Reading FAUZAN COMPLETE BY SARATU MUSA MAMAN UMAR Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kikulamun da ita sosai yana kallon Fadeela wanda kanta yake kasa domin wata irin kunyar mom takeji, insha Allah lafiya kalau zaka samu ajiyarka yarona, sannan ta maida hankalinta wajen Fadeela tana murmushi tace tashi kije kiraka mijinki zai fita.

Ahankali tamike tsaye tabi bayansa har wajen mota tarakashi yana rungume da ita ajikinshi yana magana kasa2 yakamata innadawo asake sanyawa jikina nutsuwa ko yakikace, yakanne mata ido daya murmushi kawai takeyi domin tasani Allah yabata mijin da tunaninta baitaba kaiwa zata sami irinshiba arayuwa shiyasa take matukar kokarinta domin ganin tasanyashi farin ciki duk da tasani cewa bawai don yana sonta ya aureta amma bazata iya yimasa musuba tunda tafahimci abinda yafi so kenan agareta.

Sunjima sannan yatafi.
Yana shiga palon gidan zaune yatarar da ita daga ita sai rigar bacci alamun ko wanka bata yiba kenan, kallonta yake cike da mamakin meyahanata wanka matar da yasani bata taba zama babu kwalliya ajikinta yau itace zaune babu wanka.


Wani mugun kallo tajefeshi dashi kamar bawanta sannan tace daga ina kake, ina ka kwana?
Tajero mishi wandannan tambayoyin sai kace ba mijintaba shidai kalonta kawai yakeyi domin gaba daya Feezah tasauya bakamar lokacin da sukayi aureba, lokacin kafin suyi aure wata irin soyayya sukeyiwa junansu kamar zasu lashe Kansu akan so amma yanzu duk tacanza kamar ba itaba, yatuna wata rana sunje shaping ka yace tazabi duk abinda takeso kasa daukar komai tayi saboda kunya da nauyinshi da takeji sosai.


Katsemashi tunani tayi dacewa inamaka magana amma kayi mun shiru kana kallona, ajiyar zuciya kawai yasauke yace gidan mom nakwana Dama inason inzo inyimiki bayani amma bansan yadda zaki dauki maganarba, kallonshi kawai tayi tace fadi maganarka inajinka, dama don ingayamikine nakara aure ajiya saboda wasu dalilai dasuka faru wanda inaganin kina daya daga cikin dalilan dasuka saka faruwa wannan al'amarin.





Maman Umar CE.....
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: 🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈




*FAUZAAN*



*NA*
*SARATU MUSA*(maman Umar)





*41-45*






"Sannan idan har wannan layar ta bata duk abinda akayiwa waccen yarinyar to babu shakka zaidawo akan taki yar don haka akiyaye, to boka naji za'a kiyaye nan tazube masa nashi rabon sannan ta tafi.

Bayan tadawo daga wajen boka ko gida bata jeba saboda Umarnin boka dayace kar ayi wasa da wannan layar, bayan tagama yiwa Feezah bayanin da boka yayimata sai suka fara neman tayadda za'ayi susaka wannan layar acikin dakin Fadeela, saboda babu makulli ahannunsu, amma kibari tunda gobene za'ayiwa wannan tsinanar jere inyaso sai kishiga cikin yan jeren arika yinkomai dake yadda koda kinbukaci abarmiki makulli bazasuyi wani tunaninba zasu baki amma fa sai kinyi hakuri saboda nasan halinki bakida hakuri kokadan.
Bakomai mom zankiyaye tunda ai daga wannan shikenan zan taushi zuciya domin biyan bukatata,



Haka kuwa akayi lokacin da akazoyiwa Fadeela jere hannu biyu Feezah takarbesu har wasu nacewa ashe zasuyi zaman lafia tunda sunga Uwar gidan batada matsala balle kuma Fadeela dabatada abokin fada, bayan takawomusu abinci da lemu suna aiki suna fira kamar gaske, sai karantse babu komai aranta irin yadda tasake acikinsu suna fira.

Bayan sungama suka mikamata makullai part din saboda gobene su Fauzaan zasu dawo kuma mom tace suwuce gidansu tunda komai ankammala har lefen da suka hado duk yana can ankai mata abinta.




Yau jirginsu Fauzaan yake sauka misalin karfe biyu na rana wanda Feezah ce zataje daukarsu kamar yadda suka tsara da mom dinta saboda kammaluwar shirinsu domin dole sai taja Fadeela ajikinta kafin sufahimci inda aikinsu yasa gaba.

Feezah ta saka layar a karkashin gadon Fadeela dai dai inda bawanda zaisan da wani abu awajen.


Bayan tagama abinci mai rai da lafiya tashiga wanka domin batason tabata lokaci gara taje da wuri2, karfe biyu saura ta'isa filin jirgin domin tadaukosu acewarta kar suyita jiranta gara taje da wuri2.


Bata jimaba da zuwaba jirginsu yasauka pasinja suka fara saukowa daya bayan daya Can ta hango su rungume da juna, haka suka sauko wanda shibai ma kula da itaba saboda hankalinshi yana ga nutsuwarshi.

Bakaramin karfin hali tayiba ta danne zuciyarta amma jitake kamar tarufesu da duka saboda tsabar bakin cikin da yakecin zuciyarta, nan dai tabaiwa kanta hakuri sannan takarasa kusa dasu tana murmushin dayafi kuka ciwo.



Sun gaisa da Fadeela cikin fara'a kamar daman sunsan juna, haka suka dunguma suka shiga mota domin zuwa gida.

Bayan sunyi wanka sunyi sallah suka nufi gurin cin abinci, bakaramin mamaki Fauzaan yayiba dayafahinci girkin Feezah ne don yasan ba banza tayimusu girkiba akwai wata akasa, nan dai sukaci abinci suna fira wanda rabin firar duk tsakanin Feezah da Fadeela ne akeyinta shidai yasan ruwa baya tsami banza, komai dai meye yasan kansa zata kare.


Ringing wayarsa tafara yana dubawa yaga mom dinshice bayan sungama gaisawa tace zata aiko direba yakawomusu abinci, a a mom munci abinci yanxu haka kosauka bamuyi daga wajenba, mamaki mom tayi kamar yaya kunci abinci daga zuwanku har kasaka yar mutane shiga kiching? A a mom ba'ita bace tadafa Feezah ce tadafa, karuwa mamakin ta yayi Feezah fa kace? Dakanta tadafa maku abinci? Eh mom OK Allah ya kyauta sannan takashe wayarta.




Yau Yakama dakin Feezah Fauzaan yake, shikanshi bakamin kewarta yayiba amma sanin halinta nason abin duniya yasa wasu lokutan baya damuwa da lamarinta.



Bayan yadawo daga aiki direct part din Fadeela yanufa domin haka tsarin yake duk wanda ba'inda take yakeba yakan fara zuwa sugaisa sannan ya yuce inda yake, yana shiga wani kamshi yabugi hancinsa wanda baisan lokacin da ya lumshe idonshiba fesss yasaukesu cikin nata tana zaune tana karatun wani novel mai suna *KARYAR KADA TARUWA CE* shigowarshine yasa ta'ajiye karatun domin Fadeela duk abinda takeyi ko zatayi bayan na Fauzaan yake.


Sunjima suna kallon juna cikin tsananin so da shakuwa sannan ahankali tasauke idonta kasa tana wasa da yatsun hannunta, shima cikin kasala da tsananin bukarta yazauna kusa da ita yarike hannun da take wasa dashi yace shine duk yau baki nemenibako kayi hakuri bahaka bane cikin sanyin muryar tayi maganar to imba hakabane menene yasa duk yau baki nemeniba shiru tayi domin batada aksar dazata bashi, haka kawai takejin kanta cikin damuwa da rashin nutsuwar zuciyarta wanda batasan dalilin hakamba.

Kinyi shiru ina magana bakomai kawai kayi hakuri batasan lokacin da kalmar tafito mataba, jawota yayi jikinshi ya rungumeta yasaki wata ajiyar zuciya domin bakaramin missing dinta yayiba, ita kanta kwana biyu tayi kewarshi amma batason tanunamishi tunda tasani ba'ita kadaice dashiba, sunjima suna fira sannan yawuce part din Feezah.









*Don Allah kuyi hakuri masu cewa banayimusu typing dayawa wlh bazan iyabane shiyasa.*

*Gaskiya nagode da addu'arku gareni naji sauki insha Allah, Allahyabar zumunci*




Maman Umar CE....
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: 🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈



*FAUZAAN*




*NA*
*SARATU MUSA*(maman Umar)



*36-40*




'Lefe naji dagani Fauzaan yahadawa Fadeela komai set yasakamata, ga shegen tsada atamparta babu kasa da dubu talatin 30k, gaskiya kudi sunkoka awajen, tare sukayi siyayyarsu komai iri daya suka siya ita da Feezah, bayan sundawo hotel din dasuka sauka sukayi wanka suka shirya cikin kananan kaya shiyasaka wata karamar riga da wani tiri kwata sai kanshin turare yake, itakuma wata doguwar riga tasaka mai kamar abaya tayi rawdin mayafin rigar, sukaci abinci sannan suka sauko harabar hotel din suna dan zagayawa.



Ahankali suke zagaya wajen suna fira cikin shaukin so da qaunar juna, sunjima suna dan zagayawa sannan suka koma masaukinsu domin lokacin sallah yayi, bayan sun sake wanka suka dauro alwala sukayi sallahr isha sannan kwanta, jawota yayi jikinshi yana shafata cikin kwadaituwa da ita yace gaskiya yagamata inbada ajiya wannan wajen yashafa mararta yana kallonta,
Murmushi tayi kawai batace komaiba tana wasa da gashin kirjinsa dayawanta lifb ajikinshi.
Wasan datakeyi da kirjinshi shiyakara tsokano masa sha'awarta nan da nan yahade bakimsu yana aikamata da wani zazzafan kisses masu rikita zuciya da gangar jikinta, duk yarudamata jiki da kalar wasanninsa wadanda yariga yasabamata dasu harmantawa take dacewar yanada wata matar.

Basu suka saurarawa junaba saida suka sami natsuwa sannan yasauka akanta yana wasa da gashinta, kallonta yayi cikin tsananin so yace agaskiya babu abinda zancewa Allah domin yagamun komai dayabani ke amatsayin matar aurena, saboda kedin bakaramin natsuwa nake samu idan inatare dakeba Fadeela, ke din tadabance ko acikin mata shiyasa nazabeki domin kizamemin sanyin idaniyata wanda nasan haryanxu mamaki kikeyi yadda aurenmu yakasance batare da kinada masaniyaba.




Nasan zakiyi mamakin cewar nine nace kenazaba amatsayin matar aurena wanda bakomai yasa hakanba illa najima kina burgeni akan yanayin rayuwarki maicike da tsari da natsuwa.
Najima ina sha'awar halayyarki shiyasa nake yawan zuwa gidanku badon komaiba saidon inyi takallonki wanda inba gaisuwaba babu abinda yake shiga tsakaninmu, amma idan naganki jinake kamar inhadiyeki saboda tsananin son da nakemiki wanda kebakima wannan tunanin tunda bantaba nuna miki alamun cewa inasonkiba.




"Kallonshi kawai Fadeela take domin bakamin mamaki tayiba jincewa yajima yana sonta amma koda wasa baitaba nuna mataba, wata irin ajiyar zuciya tasauke tace to yanxu inda ace akwai wanda nakeso fa kamin kazowa Abba da wannan maganar?
Murmushinsa mai burgewa yasakarmata sannan yace cikin tsokana ainasan duk wanda zakiso koyace yana sonki abayan soyayyata yake domin nasan duk nafisu sonki🀨
Tayi dariya kawai batace komai ba sunjima suna fira sannan sukayi wanka suka kwanta.




" Mom din Feezah ce zaune gurin boka da'u tana yimasa bayanin yadda takeson araba auren Fauzaan da Fadeela, kuma aciremasa sha'awar kowace diya macce sai Feezah kawai yake so.
Bayan boka da'u yagama jin bayanenta yafara sulkullenshi can yadubeta yace gaskiya wannan auren baza'a iya rabashiba domin idan har akace za'a raba auren to kema auren yarki yamutu domin bakaramin so yakeyiwa matarshiba kuma duk abinda za'ayimasa ba lallai yayi tasiri akanshiba sai dai ita yarinyar zamu iya yin nasara akanta, amma itama ba lallai bane domin iyayenta suna saye kansu.

Wani irin gumi Mom tashafe dayake tsiyayomata a fuska tace to yanzu boka meye mafita kenan domin gaskiya banason yata tazauna da kishiya, kar kidamu akwai wata laya da zanbaki asaka dakin da amaryar zata zauna wannan layar ayi matukar takatsantsan da it a domin idan akayi wasa da ita zata iya bacewa,
Aikin wannan layar shine bazata taba barin mijin yasadu da itaba saboda jizatayi duk lokacin da yace zai sadu da ita suma zatayi amma zairika shiga dakinta kuma zaiyi komai da ita saduwane kawai bazaiyi da itaba.




*Fans don Allah kuyi hakuri zakujini shiru kwana biyu saboda wani uzuri daya tasomin amma insha Allah zanazama free zakujini nagode.*





Maman Umar CE ............
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: 🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈





*FAUZAAN*



*NA*
*SARATU MUSA* (maman Umar)





*31-35*



*Gaskiya inajin dadin kulawarku ga wannan littafin Allah yabar zumunci ameen*



'Daukan wayan ta tayi takira mom dinta cikin tashin hankali domin tanada tabbacin muddin Fauzaan yayi aure tofa karyarsu takare domin ita kanta tasani dabazarshi suke rawa.
Bayan mom dinta tadauki waya kuka kawai tafashe dashi cikin kuka tace nashiga ukku na lalace, hankalin mom dinta bakaramin tashi yayiba jin irin abinda diyarta takecewa, meyafaru Feezah waye ya mutu inma mutuwane dasauki wlh cewar Feezah, to kiyimun bayani mana meyake faruwane? Wai ni Fauzaan zaiyiwa kishiya! Wani irin dariya mom tayi tace haba kekuwa meyasa zakiyimun irin wannan wasan, wlh mom bawasa nakeba yanxu yake gayamun daman jiya tunda yafita daga dakina lokacin dayace inbashi kaina nace sai yabani wannan dukiyar bankara sakashi acikin idonaba sai yanzu yashigo yake gayamun wai yayi aure kuma wai duk laifinane cikin tsananin tashin hankali take maganar.



Shiru kawai mom tayi domin maganar bakaramin girgizata tayiba wai yayi aure hummm can tanisa tace kinajina ko Feezah inason kikwantarda hankalinki kisaurari abinda zangayamiki yanzu, shiru Feezah tayi tanatsu tana sauraren abinda mom dinta zata gayamata domin tasha alwashin ganin bayan wannan auren da zata kira matacce.




Inason kikwantarda hankalinki kamar babu komai aranki domin musamu damar gudanarda shirinmu akansu, kinsan yaki Dan zambane to inason kinunamusu babu wata damuwa aranki indahali kijawo amaryar ajikinki yadda aikinmu zai tafi dai2 yadda muke sonshi, domin nikaina nadauki alwashin ganin bayan wannan auren.

Sai sannan hankalin Feezah ya dan kwanta domin tasan halin mom dinta idan tace zatayi abu babu sai ta aikatashi, bata mantawa suna yara duk lokacin da Abbansu zaikara aure itace take lalata komai daga karshe matan suce basayi, dom haka yanzuma tasan komai zaizomata da saukine, sunjima suna tattaunawa sannan sukayi sallama hankalin Feezah ya kwanta domin ganin take tagama da wannan matsalar, wanka tayi tadauki motarta tabar gidan.





Wata irin soyayya Fauzaan yake nunawa Fadeela kamar yamaidata ciki saboda yadda yake jinta ajikinshi da zuciyarshi, bayasaon abinda zaisa tayi nesa dashi shiyasa itama take kokarin ganin tafarantamishi duk da irin yadda takejin kunya idan suna part din mom bata sakewa dashi sosai amma tana kokari sosai,
Bakaramin dadi mom take da irin kulawar da take ganin fadeela nayi da tilon dan taba domin bakaramin so take masaba, shiyasa take addu'ar Allah yasa kar fadeela tayi hali irin na Feezah duk da tayadda da yarinyar amma ba'a shaidar Dan yau.



Fauzaan ne zaune part din mom suna fira domin fadeela tayi bacci tana dakin mom, kallonshi mom tayi tace yakamata kafara hadawa Fadeela lefenta kafin ta koma gidanka tunda kaga bawasu kayane tazo dasuba tun wadanda kasiyomatane ranar da zakuzo, kuma tunda angama gyaran gidan bawani lokaci za'a daukaba inason kaje Dubai da ita kuyi siyayyar a can zaifi inyaso kuna dawowa sai kuwuce gidanku.

Murmuahi yayi yace badamuwa mom yadda kikace haka za'ayi saboda nikaina nafi son ina waje daya da matana, insha allahu jibi zamu tafi Dubai ahado lefen, abindama yasa bazamuje gobe ba saboda ita Fadeela batada Visa shiyasa , to babu komai Allah yayimuku albarka yabaku zuri'a dayyaiba ameen cewar Fauzaan, sannan karka manta da uwar gidanka kasan anayin kayan fadar kishiya don haka itam tanada hakki kahado mata nata lefen, yayi dariyarsa mai burgewa yace kai mom ai sai dukan yayi yawa cikin ahagwaba yayi maganar, itama dariya tayi tace yaro angayamaka auren mata biyu wasane shima dariyar yasakeyi yace inafa aigashi nagani sunjima suna fira sai da akayi kiran sallar azahar sannan yawuce masallaci.







Maman Umar CE.........
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: 🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈




*FAUZAAN*

*NA*


*SARATU MUSA*(maman Umar)




*56-60*



"Wlh mom cikine da ita yanxu haka maganar danake miki daga hospital muke, cikin tsananin tashin hankali take maganar, kikwantarda hankalinki Feezah kinsan wannan bawani abun tashin hankali bane tunda kinadani, kuma kinsan sai inda karfina yakare indai akan matsalarkice, don haka inason kisanyawa ranki sunan wannan cikin matace.


Sai yanzu hankalina yakwanta my mom don Allah kiyi wani abu akai wlh jinake kamar inje inshaketa tamutu kowa yahuta, wlh bantabajin natsani wata halitta ba kamar wannan, kina haukane zakice kije kirufeta da duka aida kema kinsan makomar abinda zaki aikata bazaiyi kyauba.

Kawai kibar komai ahannuna kici gaba dayimusu biyayya har komai yazama namu, to mom nan sukayi sallama sannan suka ajiye wayar.



Zaune take saman bed dinta bayan tafito daga wanka tana tunanin irin son ta takeyiwa mijinta jinin jikinta, kamar ta hadiyeshi takeji aranta bakaramin kauda kai takeba aduk lokacin da zaije part din Feezah, hakuri kawai take tana danne kishin mijinta , duk da tare tagansu amma jitake tafi Feezah son shi, jintayi anrungumeta kamshin turarenshi tashaka batasan lokacin da talumshe idontaba, fuskarshi yamatsa dai2 tata hancinsu yana gugar juna yace mekike tunani natsuwata? Meye damuwarki wanda yasakaki acikin tunani mai zurfi har haka bayan kinsan nidin banason abinda zaishiga tsakaninki da farin cikinki, kigayamun mana kallonshi take kamar wani zai kwacemata shi, iska yahura mata cikin idonta yace wannan kallonfa kamar za'a rabamu, taji kunya sosai tasauke idonta kasa tana wasa da yatsun hannunta.



Ahankali tayi magana cikin natsuwa da sanyin muryarta, inason inje gida tun sanda kadaukoni bansake ganin yan gidanmuba.


Dariya yaiyi sosai sannan yace wannan shine yasa kike tunani? Shiru tayi domin dai tasan bashine ba amma dakunya tace masa tunaninshi take, can dabara tafadomata takaleshi tace kwana biyu ina tunanin mamana shiyasa, yanzunma murmushin yayi domin yagane kame 2 kawai take tunaninshine fal aranta wanda shikanshi bakaramin so yake mataba, har addu'ar yake Allah yabashi ikon yin adalci atsakanin su, kalonta yayi yana murmushi sannan yacemata zaki kiyiwa malam godeya ko? Tunda auren daya dauramiki kina kuka yayi dadi harda tsaraba zaki kaimasa, kukan shagwaba tafara tana dira kafafunta akasa nidai wlh a a tana sanya kanta acikin kirjinshi taboye.


kishirya insaukeki gida tund kinji sauki inyaso da dare inzo indaukoki, nan da nan tamike tsaye tamanta dabatun wata kunya domin gaskiya batayi tunanin zai amince da taje gida yanzuba kowata daya batayi da aureba, abinda batasaniba shine Fauzaan neman duk wani abinda zaisakata farin ciki yake domin itaba yasakamata duk da yasani bawai zai iya biyanta bane amma yanason shima yasanyata farin ciki kamar yadda take sanyashi.




'Boka aikinka yayi kyau sosai shiyasama kaga nazo yanxu domin ita yar tawa tagayamun jiya a can hospital suka kwana saboda suman da amaryar tayi, to amma sai wani sabon tashin hankali yatasomu gaba waton bullowar cikin da ita amaryar take dauke dashi wanda bakaramin barazana bane agaremu muddin mukayi sake tahaifi abinda yake cikinta,
Kallonta boka da'u yayi da kyau sannan yace bari muduba mugani, nan yafara sulkullenshi na tsafi can yadago idonshi dasukayi jajir yacemata gaskiya bakaramin tashin hankali bane taba wannan cikin domin naga taurarin wannan yaron dazata haifa masu tsananin haskene wanda baniba, duk duniya babu wani boka da zai 'iya yimuku aiki akansa yayi nasara, don haka ina maibaku shawara kurabuda wannan cikin tabbas sai anhaifeshi kuma zaitaka kasa intakaicemiki bayani wannan yaron dazata haifa shine zai zamo haske arayuwar mahaifansa kuma garkuwane agaresu, don haka nahaneku da taba wannan cikin idan kuma bakiji shawarar da nabakiba kina iyayin duk abinda kikeso amma nidai baburuwana.


Wata irin zufa mom tashare saboda tsabar tashin hankali datasami kanta aciki wanda atarihin rayuwarta bata taba saka abu agabantaba wanda bataci nasara akanshiba sai wannan, shiru kawai tayi ana sauraren tatsuniyar da boka yake gayamata wanda ita kanta batasan inda zata aza wannan soki burutsun ba balle kuma Feezah.

Nan dai tabarwajen boka tanufi wani qauye shima akwai wani tsohon boka dayayi yayin yimata aiki tun da jimawa wanda shi wannan bokan aikinshi kamar yankan wuka yake duk abinda kazomasa dashi bazaice a aba idanma sokake akashe maka mutum wannan karamin alhakine agurinsa domin bazaka bar wajenshiba mutumin zai mutu, amma shikuma sharadin aikinsa shine zaikwana da macce tsawon sati biyu idan bukatarta tabiya, idan kuma bukatarki tabiya baki dawoba asirinki zai tonu kowa yasan irin abinda kike aikatawa, sannan za'ayita firgitaki har sai kin mutu.

Abinda yasa tabar aiki agurinsa wancen lokacin shine,
Wata rana tazo wajenshi akan tanason akashe mata matar da mijinta zai aura domin tayi duk yadda takeyi domin tawargaza auren amma abu yaci tira shine tazo domin agama da matar kowa yahuta, bayan yagama jin bayaninta sai agayamata wannan ai maisaukine amma ga sharadinshi idan bukata tabiya zaiyi sati biyu yana amfani da ita idan har ta'amince shikenan aikinta zaitabbata yanxunnan, nan da nan ta amince da bukatar boka.

Bayan bukatar ta tabiya shima yace saura nashi biyan bukata, haka kuwa akayi kullum zatazo yayi jima'i da ita har lokacin da boka yadiba yayi wanda duk lokacin da boka yakwanta da ita bakaramin wahala takeba domin bakaramin mutum baneshi irin mazan nanne masu manyan kaya ga tsayi ga girma wanda inyana jima'i da kananan 'yan mata wash har suma sukeyi saboda azaba.
Wannan shine dalilin dayasa tabar aiki agurinsa , sai kuma yanxu zata koma wajensa.




Bakaramin murna Malam yayiba da yadda yaga Fadeela takomaba, alamun tana cikin kwanciyar hankali yaji dadin hakan sosai wanda har farin cikinshi sai da yakasa boyuwa, sunjima suma gaisawa da Fauzaan sannan sukayi sallama yawuce wanda tuni fadeela tashige cikin gidan.


Acen ma bakaramin mamakin canzawar tasukayiba wanda duk wanda yagamta yasan tana cikin jin dadi da kwanciyar hankali, bayan sungaisa da mutanen gida bangarensu tanufa cike da dokin son ganin mamarta wadda kunya da kawaici yahanata fitowa tarbarta.

Dasalama tashiga zaune tasameta awajen dafa abinci tana aiki dafa abincin rana, bayan sungaisa akashiga firar yaushe gamo nan Fadeelah tafara mitar wai babu wanda yaje gidanta duk anmanta da ita tunda yanxu babu mai son ta, dariya mama Asmau tayi rin tasu ta manya tace to inbanda abinki fadeela taya dazuwanki gidan miji sai afara sintiri, yanxumma nayi mamaki danaji ana zancen zuwanki gidannan, sun jima suna fira irin ta da da mahaifi kallonta mama asmau tayi tayi murmushi domin tagane yar tata tanada shigar ciki don haka tace inafatan kina kulawa da kanki sosai domin kinga dai yanxu bake kadai bace, taji kunya sosai tace eh mama don takauda wannan zance tace mekike dafa mana ne mamana, haka tawuni cikin yan uwanta har dare sannan yazo daukanta suka wuce.






Maman Umar CE............
[10/27, 11:09 PM] Sarah Friend: 🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈




*FAUZAAN*




*NA*

*SARATU MUSA*(maman Umar)




*46-50*




'Da sallama yashiga palon tana zaune taci kwalliya kamar mai shirin zuwa faty koda yake yasan Feezah game da kwalliya baya mamaki, shidai halintane kawai bayaso amma zaibimata yadda yakeso kodon azauna lafiya tunda yafahimci hakan atare da'ita.

Amsa masa sallamarshi tayi sannan tayimasa sannu da zuwa wanda ita kanta tamanta rabonta dayimasa sannu da zuwa, shima amamakance yake kallonta sannan yayi murmushi yauwa sannu da gida.
Wanka kawai yashiga abinda yakara bashi mamaki komai yasameshi yadda yakamata tahadamishi ruwan wanka da turaren wanka komai dai baisan sanda yayi dariyaba cikin ranshi yace yarinya wayagayamiki aida kitsaya har mutsadance inna biya sannan yasake wata dariyar sannan yafara wankanshi, bayan yafito zaune yasameta saman bed dinshi tafito masa da kayan shan iska tunda bafita zaiyiba, mai take shafamasa amma zuciyarta nacan tana yawo wato yadauka ko na hakura da cin amanar dayayimun shiyasa yawani saki jiki hummm zakazo ahannu wlh duk sai nafanshe wahata domin bazakaci bulus ba, katsemata tunani Fauzaan yayi dace inamaga kinyi shiru, murmushi tasakarmishi mai burgewa sannan tace kayi hakuri my baby nasan nasabamaka azamammu amma inason kabani dama akaro na biyu lallai zakayi alfahari da ni, duk maganar nan datakeyi cikin kuka takeyi domin takara nuna masa nadamarsa.


Rungumeta yayi ajikinshi domin bakamin tausayi tabashiba, kikwantarda hankalinki my dear na nidama banrikeki araiba saboda nasan daman wannan ba halinki bane shiyasa bansakashi arainaba, don haka kidaina kukan haka karkiyimun asarar hawayennan masu matukar tsada awajena, share mata hawayen yake yana kara lallashinta saboda tasaki ranta, tausayinta yakeji sosai domin baiyi tunanin zata kwantarda hankalinta hakaba lokacin da yayi aure amma gashi har yanxu bata yimasa maganar aurenshiba.



Zaunar da ita yayi sannan shima yazauna yafuskanceta domin yanason suyi magana mai mahimmamci, waton Feezah bakaramin mamaki kika baniba game da halin da kika nunamun wanda banyi tsammanin haka daga wajenkiba duba da irin rayuwar tashin hankalin da muka tsinci kammu aciki wanda haryanxu mamaki nakeyi, duk da ba abun mamaki bane amma kinshayar dani mamaki sosai narashin tankamin da bakiyiba alokacin da kikaga Fadeelah amatsayin kishiyarki sai ma wani tarin mamakin dakika bani shine lokacin da kika rungume fadeela afilin jirgi, sannan kikayi muna girki wanda nikaina rabona da inci girginki har namanta.




Wani shu'umin murmushi tayi wanda sai da Fauzaan yaji ajikinshi har jijiyarshi tana harbawa saboda tsabar shigarshi da murmushinta yayimasa, sannan tace haba mijina kai kanka kasan ina sonka wannancen lokacin ma danayimaka rashin kunya wlh sharrin shai danne, shiyasa nazauna nayiwa kaina fada, kamar yadda kace nice sanadin aurenka tabbas nidince domin dana karbi bukatarka daduk hakan bai faru daniba, nasan nice nacutar da kaina tomexaisa inkara tayar maka da hankali? Aikaga da banyiwa kaina adalciba, nagodewa Allah da ba mummunar hanya kafadaba dasai hakan yafi damuna bisa ga zargin kaina da laifin.


Matukar tausayi fauzaan yatausayamata domin yasan Feezah da zafin kishin tsiya amma tahakura, karki damu wannan kaddarace daga Allah koda bada laifin da kika aikatamunba in Allah yakaddaromun

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment