NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 1 of 6

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Real ßukar Mustapha Damaturu (DAƘIƘA SITTIN!) Ita dai dama ba kasafai a ke samun ta ba, idan kuwa ka sa me ta to yi ƙoƙari kayi amfani da ita tun kafin ta kuɓuce maka! Ni dai tawa damar ba ta zo mini da wani abu na a zo a gani ba! Domin ba bu abinda ta haifar mini face tarin da-nasa-ni da nadama, wanda a kullum take ɗa ɗa ƙaruwa a cikin zuciyata. A rayuwa mutane iri biyu muke da su masu nasara, da marasa nasara, sannan ƙaddararmu ita ce kaɗai tagirmi gobenmu, da ace mutum yasan ƙaddararsa ta gobe da tini ya yi gaggawar magance ta tun a yau, kafin zuwa gobe lokaci ya cimma sa. Kamar yadda rashin sanin ita ta je fa ni na kasance a cikin mutane marasa nasarar. Lallai mafi girman kuskure a rayuwar duniya shi ne mutum ya nemi canza wa kansa ƙaddararsa ta hanyar amfani da ƙarfi-da-yaji! Ji nake tamkar duniyata ta banbanta da ta sauran bil'adama, domin wata iriyar duniya ce mai cike da ababen ban mamaki da na al'ajabi, kai harma da na ban tsoro. A taƙaice dai duniyata tana kama ne da irin duniyoyin nan na cikin mafarkai ko tatsuniyoyi. Kada kuyi mamakin jin cewar hatta fatalwai su na zuwa duniyata su azabtar da ni tare da bani tsoro, sannan ba bu bacci ko gyangyaɗi a duniyata, saboda kullum idanuna biyu ragas tamkar fara! Nutsuwa da kwanciyar hankali sun guje ni, masifa da bala'i sun zamo mini abokan fira, tashin hankali kuwa ya zamo tunanina na ko yaushe. A shekaru huɗun da suka gabata ne, watarana abokina Bala Shamuwa ya ɗauke ni izuwa cakwalkwalin Mallam Ɗanjatau, wanda jama'a suke yi masa kallon malami, amma kuwa a gaskiyar zance ƙasurgumin boka ne! Gidansa yana can bayan garinmu. Cikin wani wagegen ɗaki ya sanya ni, na zauna a gaban wani farin ƙyalle wanda ya rufe jikin ilahirin bangon ɗakin, sannan ya zauna a bayana. Sanye yake da wasu jajayen kaya ja zir, tamkar mai shan jini! Cikin muryarsa mai hargagi da hamami wanda yake kama da muryar dodonni, ya ce da ni, "Yaro za ka yi arziƙi, za ka yi kuɗi kamar yadda ke so, kuma za ka zarce duk wani mai arziƙin dake cikin garin nan, amma fa akwai ƙalubale mai girman gaske a gabanka, kuma ya kamata ka sani ba'a shiga daƙin nan a fita lafiya, ina nufin sai wani ya mutu! Ko ka kashe, ko kai da kanka ka mutu!" Na tsorata ainun da jin batunsa, ko in kashe ko ni kaina in mutu? Haka nayita tambayar kaina sau ba
🏠