NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 26

Inna tace, "Wani iko sai Allah! Yau ke ce ki ka canza kamanni haka? cikin dan kankanin lokaci. Kai Allah dai ya saka mana tsakaninmu da su Ankudi, duk sune suka tsangwameki suka hana ki yin abin kirki. Yaya su Amina da kannanki?" Dije ta ce "Lafiya lau. Ta ce, dan Aliah na ce tana gaisheki kuma wai kun kyauta tunda kika kai ni baki sake zuwa ta." Inna ta yi dariya ta ce, "Wallahi ba haka ba ne, kullun kina raina Dije, idan na yunkura zani sai ki ga wata hidimar ta danne ni; kuma, Malan ya sami kimanin wata uku yana fama da zazzabi akai-akai." Dije ta ce, "Allah sarki, ba mu sani ba, amma dai ya warware ko Gwoggo? ta ce "E ya wartsake sarai Dije." Sun sami fiye da awa daya suna hirar yaushe gama amma zuciyar Dije batai mata dadi ba, dòmin bata yi mata zancen da take son ji ba, wato ita dai ranta na ga Yusuf, abinda take so ta ji daga bakin Inna labarin Yusuf ko ya dawo akan batun aurenta domin ita abinda ta dasawa zuciyarta shi ne Yusuf yana son ta, illa wasu kyale-kyale na matan jami'a da suka debe masa hankali wanda ta san ita da an jure an yi bikinsu, zata jure da duk wani abu da zai rinka yi mata na wulakanci, har Ubangiji ya dawo mata da hankalin sa, to bata samu goyon baya ba. Ta dubi wata 'yar karamar agogo da ke bisa tebir ta ce, "Lah Gwoggo tara ta yi, bari na je mu yi hira da Baba, akwai wasu adduo'e da na ke son dauka a hannun sa." Inna Tambai ta ce, "To Dije in ce dai gobe anan zamu sha yinin mu? ta ce "E, isha Allah zan zo." Ta shiga shagon da ke kusa da anguwarsu ta sayi dan littafi da biro saboda daukar addu'a wajen Baba Kado. Ta yi sa'a Baba Kadon na tsaye suna sallama da amininsa malan lliya. Ta durkusa ta gayas da Malan lliyasu, ya сe, "Wato Dije idan da ban zo ba sai ki koma ba za ki je gidana mu gaisa ba ko?" ta ce, "Haba Baba wace ni? Aniyata saі gobe zan zo, ai ko ban yi niyyar zuwa ba na san babu yadda za'ai Baba ya amince min har na koma ban je na gaisheku ba. Malan Illiyasu ya yi dariya ya ca "To ne yadda 22 Ta yi mashi sai da safe ta shige cikin gida. Su Ankudi da yaransu ana zaune a falo suna hira ta yi sallama ta shiga ta nemi waje ta zauna. Bayan kamar minti goma Malan Kado ya shiga gidan ya wuce kai tsaye dakinsa yasa baki ya kwallawa Dije kira, ta isa dakinsa ya mika mata wata kullin leda baka mai kulle da nama balangu ya ce, ta je ta ci. To amma ita Dije sai ta hada kan kannanta suka zauna suka ci gaba daya. To ire-iren wannan zumudin na Malan Kado suke haddasa tsana tsakanin Dije da su Ankudi. Bata gama cin naman ba Malan Kado ya sake kwalla mata kira, ta kakkabe hannunta, ta dauki litafi ta nufi inda Malan ya ke zaune wato a bakin kofar dakinsa, ta nemi kujera yar tsugunne ta zauna ta gefensa, suka shiga hirar makaranta, tana bayyana masa irin matsalolin da ta fuskanta amma yanzu ta shawo kan komi. Tace "Baba akwai wasu addu'oe da ka sha fada min cewa idan mutun ya shiga cikin rudani ko damuwa ya rinka karanta su insha Allah zai shawo kan abinda ya dame shi" ya ce "E kwarai kuwa akwai su, kala-kala, sai ki shirya na rinka fada maki kina rubutawa." A kalla ya tsara mata addu'oe kamar kala biyar sannan ta tambaye shi na tsari da na aljanu suma duk ya gaya mata. A zuciyar Dije bata cika amincewa da kowa ba baya ga mahaifinta domin a ganinta shi kadai zai iya rufa mata asiri idan ta yi abin neman rufin sirri, tana son ta ji labarin Yusuf don haka take ganin wajen Babanta ya dace ta ji wannan labarin ba tare da an yi tseguminta ba. Ta cije ta daure ta sadda kai kasa nuna alamun jin kunya ta ce, "Baba" ya amsa amma kuma sai ta yi shiru ta kasa magana, ya dago kai ya dube ta ya ce, "Menene Dije?" ta ce "Wai Baba kuna samun labarin Yusuf?" Malan Kado ya yi shiru a bisa dukkan alamu Dije ta lura bai ji dadin tambayar da ta yi ba don haka sai ta yi dana sanin yin tambayar, Sun dauki lokaci babu wanda ya yi ko wani motsi mai karfi, ko wanne da abinda ya ke raya ma ransa zuwa can Malan Kado ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi yadda 23 na ga kin murje na dauka kin manta da żan cen Yusufa, ban yi zaton har yanzu kina tuna shi ba Dije. Ki vi hakuri ki manta da zancen Yusufa in Allah ya yaırda, za ki sami miiin da ki ke so tankar yadda ki ke son Yusufa, domin a yadda na sami labari, yanzu ko mahaifiyairsa kuka take akan yarinyar da ya ke nema da aure, gaba daya an ce ya canza rayuwarsa. Ki yi hakuri Dije da Yusufa kamar yadda na yi hakuri akan shi domin nayi iya kar kokar na yaron nan yaki dawo wa gare ki, har kudi na rabawa malamai ayi mana rokon Allah akan Yusufa amma kin ji shiru, saboda haka na dangana na bar wa Allah zabi yasa hakan tafi alhairi." Kan Dije na sunkuye a kasa, kunya da bakin ciki suka baibayeta, tabbas Yusuf dan sha'awa ne, hankalinta ya yi matukar tashi, shin me ma ya kai ta ta yi zancen Yusuf hakan ta kara tsananta tausayinmahhaifinta a ranta, wai har rokon Allah ys bayes da kudı ayi akan Yusuf bayan ta san yana yi da kan shi, mya ko alhakin mahaifinta ba zai kama Yusuf ba? N
🏠