NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 11 of 26

an da nan idanunta suka cika da kwalla amma ta jure tasa habar zaninta ta goge. Та се, "Ваba, ka yi hakuri. In Allah ya yarda daga yau zan fita daga zan cen Yusuf a zuciyata ba zan kara tunaninsa ba". Malan Kado bai ce komi ba baya ga ajiyar zuciya. Ta kwan ta a dakin Ankudi ta yi lamo hawaye suka ci gaba da zuba ta gefen kunnenta, har yanzu ita tana mamaki ne irin zantuttukan da Yusuf ya ke fada mata amma ace wai bai son ta? Wannan shi yafi daure mata kai. Da niyyar kwana bakwai Dije ta sauka garin Bakori amma bacin ran da zancen Yusuf ya saukar mata sai ta ji kwata-kwata ta tsani garin. Dan haka wanshekare da Malan Kado ya ce "Mata yaushe ne komawar ta ki Malunfashi?" ta ce;" Baba ai kwana uku zan yi" ya ce, "Na yi zaton za ki mana sati anan" ta ce "Baba akwai bikin diyar kanwar su Baba Isa da za'a yi a Katsina shi ne na kë son na bi yaya." Abu daya Dije ta cire wa Malan Kado kewar tsohuwar matarsa Amina wato da sassafe idan ta tashi ta yi sallah ta kan share gidan lungu-lungu har zuwa kewaye wato bandaki, 74 cikin kwana biyu gidan Malan Kado ya canza ya rinka tuna haka su kai rayiwa da Amina. Lokacin da zata koma Malan Kado yu sai mata kaji goma. Inna Tambai ta sai mata man gyada da kubewa, haka nan Malan lliyasu ya aiko mata da kayan miya da barkono, ta sauka gida da tsaraba rankatakab. KASHI NA BAKWAI Yaya Amina na gindin turmi tana kulkula daddawa zata zuba a miyar yayin da Dije ke share tsakargida inda yara suka ci abincin rana. Malan Rilwan ya yi sallama kai tsaye ya shigo gidan. Malan Rilwan kanine ga Malan Isa babban ma'aikaci ne a garin Jos, yana daya daga cikin wa'anda su ke taimakawa su Amina da Malan Isa. Matar Rilwan daya da 'ya'ya biyar itama Binta matar Rilwan, ma'aikaciyace to ire-iren su burge yaya Amina don haka take jin zafi ada da za'a hana Dije neman ilmi. Dije ta zube kasa ta gayas da Baba Rilwan ya rike kugu yana girgiza kai ya ce, "Yaya Amina ka da kice min mutuniyarmu ce wannan 'yar Bakori?" Amina cikin nuna alamin jin kunya ta dan yi murmushi tace "Kai Rilwanu baka da dama fa!" ya ce, "Wallahi da manaki, kin san ni rabo na da ganin ta, tunda ta zo hutun farko, kin ga min yarinya ta zama mace sosai, yanzu aji nawa take?" Dije ta yi dariya ta ce saura wata biyu mu gama, da mun koma jarabawar fita za mu yi. Rilwan ya ce, "Da kyau, haka ake so, ina fatan dai ana abin kirki." Anan ne fa zancen yayi ma Amina dadi domin ta san diyar ta mai kwazo ce, sai ta ce, "To Rilwanu ka tsaya ka shiga mana ka zauna" Ya shiga dakin Amina ya zauna bisa kujera. Amina ta dauko masa refot din Dije wanda duk take daukar na daya yana dubawa tare da yabawa, sai Dije ta yi sallama ta shigo dauke da tire mai kwalbar kunun zaki da kwalbar ruwa da kofi ya ce, "Yauwa Dije, kamar kin san ina tare da kishi, ina fata kin yi shirye-shiryen shiga jami`a 25 jami'a" Dije ta koma gefe guda ta tsugunna ta dan sadda kanta kasa, tana satar kallon Amina. Amina ta ce, "Jamia! Sakandiren ma da yaya aka yi? wannan uban nata an ya zai bari kenan? Rilwanu ya ce, "Haba Amina, ki yi kokari ki samu ya amince, insha Allah ni zan dauki nauyin komi nata, domin ni ma tawa Hadizar bana zata gama kin ga sai na hada su tare" Dije ta ce, "Don Allah yaya ki tambayi Baba na nan gidan ya bar ki mu je ki ga Babana. Wallahi in ke ki kai mäi magana zai amince ya ban ni na wuce jami'a." Rilwan ya ce, "Gaskiya Hadiza ta fada zan yi ma Yaya Isa magana ya bar ku ku je Bakorin idan Malan Kadon ya amince, shi kenan sai ku aika min inshe Allah zan shirya komi sai su rinka zuwa jami'ar Jos ita da Hadiza ta waje na. Kin ga ma babu dalilin zama a makaranta, sai su zauna a gida kullun direba ya kai su." Malan isa yayi murna kwarai da shawarar Rilwan domin shi ma yana alfahari da basirar Dije. Suna isa Bekori grdan inna Tambai suka sauka, bayan sun ci abinci aka ce Dije ta je ta kira Babanta. Maian Kado ya ga Dije múrna ta lullube shi, tun zuwan da ta yi kwanan baya bata sake zuwa ba, sai dai idan ya matsu da tunaninta ya tura Tambaya ta dubo ta. Bayan sun gaisa tace, "Baba tare mu ke da Yaya Amina tana can gidan Gwoggo Tambaya tace ka je ku gaisa". Malan Kado ya rinka washe baki yana tunanin lalle kila Dije ta sami miji tunda har Amina ta zo da kan ta. Yadda Malan Kado ya ga Amina mulmul da ita sannan tana nan shar da ita sai shi ya ji duk ya muzanta a gaban ta, domin duk tsufa da rashin koshin lafiya sun bayyana a tare da shi. Suka gaisa cikin rashin saki jiki ko wanne na jin nauyin dan uwanse sei inna Tambai tace, "To Malan wannan tafiyar taka ca Amina ta yi maka". Kan sa a sunkuye yace, "To yaya aka yi?" Tambaya tace, "Sha'anin karatun Dija ne, shi ne Rilwan kanin Maian Isa da ke aiki a Jos yaca, ilen ka amince zai gama da tashi diyar su shiga jami`a. Malan Kado ya yi sauri ya dago kai ya dubi Amina 26 sosai, duba na hakika yace, "Ban amince ba, ni a zato na ma ca ni ke zancen auren Dije ya kawo Amina amma sai a zo min da wata magana ta keta haddin
🏠