An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
RUƊANI.
Labarin haɗaka (Rukuni na biyar).
Rubutu na A.
📝Hauwa Shehu
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'unn, innalillahi wa Inna ilaihirraji'unn, innalillahi wa Inna ilaihirraji'unn.
Kalmar da yake ta nanatawa kenan, lokacin da yake tafiya sauri-sauri gudu-gudu rungume da ita a hannunsa.
Duk bayan daƙiƙa ɗaya zuwa biyu sai ya kai dubansa gareta, yanayin yadda numfashinta ke tafiyar hawainiya ne ke bashi tsoro, tabbas tana cikin wani hali, kuma komai zai iya faruwa idan ba'a dauki matakin gaggawa ba, hawaye Masu zafi ne kebin kuncinsa.
Meyasa wanda ka aminta dashi shine zaici amanar ka?
Meyasa wanda ka ɗauka a matsayin garkuwa shi zai jefa ka cikin garari?
Meyasa wanda ka ke kallo a matsayin bango shi zai jagoranci rushe taka rayuwar?
Wannan wani irin zamani ne muke ciki wanda ƙananan ya'yan mu da ƙannen mu basu tsira ba? Koda kuwa mun kulle su a cikin gidajen mu. Kaico..! Da wannan zamani mai cike da RUƊANI.
Da wannan tarin tambayoyin a zuciyarsa ya ƙarasa kofar gidan, ya fara bugawa da ƙarfi, bugu yake ba ƙaƙƙautawa, kamar mai shirin cire ƙyauran.
Daga cikin gidan mahaifiyar nurse Hindu ta kalli agogo, ƙarfe biyu da minti goma sha ɗaya na dare.
Motsin hindu taji tana ƙoƙarin buɗe kofa, wannan ba sabon abu bane, domin yawanci mata a unguwar idan nakudar dare ta kama su, nan suke zuwa haihuwa.
Uhmm....! Allah ya raba lafiya ta mai da kai ta kwanta gami da jan bargo ta lulluɓe fuskarta.
A hankila Hindu ta buɗe kofa, turus ta tsaya tana binsa da kallon, cikin mamaki, fargaba da tsoro tace, Aliyu lafiya da wannan tsohon daren?
"Lafiyar dai Nazo nema, muna tsananin bukatar taimakon ki a wannan lokacin.
Ya faɗa yana kokarin miƙa mata Ilham yarinya yar kimanin shekaru hudu.
Touch light din dake hannunta ta kunna tana haska fuskar Ilham
Tabbas yarinyar tana cikin mayuwacin hali, numfashinta daƙyar yake fita.
To amma me ya sameta? Wannan itace tambayar da Hindu tayiwa Aliyu.
Cikin inda-inda yace, "kin gane ko, kawai ina kwance a ɗaki na jiyo ihunta, shine na fito naganta a wannan halin, don haka yanzu ba lokacin bincike bane, rayuwar yarinyar shine kan gaba, don Allah, na roƙeki ki taimaka ki ceci rayuwarta.
"Shigo. Ta bashi umarni yayin da ta juya cikin soron ta nufi ƙofar wani daki ta buɗe.
Da alama a dakin take duba marasa lafiya idan