An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
001 SHARRI JAKADA NE
Rukuni na shida 6
Gasar tsangayar marubuta 2020
Shuraihu Usman
Sowa hadi da ihun jama’a ne ke tashi a dankareren filin, dubunnan jama’ar da sukaiwa filin mamayar tururuwa sunyi dafifi a gaban wani makeken mumbarin katako,suna ihu suna fadin “sai kayi sai ka zarce wlh, makiyanka sai dai su mutu” .
A saman mumbarin nan kuwa wani dattijone sanye da fararen kaya yana washe baki gamida daga wa mutanen nan hannu, daga bayan dattijon wasu jibga-jibgan mutane ne masu kirar adawa, sunasanye da bakaken kwat,fuskarsu adaure tamau tamkar wayanda aka aiko ma da sakon mutuwa.
Dattijon ya daga hannu jama’a sukai tsit ya fara bayani “ruwa” jama’a suka amsa da “daga Allah” yasake maimaitawa a karo na biyu mutanen suka sake bashi amsa da amsar dasuka bashi a farko. Cikin murmushi dattijon yace “lokaci yayi kana zamani yazo da kowani karabiti ke mafarkin shugabanci, sun gaza gane kalmar shugaba me take nufi, burinsu kawai su hau mulki su cika aljifansu da dukiyar haram su bar talakawa cikin mawuyacin hali. Alhamdulillah jama’a kun zabemu da fari kuma kunga gingimemen aikin da muka dauko na shimfida muku titi a unguwanninku, sannan ga aikin kwalbati da muka faro wanda a yanzu an ci rabin aikin, ga fitilun kan hanya duka da muka sanya maku,tsaya fadin tarin ayyukan da gwamnatinmu tai maku ma bata baki ne, kundai gani da idanunku sun mulke ku a baya kunga yanayin kamun ludayinsu, shin zaku hada nasu da namu” ya karisa maganar tasa cikin daga murya
jama’an dake rike da fastocin dattijon suka amsa da “A’a”
“zabi na gareku, kuke da wuka da nama a hannunku ku sani kuri’unku sune ‘yan cinku,makaminku,martabarku hakanan kuma babban jigonku wurin tabbatar da dorewar shuwagabaninku na gari tahanyar kada wa jami’iyya mai alamar ruwan sama kuri’a ranar zabe” dattijon mai suna Alhaji Murtala ya sake fadi cikin daga murya,daga karshe yace “jama’a ku fito kwanku da kwarkwatarku ku zabi jam’iya mai alamar ruwan sama, ruwa daga Allah.”
Jama’a suka dau sowa suna fadin “sai ka zarce a kujerar sanata, sai ka zarce”
yana gama fadin hakan ya yafito daya daga cikin masu take masa baya lokaci guda ya sauko daga kan mumbarin ya durfafi wurinda motarsa ke fake,masu take masa baya da jami’an tsaron lafiyarshi suka biyoshi, yana kariso