Reading MASHI Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan durowar gefen gado, yana ta kiran layin Aliya, ita kuma ta baro ta can dakinta domin da ta Nafisa ya yi ta kira yana tambayar Hamida ko Aliya tazo? Tana fada masa cewa bata z0 ba.

Bayan yayì sallah ya ce "To yanzun sai ki bude ni in dubo ta ko?"

Ta Ce

'"Ai ba yanzun ka ke zuwa ba.

Ya cE

"To yanzun kuma zamu iya samun matsala tunda gari ya waye

Ta ce,

"Mu samu mana, dama nasan ba zaka kula dani ba kaje ka rabo ni da gidanmu ina can cikin tattali
kaje ka dauko ni."

Ya ce, "Kin raina kulawar da nake ba ki? To kifada min abin da ki ke son in ke miki don ki tabbatar da ina kula da ke

" Ya fada ranshi a bace.

Ta ce

"Ga shi ka kwana zaune kana dakina
zuciyarka na gurin wata."

Ta ce, "Yiwa kai ne dai,kuma bana fata kema wata rana in haka ta faru zaki ji dadì in ta hana ni fitowa in wofintar da ke?"

Ta ce"Ni dai ba zan bude ba, dama ka shiga wanka in ba haka ba zaka yi lattin zuwa office."

Ganin da gaske ba za ta bude ba, ya bi shawarar ta ya shiga wanka. Kan ya fito ta bude sai ya fita zuwa dakinsa ya hau shiri.

Bai ko kalli karin da Ladi Mai aiki ta hada mishi ba, ya nufi fita. Kofar a damke take, ya waigo ta fito tana tsaye a falon. Ta ce,

"Ga abin karinka.

" Ya girgiza kai, "Bana jin yunwa.

Ta ce,

'"Ai ko ba za ka dakin wata ka karya ba.

Ta soma hada mishi shayi, Har gurin Kofar ta

Zota bashi. Ya amsa tare da fadin "In da ace za ki ke hada min ko shayin ne a duk ranar da nike dakin ki da na yi tasa miki albarka Ya kai

Karshen maganar tare da kurbar shayin

Da sauri ya watso shi domin suga ya ji har

cikin kwakwalwar kanshi. Ya mika mata shayin

"Ga abin ki, bude ni." Ta kalli agogo, duk abinka sai shida ta cika,

Ya ce,

"Amna har yanzun ina mamakin ki sosai, ashe kin iya mugunta har haka?"

' Ta ce,

Na daina bari ana raina min wayo."

Ya jingina da bango,

"Shidar dai saura minti hudu.

Ta ce,Inma minti daya ne sai ya cika."

Ya samu Nafisa a yan da take, ya kira Likita ya ce zai kawo ta asibiti don fa jikinta ya yi laushi Likitan yace

"Ko ka kawo ta babu abin da zamu ¡ya mata da ya wuce wannan ruwan. Amma zan

fita zuwa asibiti, ka fito bakin titi in same ka sai
muje in ga.jikin.Haka kuwa Shatima ya fita ya yi jiran kusan

minti biyar kafin Likitan ya iso. Shi kanshi Likitan

ya tausaya ma Nafisa, ya ba da wata allura ta

tsaida amai, ya ce ayi mata a gani. Amma ciki irin

wannan Kila sai ta kai wata biyar zata samu dan Salma tana ta jiran Shatima har takwas ta gota

Ta fito taje dakin Aliya nemanshi. Aliya ta ce an fada miki nan yake?"Salma ta ce,

"Ni wallahi yanzun bana tuna in da yake."

Ta ce,

"Yana dakin Amna.

" Har zata wuce sai

taga sun fito da Likita. Ta rusuna ta gaida su,sannan ta ce.

"Yaya mun yi latti.Ya kalli agogon

hannunsa. "Haka ne, ya ba ki tafi ba? Nafisa ce ba lafiya ban san lokaci ya tafi haka ba.

Ta ce,

"Anty ba lafiya, bari in dubata.

Sun gaisa da Hamida, sannan tayi wa Nafisar sannu.

Ranar latti taje Makaranta, sai da ya roka aka bude
mata don har sun ce ta koma.

**

Wata ranar Litinin misalin Rarfe biyu da minti bakwai. Salma ta sauka daga kan Mashin a bakin

Gate din gidansu. Ta ba mai mashin kudin sai taga bakuwar mota zata shiga gidan.

Maigadi yazo yana tambayar Direban gurin wa suka z0? Salma ta kalli Direban, kamar ta taba ganinshi a wani guri. Sun yi kama da Shatima kadan.

Taji lokacin daga bayan motar an ce,

"Uwar Maigidan ce

Gaban Salma ya fadi, domin ko a

ina taji muryar Hajiyar Shatima ba za ta manta ba.
[8/19, 18:44] Ummi Tandama😇: _________
*🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️*


CHAPTER 16 Karshen book 2


*BY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHI*


Ta nufi cikin gidan gaba daya jiki a sanyaye,ta kasa bude kofarta,tabi motar da kallo har lokacin da taga motar ta tsaya daga cikin jerin motocin Amna da Shatima.

Ta bude kofarta ta shige,kasa cire kayan jikin ta tayi na makarantar haka kuma ta kasa dora girki,sai da tayi ta maza ta kunna risho ta dora tafasasshen nama.

Lokacin da su Hajiya suka shiga gurin Nafisa tana wanka,Hameeda tayiwa Mama da Hajiya oyoyo Aliya ta leko taga bakin Nafisa ne Dan haka sai ta yafa mayafi taje ta nufi wajen Nafisa da sigar duba jiki,tana shiga taga su Hajiya gabanta saida ya fadi tasan Hajiya ba kalar wasa bace, amma duk da haka saita cije ta zube ta kwashi gaisuwa a gabansu tana gaishe su yanda kasan zatayi masu sujada saboda girmamawa,Hameeda ne ta ajiye masu ruwa da lemu Aliya tace" Ya jikin Nafisa yau dai jiki da sauki? Hameeda tace "to gata nan ciki tana wanka".

Cikin kissa tace "Masha Allah naji dadi sosai,tasha magungunan ta kuwa?".

"Kinsan kuwa sai kinzo take sha,domin nidai nayi nayi da ita takisha"

Aliya tace "to bari ta fito inna lallasheta nasan zatasha haka za'ayi tayi hakuri da ita bansan inda zan samu tsakin nan bane bare ayimata abinda takeso amma ga rama can maigadi ya siyo mana".

Duk zubar da takeyi su Hajiya suna jin ta kuma sun yaba da maganganun ta musamman ma mahaifiyar Nafisa dan ance me da Wawa,Mama tace "Allah sarki kina dawainiya da Yarinyar nan Kullum Hameeda tana fadaman duk abinda ke faruwa har dare kina zuwa ki dubata."

Hajiya tace "haka akeso aishi zaman aure dama zaman tare haka akeson babba ya kasance,ita Yar'uwar takufa?

Aliya tace"Amna tana gurinta itama da sauki domin bacci takeyi,bari dai induba ta inaga yanzu ta tashi,Mama tace"Allah sarki kina dawainiya da wannan kiyi dawainiya da wancan kiyi da wannan Allah ya yi maki albarka.

Aliya ta amsa da"ameen" ta fita cikin jin dadi ta nufi shashin Amna domin dai burin ta kawai ta shiga ne gurin kowa taga yadda yake,hakan ne zai bata damar kunna wutar da take bukata a wannan gida,ta samu Amna a zaune tana kallon T.v mai aikin ta kuma tana bare mata kwai a gefe akan filet.

Tace "sannu da hutawa"

Kallo daya Amna tayi mata,sannan tace"yauwa sannunta" ta maida kanta gurin T.v.

Aliya tace "Hajiyan Shatima ne tazo tana dakin Nafisa tana bukatar ki,tace inzo inkira ki."

Amna tace "Ina zuwa"

Aliya ta juya ta fice.

Tsaki kawai Amna taja banda Hajiya ce babu abinda zaisa taje wani dakin wata daga cikin su,dan kawai ta nunamana cewa tafison yar'uwarsu ne kowaye Nafisa tafi Oho.....

Aliya na fita dakin Salma ta nufa ta sameta a jingine tayi jajjage.

Tace "to gasu Hajiyar Shatima can kije ki gaidasu Maman Shatima ne,Salma ta danyi rau rau da ido cike da tsoro,tace "Aunty tsoro nikeji"

"Tsoron wa.?"

Salma tace Hajiya wallahi,Aliya ta"sai kace wata mayya,ta haifa maki miji gashi nan yanata kashe maki uban kudi amma kice wai kinajin tsoron ta".

Salma tace "ba haka bane Aunty,ta taba man fada kuma ni ina tsoron fadanta.

Aliya tayi murmushin mugunta a ranta tace yanzu ma wani fadan zan sake ja maki,ta dubi Salma tace to wuce kije ki gaisheta," Salma tace to bari in canza kaya in cire na makarantar nan.

"Ta ya mutsa fuska jin cewa Salma zata samu canza kaya,inta cire kayan nan ai shikenan zata rage mata sauki ma har ta samu tseguntawa Hajiya irin kudin da ke kashewa Salma wadda abin ke damunta Kullum, Salma ta dauki dan mayafin jallabiyar ta tayafa tunda daga kanta babu dan kwali ta fito cikin fargaba ta nufi shashen Nafisa.

Aliya ta shiga dakin ta dama ranar itace da Shatima kuma ta shirya mashi farfesun kaza yana wuta batama gama ba,sannan tayi dafadukan cos-cos da hanta,nan ta jerowa su Hajiya a katon tire ta shigo dakin Nafisa ta samu Salma tana rabe rabe a gefe ta kasa karasawa ciki,harda tsawar ta tace "muje mana kin wani rabe gefe guda."

Hajiya tace"wacece?" Aliya cikin sigar son tura kiyayyar Salma ga surukar tasu tace "Salma ce uwar shanshanci".

Hajiya ta gimtse fuska harma da Amna da Maman Nafisa da suke zaune, Salma ta tsugunna a gabansu kana kallon ta kasan a firgice take,Aliya ta dire tiren a gabansu nan kamshi ya daki cikin su,ta kalli Hameeda "kawo filet da cukula mana kisa".

Salma cikin raunin murya tace sannunku da zuwa Hajiya,Mama ne kadai ta amsa "yauwa sannu Yarinyar nan".

Ta kalli Nafisa wacce ke zaune saman kujera tace sannu Aunty ya jikin? Itama fuskar ta a daure tace "jiki da sauki" ta yunkura zata mike Hajiya tace koma ki zauna"

Salma ta zaro ido tare da zama cikin tsananin faduwar gaba,ta tuno alwashin da Hajiya tayi sai tazo har kaduna tasa ankoreta,hawaye suka soma zubo mata...

Muryar Hajiya ne ya katseta daga tunanin da takeyi "iyayen kine sukazo daga Zaria suka saki makaranta?". Cikin in inah Salma tace a'ah.

Aliya tace "Ina sukaga halin sata a makaranta sunaji da abinda zasuci" Salma ta kalli Aliya a tunanin ta wannan maganar ta Aliya kamar tayine domin kareta a gurin Hajiya sai kawai taji Hajiya tace

"Badai shi Shatima ne yasata ba?"

Nafisa ta tabe baki "shiyasa ta mana Hajiya makaranta me shegen tsada"

Aliya tace "tsada ai ba kadan ba ma tsadar,kusan dubu dari harda doriya"

Amna ta kalli Aliya domin jin bakon lamari ita bata shiga harkar kowa batasan ma me akeyi a gidan ba.

Hajiy tace "Eyyeh!"

Aliya tace "to ai kudin shiga makarantar nan dubu saba'in da biyar ne banda kudin motar dawowar ta da Kullum sai ya bada dari biyar ga kudin namanta da komai da yake badawa dubu daya,"Aliya takai karshen maganar tanajin dadin tasamu abinda takeso.

Hajiya ta kalli Salma cike da tsana tace hakane kudin makarantar dubu saba'in da biyar?

Salma cikin rawar jiki tace "yanzu sun cike tamanin".

Hajiya ta mike da sauri tana fadin "lallai kam sun cike tamanin wato ke yakeyiwa aiki kenan kullum rana ta Allah dubu daya da dari biyar a wata nawa zai kama? Jama'a kuyi mani lissafi?

Da sauri Amna tace dubu arba'in da biyar kenan zai kama duk wata"

Nafisa tace "Kan uba!! Muna zaune?"

Hajiya tace "to aikoni dana haifeshi idan ya yi man haka nasan ya kai daa"

Maman Nafisa tace "to shime yakaishi wannan batan basira? Wai rokon Allah da goge"

Hajiya ta soma kiran layinshi ya daga tace "Ina gidanka Allah yasa ka kusa tashi" yace "insha Allahu nan da awa daya zan dawo" tace "saika iso" keda wayene? "Nida Mamanku ne Mustapha ne ya kawomu".

Salma wacce sautin kukanta ya fara fitowa tace "don Allah Hajiya kuyi hakuri....."jifar da Hajiya tayi matane da karamin filon kan kujera ya hanata karasa maganar ta.

Hajiya tacigaba da cewa "banason jin komai daga gareki Yar gidan masu asiri kawai,ai tundaga lokacin da yaron nan ya zoman tamkar zaiyi hauka akan wannan kazamiyar Yarinyar nasan aikin asirine.

Ta kalli Maman su Nafisa ki tunafa be taba kwanciya a asibiti akan wata ba sai silar wannan Yarinyar dan nace bazai aureta ba ranar ya tashi a sankare idanuwa a kakkafe mukai asibiti"

Duk matan nan suka kalli Salma cikin mamaki musamman ma Amna wadda take da matukar tsoron asiri.

Nafisa tace "wai dama ciwon nan nashi yanada nasaba da itane?"

Hajiya tace "inkinje gaba ma saiki fada daga nan abinda nayi mashi ya yi yawa kawai sai nasa ayiman tambaya wajen malamai can ne suka fadaman wai uwar tane tasa akayi masa asiri da sunan Shatima kuma an hada da naman bakar akuya da yawun bakinta da ruwan hawayenta aka bashi yaci,daf da bikin nan fa har gida sai da ya siya masu da sauri Salma ta dago tana fadin "wallahi Hajiya ba siya mana ya yi ba hayace,"Hayar.....

Hajiya ce ta sake jifarta da wayarta dake hannun ta "karya zanyi maki kenan dan ubanki?"

Aliya cikin sauri ta dauki wayar tare da fadin haba Hajiya wayarki kar tayi lahani mana.

Hameeda wacce tausayin Salma ya kamata haka kawai taji ba gaskiya bane abinda Hajiya take fada ba,dan haka ta saci wayar Nafisa tayi cikin daki ta fada bandaki domin yin abinda ya dace.

Aliya ta kalli Hajiya kiyi hakuri bari in zuba maku abinci.

Sakawa Maman ku dan ni bazanci abincin nan ba sai anyita ta kare yau din nan.

Nafisa tace"gwara ayita ta kare domin kada kowa ta yadda kiri kiri hmm"

Aliya tace "aikuwa bayin kansa bane bakiji abinda akace bane"

Amna wadda ta yadda da zancen nan dari bisa dari ta kalli Salma cikin tsana indai tana gidan nan kam nidai bazan zauna ba dan a gaskiya banason asirce asircen nan da akeyi.

Hameeda ta kira sau uku kafin ya daga tace Yaya don Allah kazo gida yanzun nan ga Salma nan an tsareta su Hajiya ne"

Gaban Shatima ya fadi ya manta da tsanar da Hajiya tayiwa Salma, yace "nagode Hameeda ganinan zuwa."

Lokacin tashinshi beyi ba haka dole ya tashi yaje gida da gaggawa domin kashe waccen wutar wadda shedan ya rura a cikin sa ya dauki uzuri gaggawa ya fita bema san irin gudun da yakeyi ba kawai saidai ya ganshi a layinsu,yana parking lokacin Mustapha ya fito daga falon Aliya.

Shatima ya nufi gurinshi "inasu Hajiya?" Mustapha yace suna falon Nafisa.

Shatima yace "to bari inje mu gaisa" Mustapha ya biyoshi domin ya gama cin abincinshine.tun daga baranda yakejin muryoyinsu daya bayan daya.

Hajiya tana fadin"ba bakin dan akuya ba ko bakin dan jakane kukayi asiri dashi yau sai kin bar gidan nan".

Cikin kuka Amna take fadin"yanzu zan kira Dadyna nima yazo ya daukeni dan bazaiyiwu in zauna ba,Ina tsoron asiri".

Nafisa take fadin" jiya nan fa saida nayi mafarki da ita gaskiya bazan iya tuno meya faru a mafarkin ba amma tabbas ita na gani,ni kaina idan tana gidan nan to wallahi Mama saidai mu tafi daku yau din nan."

Mustapha ne yafara shiga hakanne ya hana Aliya magana taso tayi magana dan ta hangoshine a tsaye.

Cikin tashin hankalin ya shigo cikin dakin gaba daya suka maida kallon su gareshi sannan kowacce ta shiga nanata abinda zata nanata, kowacce ta nanata abinda ta fada.

Hajiya tace "duk kuyi shiru yanzun dai kai kazo ka zaba koni dana haifeka ko kuma iyalanka ko kuma wannan Yarinyar ita kadai? Ta nuna Salma wacce take durkushe tana cikin firgici da matsanancin tashin hankali,itama kallon shi takeyi cike da tsananin bukatar taimakon shi,idanuntane suka nuna shi kadai take bukata,shine taimako na karshe da takesa rai zaiyi wani abu akan wannan halin da take ciki.

Hajiya ta katseshi da fadin "Zan la'anceka!!!..." Zan la'anceka!!! In ka sake kallon ta,kuma na baka nan da minti daya rak ka yanke hukunci..........


*Alhamdulillah anan muka kawo karshen littafi na biyu,a yanzu kuma labarin zai fara, akwai cakwakiya fah,anan kuma muka kawo karshen free pages idan kina bukatar 3&4 din littafin RANA DAYA ki turo kudin ki 300 ta wannan account number din👇🏻*

```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment