Reading So Makamin Cuta Complete By Surayyams Chapter 41 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

pls..

Ash yace angama boss, sai na jika suka katse wayar

Ko minti 5 baiyi ba amma sai ya zo ya same ta akasa tana maida numfashi kadan kadan

Ya karaso a gaggauce yace lpya kuwa princess ko muje asibiti ne? Cikin ne ?ena ne me miki ciwo? Yana kaiwa hannun sa yana duba ta

Ta dan danne ta ture hannun ta marairace tana cewa nifa bance maka bani da lpya ba
Kawai Amai amai nakeji
..ya dada sakalcewa tace yaya ka siya min dates shina ke so naci, ya dago yace are u sure ? Ta gyada kai tace eh.

Yace ok dates da mene kuma Kinga yanzu kamal zaizo sai muje na siyo miki..
Tace ok,sai wani abu mai tsami tsami sugar sugar mai tauri bana son mai mai ajiki.

Ya takune fuska yace what' me wannan din kenan, name pls?

Ta sake bakin a sakalce tace nima i dont know kawai ka nemo min tabi ta karashe da muryan kuka.

Ya ce o my god wai. nace bazan nemo ba ne ko meye,ke fa bakki gajiya da kuka ko?
Zan shiga zane ki in kina dama min baby na da kukan banza katuwa dake,

Ta sake karkacewa zata fashe da kukan yace toh yi hakuri, muga bakin kukan tana mikowa ya cabe ya shiga kissing
Anan har ya sata baccin dole, bata ma san lokacin da kamal yazo har suka fice ba.


Shi da kamal din Sosai suka rungume juna don dama tun awaya yake Allah Allah su hadu ya taya shi murnan samun abunda yake matukar so a rayuwar sa,

Kamal yace na fika jin kai na yanzu ash kwanan nan zamu dawo fathers,
Ash yayi dariya yace abu kamar da wasa Allah dai ya dada albarkatan rayuwan mu da yan uwa musulmi baki daya

Kamal yace ameen suka nufi katon shoping mall na garin,

Tun isarsu ash yake tunanin me zai samu mai tsami tsami suga sugar mai tauri wanda ba mai ajiki?
Iya tunani yayi amma ya kasa gane abun,
Yay ma attendance din bayani iya bayani amma sukan su basu san ya zasuyi ba

Kamal in banda dariya ba abunda yake ,
Duk yabi ya damu don ya san akwai rikici in bai nemo ba.

Bayan kammala shoping din nasu yayi zugum cikin motar yayi shiru

kamal har yanzu bai daina dariya ba
Ash ya ja tsaki yace bakomai ka cigaba, ai gwara ni ..kaifa har nan aka turo ka siyayyan turare,

Nan ma kamal ya dada fashewa da dariya yace oho dai kuma wallhy sai an nemo abu mai tsami tsami,sug..r
Sai bai karasa ba yace hey i got an idea

Ash ya saurin sauke numfashi yace alhamdull ka samo sunan abin a wani kasa ake sayarwa muje.?

Kamal yya murmushi Ya dan ja kunnnen Sa yace dis is serious ash to kwanan nan zaka haukace fa, sukayi dariya duka
Kamal yace "Maganan gaskiya dai ,i think is better mu nemi quava,ko mangoes mai tsami tsami mai zaki zaki kuma kaga ai shi baida mai ajikin sa.

Ash yace bright idea, gaskiya kadan yi kokari,to muje
Nan suka shiga wani local market don su tabbata exactly abunda take so aka kawo mata,

duka biyu suka hada da quava da mangoes
Sannan suka nufi bank

kamal yace me zakayi kuma a bank in wani abu ne ai akwai kudi anan din.

Ash yace zahida ce take bukatar kudi bansan me zatayi ba bt i kind if think i should help ,

Kamal ya dan jinjina kai a ranshi yace Ash kenan,jini jini ne ..nasan tausayin ta kawai kake ji anyways hakan yana da kyau..

Sai yace ok muje
Yau Ka karbi girman ,yayi dariya

Nan suka shiga ya mata processing 45million a wani acct Na daban da ta turo cikin sakon,suka fito

Mamakin kamal shine mai zahida zatayi wanda har sai ta nemi kudi awani wajen bayan tana dashi

Ash Yace kamal nifa yanzun bata su nake ba tukun ..yanzu dai nafi so naga jasmine tana cikin farin ciki da kwanciyar hankali shikenan

Kamal yace of cous,kawai nasha mamaki ne.ai mun gama namu saura ya rage ma zahida da mum dinta yanzu su muke sauraro.


A haka suka cigaba da hirar har suka kai gida sun samu kuwa
Lokacin jasmine har ta tashi a bacci tayi wanka tana zaune shiru a farfajiyan gidan tana shan fresh air.

Sai ta sake wani faffadan murmushi ma kamal da ya gama yin saitin tsokanan ta

Lpya ,lpya suka gaisa ana hira gwanin burgewa,
Don Ita kanta ta kanyi admiring din frndshp din Ashween da kamal

ko suna fushi da juna basu taba rabuwa bare aji su duk wuya duk runtsi suna tare.

Anan ta soma cin quavar sa'ar su kenan daya bata ce bai mata ba.

Taci sosai kusan guda uku suna kallon ta sai tayi wuf ta mike zata dauko dates din ,

Ko step biyu bata kara ba Wani murdawa cikin ta yayi ta kame cikin tayi wayyo Allah na,anan take ta fada kasa sumammiya.

Duka suka yo kanta a rikice suna kiran sunan ta jasmine,jasmine ,shiru bata motsawa sai ma jini daya soma biyo baya

A gigice Ash ya mike tsaye ya lumshe ido cikin razana ya koma da baya ya jingina,

Aka bar kamal ya rasa wa zai kula acikin su, a daburce yake ce ma abokin sa pls calm down ash, kayi hakuri mu taimake ta she s going to be fine
Kira mana ambulance muje asibiti huryyyy.

Ya tallafo jasmine din a a hannun sa ta sake hannuwan ta kamar mutacciya jini na bin Kafar ta

Kan ace 5minutes an taho da motar asibiti anan suka shiga ash ya kife kansa yana hawaye yaki Ma magana yayi shiru..
kamal ya dubi jasmine ya dubi Ash ya rasa abunda ke masa dadi

Sai da aka shigar da jasmine emergency kafin ya samo daman rarrashin sa 'kamar karamin yaro yake gyada kai yana saukowa ,har ya samu dan sauki sukayi zugum suna jira.

Minti 40 kacal doc ya fito fuska ba yabo ba fallsa yace musi su kwantar da hankalon su" ba matsalan komai da cikin ya na nan,
Amma tana bukatar kulawa ne sosai

Yace ma ash ya duba ya gani akwai ragowar wani sex adiitive a cikin jinin ta, kuma ya tabbata lokacin da abun ya faru already akwai ciki a jikin ta.
So dole sai anbi a hankali zata warware gaba daya

Ash yayi masa godiya ,yace bakomai zai kula. Doc ya barsu a wajen

Kamal dake gefe fuska a daure ya juyo gaban ash yace bangane sex additive jinin jasmine ba? Pls can u xplain' waht did u do to her ash,me nake ji haka?ya karashe a zafafe

Ganin yadda kamal din ya haura dokin zuciya sosai ya bata rai

ya sa shi yayi calming kansa,
Nan ya nitsu ya bashi labarin sarkakkiyar da zahida tayi niyyan daura sa akai har ya fado kan jasmine.

Gaba daya sai yanayin su ya sauya,
Kamal yace lallai da an tafka babban kuskure Allah dai ya dada kare mu.yayi dan furza iska cikin naxari yace ma ash
I think this game is becoming risky, zahida bata da hankali jahila ce,da na sani wallhy da baka tura mata ko sisi ba.ya karashe a zafafe

Ash yayi ajiyan zuciya yace ,kamal ya na iya toh? Nasan Zahida bazata rabu dani ba i know...
Gashi yanzun dole na kula da jasmine sosai,ya
Dubi kamal da kyaua yace
Ena ga mafita daya ne gare ni yanzu.

Kamal yace and whats dat?
Kar kace min ka cire hannun ka ,is the same thing as sake jefa jasmine cikin wani mummunan hatsari ash .

Sai Ya juyo a kasale yace c'mon relax kamal, ba wannan bane
Kawai ena tunanin na gaya ma jasmine duk abunda ke faruwa ne, atleast ko ma bakomai ba i want to tell her wacce zahida a waje na ta sani.


Kamal ya danyi shiruuu ,sannan yace nima ena bayan ka Ash,ka fada mata zahida yar uwar kace kuma ga abunda ya hada ku koma ba dukan ba kamar yadda kace,fatana
Allah ya sa ta baka goyon baya wajen kula da kanta

,enaganin intasan da haka bamu da matsala wajen kare ta daga sharrin su..
Sannan Ya dafa kafadun ash yace masa good luck bro
Sai dai Amma ya kamata a bari ta dan ji karfin jikin ta ko?

Ash ya gyada kai a sanyaye yace ,bakomai
Ena ganin sai mun koma nigeria jibi zan gaya mata...lets go in an see her
Nan suka tashi suka shiga ciki,..



Gefen zahida kuwa ganin alert din 45million a sabon secret acct dinta Daga ash ya sa ta haukace da murna a dakin ta.

Duk da ta kikkirasa bai dauka ba sam bata damu ba.
Ranar gaba daya sai taji tsumin kaunar nasa ya sake sabon toho a zuciyan ta

daram take jin kanta duk wani fargabn ta sai ya dauke chak fuskan ta ya haska da annuri

Ba bata lokaci ta kira saminu ta masa kudin sa
Ta bar ragowar 5 million xtra a boyayyaen acct din


Yanzu burin ta daya shine tana jira ace mata ta samu duk wani news da information wajen saminu kafin sai ta koma yola ta kwato Ash din ta a hannun jasmine ta Aure shi.



*Good mrninh tities Allah ya baku ladan comments ena kaunar ku kamar yadda jasmine ke son ashh*❤
*Uh uhm ai 🙊🙉zahida nake nufi🐶🐶*







*surriem*
[23/08, 06:18] Surayyahms Frd Ruky. Raheema: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.



*Page▶70*





Ba wani bata lokaci zahida ta kai ma saminu kudin aikin sa in cash,
Ya sha mamaki sosai sannan yayi murnan ganin haka.


Tana tsaye a kansa ta daure fuska tana yatsine
Tace oya" my own part of the deal "yanzu nake so ka fada min kanun labarai

Ya lashe baki yana bin ta da wani irin shu'umin smiles yace kai da Allah kin cika gaggawa
Zauna nan ya mata nuni da gafen gadon sa

Anan ya sa seriious face ya kauda wasa ya dube ta
Yace zahida abdul fatah rod"
Tace yes saminu.

Ki nitsu kiji abunda zan fada miki yanzu in ba haka ba ki sani kece da asarar duniya da lahira

Tace hold on,
Kawai kafada min abu this is a deal ba family meeting mu keyi ba sannan ena so ana hada min da tangible proofs ta calla masa harara


Yayi yar dariya yace kar ki raina ni zahrod"don zan iya maida miki kudin ki kuma na kore ki so just shut up and listen silly girl..

Ta sani sarai zai iya sai ta ja tsaki ta kau da kai ba tace uffan ba

Yace ena so komai ya tafi mana dai dai ne yarda bazaki fada tarkon uwarki hidayat ba, amma in kika min taurin kai ya dage kafadar sa yace is all up to u,

Ni ena da manya manyan makaman da zan yaki hidayat rod so bana shayin ta.

Ta juyo ta kalle sa tace " pls enough of all dis naji
Na fahimta waccece hrod ?

Yace ba daganan zamu fara ba sai ya dauko wasu files a kasan wani tsohon carpet ya zuba mata su agaban ta

Nan ya bude daya bayan daya ya shiga nuna mata arzikin su gaba daya komai da komai yadda mum din su ke monitoring din komai na gidan,,sai yace kinga plantation din nan shine yake da babban kashi na tattalin arxikin mahaifin ku da ya rage,
Gashi ba naku bane n yan biyu ne da suka mutu,

Tace na san da wannan
Yace good,
Ya sake dauko wani file ya baje mata su a kasa ya nuna mata dumbin arxikin da Hrod ta mallaka a duniya.
Sannan yace H yana nufin hanan hernandaz rodriquez.

Zahida tace ok Hanan, wacece ita ? Kana nufin itama rod ce amma arzikin ta baya cikin na mu,but how comes ita kadai take da wannan

Ya ce relax, ai wannan dumbin arxikin da kike gani ba na wani bane naki ne ,infact ke ce wannan Hrod din da kike nema a yanzu

Ta tsaya ta dake ta dan yi shock na seconds biyi sannan ta tuntsire da wata mahaukaciyar dariya mai cike da mamakin
cikin dariya tana cewa ka raina min wayo saminu..u think im mad? fuck u, you bastard.


Nan shima yayi murmushi " sai ya dube ta da dan serious look yace wacece mahaifiyar ki ta asali zahida ? Tell me pls

Sai chak dariya ta yanke ta tsaya kallon sa irin me kake nufi
Yace answer me ,cikin tsawa daa daure fuska ba alaman wasa

Tace ,i dont know,mum hidayat tace tun ena ciki ta rasu and har yau bantaba ganin hoton ta ba

Bai ce komai ba ya dauko wani envelope ya mika mata.
Nan ta soma ganin tsoffin pics ,na hanan tun tana modelling har na auren su da rod kaf ta gani,

Take taji hawaye na so ya zubo for the first time taji son asalin uwar ta ya mamaye zuciyan ta,

shiko saminu bai bari abun yayi sanyi ba
ya shiga bata tarihin komai da komai abu daya bai rage ba, har da cewa mata ai rayuwar ki a gwalba yake
Kina ganin Wai hidayat tana son ki ne toh bata bar uwar ta ba bare yayan ta na cikin ta bare kuma yar wata

Baku sam waye uwarku ba ne shyasa ,mata fe wanda duniya kawai ta sani da son zuciya da mugunta

Kinji waye hrod sannan kinji dumbin arzikin da yake nanike da destinyn ki ake so a miki yankan baya.

Yana maganan ne amma
Zahida kam lokacin ta daskare awajen kamar wanda jinin ta ya tsaya,waje daya idon ta ke kallo notin din brain Dinta suna kan kuncewa

Ta tashi a tsaye cikin firgici ta dada duba komai taga ehhh fa gaskiya ne babu yadda zatayi ta karyata zancen nan

Ta lumshe ido cikin dacin rai a ranta tace da wani ne ya gaya mata zata ce karya akayi ma mrs hidayat ba zata mata haka

Girgiza kai take tana huci hannun ta na bari kamar mai jin sanyi

Saminu yace im sory this is part of the deal dole na fada miki gaskiya kenan..

Bata jira ya sake magana ba ta dafe kirjin ta sai ta sulale kasa sumammiya

Ba yabo ba fallasa ya debo ruwa ya watsa mata ,ya kuma tsaya mata
Hakan ma da kyar ta farfado, sai ta fashe da kukan tashin hankali

Duk da zuciyan sa a bushe yake amma sai ya dan tausaya mata
Cikin rarrashi anan har ya lallaba yayi sex da ita.


Bacci mai nauyi tayi a gefen sa washe gari ta mike da wani azababen ciwon kai.
Gani tayi ba kowa ga jikin ta duk yayi tsami ko ena ya jigata,

Tana kai hannun zata zare bargon wani letter ya fado kasa
A hujajan ta dauka ta bude ta shiga dubawa,
Saminu ne ya rubuta mata,shawarwari akan yadda zata tinkari abun
Ya mata nuni da in har tana son ta kwace dukiyar ta shi zai taimaka mata suyi komai cikin siirri ta karbi cikakken yancin ta a wajen hidayat ,

iya saukin da ya mata shine yace ba zai sake karban kudin ta ba amma zata na bashi sex kamar yadda sukayi tun a farko,

Duk da ma taji dadin abun don dama shiri take taje ta cinna ma gidan su wuta ta kona mrs hidayat da ranta a ciki ta huce.

Amma ganin in ta biye zuciya karshen ta zatayi biyu babu sai ta hakura ta dauko shawaran saminun

Da kyar ta tashi ta shirya har yanzu abubuwa na cinta arai sosai
Kuka tayi ba adadi tace ashe makashin ka yana nan tare da kai? She ruined my life ta kashe min uwa and now hakki na zata karbe?

Wallahy bazan iya zama inuwa daya da ita ba dole na tafi na bar garin nan inyaso idan muka sake hada plan da saminu zan dawo na cigaba da aiki na akanta sai naga bayan ta.
Ta yi dan karamin sight relieve tace i cant live with dis monster don zan iya kashe ta na huta azzaluma..


Ranar gaba daya zahida bata bari sun hadu ba sai ta zauna wani hotel ita daya , mrs rod taci kiran ta tana gani bata dauka ba
Duk tabi ta shiga damuwa don kwana biyu take ganin zahida bata cika kwana a waje ba


Tsaf zahida ta shirya duk da ma ranar gaba daya a dull din ta take ko kyayakywan murmushi bata iya yi

Sai da ta tabbata na kowa gidan ta shigo Ba bata lokaci ta tattatara kayan ta duka a sace ta bar gidan ba wanda ya sani

Tana cikinn jirgin ma tana kuka, duniya ya mata zafi sosai
Cikin ranta tace" i just lost evrything ba family,no friends,gashi ni kenan babu wanda yake so na na gaskiya a duniya? Babu mahaifina
An kashe min mahaifiya ta shine take neman raba ni da ashween?
No, ai na gwammaci na zauna da shi har na mutu ena saukar masa dakai tunda naga shi kadai ya san mutunci na a duniyan nan koma wani irin laifi na masa ,

Ashween shine masoyi na na gaskiya da amana cos he neva lives me duk munin hali na.
Yau ko zanje ya dinga kunna min wuta ne a jiki na na amince da na zauna da muguwa azzaulamar matan nan.
Cikin wannna halin ta isa yola.

Ko kafin ta isa gidan ma tuni wani zazzafan zazzAbi ya sake rufe ta.
Bacci kawai take yi in ta shi ta sha giya ta sake komawa aikin kenan sai ta dawo bata damu da kowa ba.


Har tsawon kwana ukun ana yau su jasmine zasu dawo,
Shima ashween yau ne yayi niyyar fada ma jasmine komai akan zahida in suka koma gida

Don sosai jasmine ta warware ta samu sauki.
Jirgin karfe 9 na safe ya dawo da su nigeria..

Yau da aka sanar ma zahida ash zai dawo sai ta shirya tsaf din har ta zube cikin kwana ukun fuskan ta ya lotse kadan alaman ba adai dai take
ba.

Haka tayi zaman diris tana jira ya shigo gidan ta samu wanda zatayi sharing worries dinta da shi ko zata samu sauki saukin abun aranta.

Kullum wutan daukan fansa ke huruwa aranta gashi ta kasa daga waya tayi magana da madam hidayat gani take zata iya kwaba komai intaji muryan ta.


Tun a hanya doc yake kiran Ashween akan ya kawo masa medical history na cikin jasmine
Komai da komai kamar yadda ya bukata.
Don yana so dama yayi employing home nurse wanda zata na zuwa jofa jifa tana kula masa da lpyar su.


Wani sabon kwanciyar hankali jasmine take ji musamman da taga yana nuna kulawar sa kanta sosai har da kari.

Sai dai ta matsu taji meye yace zai fada mata in sun zo gida.
Don tun jiya da dadddare yake maimaita mata akwai muhimmin maganan da zasuyi da ita.


Suna isa gida Baibi ta kan kowa ba yayi sauri ya sake ficewa don yayi muhimman baki a office din sa,ya ce ma jasmine ta huta
In yadawo zasuyi maganan
Anan dakin ta kwanta tana hutawa cikeda tunanin lovely memories din da sukayi sharing da shi cikin kwanakin
A hankali take shafa cikin ta tana lumshe ido cikin godiyar Allah da kaunar mijin ta

Yana fita da mota a gidan nan zahida ta farga ta sauko da gudu don ta tare sa ta ko don ma ta gwada masa ai ta dawo gidan amma da shikd sauri yake sai bai ganta ba.

Anan ta tsaya ta dan ciza yatsa wani abun yace mata ki shiga kawai ki jira shi ai zai dawo gidan.
Tana kaiwa one step taji an sake bude gate

Juyowa tayo taga wani motar ne daban ya shigo sai ta tsaya

Doc ne ya fito, tana kallon sa har ya karaso sai suka gaisa
Yace madam na zo ganin oga ashween ne.

Tace oh ai yanzu ya fita.i think he's in a rush
Lpya kuwa?

Doc yace lpya lau dama na kawo masa files din dayayi requeasting ne na medical history
Bata bari ya karasa ba tace ok ,bani na ajiye masa ai nice matar gidan

Shi dai doc baiga kamar ta da pasport din jasmine ba amma sai ya mika mata ya juya abun sa ya fice

Dakin ta ta nufa straight da shi da har zata ajiye ta fada wanka ,sai ta dawo ta dauka
Ita kanta bata san meya sa ta bude ba, ba ta jira komai ba sai ta soma karantawa a nitse

Gani tayi, sunan jasmine da nashi an cike su ga pasport din ta a manne
Ashween As father da jasmine mother na unborn baby 6weeks old
Sannan ta karanta komai information daya biyo baya Har da date in haihuwa kaf ta gani..

Kafim ta gama dama ta soma diga da hawayen hannun ta na karkarwa
Kanta ta rike,tana jin wani mutsa mutsan hauka na hargowan subuce mata,

Ta kalli gabar ta kalli yamma a haukace Tayi wani irin firo da abun akasa ta channa wani firgitaccen ihu ta dire kasa tana birgima kamar zarrariya.
Cikin bala'in kunan rai ta ce ""Ash ka cuce ni,ma yaudari yau sai na tarwatsa ka
Ta sha numfashi mai zafi kirjin ta na dagowa sama sama

Ta mike tsaye tana zare horrible and furious eyes din ta tace :Yau sai na nuna maka ni ba kanwar lasa bane Ashween.



Da sauri ta fito fuuuuhhh kamar zata tashi sama zuciyan ta ya kafe tana cewa yau kowa zai san wacece zahida a gidan nan,kowa sai ya dandani azaba yau bazan kyale uban kowa ba a gidan nan......




*nikam bana nan ooo🤷🏼‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀*



*FILIN NAZARI*


*nace ba,amma fans ya kuke ganin ashween zai kare kansa da jasmine a hannun zahida after dis tangible proof ?wai shin in akace ya tona asirin kansa wa zahida agaban jasmine,.. jasmine ta tsira kuwa?*

*To inya ki tonawa ita matar sa ce har ila yau wani hukunci jasmine zata dauka musamman da baisamu dama ya sanar da ita wacece zahida ba?🤔🤔🤔*







*surriem*
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.






*Page▶71*





'Zahida ta fito Ba kowa a wajen sai mai gadi da driver suna hiran su

Ba takalmi a kafanta sannan idon ta sun kafe sunyi ja zir da hawayen bakin ciki da kunci..jikin ta na bari tana kyarma ta kira su a gagauce ta ce ma driver ena zata samu hot acid?

Ya gwalo ido cikin mamaki yace madam babu anan kusa gaskiya
Sunayi suna dar dar don yanayin ta ya nuna alaman ba lpya ba

Tace toh kaje ka bude gareji ka bude motar uban koma waye
Ka hado min ruwan batir yanzu tafada da commanding voice.


Cikin tsananin tsoro dukan su sukayi shiru suna kallon ta basu motsa ba
Cikin Wani razannanen tsawa tace me kuke jira ne?look na baku 10 mints in ba haka ba harbe ku zanyi yau a gidan nan .ta ja gefe ta tsaya

Ba musu suka bar wajen
Kowa jikin sa na bari hanjin su na kuka don tsoro

Duk sun sani cewa ruwan ba3 wani bin ma yafi hot acid illa domin kuwa zallan concentrated sulphuric acid ne wanda ko ma ginin block aka zuba sai ya narke ya zube kasa bare mutum..

,a yanayin zahida ko da ba'a fada musu ba sun san ba alheri za'a aikata da ruwan bat3n ba

Nan driver ya shiga kunce kunce ya soma hada ruwan ba3
Ganin yadda abun ke watso musu wani mummunan wari mai hatsari ma numfashim dan adam ya sa mai gadi yace wallhy wallhy nikam zan kira oga
Don Ba zan iya wannan aikin ba

Driver yace ka rage murya kar taji ka
Kayi sauri kayi hakan don nima bansan me zance ba in wani abu mummana ya faru.

Nan mai gadi ya boye bayan bishiya ya ci kirar ash bai daga ba
Chan hikima ta zo masa sai ya tura masa tex massage.


Suna gama hada ruwan ba3 ta karbe bata ko sauraran zafi da hargowan da yakeyi sai ta ajiye a dai dai kan step daya raba site din gidan

Ta kamo hanya ko ajikin ta sai sauri take ta tayo dakin jasmine.


Idar da sallar ta kenan ta zauna tana lailaya cikin ta duk hankalin ta ya koma kan yaushe ashween zai shigo don tana mugun jin missing dinsa.


Zahida ta banko kofa tayi Wani munafikin murmushi ta bangaje kofar sai dayayi kara
Kallo daya zaka mata kasan bata cikin hankalin ta

Jasmine ta mike tsaye a dan razane tace mata lpyar ki?

Dariyar hauka ta bushe da shi gashi

Please Login or Register in order to submit comment