Allah, ina laihin
wanda ta yi? Allah ya anfana ya isa haka, ki dubi Dije
yadda ta koma kusan kansu daya fa da Amina! Sannan ace
wai taje jama'a kamar da namiji."
Amina tace, "Malan ba ni aron hankalinka nan, ka
taba jin inda aka ce aure ya hana neman ilmi ko ilmi ya
hana aure? Wallahi tana cikin makarantar idan Allah ya
kawo mijin na kirki sai ayi auren, amma yanzu na hanga
ban ga wani tsayayye ba, Allah kadai ya san lokacin auren
mutun, saboda haka tunda Ubangiji ya baiwa wannan diya
taka basirą ka barta ta nemi ilminta ba' a san iyakar al'umar
da za su anfana də ita ba, wallahi da yau bata san komi ba
su Rilwanu ba za su matsa maka ba akan son ta ci gaba da
karatu, mun yi maka alkawari a yau ta sami miji za'a daura
mata aure. Ka yi tunani ana son taimaka mata ne a bisa
baiwar da Allah ya yi mata".
Malan yayí jigum, can yace, "Haka ne Amina, yadda
na ke jin zafin Dije kema na san haka kike jin zafin ta, na
tabbata ba za ki so ta da halaka ba, tunda kin ga akwai
alhari idan mun bar ta ta je neman ilmin shikenan a dai
shaidawa Rilwan din wannan yarinya amana ce fa a
hannunsu". Amina ta yi dariya tace, "Dan wannan Malan
kada ka ji komi ka rinka sawa ranka tamkara gaban ka take
ko a gabana, kar kaji komi wallahi."
Dije da mahaifiyarta Amina suka koma Malunfashi
cike da murna da zakwadin an amince masu zuwa jami'a
don haka ko da Dije ta kare hutunta ta koma makaranta bata tsaya bata lokacin ta ba ta kama karatu fiye da yadda
ta saba.
A ranar da suka aje biro wato sun gama jarabawar karshe a makarantan 'yan mata ta garin Malunfashi a rannan Dije bata kara kwana ba sai dakin Yaya Amina.
Wanshekare Amina ta ce ta shirya ta je ta yo sallama
da mahaifinta Malan Kado domin a yadda Rilwan ya ce ran
asabat zai zo ya tafi da ita za su fara kwas din konfuta na
07
wata uku kafin jarabawarsu ta fito. Dadi ya kara lullube
Dije.
Kwananta daya a Bakori ta dawo Malunfashi ta shiga
shirin tafiya Jos.
Mahaifiyarta Amina ta ce, "Ina so ki kara natsuwa
bisa wadda ke gare ki, wannan gida da za ki wata rayiwa
ce ba irin ta mu ba, rayuwa ce irin wadda sun mallaki komi
na rayuwa, ta fannin abin duniya to kada ki ga an sakar
maki komi, ki nemi wuce gona da iri. Ki iya da talaucinki
haka nan ki tuna karatu za ki yi ki dawo wajenmu masu
talauci, ki kama kan ki ban da kananan maganganu, sánnah
ki yarda da Allah a komi na al'amarinki, yarda da Allah zai
kai ki matsayin da ba ki zata ba, ki mallaki abinda ba ki
taba mafarkin mallaka ba.
KASHI NA TAKWAS
Hadiza Abdulkadir ta bude sabon babin rayuwa mai
cike da al'ajabi a birnin Jos.
Gidan Rilwan gida ne irin na`yan bokon zamani duk
abin jin dadin dan adam ya tanadar masu shi a gidan. Lokacin
da Dije ta isa gidan tun a harabar gidan gaban ta ya rinka
faduwa bal-bal, suna shiga falon hatta kafarta rawa take,
ta nemi kasa bisa kafet ta yi zaune. Rilwan yace, "ki zauna
bisa kujera mana". Amma ina! tamkar Dije bata ji shi ba ita
dai gabanta kawai ke faduwa, bata taba ganin gida irin
wannan ba.
Dakunan bacci a bisa bene, don haka Rilwan ya haye
zuwa dakin baccinsa yayin da iyalin gidan su ka san dawo
war sa nan da nan suka zo falo gaida Dije.
Babbar 'yar itace Hadiza ta mikawa Dije hannu tace,
"Sannu da zuwa ni sunana Hadiza Rilwan". Dije ta ce "nima
suna na Dije Kado". Hadiza ta yi dariya tace "sunan mu
daya kenan" Mama Binta itama ta iso cike da fara'a tacе,
"A'a sunanki Hadiza kinji daga yau kada ki sake kiran kan
ki Dije Kado sai dai Hadiza Abdulkadir shi ne ainihin
sunanki."
28
Hadiza Abdulkadir dai har yanzu tsokar cinyoyinta
rawa suke yi a firgice ta ke, har Hadiza ta dauko jakarta ta
ce ta zo su je dakinta inda zai zama dakinsu su biyu.
Ganin yadda aka kayatar masu da dakin ya kara bugun
kirjin Hadiza, komi ya kara rikice mata a zamanin da Hadiza
ta shigar da Dije kewaye don ta yi wanka ta rasa yadda
zata bullowa wajen wanka balle inda zata tsugunna don
fitsari dole ta nemi alfarmar Hadiza don ta koyar da ita.
To haka Hadiza ta rinka fuskantar irin wa'annan bokin
al'ammura amma cikin kwana bakwai ta fahinci komi.
Suka fara zuwa kos din konfuta na wata uku, inda
anan kuma kullun suka dawo gida Hadizan Bakori ke kara
yi ma Hadizan Jos bayani (yadda mama Binta ke kiransu
kenan har sauran jama'ar gida suka dauka yadda za'a rinka
banbanta su).
Daga Hadizan Bakorin har Hadizan Jos babu wadda
ta fito da sakamako mara kyau a lokacin da wata ukun su
ya cika a makarantar koyon konfuta, saboda haka ne ma
Baba Rilwan ya yi sha'awa ya sawo masu konfuta ya aje
cikin gidansa har suka rika koyar da kananan kannensu. A
daidai wannan lokacin ne kuma WAEC ta sakar masu
sakamakon jarabawarsu.
To Hadizan Jos mákarantar gwamnatin tarayya ta
Bauchi ta yi don haka Baba Rilwan ya bada mota suka tafi
Bauchi amso sakamakon jarabawa.
Lokacin da za su shiga ofishin malamin da sakamakon
ke hannunsa Hadizan Jos ta rike Hadizan Bakori gam-gam
tace, "Wallahi Hadiza gabana tamkar ana luguden uku, uku,
na tsorata kada fa na