NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 1 of 404

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🔥🔥🔥ZAKUNA BIYAR.🔥🔥🔥 FIVE LIONS🦁🦁🦁🦁🦁 MALLAKIN FATEEMA ZAHRA MUSA. A-K-A PRINCESS TEEMA STAR LADY. 31-10-2025.🔥 THE STORY OF DEATH OR LIFE🔥🧠 E_____________1 DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI. *Wannan littafi na ZAKUNA BIYAR tin daga page 1 na step 1 har zuwa karshen step 1 sadaukarwa ne ga mutanena na ƙasar Niger, ƴan Niger ƴan amana, ƴan Niger sun mun abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba, Niger gidan karaminci da mutunci, gidan amana da kyautatawa, kai ƴan Niger baki na ya yi kaɗan wajen iya faɗan alkhairanku, kun mun na gani! Ban san da me zan biyaku ba shiyasa na yi maku wannan sadaukarwan, ALLAH ya kara maku lafiya da zaman lafiya, kwanciyar hankali da farinciki, jin daɗi da walwala mara yankewa har illarh Masha ALLAH, hakika ina kaunar mutanen ƙasar Niger kauna sosai mara misiltuwa, much love.*🌹♥️ _________________🔥 U.S New York City. New York tana daga cikin birni mafi girma a cikin Amurka, wanda ke ɗauke da manyan cibiyoyi na kasuwanci, kuɗi, da al'adun kasar Amurka. Tana daga cikin jahohin da suka fi kowanne daraja a fannin kuɗi da al'adu. Unguwar upper east side, manhattan kenan. Wuri ne da ya shahara da manya-manyan gidaje na alatu, gine-ginen tarihi, da tarin art galleries. Yana kusa da central park, fifth avenue, da manyan kasuwanni kamar bloomingdale's. Unguwa ce ta manya-manyan kai, irinsu manyan lauyoyi, ƴan siyasa, da masu nasara a wall street!. 02:00AM. Agogon birnin YEW YORK ta buga. Dare ya yi sosai, dik wata halitta mai rai da natsuwa tana barci dan kara samun natsuwa. Kwance take a saman katafaren bed ɗinta, ta yi lamo cikin lallausan bargonta, da alama tana jin daɗin wannan barcin da take yi. Tamkar a mafarki haka ta fara jin alamar ana dukan gate ɗin gidanta, lamarin da yasa ta ɗan motsa daga yadda ta kwanta kenan. Lokaci guda ta zabura ta miƙe zaune sakamakon dukan gate ɗin da aka yi da karfi tamkar za'a rugujesa. Zazzare ido irin na mai barci a cikin duhu ta fara yi, take ta fara ƙoƙarin saita natsuwarta dan ta fahimci da gaske dukan gate ɗin ake yi ne ko mafarki?. Jin tabbas da gaske ne yasa ta kai hannunta saman phone set dake jikin bedside
🏠