An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Ummee Garkuwa
·
. AGOGO .
"A a, me zan gani? yanzu-yanzun nan daga tafiya yin alwala har an samu wacce ta sace min agogona ?"
a razane matan da ke cikin ɗakin su ka kalleta haɗe da nuna tsananin mamaki a fuskokinsu,
cigaba da bincike jakarta ta yi tana yi tana haki kamar wacce ta yi gudun mita dubu da ƙafarta.
wata da ke gefe ta ƙaraso kusa da ita cikin yanayin lallashi-lallashi ta ce,
"haba baiwar Allah duba jakar ki dai da kyau." a ƙufule ta waiwayo bayan ta mata wani irin rikitaccen kallo.
"ba ga shi ba kina kallo ba agogon a cikin jakar, wacce irin dubawa zan yi wacce ta wuce wannan?" ta nuna mata ƙasan jakar.
itama cikin ƙuluwar ta mayar mata da amsa.
"to, ko ma meye nan ba wacce ta tunkari inda jakar ki take sai dai in wani wajen kika jefar da shi."
jefo jakar ta yi wajen da matar take.
"ki yi wa Allah ki duba da kanki tunda kina ganin sharri nake.." da sauri ta katseta.
"Ni asuwa? ke dai da take taki ke zaki duba, kin ga ni na matsa ma."
ta ja gefe da sauri.
"na rantse da rabbil izzati ko a fito min da agogona ko kuma na yi rashin mutumcin da ba shi da magani."
wata kakkaurar mace ce ta shigo ɗakin da sauri jikinta sanye cikin danƙareran leshi. cikin yanayi na firgici da mamaki ta ce,
"Hajiya Sa'adatu menene ? me ya faru?"
matar da a ka kira da sunan ne ta yi tsaki.
"hmmm, Hajiya A'i, daga na fita ɗauro alwala aka samu wata ta yashe min agogona na gwal."
wacce aka kira da Hajiya A'i ta kama baki da yatsunta haɗe da salati, kallon mutanen ɗakin ta yi su biyar cif ta sauke numfashi, cikin ƙasa-ƙasa da murya ta ce,
"gaskiya bana jin ɗaukar shi a ka yi sai dai in jefar da shi kika yi Sa'adatu."
"ai ga jakar nan a gabanki ki duba da kanki ki gani."
sunkuyawa ta yi ta ɗauko jakar, duk wani lungu ta saƙo sai da ta bincike babu alamar a gogo a ciki. cike da mamaki ta ɗago kai tana kallon Sa'adatu.
"a ina kika yi alwalar?"
kasa magana ta yi sai nuna mata banɗakin da ke cikin ɗakin.
da sauri A'i ta tafi banɗaki ta shige ta daɗe tana dube-dube ba abinda ta gani hakan ya sa ta dawo cikin ɗakin jikinta na rawa.
"ki yi haƙuri Hajiya Sa'adatu, zan duba miki a nutse."
"ban gane ba ? wanne wani irin zance ne mara kan gado ? haƙuri fa kika ce ? agogon zinaren zan yi zaman jiran haƙurin har a ganshi ? taɓ ! na rantse da Allah ba wacc