NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 1 of 26

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KOWA YA RAIN TSAIWAR WATA 2 Bilkisu S. Ahmad Funtuwa KIYAYEWA Don Allah jama` a a rinka kula da abinda mu ke rubutawa mu na yi ne don mu kubutar da wanda ya shiga matsala ta fannin rayiwar aure, ba lalle sai ka tonawa kan ka asiri ba, idan ka yi anfani da shawarwarinmu sai ka ga Ubangiji ya warware komi. Kada a shagala da barin ibadar da ta hau kan mu a rinka kiyayewa. haka nan banda shiga kewaye da litattafanmu domin akwai sunan Allah a ciki. ni Daga Anti Bilki 1/Jan/2000 Rabin wannan labari da gaske ne, yayin da rabin ya zama gyaran marubuciyar ne, an bayas da shi ne don bada gudummuwa ga jama a don haka kada a tsani kowa a littafin sha anin rayiwa kenan. Idan ka ga wanda ya fito da halin da bai dace ba, ka taya shi addu a Allah ya shiryemu baki daya, amin, Ya shirya kudinsa tsab a kasan jakarsa sannan ya maida rigunansa saman kudi. Azuhur na yi ya shiga cikin gida wajen Goggo Halima sallama, tana rabon abinci ta ji maganar Yusuf, ta dago kai ta dube shi ya tsugunna ya yi mata sallama akan zai koma Zariya, ta juya ta ci gaba da rabon abincinta ta ce, "Allah ya kiyaye hanya". Daga can bakin kofa Hassi ta ce, "Yaya ba ka tsayawa ka ci abinci?" Gwoggo Halima ta daka mata tsawa ta ce, "Me ya shalleki! Cikinki, ko kin fi shi ido ne, ai yana ganin abincin ya ce zai tafi". Yusuf dai ya mike ya yi gaba abin sa. Ba Zariya ya nufa ba wannan lokacin Kano ya mike. A tun zamanin yana dan sakandire suke tare da wani shakikin abokinsa mai suna Amiru, suna son juna shi da Amiru kamar yadda aminai kwarai ke son junansu. To bayan sun gama sakandire fitowar Amiru dan masu hannu da shuni sai ya sami shiga jami'a BUK akan lokaci, shi ko Yusuf da ya kasance dan yaku bayi ne sai da aka yi kwadago sannan aka sami na hidimar makarantan, saboda haka yanzu akwai shekara daya tsakanin karatun Amiru da Yusuf, amma ako yaushe suna kokarin rubutawa juna wasika haka nan Amiru ya sha gayyatar Yusuf zuwa gidansu ya kwana biyu, don haka kowa ya san Yusuf a gidan su Amiru, ita ma Gwoggo Halima da zarar ta ga 'yar sabuwar kwancen shadda ta san Amiru ne ya ba shi, haka nan idan ta ga ya sami wasika da kudi a ciki ta san aiken Amiru ne. Ya isa gidan su Amiru kai tsaye ya zarce sashin da su Amıru su ke. Ya yi sa'a ya same shi, ya ci abinci yayi kat sannan ya yi s
🏠