NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 13 of 26

fadi jarabawar nan!" Hadiza tacе, "Haba don Allah ki rika addu`a Insha Allah za ki ci ne". Hadizan Jos tace "Masifar Baba kadai ma ta ishe ni". Ta ce "Babu komi za'ai nasara." Suka saki juna, Hadizan Jos ta murda kofa zata shiga ta juyo suka kara dubar juna ita da 'yar Bakori sukai murmushi tare da dagawa juna hannu, Hadizan Bakori ta ce, "Ina nan ina maki addu`a." Minti uku, minti biyar, har zuwa minti ashirin Hadizan 29 Jos bata fito ba, sai 'yar Bakori ta fara tsorata, tayi uagumi har tana hardewa wajen adclu'a, zuwa can ta fito ta fada kan Hadizan Bakori tana fadin taya ni murna Hadizaı, tare da mika mata takardar. Hadiza tana dubawa tare da cewa "Eye! Hadizan ba 7 Credit. Credit a lissafi, Credit a turan,ci ai kuma jarabawa ta hadu Allah ya maida mu clanshinki." Baba Rilwan ya yaba yace, "To abinda za`a yi gobe sai ku je Malunfashi ku amso ta Hadiza idan ta ci ku zo na shirya maku gagarimin bikin taya murna." Hadizan Bakori gabanta ya fadi ras wato tana cikin hatsari kenan tace, "Baba idan ban ci ba fa?" Yace, "sai ki sake daukar wata jarabawar har sai kin ci." Ai ko rannan 'yan Bakori ba ai bacci ba kwana ta yi cikin zullumi. Sun zuba ado na atanpa iri daya wadda Mama Binta ta dinka masu. Suna isa Malunfashi Hadizan Bakori tace a wuce zuwa makaranta kafin aje gida, Hadizan Jos tace, "Haba ba kya bari mu je gida ko ruwa mu sha?" `Yar Bakori ta galla mata harara tace, "Tafdjam! Ko kin san jiya kvvanan zullumi na yi, shi ne ba kya tausaya min? Ai duk na kosa na ga abinda na shuka ko hankalina ya natsu." Suna isa suka ci karo da malaminsu yace, "Ina taya ki murna Dije domin gaba daya jihar Katsina ke ce ki ka zo na daya a kyaun sakamakon jarabawa". Hadiza ta dubi Hadizarı Jos ta kwantar da kanta bisa kafadar `yar Jos tace "Na gode Allah da ya fid da ni wannan shedarar siradin." Lokacin da suke bude mota suna fita a kofar gidan Malan Isa, kowanne Hadiza ta koma mashi kamar bakuwa don tsarin kyau a cikin gida ma Yaya Amina na ta wangale baki ganin yadda diyarta ta canza wata uku kacal. Abinci kawai suka ci sukace zasu wuce Baba Rilwan yace kada su kwana kuma suna son tsayawa Bakori su gaisa da Baba Kado. Cikin kwana bakwai aka gama shirye-shiryen karatun su Hadiza suka kama karatu a jami'ar Jos; Hadizan Jos na 30 karanta fannim Public Admin,yayin da Hadizan Bakori ke karanta fannin Account. A farkon shekarar karatunsu direba ke kai su daga bisani Mama Binta da kanta ta rinka koya masu motar har suka kware suka rinka kai kan su makaranta, idan an tashi su dawo gida. Yadda duk ake son diya mace ta kile to Hadizan Bakori ta kai karshen kilewa, an goge an cakare har an koma bayan cakarewar an cake, abin nufi anan Hadiza ta zama macen shiga gaban kowacce irin kasaitattar mota ko kuma muce ta shiga dan tsuntsun nasara mai shawagi. Hadiza Abdulkadir sanbaleliyar mace, doguwa mai kyan tsayi, akwai ta da shafaffar mara, cikin ta ya dame daf don haka ya fid do da tudun mazaunanta a sarari damewar cikinta ya kara sawa kirar nononta su fito das. Abinda ke jan'ra'ayin jama'a da nacin kallon fuskar hadiza Bakori shi ne, `yan kananan hakora masu kyalli da daukar hankali yayin da suka yi daidai da `yan kananan labbanta, labban da akodayaushe suke walkiya. Hancin Hadiza dan guntu ne ya yi tsari da`yan kumatunta, 'yan gwibi-gwibi idanuwan Hadiza ko sune abin sha'awa a irin kallon Hadiza tamkar an watsa taurari don walkiya, mawuyaci ne Hadiza ta dubi mutun da kwayar idonta bata saukar maka da sha'awa ba, domin akwai baiwar kwarjini na musamman da Allah ya yi ma Hadiza cikin taurarin lelonta wannan kenan, akwai ta, da sambala-sambalan yatsu don haka ne ma a kullun idan tana latsa lambonin konfuta Hadizan Jos ta kan ce mata "kai Hadiza Allah ya yi maki baiwar yatsu na gari tamkar an halitta maki su ne don ki rinka watsa su a bisa konfuta." A cikin makarantarsu, Hadizan Bakori bata da kawa ko saurayi baya ga Hadizan Jos sai ko Abba Abba. Shi ko Abba Abba irin karatu daya suke yi da Hadizan Bakori sai dai ya na gabanta da shekara daya, saboda haka, a kullun suna tare suna bitar karatunsu. Ita kam Hadiza a yadda ta dauki Abba Abba abokinta, wani mutun mai natsuwa wanda ya san abinda ya kawo 31 shi amma shi abinda ke zuciyar Abba Abba son Hadizan Bakori yakes, so kuma wanda ya ke kyautata zaton zai kai su ga aure, domin shi a duniya bai ga abinda Hadiza zata yi ba bai birge shi ba, komi na jikinta sha'awa ya ke ba shi, ya yi kokarin ya furta ma Hadizan amma ta ki bashi fuskar hakan, har lokacin fitar shi ta zo. A wata rana yaje ajin su Hadizan Jos ya nemı ganinta, tace, "Yaya dai lafiya ko Abba?" Yace, "Babu wani abu Hadiza ina son mu yi wata 'yar magana ne da ke". Tace "To mu je mu zauna". Suka jera suna tafiya har zuwa wajen da aka tanada don dalibai idan suna son zama su huta, ya dan jima yana mata `yan kame-kame daga karshe dai ya yane rigar kunya yace, "`Yar Jos tsakanina da ku yanzu mun zama tamkar `yan uwa domin haka ma wasu ke d
🏠