Reading So Makamin Cuta Complete By Surayyams Chapter 40 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta keyin dishi dishi kamar ta shawu,
Ya kama hannun ta tana kwance kan gado chan ta soma surutu tana ce masa i love you,yayi shiru yana rike da hannun ta yana kallon ta da wannan kalmar a bakin ta har ta yi bacci.

Sai yayi kissing forehead dinta ya gyara mata kwanciya yace i love you more princess.sannan ya fita.


Kafin nan zahida ta nan har yanzu a sume
Ga Hannun sa har yayi layi a wuyan ta wajen yayi jajir dabn da fatan jikin ta.


Bibiyan hanya karime take yi amma shiru har karfe 12 rana bata ga zahida ba.

Shine ta yanke hukuncin shiga dakin anan ta samu ta taimaka mata har ta farfado a gigice tare da wani irin kuka

'kukan kawai take yi tana cewa shikenan mumy ta cuce ni na shiga uku ash ya rabu dani,

Bata ji bata sauraran kowa ta haukace ta zauce ko tsayawa sauya kayan jikin ta batayi ba shiga dura zage zage tana cewa wallhy bazata tafi ta bar gidan ba dole sai ya aure ta
sosai hauka ya soma bayyana mata lokaci guda tana fincike fincike tana fashe fashe

Hankalin karime yayi mugun tashi don bata taba ganin irin wannan tashin hankali ba.

Haka tayi har ta gaji ta koma ta kwanta a kasa ta cigaba da kuka tana kiran sunan sa tana cewa "pls dont leave me Ash i love u..ta nayi tana maimaitawa
Har zazzzabi mai zafi rufe ta,

Ga shi karime tana tsoron tace zata kai magana ma ogah, bata san meya faru ba hasashe ya nuna ba lpya ba..
Sai tayi kokarin kiran mata home doc akazo aka soma ba zahidan treatment.

Ash na chan part din sa yana kula da jasmine bai ma san me sukeyi ba

Jikin zahida na dada zafafa ,don sosai tasa abun aranta har ta samu nervous breakdown da high blood pressure.

A dakin nata aka jona mata engine oxygen aka kyale ta on bed rest.


Jasmine tun bayan baccin da tayi shikenan ta dawo normal kamar ba abunda ya faru da ita,
Sai dai har yanzu ash yana jimamin abun a ransa duk da ma sam ta hana shi nunawa,
Yanzu Burin sa ya baata farin ciki mai daurewa me don
Haka ya sa ya yanke hukun ci zai bita ukraine tunda yau saura sati biyu kacal wata 6 ya cika ta soma practical classes dinta..


Washe gari zahida ta soma samun Sauki amma sai ta dawo shiru shiru kamar mai ciwon haukan gaske.

Kullum tana jira taga ko zai leko ya ga halin data ke ciki amma shiru karime ne kawai ke jigila da ita,
Gashi duka suna tsoron zuwa duba shi ko masa magana gani take wannan karon zai kashe ta in ya sake ganin ta a gidan sa

Amma taurin kai ya sa ta dawo bata da Burin da yawuce tayi ta zama a gidan har sai ya hakura ya sauko sun dai daita.


Bayan kwana biyu da faruwan abun jasmine na zaune a falo misalin karfe 8 na dare

bayan isha ya shigo da dan gudun ta ta fada jikin sa yayi murmushi ya dago ta sama ya mata juyi sannan yace r u ready?
Ta gyada kai tana smiling tace yes 'yace to zo muje mu shirya
Nan suka shiga suka shirya tsaf,inda tasa wani riga mai kyau black iya gwiwa sannan da turkish jacket iya knee pepper red mai manyan buttons , sai ta hada da bakin wando tayi roling da bakin veil dan karami .barakallah

Shima leather jacket ne jikin sa baki da farin riga ta ciki sai bakin wando ya kamo hannun ta daya yana amsa call da dayan hannu har suka kai bakin motar sa.

Daga jikin window zahida ke kallon komai ta harde hannu tana ruwan hawaye masu zafi, sunyi kyau na fitar hankali gwanin sha'awa

A idon ta ya bude ma jasmine motar ta shiga driver na kan loading trolleys din su,
Sannan shima ya shiga aka ja su suka bar mata gidan.

Tun a mota yake rungume da abun sa har suka kai aiport gashi ko wani minti goma basu kara ba jirgin su ya tashi sai kasar ukraine.


Kafin nan zahida ta kasa daurewa ta rugo a kuje akan zata zo waje sai ta tambayi mai aiki inda ya shaida mata ai makaranta madam zata je amma tare da ogah.

Tace what Tafiya ma Ash zaiyi ya barni a gidan nan a haukace
Ta rarumi key kanta ba ko dan kwali ta bi su aiport,.
tayi neman duniya har ta gaji ba su ba masu kaman su.

Da kuka ta dawo gidan ,gashi maimakon son shi yayi sanyi a ranta sai taji a duniya yanzu aka fara zuba mata kaunar sa a jinin ta.gani take zata haukace in wata ta mallake shi
Tayi kuka tayi jimamin har ta gaji ,bayan 2days da tafiyar su itama ta tattara komai nata ta tafi abuja.


Nan tayi zaman ta batare da ta gaya ma kowa halin da take ciki ba,

Asali ma sai ta danne abun aranta ta sa a zuciyan ta duk mum dinta tane ta jawo mata komai.

Kullum takan fita club tayi dare ta sha giya iya son ranta don ya fitar mata da tunanin Aash da jasmine ..
yau ana neman kwana biyar kenan da barin su nigeria
Har yanzu bata faskara ba.

Mrs rod ta buga ta rawa ko zataji silar dawowar ta amma sai tace ai ashween yayi tafiya ne kuma jasmine ta tafi schl
Itama Ta dawo abuja ne don tayi aiki.
Da haka suka rabu lpya.


A chan bangaren su jasmine kuwa sosai take ganin duniyanci wajen ashween sun isa ukraine sukayi kwana biyu, daganan ya soma debar ta suna yawo a nearby countries suna shakatawa..


Gaba daya ya dada sakalta ta har mota ya sa aka mata designing na musamman a companin roll rolce mai shegen kyau.

Rayuwar su suke cikin tsafta da soyayya shakuwa na dada ninkuwa a zukatan su.


Sai da ya rage sauran 6 days sati biyun ya cika suka dawo cikin garin ternopil enda universtyn su jasmine yake.

Nan ma ya kaita suka zaga sosai, don ternopil state medical university is the best medical schl a kasar baki daya,
Anan Jasmine zata karanta human anatomy and phisiology science,

Shi da kansa ya dauki alhakin zagawa da ita cikin schl din taga wajaje sosai sannan suka dawo ma saukin su.


Sai dai duk abun da ake taki ta bayyana ma Ashween halin da take ciki tun a gida nigeria.

Don tun kafin ranar da tasha wannan coffee din
Take fama da morning sickness da mutuwar jiki amma sai ta waske ta bar ciwon yana cinta ta ciki har ya sake ta..

Yanzun har ta saba ,da shike in ta daure yakan zo ya sauka sai ta barshi a hakan,

sai dai zuwan su dubai a cikin kwanaki nan ta soma jin wani abu na daban
Cikin ta na yawan ciwo sannan boobs dinta sun ciki har suna mata nauyi ga zazzabin safe da yamma.

Yau ma zazzabin ne ya tashe ta amma sai ta ce masa ai weather ne yake sata jin haka,

yayi da ita ta bari aje a duba Lpyar ta tace sam
Ita kam ma doki take so ta hau,

Bai sha mamaki ba don ra'ayin su kusan daya ne yana mugun son wasan polo,

Sai Da yamma late around 5 aka samo horse kosashhe
Tana gani amma sai tana fargaban wasan sabida yau fa ita kadai tasan me take ji a jikin ta.

Ya hau yana gwadawa tana zaune tana kallon sa a farfajiyan gidan
Daga bisani ya karaso daf yace mata 'u wanna try?
Sai ta gyada kai ya sauko ya tallafa mata ta hau,
Lapya lapya take zagawa yana videon suna hirar su gwanin shaa"awa

Can kawai cikin ta yayi wani irin murda wa a hujajan ta sake sirdin horse din ta soma layi zata fado kasa.


Jasmine,!!!!!!!!? ya kwala kiran sunan nata yayi saurin gudu ya bi bayan dokin ,
Yana samun nasaran kamowa ta sulale kasa da kyar ya samu ya taro ta ta fado akan hannun ta.

Cikin rudewa yake kiran sunan ta yana dan girgiza ta amma shiru bata motsa ba.
Yana dago kanta zai dauke zuwa asibiti ta wani yi yunkuri ta fetso masa amai a jiki.

Tun daga nan sai ta soma kwaza amai kamar zata fitar da hanjin cikin ta sai da hawaye suka wanke fuskan ta dan wahala.

Ba abunda yake yi sai sannu duk hankalin sa ya gama kaiwa 390 a tashi ya bi ya sukurkuce,
Goran ruwa ya dauko ya dan bata ta wanke baki sannan ta sha kadan .sai tayi lugwi ta koma kasa anan gefe ta kwanta.

A daburce ya sake biyo ta ya kinkimo ta suka koma ciki ko numfashi ma da kyar takeyi bare bude ido
Lokaci daya kawai jikin ta ya sauya tayi laushi.


Nan Ya musu wanka ya kimtsa su sannan ya ja ta zuwa asibiti.
Hankalin sa sam bai jikin sa don yanayin yadda ta gama narkewa ta kwanta anan ta tashi anan yayi mugun damun sa.

Ita da doc Sun kai 20 mint a ciki sannan ya fito da sakamako enda ya tabbatar ma Ashween jasmine na dauke da cikin 1month and 3days.


Murmushi ta sake ta ce alhamdullhi a zuciyan ta,lokacin shikuma na famar zuba godiya ma likita kamar shi ya basa kyautar cikin.

Farin ciki daya dade baiyi irin sa ba ya balbale sa.
Suka rungumi juna yana gode ma Allah tare da sa mata albarka har sai da yayi hawaye
ya shiga tuno ammyn sa.

Ita ma ganin ya birkice cikin farin ciki ya sata silent tears,daga nan yabi ya manne mata tun a hanya yake tambayar ta abubuwan data ke so ya mata har suka koma masaukin su.







toh fa we are pregnant👯🏻‍♀



*Jazakhallahu khairan fans and friends na kusa da na nesa,ena ganin comments yana kayatar dani, Don nima cikin comments dinku nake dada karuwa da ilmi Allah ya saka muku da Alkhairi netwk bai bari nayi magana afterr post kuyi hakuri ilsm...keep d fire burning ana tare*


*TEAMSMC💋💯🤝🏼*

*TEAMJASMINASH ❤💋*

*TEAMZAHROD😛😂😂*







*surriem*
[23/08, 06:17] Surayyahms Frd Ruky. Raheema: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.



*Page▶68*




A bangaren mrs rod kuwa bata damu ba tunda ta san ba wani matsala komai na tafiya normal da zahida a gidan

Sai ta cigaba da plans din ta
Abu biyu ne a gabanta yanzu
Ta samu ta karbe ragamar plantation din su lailah da lateef, sannan ta maida arxikin zahida ya dawo nata batare da kowa ya sani ba..

Taa sa kai ta durmuya tana aiki ba dare ba rana. ranar kicibis zahida ta sake gamo da key mai tambarin Hrod a office din mrs hidayat
Nan ma zuciyan ta ya sake karkata da son tasan wacece ki wanenee Hrod
Ta dauki keys din tana kallo tana maganan zuci bata hankara ba daga bayan ta taji murya a saman ta ance "uhmm kyau da kanta,

Tayi saurin ajiye keys din a dan tsorace ta juyo sai charaf sukayi ido hudu da barister saminu

Ta ja tsaki mai sauti ta kama hanya zata fice ta bar masa office din
Sai yayi sauri ya sha gaban ta yana wani shu'umin murmushi

A hatsale tace please excuse me saminu bana cike da iskancin ka..

Yay murmushi Ya shafa gefen fuskan ta yace
Zahida kenan,
Dani dake ai duk yan iska ne kuma zan so ace kin sauke girman kai kin fahimci hakan


And remember am ready to help u Kowani lokaci ba ha'inci

Ta bangaje hannun sa,tayi tsuka tace who need ur help ? Just get out of my way..

Yayi shiru ya kure ta da ido sai ya dauki key din Hrod yana kallo ,
Ya tabe baki ya ja gefe ya bata hanya ,
Tare da cewa kinsan inda zaki same ni in kika gama bata lokacin ki wajen neman abunda ba zaki taba samu ba
Ya kau da kai ya juya ya fuce ya barta a tsaye


Bata iya cewa komai ba don tasan baristr saminu ya kure wajen saurin gano dan uwan sa munafuki

a duk halin da kake ciki in ya ganka yakan iya karanta ka ba matsala

Sauke ajiyan xuciya tayi tace 'mstsw ,nasan duk take taken ka saminu, ai bazan sake baka dama ka lashi jiki na ba zan dai nemo waye Hrod da kai na kuma zan samu,

Tun daga ranar hankalin ta ya soma kaiwa kan abun
Sai ta soma bibiyan harkan mumyn nata komai ta ajiye sai ta karanta

duk dama taga hidiman su da saminu ya dada karfi sosai cikin kwanakin Itama bata rusuna,ga secret calls ga visit akai kai.kuma ba wanda yasan meke faruwa tsakanin su.

Ranar tana wani club da da daddare tana shan wine sai taga wulgawar saminu ya saje
a hujajan ta koma gefe ta kebe tana kallon sa

Wani dattijo ne ya basa files amma bata san ko shi waye bane.

Sai ta koma cikin motar ta ta labe ta soma binsa har suka kai gidan sa
A sace take binsan har ya shiga ya zuba wannan files din akan gado ya fada wanka


Lokacin Ko takalmi babu a kafarta take sanda har ta shigo,ba jira ta dau file din ta soma karan tawa a buge take don tasha giya sosai kafin ta taso don bata masan me take fada ba


Nan taga ashe legal request deal ne amma da sunan Hrod da lailah da lateef, bata san akan meye bane amma tasan transfer of will ne

Ta tabe baki cikin ranta tace
Ok dama mai taken Hrod ma baya raye?aha no wonder ai da na san shi, Wow amma yana da uban kudi koma waye ne"toh shima dan mummy ne ko meye matsayin sa a famlyn mu? A yanayin maye take maganan kamar tana da mai taya ta.

Ta cigaba da hude file din tace "ahhhhhhh Mumy ai da ba boye w zatayi ba tunda duk sun mutu me aciki in aka mana transfer of will din muka maye gurbin su.

Sai ta dada bude fwani page din
Ta riga ta shagala har ta mance ma sanda tayi ta shigo gidan, ta na gama karantawa ta kwashe da dariya mai sauti har tana hiccups.

Tayi tsaki tace bura uban chan, me nake gani kamar ma kanta kawai take transfer of will din,huuhhh wannan uban arzikin?

Bata ko kara cewa wani abu ba taji an fincike files din a hanun ta da karfi

Dum zuciyan ta ya buga nan ne ta dan dawo sense dinta kadan ta kalle saminu dake tsaye ya harde fuska
Yace mata"toh makira munafuka so ,u stoop so low to follow me up kuna min bincike
Wai Bashin meye kike bi na ne zahida?

Tayi lagwas da wuya tana masa kallon banza tace saminu dama abunda kukeyi kenan harkan sata?
Barayi ,barayin kudin marayu kai da mummy sai na tona muku asiriiiii"

Nan Ya kamo ta ya matso bakin ta da karfi,
Cikin bacin rai da mugunta yace ' ki tonawa kan ki asiri dai yarinya,
Ure a fool zahida ke zaki cutu a harkan nan.kin ma san wacece Hrod kuwa?


Idon ta har sun kawo ruwa sai ya dan sake ta kadan tace ohh dama mace ce ?
So u knew abt it,tih ita waccece?

Cikin huci yace bazan fada ba, c'mon zo nan
Ki fice min a gida na .

Ta ce anki afice maka a wawan gidan naka saminu,kuma bari kaji i don't care wani irin cutuwa zanyi sai na tona asirin ka kai da mummy..ta kyal kyale da dariya


Abun ya dan tsorata shi don yasan basu bukatar barazana akan harkan is a very delicate issure.
Muddin yanzu maganan ya isa media abu daya aka bude zai tonu abubuwa da yawan gaske.


Sai ya saje ya waske kamar bai san me take yi ba ya kwantar da murya kasa yace ok fine.jeki tina mana asirin zahida
Ni dai Ena shan mamakin yadda kike saurin mancewa da taimakon da nake miki ne a rayuwa
U know dat ban taba baki wrong ba a harka na dake ba ha'inci .ya dube ta yace kar kice ban fada miki ba
Zahida, wannan tonun asirin ke zaifi tabawa belive me..

Nan ta tsaya galala tana binsa da kallo yana goge jikin sa da towel.tayi shiru chan ta ja gefe tana kada kafa.

Muhawara ta shigayi sosai da zuciyan ta ' ance Hrod mace ce, sannan kuma ance ita za tafi cutuwa in aka bude magana' to wannan wani magana ne haka?
Cikin wannan zulumi
Tace saminu kafada min wacce hrod din nan kuma meye alakan ta da familyn mu

Yayi yar dariya yace is very xpensive kin tabbata zaki iya biyan kudin baki na?
Tayi tsaki tace haba saminu, u disgust me wallhy
Kai komai sai anyi business da kai akai ne?

Yace yes,tabbas ma kuwa musamman in akace ma ke ce
Don ni kadai nasan ke wacece a zahiran ce inda ke kanki baki sani ba..

Nan ma Kanta ya dada daurewa tace ban fahimce ka?
Me kake nufi saminu

Ya zame towel din sa kasa ya bar lilin sa na yawo gaban ta,
Hannun sa akan kugu yace yar da uwa ta ta haife ni, bana ganin zaki iya samun wani bayani abaki na sai munyi cikkkaken deal an fahimci juna and
I swear to you ranar da kika cika part din ki nikuma zan fede miki biri har wutsiya game da ke ,da Hrod sannan da uwarki hidayat.

Zahida tayi ajiyan dogon numfashi tace ok whats the deal ,nasan bazai wuce kace jiki na ba ne.
Ok fine
Na amince once in evrey month kana sex dani a madadin part dina .

Yayi wani irin dariya mai sauti yana kallon ta cikin kaskanci da rainin wayo
Sai da yayi mai isar sa sannan ya zago daf da ita ya shafa fuskan ta dake kule da haushin sa a lokacin yace
Naji, na kuma yarda da wannan amma ba shi nake so ba,
Mmmm but tunda kin bani kyautar bozon jikin ki
I think is not bad,zan na rage zafi

Tayi tsuka cikin kunan rai tace aikin banza to me kake so saminu,look
I just hate dis attitude of urs.

Nan ya daure fuska ya zaro takarda yace a sex every month and 40millon naira cash na baki sati daya tal ki zubo min su kiga aiki

Ta karkace ta dada kallon sa tace what?
Ka haukace ne saminu? Look 40million naira bawai bazai samu bane amma kasan cire kudi a jiki na mum zata tambaye ni me zanyi da shi
Sai kuma nace mata me?
Kayi hakuri ka sauya plan gaskiya wallhy kudi mai yawa haka bazai samu da wuri ba sai na san yadda zanyi na cire

Ya tabe baki yace ok,toh shikenan jeki kawai no deal...
Ta tsaya baki bude tace me yayi zafi haka saminu..bai kula ba yace nace:
Ki Tattara kafar ki ki bar min daki na dis minute ko jiki yayi tsami

Ta sauke ajiyan zuciya tace'cmon saminu
Abun bai kai haka ba ai.
Kasan fa kai ne kafiya azzala abu why not
Mu xanza deal

Fuska ba yabo ba fallasa
Ya dube ta yace Allah sarkii yaro dai yaro ne
In da kin yarda dani da zaki so kiyi wannan deal din ko 100 million nace a kwana daya.
Don kwanan nan zaki samu ninkin banin kin arxikin da kike dashi"

Cikin mamaki Tace what,are u serious but how?
Ya wurga mata paper yace just sign it ki bani kudi nan ne zaki sani

Ba tace komai ba Jiki a sanyaye ta dau paper tayi signing akan zata bashi kudi 40mil da sex.

Yayi dariya yace good girl, ke fa mace ce kyakkyawa sosai
Kin san kan makirci da munafuci i know kinsan yadda zaki samo kudin nan ba wani matsala
Sai ya soma tahowa daf jikin ta yana cewa Yanzu ma ai sai a soma bani jiki na lasa ya kawo hannu kan boobs dinta

A hujajan ta ja gefe tace bye saminu
In nazo maka kudi zamu fara deal ba yau ba.
Sannan ta fice..

Murna yayi sosai dama shi baruwan sa kowa ,business din sa kawai ya sa agaba bai damu da wani amana ba.



Gefen su Ash kuwa jasmine har bata son ayi dare gari ya waye bare yace zai koma nigeria ya barta

Don Kullum yana nan ya zamo mata komai ko motsi bai barin ta tanayi.

Kamal ne ya kira su yau ma cikin tsokana da annashuwa suka yi hira
Musamman da jasmine

Don shi kadai yasan yadda Ash yake son haihuwa hakan tamkar cikar wani burin sane na rayuwa

Don haka ash sai ya kwantar da hankalin sa yana rayuwar sa da baby maman sa a nitse
ya ma mance yana da wani side na rayuwar kunci a duniya..

duk abunda ke masa zafi a rayuwa ya kaucar ya sa hankalin sa kan jasmine da abunda ke cikin ta.

cikin nasara kuwa ya yanke hukuncin zai zauna ya cigaba da kula da ita har sai tagama classes dinta su dawo nigeria tare.



Kwance tashi Yau ana kwana na hudu da making deal din su zahida da saminu

Duk hankalin ta ya taashi sosai don tasan tabbas ta taba kudin ta mum dinta zata fara suspecting din ta.

Madam hidayat bata bacci bata duba lapyar arzikin gidan ba
ita kanta zahida ta san hatsari ne babba ta zare 40mil haka kawai ba dalili.

Ga Saminu ya dame ta sosai akan yana jira duk yabi ya sa ta a hot sit, ga shi ba jamal ba jabir
Ba kawaye bare aminan business kowa yayi sanyi da ita wajen ta rasa wa zata amsa kudin waken sa ko da aro ne ta mayar daga baya?


Ganin saura kwana biyu tal ya rage ma deal din yayi expire ya sa ta shiga rudanin tunani ga shi ta kwallafa aran ta tana so taji komai
Dadin karawa ance zatayi kudi ninkin ba ninki

Wani zazaffan ajiyan zuciya tayi ta rarumi wayar ta tace " bari dai na gwada na gani
Nan ta nemi numberr Ashweeen ta soma dialing
Har zuciyan ta na bipping tsaban bugu tana Allah Allah ya dauka ko da bazai bata ba ma ta dai ji muryan sa ko za taji sanyi a ranta.

Amma kash sai bai daga ba
a haka ta hakura ta goge hawayen ta da suka riga suka zubo

Cahn ta sake yanke wami hukuncin cikin dauriya ta rubuta masa sakon tex mesage mai cewa

__" how may times can i be wrong to u ,
nasan ba na maka adalci baby na. and dis time i can't even ask u for forgiveness cos im dispointed at myself, ena bukatar taimakon ka 40million naira pls help me Ash, ba don hali na ba for godsake."urs zahrod_
.

Suna kwance Jasmine ta mika masa wayar tace husband sakon ka ka ne.





*😅😅🤷🏼‍♀🏃‍♀ to ni dai nace ashween ka taimaka ma baby da kudi, fans ku tayani sa baki ko wajen hjy jasmine😅*





*surriem*
[23/08, 06:18] Surayyahms Frd Ruky. Raheema: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*



💔

*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_


_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥



*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.




*gaskiya Bakin ganga na kai min❤😪😪😪 Allah yy miki albarka asmeen💋*




*Page▶69*




Ashween sai ya motsa kadan Fuska ba yabo ba fallasa Ya karbi wayar ya duba ya karanta sai ya mayar ya ajiye a gefe.

Duk tana binsa da ido ba tace komai ba..
A ranta tace hmm maza kenan, i tot yaya ita yake so to meyasa yake waina ta haka akaina?

Hm maybe ko don kawai ya cika alkwarin ammy a kaina yake nuna min na fita daraja a wajen sa..tayi Zugum

what a pity for us both duk mun zama prisoners of love, ni ba a sona tun farko ita kuma ana kan yaudarar zuciyan ta wai ni sister sa,.wato shi so makamin cuta ne ,hmmm Allah dai ya nuna min ranar da zai zabi daya daga cikin mu kowa ya huta.

Tana ta kan maganan zucin ta shikam Yana kwance ya lumshe ido nan wayar sa ta sake ringing wanda ya dada sa zuciyan jasmine din sake bugawa ta dauka ko zahidan ne

Kafin yace zai motsa har ta dauke wayar ta duba,ya bude ido ya na kallon ta da sauri ta mika mas tana tura baki a shagwabe tace to yaya kamal ne.
Yay dan murmushi da gefen bakin sa ya karba ya tashi ya fita waje

Kallo ta bishi da shi tana dada surutu aranta don in yan kishin suka motsa komai ma bata yarda da shi..

Ya ce ya akayi ne ,kamal yace lpya gani nan nazo ena aiport en nagama da nan zaka raka ni siyayya

Please Login or Register in order to submit comment