An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KOWA YA RAINA TSAYUWAR
WATA
1
NA
BILKISU SALISU AHMAD
FUNTUA
KAREWA
Ya musulmi `yan uwana don Allah a rinka
kiyayewa a daina shiga kewaye da
litattafanmu domin akwai sunan ALLAH.
Saboda ba shi yiwuwa mu yi rubutu mu
kare mu kasa anbaton Allah a ciki.
Don Allah ina fata ana anfani da
gargadinmu na cewa a daina shagalta da
barin ibadar da ta hau kan mu, kada
karatun littafinmu ya shagaltar da kai daga
barin addininka, in ka yi haka kai da AIlah.
iv
Daga
Anti Bilki
25/11/99.
Malam Kado ne ke tafe ya na janye da kekensa, ga kuma
fatanya rataye a kafadunsa, a bisa dukkan alamu daga gona ya
fito. Can daga nesa amininsa Mallam lliyasu shi ma bisa nasa
keken ya kira Malam Kado in da ya ke cewa "A`aha Malan
Kado, kada dai ka ce har ka baro gonan kenan?" Malan Kado ya
waiwaya ya dubi Malan lliyasu ya dan matse fuska nuna alamun
damuwar ciwo sanna ya amsa, "Bar ni kawai lliyasu ciwon kai
ke neman kai ni kwance. Na rasa wane irin magani zan saya a
kemis ko kuma wane irin sauyu zan jika domin duk wanda na
sani na yi anfani da su har na kai makura".
lliyasu ya kafe kekensa ya rike kan ya zubawa Malan Kado
ido cikin damuwa, ya dan lunfasa sanman ya ce "Malan Kado
ban san ka da kafiya ba, sai akan ciwon kan nan, wai har sau
nawa zan gaya ma ne kaje asibiti su yi maka gwaje-gwaje don
su san abinda ke damunka? Ka ga anan za'a san maganin da ya
dace da irin ciwon ka, amma har yaushe za ka yi kwance a gida
kana shanye-shanyen maganik daban cuta daban".
Malam Kado ya ce "Ai ni tsoro na Allah tsoro na asibiti
yanzun nan sun labta maka cutar da tunda iyayena suka zo
duniya har su ka bar ta ba su taba jin ko sunanta ba amma ace
mutun na da ita, haka nan kuma ga wani tsire-tsire ace kada
mutun ya ci kaza kada yaci wancan, shin ina dalili? An taba
ganin abinci ya haddasa cuta? Sai dai ya yi sanadiyar warkewar
cutar, to ni kaji abunda ke hada ni da asibiti". Iliyasu ya yi dariya
yace, "Har yanzu dai kana nan da halayyarka ta mutanen da?
Don Allah ka janye wannan ra'ayin ka shirya gobe na raka ka
asibiti, yanzu idan da Allah ya raya mana Tasi'u haka zai dinga
wahala da kai akan zuwa asibiti?" Malan Kado ya dan yi
murmushi yace, "Ka san ko Tasi'u har ya rasu ba shi da wani
buri illa na son ya zama likita". lliyasu yace, "Allah ya jikan
Tasi'u ai ga kanwarsa