tunda kina tsoron kishiya ga saurayi ya aiko ni gareki". `Yar Bakori tace, `Wanene?' Hadiza tace, `Abba Abba'. Hadizan Bakori ta yi dariya tace, "Ya sha gas, wai me ke damun Abba ne? Mutumin da na dauka tamkar dan uwana shi ne zai wani bullo da zancen so? To a gaskiya ban amshi tayinsa ba". Yar Jos tace, "idan ki ka yi haka ba ki kyauta min ba haka nan ba ki kyauta ma Abba ba". Hadiza tace, "To sai na cuce shi don na gyara masa rai? Kin san Allah mai sunan kada ya wahalad domin ni kam ban taba jin daidai da rana daya ba ina yi masa irin sha'awar nan ta saurayi da budurwa ko har na kai ga sha'awar ace yau ga shi a matsayin mijina, a kullun mu ke tare da shi na kan tsinci kai na ina tare da wani haramiyana, wato kaman kanih mahaifina ko yayana wanda mu ke uwa daya ko uba daya to ki kamanta kan ki a 33 irin haka, yaya za ai har soyayya ta aure ta shiga tsakaninku? Bana jin zan iya soyayya da Abba don haka kice ya yi hakuri mu kasance a matsayin `yan uwa ko a ina nake kuma ko wa na aura Insha Allah zai zama na daya abokin shawarata." Hadizan Jos ta yi shiru tana tunani, tabbas `yar Bakori ta yanke hukunci game da Abba babu saurany wani sa rai domin tace kamar haramiyarta take ganinsa, `yar Jos a hankali tace, `Na tambayeki tsakani ga Allah?" tace, "Insha Allah na yi alkawarin gaya maki gaskiya." Tace, "Wai akwai wanda kuka yi alkawarin aure da shi ne a kauyenku Bakori?" Itama ta yi dariya tace, "Ke ko meyasa ki kai min wannan tambayan?"`Yar Jos tace, "To na ga kowa yace yana son ki ba kya yadda ya-zo gida ma sai ki bata maganar, sannan na lura kin faye zurfin ciki shi ne na yi tunani kila kina da wanda ki ke so, ba ku gama shirye-shiryenku bane." Hadiza tace, "Bana son na karyata ki amma ke saboda Allah duk wanda ke nuna suna so na kin ga ya dace na aure su?" 'Yar Jos tace, "Me zai hana su ba maza bane?" Hadiza tace, "To shikenan na amince da ke anan mu bar wannan labarin amma bari na ba ki tarihin aurena da wani dan kauye dan uwana." Hadizan Bakori ta warware mayar Jos tarihin rayiwarta har zuwa ranar da ta dawo gidansu. Hadiza `yar Jos ta baro gadonta ta dawo gadon Hadizan Bakori tace, "yanzu Hadiza wa'annan matan da mu ke zuwa sune suke gana maki irin wannan wahalad? Ta amsa "Wallahi kuwa yadda ki ka gan su a raine din nan sai mugun abu da bakin wulakanci iri-iri." `Yar Jos tace, "kai lalle akwai maza `yan garari`yan iska a duniya yanzu shi wannan Yusuf duk irin kaunar da ya rinka nuna maki amma shi ne
๐Ÿ