Reading UWA UWACE COMPLETE BY FATTY NOOR Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zo da kaina. Ban fada mata ba ma na ce sai naji amsarki."

"Allah Sarki Mamin Suhaib. Yasin shi yasa nake kara ganin girmanki. Kina da mutumci kuma kin san mutumci. Allah na tuba banda ma kin dage ai da ko kwandalarku ba zan karba a matsayin albashinta ba. Ciyarwar da kuke mata damu kanmu ta wadace mu."

A zatonta sai washegari ko nan da kwana biyu Nasima za ta taho sai gata ta dawo da kaya niki-niki kafin magariba. Lokacin ko cikakkun mintuna talatin bata yi ba da tafiya. Da mamaki Khadija take kallonta tana turo katuwar jaka da wata karama sai ghana must-go.

"Ashe da shirinki."

Tabe baki tayi Nasima tayi ta ce "uhm".

Khadija ta daure zuciyarta daga take taken fitsarar da take gani a wurin Nasima. Shirin nata cikin kankanin lokaci ya bata mamaki ganin bata san da zuwan ba sai da ta gama aiki za ta tafi ta fada mata. Ita kuwa tuni sun gama shirinsu da Tahir.

Mamakin Khadija ninkuwa ya yi da taga Nasima ta nufi dakin baki da kofarsa take a cikin falon da kayanta. Idan tayi tunanin ko mamanta ce ta hada mata kaya kafin ta koma gida to da ya akayi ta san dakin da za ta zauna bayan ko su Suhaib basu sani ba. Kama bakinta dai tayi tana kallon ikon Allah.

Nasima kuwa tana shiga dakin ta buga wani uban tsaki. Ta lura Khadijan sai wani fiffika take yi ita mai miji. Mijin da yake a tafin hannunta matarsa har wani daga kai za ta yi mata? Sake yin tsaki tayi da ta kula tsohuwar katifarsu Lilu ce aka ajiye mata a dakin da wankakken bedsheet da pillow.

"Kut! Ai wallahi gado za ka zo ka saka min a dakin nan ko na kama gabana. Lallai ma Khadijan nan kin rainani."

Shu'umin murmushi tayi da ta tuna tuggun da ta shirya mata. Lokaci ya yi da Tahir zai bata nata 'yancin ko ta kwata ta karfi. Ba zai yiwu bane ya cigaba da raina mata wayo. A gaban matarsa ya fada mata magana a bayan idonta kuma ya dinga lallabata. Da Tahir ya dawo Nasima tana daki ta ji hayaniyar yaran.
Da saurinta ta mike ta gyara kwalliyarta ta fesa turare ta fito.

Shirt dinsa ce a jikinta ta hada da zani da dankwali iri daya.

"Daddy oyoyo" ta ce da karamar murya kai a kasa.

Kallonta ya yi sama da kasa wani abu na fizgarsa gareta. Ba don idon yara ba da sai ya biya ladan wannan ado. Gwalo tayi masa karaf a idon Khadija wadda ta fito daga kitchen da tray a hannu. Nasima sai ta wayance ta kuma yin gwalon.

"Nima na rama Lilu." A zuwan wasa suke yi dashi.

Tahir sai ya karbe da cewa "anya Khadija ba rainon mutum hudu ki ke ba? Ita da ta zo taimaka miki ta buge da wasan yara."

Bai bawa Khadija damar yin magana ba ya bukaci ta tara masa ruwan wanka. Daki ta nufa zuciyarta cike da wasi-wasin abin da ba ta son zargi. Abincin ma daki ta kai masa a ranar. Sai da suka kwanta ta sako zancen shirt din.

"Ni fa kamar shirt dinnan taka da nayita nema wancan wankin na gani a jikin Nasima dazu."

'Jaraba sai da ta gane' ya ce a zuciyarsa.
"Oh ashe bamu yi maganar ba. Rannan na tsinceta a bayan mota tayi datti. Ina jin daga kayan wankin ta fado. Na dauko zan yar shi ne da ta gani ta ce tana so."

"Ka dai san ina bata kaya. Idan kari take bukata ai da sai kayi min magana. Rigarka ai ba abin sawarta bace."

Da bacin rai take magana ya soma bata hakuri. Zuciyarta sam babu dadi har wani zazzabi taji yana neman kamata. Abubuwan da take ta son turewa game da Nasima sun sami wuri sun manne mata a rai.

Bayan kamar minti arba'in tana fama da guntun ciwon marar dake tsungulinta taji kamar hannun Tahir a saman fuskarta. Da alama karkada hannun yake ya gani ko tayi bacci. Da gangan tayi motsi ai kuwa ya dauke hannu ya kwanta da sauri. Juya mata baya ya yi ta bude ido ta tabbatar baccin karya yake yi. A hankali tayi kwafa ta sake rufe ido. Ba afi minti goma ba ya sake kada hannun. Wannan karon luf tayi takaici na nukurkusarta. Akwai abin da yake boye mata. Fatanta Allah Yasa ba Nasima bace. Tana jinsa ya tashi ya shiga bandaki. A cikin kunnuwanta taji ana bude dakinsu shi ma ya bude bandakin. Sannu a hankali ta bude ido kadan don kada a san ta farka ta hango Nasima a bakin kofar. Abin ya daina bata mamaki ma tunda har take da karfin gwiwar zuwa dakin. Da yatsa Nasima take yafito Tahir da ya fito daga bandaki, shi kuma yana nuna mata Khadija wadda duhun dakin yasa basu gane ta bude ido ba. Barazanar shigowa Nasima tayi masa ya yi murmushi yana yi mata inkiya ta karaso mana. Ba kunya ta sako kafa a kofar dakin ya yi saurin karasawa ya dagata a kafadarsa suka yi gaba. Kememe Nasima taki yarda a koma dakinta wai ita a gadonsa za ta kwanta. Sanin rigimarta yasa ya ce da Khadija su kwana a nata dakin.

Rufe kofar da ya yi a hankali ya yi daidai da matsanancin bugun zuciyar Khadija. Hawaye take yi ba tare da ta sani ba ta tashi da kyar ta bude kofar ta fita. Dakin Nasima ta nufa bata same su ba sai ta nufi na Tahir. Daga bakin kofa take jin dariyar Nasiman tana rokonsa ya daina yi mata cakulkuli. Shi kuma yana cewa ta rage murya.

Sai da ta tsaya ta hadiyi wani yawu mai daci sannan ta murda kofar da karfinta. Ganin da tayi musu yasa komai na jikinta tsayawa cak. Murdawar cikinta ce ta dawo da ita duniyar mutane ta rike ciki tana salati.Wattpad: https://my.w.tt/Fae5U4oHh8


UWA UWACE...2

Batul Mamman💖



Duk hukuncin da uwa za ta yanke akan 'ya'yanta tana yi ne da tunanin hakan shi ne maslaha a rayuwarsu ko da kuwa a gaba shi zai zamto mafarin kukansu.

***
Kwakwalwarta babu abin da take hasko mata sai yanayin da ta ganshi tare da Nasima lokacin da ta farfado. Idanunta a rufe amma hawaye yana sintiri daga kwarmin idanun zuwa kunne ya sauka akan pillow. Daga kamshin da take ji na dakin kadai ta fahimci a gadon asibiti take. Sakayau take jin jikinta babu wani nauyi sai na zuciyarta da ta koma tamkar dashen dutse. Cikinta ta shafo a hankali taji babu tokarewar nan ta dan da ya kusa zuwa duniya. A firgice ta tashi wani irin radadi na ban mamaki ya soki mararta.

"Bar garaje Khadija jikinki da danyen ciwo." Cewar Yakumbo mahaifiyar Tahir.

Da yake bata san da ciwon ba tashin bai wahalar da ita ba kamar komawa ta kwanta. Ita ba a kwance ba ita kuma ba a zaune ba haka ta saka hannuwanta ta dafe gefen gadon don kada ta fada da karfi. Yakumbo ce ta taimaka mata ta koma ta kwanta tana rarraba idanu. Tambayoyi ne akan harshenta ta kasa amayar dasu saboda sabon al'amarin da take ji a jikinta.

Yakumbo ta sake cewa "Bari na fadawa nos kin farfado" har ta kusa kofa ta dawo ta dafa mata kai "sannu kin ji. Allah Ya baki lafiya."

Khadija ta kula da hawayen da Yakumbon ta dauke daga gefen idonta kafin ya sauko. Jikinta sai ya kara yin sanyi da tunanin ko me yake faruwa ba alkhairi bane.

Yakumbo bata jima da fita ba Mamanta ta shigo tare da kannenta da su Farha. Kowa sannu yake yi mata tana amsawa da ka. Sallamar Tahir taji ta dawo mata da duk wasu lokuta da sai a yanzu take fahimtar raina mata wayo suka yi shi da Nasima. Runtse idanu tayi tana jin Mamanta tana tambayarta ko cikin ke mata ciwo ta girgiza kai. Shi kan shi Tahir din ganin idonta biyu sai da yaji kamar ya koma saboda firgici. Saukinsa daya yaransa da suke wurin Mama jikinsu a sanyaye da yanayin Maminsu. Yana da tabbacin ba za ta yi wani abu a gaban 'ya'yanta ba.

"Ku bashi wuri mana ya zauna kun yi ďare-ďare akan gadon." Mama ta furta tana nunawa kannen Khadija hanyar fita daga dakin.

Mutum biyu ne dama suka zauna a gefe sai suka tashi amma basu fita ba. Tahir ya kalli Khadija ba shiri yau shi ne da sauke kai kasa. Tsoronta ne ya mamaye masa zuciya saboda irin kallon da take yi masa babu komai a cikinsa sai tsana da disappointment.

Mama kuma ta kara masa zafi da cewa "Ina mai-aikin taku yau? Kodayake ya kamata yau ta huta."

Dawowar Yakumbo da likita ce ta taimaka masa bai bayar da amsar da za ta zama zallar karya ba. Kukan jinjiri ne ya biyo bayan shigarsu dakin a hannun Matron. Da dan murmushinta ta nufi gadon bayan gaisawa da jama'ar dakin.

"Ina nan ni dai. Doctor ki gama dubata ta bawa bebina abincinta mun gaji da shan madara."

Kallon kunshin shawul din Khadija take yi a lokacin da likitar ke yi mata tambayoyi game da jikinta. Babu abin da take fahimta sai gyada kai da take yi idanunta fal hawaye akan dan da bata ganin fuskarsa.

Likitar sai ta kalli Yakumbo da alamar tambaya "Maman Khadija ya naga kamar bata san me ya faru da ita ba?"

"Farfadowarta kenan na taho kiran Nos sai na hadu dake."

Da ido Maman ta kalli kannenta suka fice tare da su Suhaib. Tahir kamar ya nutse ya kasa kallonta. Likitan ce ta karbi bebin ta dora mata a cinya.

"Khadija kin san cewa tun farkon cikin nan akwai matsala har kina yawan zubar da jini ko?"

Bata amsa ba sai bin fuskar yarinyar da har kunne an bula mata take da kallo.

"Yau kwana kenan..." da sauri ta daga kai ta kalli likitan jin cewa kwananta biyu bata hayyacinta "maigidanki da mai-aiki sun kawoki cikin dare kina ta zubar da jini a sume. Ta ce zamewa ki ka yi a toilet wurin faduwa cikin ya bugu da sink. Kafin ki farfado faya ta fashe ga jinin bai tsaya ba."

"Hummm" ta ce da guntun murmushi idanunta akan Tahir. Yakumbo tana kallonsu ta kuma ha yadda yaki daga kai ya kalli matarsa.

"Ba cs din bane kadai Khadija harda mahaifar muka cire."

Sautin da taji ya ziyarci kunnuwanta ga dukkan alamu shi ake kira saukar aradu a yanayin tashin hankali. Zabura tayi za ta tashi a karo na biyu tana fama dinkin kasan mararta.

"Kwanta don Allah kada ki yiwa kanki rauni. Kaddara bata wuce kowa. Gashi an ciro miki jaririyarki lafiya kalau."

'Yar ta rungume ta fashe da matsanancin kuka.

"Ki yi hakuri Khadija. Mun yi iya yinmu amma jinin yaki tsayawa. Taimakon Allah ne kawai muka sami baby din tunda sun ce basu san tun yaushe ki ka fada kan cikin ba." Likitar ta karasa yi mata bayani.

Kukanta bai tsaya ba kowa na dakin ya tausaya mata. Yakumbo kuwa haka kawai tun farkon labarin dama bata wani yarda ba. Yanayin Khadijan a yanzu sai ya karfafa mata zarginta. Don ta tabbatar sai cewa tayi da Tahir ya rarrasheta mana. Mugun kallon da Khadija ta watsa masa wanda ya dakatar dashi ya bata amsarta.

"Mijin naki ki ke yiwa wannan kallon don rashin hankali kamar shi ya dora miki lalurar." Mama ta ce da ita cikin fada.

"Allah sarki" inji Matron "kar ki ga laifinsa da kyar ya yarda yasa hannu. Yarinyar da suka zo tare ce ma ta dinga tausarsa akan ya amince a cire saboda kada a rasa ki."

Numfashinta neman daukewa ya yi a wannan lokaci. Wato duka karairayin zuwanta asibitin sai da Nasima ta ingiza shi ya yarda aka cire mata mahaifa. Bata san me za ta yi musu ta huce ba. Ya ci amanarta ya kuma cutar da ita.

Gani tayi su Mama na fita daga dakin tayi murmushin takaici. Ta san irin abin nan ne ace a basu wuri ita da mijinta. Ana rufo kofar ya taho gareta da sauri.

"Nasima don Allah kiyi hakuri ki rufa min asiri. Na san ban kyauta ba amma don Allah in ci darajar 'ya'yanmu."

Tahir ya cika babban munafuki har tana mamakin yadda akayi ta kasa daukan haske ko sau daya. Saboda nisan da ya yi shi yasa bai ji kunyar kiranta da sunan mai-aikinta ba.

"Khadija. Suna na Khadija." Ta ce dashi muryarta a dake.

Bakinsa ya doke da sauri ya sauka kan gwiwoyinsa.

"Ki yafeni Khadija."

Ba shi take kallo ba. 'Yarta ta karshe a duniya take kalla tana nadamar biyayyarta a baya. Da bata amince ta aure shi ba da basu hada jini da mazinaci ba.

"Na yafe maka tun kafin ka roka duk da baka yi nadama ba."

"Nayi. Wallahi nayi nadama sosai."

"Baka yi ba. Na rantse da Allah da kayi nadama da baka taho da ita kawoni asibiti ba. Da bata zauna jinyata har ana cigiyar rashin zuwanta a yau ba."

Busassun labbansa ya lasa a hankali. Ya san ba za ta taba yarda ba amma shi ya san cewa ya yi nadama. Yana dai yiwa Nasima irin son da ba zai iya hakura da ita ba. Idan kurar nan ta lafa aurenta zai yi ya kama mata gida daban. Zai cigaba da zama da Khadija saboda wani sashe na zuciyarsa yana ganin girmanta. 'Ya'yan da ta haifa masa kuma duk munin halinsa yana sonsu kuma ya san suna da hakki a kansa. Muryarta ce ta katse masa tunani.

"Kafin a sallameni ka rubuta min takardar saki. Ba zan tona maka asiri ba saboda bana son duniya ta nunawa 'ya'yana yatsa akan halinka. Kai dai ka tanadi abin da za ka fadawa iyayenmu tunda karya a jininka take. Sharadi na daya ne." Kallonta ya yi "kada ka yarda ka dora min laifi a matsayin dalilin rabuwarmu. Ina fata ka fahimceni."

"Ba zan iya sakinki ba. Khadija ina sonki."

"Ka daina yiwa kanka karya akan abin da baya zuciyarka."

Zancen gabadaya baya so ayi shi a asibiti amma ya san ba shi da hurumin cewa tayi shiru. Yana son cigaba da zama da ita amma ba ya jin zai zama adalci gareta ya tursasata ta cigaba da zama tare dashi bayan yanzu ya fara son Nasima. Tunda dai za ta rufa masa asiri ya san komai zai zo da sauki. Juyawa ya yi zai fita ta kira sunansa.

"Tahir! Za ka yi nadama a nan gaba sai dai ina tsoron kada ta zo a lokacin da komai ya lalace. Ina gudun kada hakkin 'ya'yan da ka batawa rayuwa ya rataya a wuyan 'ya'yana."

Da yake maganar ta tsorata shi bai san lokacin da ya ce "wallahi ba ni na bata Nasima ba a haka na sameta."

Kallon da tayi masa ne ya sa shi jin nauyin furucinsa. Sunkuyar da kai kawai ya yi yana jiran ya ji me za ta ce sai yaji shiru. Juya masa baya tayi tana zubar da zazzafar kwalla. Ta so Tahir a lokacin da bata da zabin da ya wuce bin umarnin iyaye. Ta sadaukar da farincikinta na son waninsa saboda tsira daga azabar Allah. A yau ta rasa mahaifi da kuma igiyar auren da take jira ya datse duk a dalilinsa. Ita mai iya tsaya masa ce ya kara aure idan yana so. Shi yasa take mamakin dalilinsa na yin zina. Zinar ma ta fuskar wulakanci gareta. Kalaman mahaifiyarta take tunawa a wani lokaci da ya wuce tana yiwa kaninta fada zai tafi jami'a a wani garin.

"Zina masifa ce. Idan ka yi da 'yar wani kai ma sai ta zagayo jikinka inda za ka ji ciwo mai radadi. Ko ni, ko 'yan uwanka, ko iyalinka ko 'ya'yan cikinka"

Addu'a ta soma yi musu tana fatan Allah Ya karesu daga wannan mummunar dabi'a. Za ta sadaukar da rayuwarta wurin kula da tarbiyarsu da fatan rufowar asirin mahaifinsu. Aure kuwa ta yi ta gama. Abin da ya yi saura ba rayuwarta za ta yi amfani dasho ne wurin ganin yaranta sun sami ingantacciyar rayuwa.

Bayan kwana biyu suka sake kebewa da Tahir a dakin. Tuni tayi masa akan takardar sakin ya ce da ya saketa gara ta tona masa asiri. Amsarsa ta tayar mata da hankali ta kuma sanyata tunanin dalilinsa na sauyawa bayan da ya amince.

Yanayinta ya kalla a ransa yana yabon kaifin basirar Nasima. Yana fada mata zai saki Khadija ya aureta ta fitittike ta ce sam bata yarda ba. Nuna masa tayi duniya za ta zagesu idan suka yi haka. A ranta kuwa gudun kada ya bata rikon 'ya'ya take yi. Tafi son ayi auren a gaban Khadijan ta ganta suna masu matsayi daya a gidan. Ita ta bashi shawarar wadancan kalamai domin a cewarta Khadija za ta zauna don 'ya'ya. Tunda aka kai yanzu maganar ganinsu bata tashi ba to ya sani cewa indai akan 'ya'yanta ne za ta rufa masa asiri.

Ga zahiri ya gani. Sai ga Khadija tana kuka tana rokonsa saki kamar ba ita ya yiwa laifi ba. Da aka murda kofar dakin da sauri ta share hawayenta harda karyar ciwo ke cinta. Da wannan barazanar ya samu ya rufe bakinta har aka yi sallama. Da wani ya san abinda uban 'ya'yanta ya aikata ko da kuwa mahaifuyarta ce gara ta cigaba da zama dashi ko babu soyayya. Ba za ta so labarin gamon da tayi ya taso a lokacin da wani alkhairi ya doso rayuwar 'ya'yanta ya wargaza ba.

KHADIJA: A jerin ire-iren iyaye mata ta fado a jinsin masu shanye komai domin 'ya'yansu. Ta yarda ta fanshi zubar hawayensu ta hanyar sadaukar da farincikinta. Karesu zata yi muddin rai kada kazantar mahaifinsu ta wargaza rayuwarsu a gaba.

*****


KIRIKASAMMA
1995


Ta san ya ji ta sarai amma bata sare ba ta cigaba da binsa da roko da laluma saboda muddin ya sa kafa ya fita yau to magana ta kare. Kiran sunansa tayi da dan karfi ganin ya kusa kofar fita. Indai bukatarta za ta biya tayi alkawarin jure duk wani jan rai da wulakanci daga Inuwa.

"Malam inata magana baka ce komai ba har za ka fita."

A fusace ya juyu kamar zai mangareta ya soma fada.

"Ke dai Mari da mayya ce ki ka kama mutum Yasin sai buzunsa. Haba! Ni na taba ganin bakin naci irin wannan? To duk jarabarki sai ya tafi yadda ake tura 'ya'yan kowa."

Hargaginsa ya fito da sauran matan gidan daga bangarorinsu. Zaman kauye babu abin yi har jiran barkewar rikici suke don a bawa ido abinci. Gidan nasu kuwa an sami karuwar jama'a, kama daga matan da ake kara aurowa zuwa hayayyafar da ake yi kusan duk shekara.

"Rigimar me ku ke yi da rana tsaka Inuwa?" Mal. Sa'idu babban wa ga mazam gidan ya tambayesu amma aka rasa mai bashi amsa.

Mari sadda kai tayi kasa zuciyarta tana bata cewa hakuri kawai za ta yi wannan karon a tari gaba. Mal Sa'adu da sauran 'yan uwan Inuwa babu mai goyon bayanta. Maganar nan kuma ko Inna Mairo ba bayanta za ta bi ba.

"Kya yi shiru kuma yanzu? Ai sai ki bude baki ki fada musu abinda ki ke rokona" cewar Inuwa yana duban yayansa "wai makaranta ce bata so a tura Abbati."

"La haila ha illallahu..."

Mata sai tafa hannuwa kamar sun ji gagarumin sabo. Shi kuwa Mal Sa'adu cewa ya yi maganar ba ta tsaye bace su biyo shi sashensa.

Durkuso Mari tayi a gefen tabarmar da Inuwa ya zauna. Bata ma yi niyyar zama ba domin rashin kunya za ace tayi. Mal Sa'adu ne ya yi magana cikin jimami.

"Yanzu ke Mari karatun Muhammadiyyar ne ba kya so? To ko dai kin canja addini ne bamu da masaniya?"

Kai da hannuwa ta karkada a tare "a'a Malam. Cewa nayi a barshi ya cigaba da karatun a nan ba sai an kai shi Kano ba almajiranci ba."

Matan gidan dama ba kaunarta suke sosai ba saboda fifikon da Inna Mairo ke nunawa a kanta. Gashi tayi karatu har matakin aji uku a firamare kafin Inuwa ya aurota. Su kuwa babu arabi ba boko. Anyi musu baiko tun tana shekara goma. Sai ta tafi aikatau Dutse inda ta sami wayewar kai. Gidan da tayi aikin suka saka ta a makaranta. Sun so a barta ta karasa amma gidan su Inuwa suka ce idan bata dawo anyi auren ba a dawo musu da kudinsu. Haka nan tana ji tana gani aka rabota da ilimin da ta fara jindadinsa. Wannan ne yasa ta dage aka kai 'ya'yanta firamaren garin sannan suna zuwa makarantar allo da ta dare. Da sana'ar dinkimta da take dan samun kudi take yi musu hidimar makaranta. Su biyar ne yanzu. Abbati babba da mai binsa Sani sai 'yan mata uku. Al'adar gidan ta tura yara maza almajiranci kwatakwata bata burgeta. Ta ga yadda almajirai ke watangaririya idan sun tafi karatu, bata marmarin 'ya'yanta suyi irin wannan rayuwa.

"Lallai Mari. Ke ko 'yar kunyar nan ta dan fari ma ba kya ji har kike kallon idon Malam kina cewa a bar miki da a gabanki?" Uwargidan Mal Sa'adu ta furta da sigar nuna tayi ba daidai ba.

"Ko ma dai mene ne wannan sabon abin da ki ka zo dashi ba al'adar gidanmu bace. Zuri'ar gidan nan suna zuwa almajiranci tun talan-tale. Naki dan da bai fi na kowa ba shi ma zai je. Sai dai kuma idan zaki sake masa uba." Mal Sa'adu ya kare da tsorata ta.

Idan aka ce ta sake masa uba tamkar ana tuhumarta da laifin haifar dan da ba na sunna bane. Muryarta a karye ta bashi hakuri "Allah Yasa hakan shi ne mafi alheri."

"Karatun allo hairan ne! Abbati zai je kamar sauran 'yan uwansa ya rubuce sittin kuma ya haddace shi."

'Nima haka nake fata' Mari ta ce a ranta tana mikewa tsaye. Jiki ba kwari ta shiga dakinta tana jin kamar an zare mata laka. Wannan karon an mata fin karfi amma ba za ta yarda badi a kai Sani ba.

Kafin ranar tafiya ta shanya kanzo gari guda ta gyara masa. Man gyada ma ta soye shi da albasa ta kuma daka masa yaji. Tayi kuli-kuli, carbin malam, hallaka kwabo da duk wani abu da take tunanin zai ci daidai karfinta. Nasiha kuwa har ya soma gajiya da ji.

"Ka yiwa malaminka biyayya Abbati."

"Banda kwadayi ko dauke dauke."

"Idan an turaku bara ka ce na hana. Ga kayan abinci nan ina ta hada maka hatsi. Zan fadawa Babanka ya bawa malamin. Idan ya so in sun dora sanwa a dinga dibar maka."

"Abbati kada ka je bara fa. Daga cikin gidan wani zubin sai an zageka an zagi uwar da ta kawoka duniya kafin a baka kwantai."

"To Baaba" yake cewa ga duk nasihar da fadan nata. Har yanzu bai san ma'anar karatu da ake cewa za'a kaishi tare da sa'ansa dan yayan Inuwa ba. Yayyansa da suka tafi garuruwa daban daban yake sha'awa. Idan zasu zo suna dan kullo tsarabar birni su kawo. Kuma shi da Baaba ke son ya zama likita yanzu ne zai yi karatu na 'yan birni ya fara allura.

Mari tayi kuka sosai ranar da zasu tafi. Bai taba nisa da ita ba musamman saboda tsoron fadansa. Indai rigima ake yi da wuya ka ga Abbati a ciki. A gidan manya da yara idan ka cire mahaifansa da 'yan uwan babansa ana tsokanarsa da Abbati solobiyo. Rashin kuzarinsa yana daga cikin manyan dalilanta na son ya zauna a gida. Kazalika shi ne ya kara rura wutar kiyayyarta da zuwansa almajiranci. Banda iyayen sun riga sun farlantawa kansu kai yaransu maza akwai makarantu yanzu a garin nasu na ilimin islama.

Har soro ta fito tana kuka da zasu shiga a-kori-kurar da ta zo daukarsu. Hawaye take wani na bin wani tana ta nanata masa abubuwan da ta fada masa.

"Mu kuwa kamar tsinar namu 'ya'yan muke bamu san zafin nakuda ba." Cewar guda cikin faccalolinta.

Wata ta amshe da cewa "mu da aka jima ana daukar namu ba."

"Wai kuma a haka fa don dan fari ne. Wannan da Sani ne zai tafi sai tayi mana karamin hauka."

A gigice ta kalli amaryarta da ko haihuwar fari bata yi ba tana neman ballo mata ruwa. Ranta a bace ta ce,

"Bakin ki ya sari danyen kashi. Sani ba zai je bara ba da yardar Allah. Wannan ma don anfi karfina ne."

"Ai kuwa zan nuna miki babu dan da za ki fi karfinmu a kansa. Kai Inuwa.." Mal Sa'adu dake bayan matan ba tare da saninsu ba ya yafito kaninsa "tsayar da direban nan ka hado kayan Sani."

Ba Mari ba shi ma sai da ya razana.

Please Login or Register in order to submit comment