Reading So Makamin Cuta Complete By Surayyams Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ok
Naji ..kanada gaskiya kaima just calm down

No mummy dont tell me to calm down
Wannan Ba karamin barazana bane ke tasowa mana baki daya
Gashi nasa an bincika min wanda ya turo videon nan har yanzu ba asamu komi akan sa ba
Wht if ba shikadai bane yake da videos irin haka
In ya tura ma su lawyer ashween fa shikenan
Wallhy tamu ta kare "

Shiru duka sukayi suna kallon sa kowa da abunda ke ransa..

Ya cigaba
Yanzu sai ankai zahida prizon zaki ga yadda mutane zasu fara kwakwulu asirin mu suna tonowa tunda na gaza yanzu
Ya karashe maganan sa a raunane fuskan sa dauke da damuwa

A hankali madam hidayat ta dafa sa cikin rarrashi" Bakomai ,kai dae ka cigaba da abunda kake yi
Ni na san me zanyi bari na kira minister tace tana dialing wayar ta
Ko da ta kira yayi ringing sau uku ba daga ba
Tasan akwai wani makar kashiya dan haka ta hakura bata sake kira ba

Jim tayi sannan ta dan Dan tabe baki tace hmmm duniya kenan
Dama inbakayi bani waje
Amma ba komai zamu hade ta wani wajen tafada tana kada kai

Jin hakan ya sa zahida fashewa da wani sabon kukan
Don tasan shine hope dinsu na karshe yanzu kam
don duk ashween ya bi ya toshe musu hanyar samun alfarma

Dama minister Shi kadai ne inya ce akashe shariar zai iya tabbatuwa tunda alkalin case din dan gidan sa ne"
Amma sai gashi bai daga waya ba ..

Zahida kuwa Kuka sosai takeyi tana tunani kala kala a ranta
Bakin ta sai maganganu ya ke fitarwa ita ba zata je prison ba
" ga ta kyakkwa mai aji da kudi,
Kamr zararrriya hakan nan"
Ganin abun na nemar zautar da ita ne ya sa duka suka dukufa suna bata hakuri
Amma ena sai bori take tana rusa ihu ..har baban ta mr abdul fatah saida ta tuna ranar

Mrs rod da duniya gaba daya ta tsaya mata chak
Abun ma mamaki yake ba ta
Ita ne hakan yake faruwa da ita" tace mutane nawa na kashe kuma nawa na batar na murkushe sai gawar wata banzar yarinya ne zai daga mim hankali?

Cikin nazari tayi nisa
alaman tana neman wani mafitar sai sake sake take
Jamal da tuni ya dukufa wajen ba zahida baki
Baiji sallamar da aka yo daf da su ba
" Ash?
Tace tare da Dago kai tana binsa sa kallon mamaki

A haukace ta ture jamal ta yo kansa "Ashween pls dont send me to prison ta tsuguna gaban sa tana rirrrike masa kafa cikin kuka
Tuni zuciyar mrs rod ya soma harbawa tana takaicin saurin karayar zahida akan al'amarin
Kallon kallo jamal ke binsa da shi
Kana ganin kasan ji yake kamar ya shake shi
Don shi ba ta zahida kawai yake ba
Har da bata masa suna da zubar masa da kima da shariar tayi yake jin a ransa
Yya haka? Ka zo ka karasa kashe min yata ne? ,, toh ga fili go ahead
Mummyn tafada tana masa mugayen kallo

Baice uffan ba shi dai yana tsaye
Gamshin jikin sa sai ratsa wajen yake fuskaN sa normal ba alaman wani damuwa

Malam kafadi abunda ya kawo ka in babu kuma just Get out,
bamu bukatar ganin ka jamal ya fada rai abace

Itako zahida kuka kawai take rike da kafar sa tana furta pls..pls ..
Dan karamin murmushi ya sauke kafin ya tsuguna daf da fuskan zahida
Ya kure ta da ido ..da wuri ta sauke kanta gwanin tausayi tana sheshsshekar kuka
Bata hankara ba jitayi ya dago ta sama daf da shi tana fuskan tan sa
" ya isah haka beauty queen its ok..
Ba wanda zai kai min ke prison i promse

Wani dum duka suka ji a kunnen su
Barin ma zAhida data yanke kukan chak tare da dago kai tana kallon sa
Dauke da wani sabon murmushin ya gyada mata kai alaman da gaske yake
sannan ya sa hannu yana share mata hawayen ta
Cikin wani irin tsananin farin ciki ta kankame sa ta kasa cewa komai sai kuka
Mrs rod da jamal da abun ya matukar dauree musu kai suna gefe kowa na nazari
Jamal ne ya soma tambayar sa
" meyasa ka ke so ka zautar da ita ta hanyar mata karya
Bayan kowa yasani kai kake neman jefa ta a prison da hannun ka ?
Ashween Bai jira ya sake cewa wani abun ba ya ce
Kuma nace ba zata je ba yanzu ko?

Meyasa ? Mrs rod ta katse sa itama

Dago zahida yayi a jikin sa ya ya kalleta yace sabida na yafe mata
And she's not spending anoda minute anan wajen
wani kallo suka bisa da shi na mamaki da daure kai
Dan karamin scoff yyi yace
Amma its fine in kuna da plans dinku na cire ta sai na bari ya fada sounding ko ajikin sa
'
Ba musu mrs rod ta ce no, ba komai
Ya fitar da ita din ..ta dakatar da jamal da ga yin maganan da yake shirin yi

Kamo hannun ta yayi Tare suka fice zuwa offishin babban mai kula da wajen
Da shike zallan manya ake kawo wa wajen ba takuri sosai sannan komai a tsaftace yake kamar suna muhallin su

Jamal da ya kasa amincewa da sauyawar ashween din lokaci guda bai jira ba ya bi bayan su
Haka ya dinga bibiyan su yana ganiN yadda ashween yake da mutanen alfarma yaga yadda ake masa biyayya

Nan take aka har harda aka rubuta bail ma zAhida
Daga nan duka suka rusuna suka kau da wani tunanin aran su ..musamman mummyn su mrs rod data gama bari akan hala wani sabon cin mutuncin ya kunso musu yake wasa da hankalin su

Da shike karfe 4 saura ne na yamma haka ya sa zahida a motar sa don tsam ta rike sa kamr ba shi bane ya jefa rayuwar ta a tsananibcikin kwanakin
Nan ya ja ta zuwa asalin mansion na rodriquez wato family hause dinsu kenan
Su jamal da mrs rod suna biye da su
Har ya tallafo zahida ya shigar da ita har cikin gida
Murmushi kawai yake yi amma zuciyan sa da idanun sa sun kasa boye garwashin wutar da yake ci aran sa

Jeki shirya baby,yafada yana mika ta ma masu aiki
Kamar bazata sake sa ba haka take kallon hannun nasa
Dan shagawabe fuska tayo tace
Kar ka tafi pls

Of cous ..take your time
Ya fada da dan light murmushi
Nema wa kansa waje yayi ya zauna
Already jamal da mrs rod suna zaune
Shiru ne ya ratsa wajen
Kafin jamal ya ce
Me za a kawo maka?
Ruwa ,,yace a takaice ba tare da ya kalle su ba duka
Dan gyaran murya mrs rod tayi cikin nitsuwa ta kalle sa
' na kasa fahimtar komai
Ashween
Meya sa kake taimakon mu ?
Na dauka laifin da zahida tayi is unforgivable naji ance budurwar ka ta kashe ko?why did u cme bak for her? Mikewa tsaye tayi
Ta cigaba da magana "pls kafadi abunda zan maka, nayi alkwari zanyi
Amma kar ka jefa rayuwar yata cikin hutsuma
Na tabbata zahida batayi kisan nan ba ..bata boye min komai.sannan ta juyo ta maida kallo kansa alamn tana jira amsan sa

Ko daga kansa baiyi ba alaman duk maganan data keyi bai bada hankalin sa ba
kusan minti 2 yana shiru chan daga baya ya dago kai ya kalle ta
Dan takaitaccen numfashi ya ja
Sannan yace "
Ba laifin ki bane mrs,
Na san ba zaku yarda da ni ba
Gashi bana maimaita magana sau biyu"
in kinji ni dazu shikenan take it or leave it..

Zahida ce ta karaso wajen cikin light gown na material ba ko kwalliya fuskan ta sai tayi looking very innocent

Yadda ta ke karasowa zaka san sharp sharp ta kimtsa ta sauko don taga meke faruwa don itama har yanzu bata gama amincewa da sauyawar ashween din ba

Bai karashe maganan sa ba, ya mika mata hannu
Ba musu ta zo ta zauna daf da shi
" murmushi mai dauke hankali ya sakar mata sannan ya juya ya kalle su jamal da mrs rod
' zahida masoyiyata ce
Ni din nan zan iya banbance haka ba sai an fada min ba"

I know its just a coincedence ta kashe min budurwa amma ba dagangan tayi ba, ya juya ya kalle ta yace
Na so na yafe miki tuntuni
Ai nasan mutuwa na Allah ne
Ke baki isa ki kashe tania ba in kwanan ta bai kare ba, am i right? ya kalle su duka

Gyada kai kawai tayi
Kowa na binsa da ido
' duka biyu kun min laifi don na hanaku wannan fadar naku "amma kun ki ji na
sannan
ke zahida har da hada party ki boye min?

Shiru tayi ta sun kuyar da kanta tana mus mus zata fitar da hawaye
Yanzu ne zuciyar ta ke nuna mata ashe yafi ta hangen nesa daya ke cin zarafin ta akan tania don su dena gaba

Itama mrs rod fadan ganin ido ta shigayi ma zAhida" ai kinga ashe ba laifin sa bane duk abunda ya same ki ta karashe maganan ta

Ashween ma yace 'Toh kinga ga Idan ban rufe ido na na karbe wa tania hakkin ta ba duniya zata zage ni i hope u understand? ya maida maganan ma mrs rod wacce ta tsaya tana kallon sa

Haka ne ,,amma meyasa ka fasa qudirin ka na karba ma tania hakkin ta yanzu?
Mrs rod tace

Da kamar bazai amsa ba sai yace "Huhmm bawai na fasa bane

Dum suka ji a ran su lokaci guda barin ma zahida
Nan ya cigaba da cewa'

Zan taimake ku ne muddin zaku bani hadin kai
Don ni ma bana son akai beuty na prison..u dont derserv dat
Ya dan tallafo fuskan ta yana kallo
Gyada kai kawai tayi tana murmushi da kyar

Share mata hawaye yayi yace
Ena jinku ...the choice is yours
In zaku bar wannan a matsayin sirri tsakani na daku
Fine..
Afterol duk randa kuka fallasa ku sani zahida zata je prizon ba fashi"

Na amince jamal ya fada ba tan tama
Haka ma mrs rod

Ba yavo ba fallasa yace good
Abun shine ,zan soke duk wani shaida da zai bayyana zahida a matsayin suspect

Jamal zai budi baki ya dakatar da shi da cewa na sani
Kar ka damu da videos
Ena da details din duk wanda yake dashi da wyanda suka je partyn
Duk zanyi handling "
Kai abunda nake so da kai shine
Ka ajiye case din gobe ka sanar ma media
Ka jannye , ni zan aiko da nawa lawyer amma
Mrs rod zaki amsa lawyer ki ce
Agree?
Ya daga ido yana kallon su duka

Zufa ne mai zafi ya keto ma jamal
Wani jiri yake ji" yanzu haka zan tarwatsa career ta da kima na akan ceto rayuwar zahida ?

Wannan ya ma san me yake nufi ga babban lawyer iri na yafito media yace ya janye case ?
Damn it! Yace a zuciyar sa

Mummy i c...

Shhhhh jamal..don t be selfish
Rayuwar sister ka ce anan fa
in ma kana tunanin kimar ka ne da aikin ka
Ai shima budurwan sa ya rasa amma kuma ya zo yana taimakan mu '
Bana son jin wani korafi

Ranshi baiso ba ,amma dan dole ya ja baya ya tsaya
.bai kara cewa komai ba

We are in ,..ta juya ta fada ma ashween

Dan tabe baki yayi yace ok done deal
....Infact yau na bawa dan uwar ku jabir aiki akan haka
Nasan insha Allahu komai ya tafi dai dai ..

Jabir ya san da plan din nan kenan ?
Yes zahida ,ya sani..shi na fara haduwa da shi ya bani labarin komai
Nd I felt sorry fr yhu,.in kika duba meye ma duniyan nan ne?

Kifi kifi take da ido tasa fuskan tausayi tace
"kayi hakuri
Dan Allah ka yafe min . I so much love you ash fatan im still d same a zuciyan ka?.

Murmuswa kawai yayi kafin yace karki damu.
Just don make it look like ena tare da ku kinji?

A hankali tace Trust me...

Murmushi mrs rod tayi itama tana kallon su tace baka da matsala
Zaka samu duk wani hadin kai daga wajen mu
Na maka alkwari

Baice komai ba ya mike tsaye yace toh
Na barki lpya ...ya ma zahida ligh peg a kuncin ta ya fice abunsa
Sosai abun ya basu mamaki
Gani suke kamar a mafarki
Banda jamal da ya san nashi tagama karewa yanzu kam
Sai jimamin yadda gobe zata kasance masa yake

Bayan kwana uku
Komai ya soma sauki
Wa su zahida ashween sai dada shiga jikin su yake yi musamman mrs rod da gaba daya taji yana burge ta
Ena ma ace ita ta haife sa ?
Lawyr ne mai ji da ilimi da kwarewa Ashween ya hada su da shi don haka
Jamal ya kasa samun sukuni a zuciyar sa
Kishin abun na matukar damun sa
Ga maganganun banza da ya ke artabu da su wajen yan jarida da abokan gaban sa

Ganin hankalin mummyn nasu da zahida ya komA Kan sabon lawyr ya sa shi jan jikin sa kwata Kwata

A daki yake wuni yasha wannan ya sha wannan
In dare yayi ya sa akawo masa mata ya kwana dasu abun sa

A haka a haka kafin ranar shiga kotu ,,ashween ya zama zuma wajen mrs rod
Bata jin maganan kowa sai nashi
Musamman Da ya nuna mata zallan gaskiyar sa akan al'amarin

Duk da yadda zahida ta so ace tana tare da shi
Hakan baiyuwa
Gashi yanzu bata iya bacci tsaban radadin son shi da take kwana da shi ta wuni da shi

Ranar da aka shiga Kotu
Komai kaMr yadda ya tsara musu suka bi
Alkali ya wanke zahida tas akan cewa tania ta mutu ne sanadiyar samun wani choke a breathing tubes din Ta , sannan ya kori karar

Murna wajen su ranar kamar yaune suka soma shaRia suna lashewa

Musamman ma zahida data ga tashin hankali da bata taba ganin irin sa

Da daddare bayan waje ya lafa Kwance mrs rod ta same ta tana chat da alaman ashween ne kan layi " murmushi ta sakar mata ta dana shafar suman kanta
" komai ya wuce zahida na

Mirmshi itama ta mayar mata tace yes mummy
Komai ya wuce
Ya kamata na gwada ma yaron nan godiya ta koya kakice?

Of cous, nima nayi tunanin haka
Kinsan ma wani abu kuwa zahida ?
Yanzu nake ganin abubuwan da kika dade kina gwada min akan sa
Hes so matured" wani abun in yanayi sai naga kamr jini na ne ke bin jikin sa zahida

Dan dariya zahida tayi kafin tace
Mummy kenan
Kawai kice electric shock din ya kama ki kema
Ashween ya iya sace zuciya mummy
And im not letting him go
Murmushi muumyn itama tayi tace
Sosai ma ,zanso na malleke sa a nan familyn nan
Don kuwa we definatly need him..

Yes ,mummy
Uhm. Kin kuwa duba
jamal? Naga kamr baijin dadi ko court baizo ba fa

Hmmm kyale shi
Nasan matsalar sa
Ai yanzu baida wani amfani awaje na sosai
So i dont have his time
Yanzu so nake ki dage ayi ayi bikin nan
Na tabbata ashween is part of rodriquez kinji beauty na?

Dan shiru tayi tana jimamin maganan jamal din
Amma saita basar ta sake murmushin Yake tace toh mummy

Nan sukayi sallama ta fuce abun ta

Ta shi tayi ta sulale ta nufi site din jamal din
Jin karar music na tashi ya sata turo kofar a hankali
Da sauri ta kau da kanta amma ena abunda ta ci karo da shi ya tsaya mata a ido

Ko ajikin sa sai riding din ta yake
Ga dayar budurwan a gefe tsirara tana kan lashe sa
Ganin ba kula ta zAiyi ba ya sa ta fice ta bashi guri ya cigaba da abunda yake yi

Dan tabe baki tayi ,
Tace hmm
Jamal ya saya makan sa wahala
En nine shi kawai zAn cigaba da aiki na ba sai nayi suna ba

Mummy kam dama In kana da shi kaine nata amma inbaka da shi ure useless".



🤓



*surriem*
[23/08, 03:02] ‪+234 806 071 2446‬: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.


*Masoya A duk enda kuke surayyahms tana kaunar ku* 💋❤💯




*Page▶11*






Zaune suke a karkashin wani open air cool down,suna shan drinks sai kyalkyelwa sukeyi da dariya kamar kananan yara
Amintaka irin na kamal da ashween tamkar jini daya ne ya hada su
Duk da ma a secdry achl suka hadu ba wanda zai iya cewa hakan
Domin savuwr tasu yayi kama da wanda suka tasu tun suna kanana..

'lallai yaron nan ,
Ka tabbatar min da zaka iya jefar tsuntsu goma ma da dutse daya

Dan murmushi kaqai ashween yayai yace
Nothing is impossible bro
Sun dauka abun wasa ne ,
dama mutanen da suke kallon rayuwa a irin wannan madubin ba wahala zasu fada cikin kowani irin tarko,
Wht yhu need is ka nuna musu abunda suke so, to shikenan ka gama da su

Kaml ya nitsu yana jinshi " Hmm amma Allah ya dai sawwake ,to ena ilimi da power ? Ba basirah mswww
Yanzu shi jamal ka gama da shi tashi ta kare tunda yan jarida ma naga sai dada hura qutan abun suke' yanzu sai kuma waye next?

Uhmm bari fa ai jamal hakki mutane ke binsa sai dayan wawan ,,shikam ai one blow ne zan masa muje zUwa
Don Yanzu bani da wani matsala sosai tunda na samu shiga wajen uwar tasu
Sannu a hankali zan durmuryarta da ita da yarta ,amma nafiso komai ya tafi steady
clean bana son nayi garaje ka fahimta

Of cous, kar ka manta ena tare dakai,kasan
Ciwon dayafi zafi shine wanda ba ganin sa sai da aji sa,

Dariya sukayi tare ,sannan ashwewn yace kaga ni zan koma gida kwana biyu ban kula da tsohuwa ta ba duk aikin wayyanan banzayen sun sha min kai,
Ya mike tsaye ,,
Tohh shikenan ash send my regards ,nikam jiya naje ai
Later,suka yi musabaha sannan ya kallesa ya dan kashe masa ido yace
And my princess too
Da sauri ya kwace hannun sa yana harar sa cikin sigar wasa
Kwara ma ka cire my din nan
Princess din dan ma kaine ?

Shikam kamal dariya kawai yake don yasan dole ya amsa shi haka suka rabu kowa yayi nashi hanya


*Bayan wata daya,*

Haka rayuwa ta cigaba wa ashween da familyn rodriquez
Sosai yake samum karbuwa yanzu ya kaiga madam hidayat ta sake masa wasu harkokin ta yana juya mata su

Yarda da so sosai ta soma qallafawa akansa dun dama tun tuni takejin sa kamar dan cikin ta,

Zahida ko hankalin ta kwance sai baza mulkin ta takeyi iya son ranta,
Cikin kawayen ta kuwa har takanyi birgan cewa ta kashe tania ta gaje ashween ma kanta,

Ranar laaraba da aafe misalin karfe10 Zaune tayi gefen sa ta hanasa sakat, shiko sai aikin sa yake baya ma kallon me takeyi
Yana sane da Duk ma aikatan sa ba su samun sakewa musamman inta na offishin
Saboda zahida asalin ta bata san darajar dan adam ba' wani abun ma don tana tsoron ashween ya sa take ragewa

Baby"? Ta kure sa da ido tana kashe muryan ta
Ya akayi,yace a takaice bai dago ba

Sai Yau naga kamar ranka a bace
I mean, lpya kuwa? Yhu look sick ko kwalliyar ma da aka saba min yau ba ayi ba" ta karashe a marai raice

Dan takaitaccen kallo ya bita da shi yace
Kar ki daga ma kanki hankali beauty
Im ok,just need some time alonee
Shyasa ma naga zai fi dacewa kije gida zamu hadu anjima kinji? Ya kau da kai

Ranta baiso ba amma sai ta yi saurin kawo murmushi kan fiskan ta tace
Anything for yhu,
Kar ka manta duk aBunda kake bukata ena nan,
Gyada kai kawai yayi baice komai ba harta fice
'yana jin karar rufuwar kofar ya kife kansa da tebur tuni wasu zafafan hawaye suka soma sauko masa"
Yakai minti 20 a hakan kansa har na hargowa tsaban ciwon dayake ji
Karshe rufe file din yayi ya wuce gida abunsa

Haka ya wuni a daki sai juye juye yake' yaki sanar da kowa yana gidan don kar hankalin ammyn sa ya tashi
Ita kadai ce ta san yadda ya tsani ranar zagowar haihuwar sa
Don tun safe take kafa kafa da shi amma yaki nuna mata komai

Kamal ma ranar shiru bai neme sa ba don ya tsani ganin yanayin ashween a ko wani ranar bufdayn nasa
Gashi duk lokacim da ya so ya shiga al'amarin yakan so ya zame musu sabani,
sai ya yanke hukun cin masa addua da sadaqa duk ranar zagowar haihuwan sa ba tare da ya sani ba ma

Gefen ashween kuwa yayi nafila ranar ba adadi, amma sam jikin sa yaki sake sa,a hankali ya jingina kansa da pillow idonsa a lumshe yace "ya Allah ,kullum dai haka ne...pls ka saukaka min
Sai bai kara cewa komai ba

Tattara kaya ammy keyi bayan ta kammla rubuce rubucen ta ,
Bata hankara ba jitayi mutum agefen ta but

Ke,kaji min yarinyar nan ai sai ke tsorata ni tafada cikin sigar fada ,
Ita kam shiru tayi saida ta kammla karanta dan papern da ta sa mu a kasa sannan ta ce Ammy"
Daga zuwa duba ki sai kimin masifa? , share ta ammyn tayi batace komai ba

Ta rike kogun ta ,sai kiriniya take
Cahn tagaji dan kanta tace
Ammy naje?

Ohhhh jasmine wai ena zaki je ne?

Zaro ido waje tayi tace " tuntuni nake tace wa zanje kasuwa ammy ashe bakki ma jina ?

Ohh sorry ,
Ke da wa?
Nida driver ne kawai

Ammy tace Ok
Ena fatan bazaki dade ba ko don wallhy ba ruwa na tohm
Da sauri ta gyada kai tace " yanzu zan dawo ammy
Toh shikenan ..nan ta fice a gurguje

Wanka ta sha mai shegen kywu cikin atamfa dark green
Ta nufi kasuwa don yo shoping
" zuciyan ta fall take tafiya cikin mall din
Tunanin ta gaba daya me zata siya wanda zai burge yaya ash"
Kiran salma ne ya sake shigowa wayar
Ba jira ta dauka
Tace yawwa dazu muna magana"
Kinsan ban san yau yake bufday ba sai da naje dakin ammy
Naga ta rubuta masa wish a wani paper,ai itama bata san na gani ba na yar mata abun ta
Ta karashe da dan dariya

Hmm jasmine kenan,
Toh me da me kika saya
Ko har kin gama?
Ehmm toh gani nan dai

Huhh,ta yarfa hannu a gajiye tace
Na ma rasa me zan dauka masa salmah
Im so confused
Uhum uhm dont be ,kinga take your time kiy masa abunda ya dcw da shi
Nikam bari na je my prince charming is coming today

Hmmm kaji masu love,to ki gaishe sa,
No wonder bangan shi a gidan mu ba ashe wajenki ya nufa,

Dan dariya salma tayi
Barshi kawai,shifa har yanzu baisan kinsan shine saurayi na ba,

Uhmm ai ni kanwa ce,na masa uziri. Allah dai ya tabbtr mana da alkhairi

Ameen jasmine,ke ma

Please Login or Register in order to submit comment