Reading ABU NAKA Book 1 By SODANGI Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan kammala karatun da ya kai shi. Ya gina gidan ne a Misau don cika burin da ya dawo a kai na kyautata mu’amala tsakaninshi da mahaifinshi, wacce ta gurvace tun zamanin quruciyarshi.
Gidan Mus’am gida ne da ya amsa sunanshi, a garin Misau kawai ba har a garuruwa dake kusa duka kwatancenshi ake yi, shi da kanshi kuma ba zai iya faxin ga iyakacin dukiyar da ya kashe ba wajen gina gidan.
Tun dawowarshi daga wurin ta’aziyyar zaune yake shi kaxai a cikin falon, zuciyarshi sai kai kawo take yi kan shirmen da ya yi na cewa Saddiqa ta kawo mishi farfesun gidanshi bai ce mata zai turo direbanshi ya xauke ta ba.
To in ba ta zo ba fa? Ya tambayi kanshi. Dai-dai lokacin da ya sake mai da idanuwanshi kan agogo don ya qara ganin lokaci, qarfe uku ne da minti biyu, wajen awarshi biyu uku kenan rabonshi da ita. To farfesun kifi wani daxewa yake yi?
Maigadin gidan ya yi sallama Mus’ab ya amsa da fitan isowar Saddiqa zai gaya mishi. Sai ya je ya ce mishi “Wasu mutane ne suke son ganin ka ranka ya daxe”.
Takaici ya kama shi, ya ce, “Basu haquri Baba ka ce musu sai gobe su dawo”.
Baba ya xan rusuna kafin ya ce mishi, “Masu lalura ne na kuma ji ka ce lalura ta ciwo in aka zo da ita……”
Bai qarasa ba ya sake kallon Mus’ab a yanayin girmamawa ya ce, “Taimako suka zo nema suna mara lafiya ke garesu a asibiti”.
Mus’ab ya miqe tsaye ya ce, “Jira ni”. Ya shiga xakinshi ya fito ya miqa mishi bandir xin dubu ashirin.
“Ungo ka basu”.
Baba maigadi yasa hannu biyu ya karva tare da yi mishi addu’a.
“Yallavai Ubangiji ya saka maka da alheri, ya baka abin da kake nema na alheri duniya da lahira”.
Addu’ar ta yi mishi daxi. Ya ce, “Amin Baba”.
Huxu ta wuce Mus’ab yana zaune wurin da ya idar da sallar la’asar, har ya soma fidda rai game da zuwan Saddiqa, ya mai da hankali wurin jan carbinshi, lazimin yamma yake yi.
Sai da ya gama ya yi addu’o’inshi ya shafa ya tashi, juyowar da zai yi sai ya ganta a zaun, cikin zuciyarshi daxi ne ya kama shi, amma bai yarda ya nuna ba.
Sai ya ce mata, “Ke Aisha kin shigo min gida babu sallama, ya ya aka yi haka?”
Ta ce, “Na yi hankalinka yana wurin sallar da kake yi shi yasa baka ji ba”.
Ya ce, “To na yarda”.
Ya zauna can gefe kan wata kujera suna fuskantar juna.
“Ina jin dai da an fasa kawo min farfesun nan ne ko? Ko kuma an gama samari suka zo taxi aka mance da Yaya”.
Cikin nutsuwa da girmamawa ta ce mishi, “Ka yi haquri, cewa na yi tunda zan kawo maka to bari in yi maka abincin dare”.
Ya kalle ta ya ce, “Ke, ki ce min hankali ne dake ban sani ba”.
Cikin zuciyarshi kuwa yanayin girmamawar da Saddiqa ke yi mishi ne ya fi tsaya mishi, so yake ta rinqa sakewa sosai don ya ji daxin jawota a jikinshi ta yanda zai canza yanayin shaquwar dake tsakaninsu daga yanayin shaquwa irin na qaunar zumunci da girmamawa, zuwa shaquwa ta mu’amala mai sauqi.
“To me kika girka min?”
Ya yi tambayar cikin sakin fuska sosai. Ta tashi ta xebi kwanukan ta kawo gabanshi tana buxewa. Ya zubawa abincin ido yana kallo cikin sha’awa.
“Ashe dai aiki kika yi sosai, Ubangiji ya baki miji na kirki mai sonki ya sha lagwada a wurinki”.
Ya tsareta da ido don ganin yanayinta.
“Ba fa wannan saurayin naki nake yiwa wannan addu’ar ba, wani daban don ni bai kwanta min a zuciyata ba, sai nake ganin kamar akwai wanda ya fishi cancantar samun ki. Amma fa in maganar tawa ba ta yi miki daxi ba to ki yi haquri”.
Bai kawar da kai daga gareta ba, ita ma tana nan a yanayinta na sunkuyar da kai qasa.
“Kinga Baba maigadi da za ki shigo?”
Canzawar yanayin maganar tashi ya ba ta damar da ita ma ta canza.
Ta ce, “Eh, har ma ya tayani shigo da kwanuka”.
Ya ce, “To dama shi nake so ki xibarwa abincin nan, bi ta can za ki ga qofa kicin ne, ki buxe ta ki shiga ki xebo plate nawa da naki da na Baba maigadi”.
Ta ce, “Ai ni na qoshi”.
“A’a, to a ina ake yin haka Aisha za a kawowa mutane abincin da kai ba za ka ci ba”.
Ta sake cewa, “Na riga na ci a gida”.
Ya ce, “To shi kenan, kawo mu ci zubana”.
Ta tashi ta nufi inda ya yi mata kwatance, kicin xin da Saddiqa ta gani irin wanda take gani ne a mujallun Turawa da take karantawa, ko kuma a finafinan Indiya da take kallo, kusan mancewa ta yi da aiken da Mus’ab ya yi mata ta lalace wajen kallon tsarin kicin xin, bai da mace a gida amma ya yiwa kicin…..
Kiran da ta ji ya yi mata ya dawo da ita cikin yanayinta, ta yi maza tasa hannu ta xebi plate xin da duk wani abin da ta san za ta buqata ta fita.
“Hala kin tsaya kallon kyanki ne a madubi”.
Maganar tashi ta sata jin kunya, ta sunkuyar da kanta.
“Ai ba sai kin kalli mudubi za ki gane hakan ba, Aisha ke mai kyau ce, ko kina so ne ki nuna min cewar shi wannan saurayin naki bai gaya miki irin kyan dake gare ki ba?”
Shiru ta yi ba ta tanka mishi ba, sai dai kuma ta kasa zuba abincin a sunkuye kawai take.
“Ai in nine saurayinki kullum sai na gaya miki kina da kyau Ai…..”
Yanayin da ya gani a fuskarta ya sa shi hanzarin canza maganar tashi.
“To zuba mana abincin mana”.
Ta zuba ta haxa a kan madaidaicin tire da nufin ta kai wa Baba maigadi, ya yi maza ya miqe ya xauka.
“Yi zamanki bari ni in kai mishi”.
Ya gama cin abincinshi ya qoshi ya xan kishingixa suna hira bayan ta kawar da komai daga wurin ta gyara ta mai dasu mazauninsu.
“Hala Abu ke koya miki girki?”
Ta yi murmushi ta ce, “Gwaggona fa?”
Ya ce, “Uhm! Kin san ni ban cika sanin daxin abincin Inna ba, saboda sanda nake yaro sau da yawa na kan ci abincin ne bayan an yi min duka, ina kuka kuwa ai ba zan ji wani xanxano ba ko kuwa?”
A hankali ta xago ta kalle shi a yanayin muryarta mai cike da nutsuwa ta tambaye shi, “Dama Gwaggo tana duka ne?”
“Saboda bakya gagara shi yasa ba za ki san hakan ba, amma ni sanda nake yaro rigama ce dani, kina nufin baki tava jin labarin gagarata ba?”
Ya yi tambayar yana mai kallon ta.
“Uhm! Ai ba ta yin hirarka”.
Suka xan yi shiru, jimawa kaxan sai ya sake shigo da wani zancen.
“Wato kenan tunda kika gama sakandire shi kenan kin gama karatu ko? Kin dena neman ilimi kin fi so ayi miki aure ko?”
Ta ce, “A’a”.
Ya ce, “A’a, ya ya ne?”
“Gwaggo ce ta ce ya isa haka”.
“Shi yasa kike hira da samari? Kullum na zo garin nan sai na ganki kina hira da saurayi ko kunyata bakya ji ko?”
Ta sunkuyar da kanta qasa.
“Wai jiya ma har na shiga gidan na fito ko zuwa mu gaisa baki samu damar yi ba don kina tsoron kar ya yi fushi ko?”
Ta ce, “A’a, ba zai yi fushi ba, ai shima ya ce wai zai zo ya gaishe ka kafin ka koma”.
Mus’ab ya ce, “A’a, ya sha zamanshi bana son gaisuwarshi”.
Ta xago ta kalle shi saboda maganar tashi, idanuwansu suka haxu ta yi hanzarin kawar da nata.
“To meye gamina da shi da zai zo gaisheni? Ba yana zuwa gai da su Abu ba? Ki gaya mishi ni na ce bana son gaisuwar shi don ba zan yi surukuta da shi ba, ya rinqa zuwa gidan su Inna da su Abu da suka san da zaman shi suke kuma xaure mishi gindi, sai ko ke da na ji an ce wai kina mutuwar son shi”.
Ta sake xagowa ta sake kallon shi a wani yanayi. Bai kawar da kai daga gareta ba ya ce, “A to, nima a bakin Abu na ji, abin da ta gaya min kenan wai kuna mutuwar son juna”.
Ta sake kallonshi, “In ji Abu?”
Ya ce, “Eh, ko ba haka bane?”
Ta yi shiru. Ya ce, “In ba haka bane ai sai ki gaya min in ji”.
Ta ce, “Ai ni na daina yin wannan maganar alqawarin da na yiwa Gwaggo kenan”.
“To na ji kin yi alqawari, amma kina son shi ko bakya son shi?”
Ta ce, “Ina son shi”.
Falon ya yi shiru na wani tsawon lokaci saboda faxuwar gaban da Mus’ab ya samu.
Ya yi qoqarin kawar da damuwar ta hanyar yin jarumtakar faxin “To ko kina sonshi ai yin karatu ba laifi bane”.
Ta langavar da kai kafin ta ce, “Tunda Gwaggo ba ta so shi kenan na haqura”.
Ya ce, “Haka ne Aisha, ga dukkan alamu dai kirki ne dake, don waxannan kalaman naki alama ne na zurfin nazari”.
Ta ce, “Zan tafi, don Gwaggo ta ce kar in daxe”.
Ya ce, “To Aisha, ai na gode miki kin yi min abinci mai daxi na ci na qoshi, ban da haka kuma kin yi min hira, iya kai dai hirar taki ba ta ishe ni ba, na kuma san in na ce zan biyoki gida mu qara ba yarda za ki yi ba, za ki ce saurayinki zai zo kar in zo in yi muku buqulu in hanaki hirar soyayya”.
Ya zuba mata ido a yanayin zolaya, “Ga kuma irin toshin nan da samari ke yiwa ‘yammata in sun zo hira”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ba fa kullum nake hira ba Yaya, sau xaya nake yi a sati Juma’a, dace kake yi kana samuna ina hirar saboda qarshen sati kake zuwa”.
Ya ce, “Ai shi kenan Aisha, zan iya yarda dake a kan komai tunda na san ba za ki yi min qarya ba”. Ya ce, “To yanzu tunda nima kin zo min hira me kika gani ya baki sha’awa a gidan nan?’
Ta yi murmushi ta ce, “Komai na gidanka ya bani sha’awa, musamman kicin xin. Sai dai ban buqatar ka bani komai na gode”.
Ya tashi ya shiga xakinshi ya fito da kwalin handset ya miqa mata, ta zuba mishi ido nuna alamar ba za ta karva ba.
“Gaskiya kyautukan da kake yi min sun yi yawa, ni wani lokacin ma har tsoro suke bani”.
Ya tsareta da idanuwanshi ya ce, “Wace irin magana Aisha ke gaya min? Nine mai yi miki kyautar da take baki tsoro? Kina nufin su Bilki sun fi kusa dani ne? Don dai baki da wayo ne sanda Inna take raye ko? Ina ganin da ba sai na tsaya ina gaya miki muhimmancinki a wurina ba, ba sai na tsaya ina gaya miki cewar bani da wata wacce zan yiwa alherin da zai sani jin daxi fiye dake ba. Ni dama na daxe na gane yanda nake jinki ba haka kike jina ba”.
Da sauri ta ce mishi, “Ba haka bane Yaya”.
“To in ba haka bane ya ya ne? Yanzu da kin mai dani nine na fi kowa kusa dake kamar yanda kike a wurina kya gaya min wannan maganar don kawai na ce ga waya, ko gaisuwar safe ma rinqa yi da safe”.
Tasa hannu biyu ta karva tare da yin godiya. Ya miqa hannu ya xauko xan makullin motarshi dake ajiye ya ce, “Muje in kai ki gida”.
Ta ce, “To”.
Sun fito harabar gidan kenan su kai kicivis da wata mota qirar Honda mai nambar Azare tana shigowa.
Mus’ab ya kalle shi ya ce, “Sai dai ka jira ni in je in dawo don ba zan fasa mai da yarinyar nan gida ba”.
Mutumin ya fito yana murmushi, ya ce, “To ka tsaya in zo mu gaisa mana don mu san juna ko kuwa?”
Ya ce, “A’a, ba sai kun san juna ba qanwata ce wannan, don na ga kana wani murmushi”.
Ya ce, “Eh, in dai gantan a haka tunda ku dama Fulani ai qannenku ne suke rikixewa su zama matanku”.
Mus’ab ya ja mota ya tafi, sai da suka hau hanya sosai sannan ya ce mata, “Aisha”.
Ta yi maza ta juyo gare shi. Ya ce, “Wannan fa shine Sham’unu abokina da nake zuwa wurin shi a Azare”.
A nutse ta ce mishi, “Na gane shi, watannin baya ka zo bikin shi”.
Ya ce, “Haka ne baki manta ba”.
Qofar wani hamshaqin kanti ya tsaya, fuskarshi a xaure ya kalli Saddiqa a yanayi na rashin wasa ya ce mata, “Muje ki duba man shafawa”.
Ta xan yi shiru. Ya fita ya rufe motar. Ya kusan minti talatin kafin ya fito, ana biye da shi da manyan ledojin sayayyar kantin guda biyu. Ya sake tsayawa a wani wurin ya sayi gasassun kaji sannan suka tafi gida.
A qofar gidan ya sauke ta da kayan ya juya ya tafi.
Cikin dare tana kwance a xakinta Mus’ab ya yi mata waya.
“Tun xazu na so na bugo in tambaye ki wani abu sai na fasa don tsoron in bugo in sameki kina taxi”.
Ta ce, “Taxi kuma Yaya? Ba ka ce in na gaya maka magana za ka gaskatani ba don ka san ba zan yi maka qarya ba?”
Ya ce, “Qwarai kuwa Aisha, ai na yarda dake da kuma zan samu yanda nake so da kema sai ki yarda dani mu yarda da juna”.
Ta ce, “To ai na ce maka sau xaya nake hira a sati, kuma xazu ka ce min in na zo gidanka za ka gaya min laifin da na yi maka na zo baka ce min komai ba”.
“Dama maganar karatunki zan yi miki, to kuma na gane bake ce bakya son yi ba Inna ce ta ce ya isa haka ki yi aure. To ai ba zan ce kar ki yi ba Aisha, tunda na san alheri ne nima da kika ganni ina zaune haka tuzuru don tawa uwar ta rasu ne da ban kawo yanzu a hakan ba”.
Ta kawar da zancen nashi ta hanyar tambayarshi, “Me kake son tambayata?”
Ya ce, “Lokacin da nake yaro na san Inna da yawan nafilfilin dare, har nima ta kan tasheni ta ce wai in yi sallah in roqi Ubangiji ya shiryar dani, kema tana yi miki haka?”
Ta ce, “Ai na riga na saba yanzu ba ma sai ta tashe ni ba da kaina nake tashi”.
“To in roqe ki mana Aisha”.
Da sauri ta ce mishi, “To”.
“Ki rinqa yi min addu’a”.
Ba ta ja maganar ba ta ce, “To zan yi”.
Ya ce, “To sai da safe”.
Saddiqa ta ajiye wayar tana tunanin tsakaninta da Yaya Mus’ab, a saninta dai tun tana ‘yar qanqanuwarta yana cikin mutanen da suke da muhimmanci a wurinta, saboda xinbin kulawarshi a gareta. Shi mai sonta ne, mai kula da ita, mai yawan alheri a gareta, a dalilin hakan ne ma ta fi kowa farin cikin dawowar shi.
To amma a yanzu halin da take ciki, tana cikin ruxani ba ta fahimtar al’amuran, varin dukiyar da yake yi mata bai yi mata daxi, a ganinta ko ‘yan’uwanshi da suke ciki xaya ba ya yi musu haka.
Washegari da safe ta idar da sallar asuba kenan ta ji qarar wayarta, ta sa hannu ta xauka.
“Ina kwana Aisha?”
Ta amsa, “Lafiya lau Yaya, ya ya gidan?”
Ya ce, “Lafiya, sai dai ban yi bacci ba jiya”.
Da sauri ta mishi, “Nima haka?”
“Me ya hana ki bacci Aisha?”
Ta yi shiru. Sai ta ji ya soma yin bayanin cewa, “Ni kin san ban iya voye-voye ba, tunanin aure ne ya hanani bacci, Aisha sai na ga ke gaki yarinya ‘yar qarama don sanda aka haifeki ina ganin kamar in ban yi sha bakwai ba na kusa, amma ga shi iyayenki sun tsaya suna son ganin sun aurar dake, ni kuma ina zaune a haka.
Sai na ga to ai dama an ce wai in ka rasa uban da zai yi maka faxa sai ka ga wani yana yiwa xanshi faxa. To sai ka rava kusa ka ji abin da yake gayawa xan nashi, don kai ma ka amfana da kalaman nashi. Shi yasa na ce to bari nima dai in hankalta da abin da ake shirin xora ki a kai in yiwa kaina qiyamullaili, ko kuwa?”
Cikin nutsuwa ta ce mishi, “ Haka ne”. Ta ja bakinta ta yi shiru.
“To ni na gaya miki abin da ya hanani bacci ke fa? Me ya hanaki yin bacci?”
A hankali ta ce mishi, “Anti Kuluwa ce ta zo gida jiya da daddare suna rikici da mijinta, ka san zai yi aure?”
Mus’ab ya ce, “A’a, wa zai gaya min Aisha in ba ke ba? Inna ba ta hira dani, Baba kuwa cewa zai yi nima ba auren gare ni ba balle aje ana tsomani cikin lamarin rikicin aure, amma in zai yi aure Aisha sai ta je tana rikici da shi?”
Ta ce, “Ai shi ya ja bai biyo ta hanyar son a zauna lafiya ba, lokacin da ya zo gaya mata zancen auren shi sai ya yi mata alqawarin canza mata kayan xaki, yanzu kuma bikin ya zo ya ce mata wai hidima ta yi mishi yawa bayan da can ba roqon shi ta yi ba. Shine abin ya tsaya min a rai, na ce to dama haka ake yi ne in za a kawo sabuwa sai ayi kamar ta gida ba sonta ake yi ba?”
Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “To ni kam ina zan sani tunda ani ko xayar ma ban yi ba. Ai shi yasa na tsarawa kaina tunda dai ni na san kaina ni ba wani jarumi bane fitina tsoro take bani, don haka na ce to in dai har na samu na auri matata guda xaya in dai har na samu wacce nake so xin to ta isheni”.
“Ai nima shine na ce ko randa za a yi min tawa amaryar ya ya zan ji oho”.
Mus’ab ya qyalqyale da dariya ya ce, “Ya ya za ki ji kuwa ban da yanda sauran mata suke ji, ga dukkan alamu dai ina jin kishi za ki yi Saddiqa?”
Ta ce, “To a yanzu dai kam ban sani ba tukunna sai a nan gaba”.
Ya ce, “To da na y niyyar sai na dawo daga Kano in zo gidan, amma ina ganin zan zo yanzu kafin in tafi”.
Ta ce, “To, sai ka zo”. Ta ajiye wayar.
Mus’ab yana zaune a falon baban shi bayan fitar Malam Abdullahi jiran shigowar Saddiqa yake yi.
“Wa alaikumus salam”.
Ya amsa. Ta shiga ta zauna ta ce,
“Ga ni Yaya”.
Ya xauki rubutaccen chaque xin dake ajiye a gabanshi ya miqa mata ya ce, “Ki kai wa Kuluwa wannan chaque xin ta karvi kuxin ta yi hidimomin gabanta, ki gaya mata kar ta sake yiwa mijinta wata magana su zauna lafiya kawai”.
Daxi ya kama Saddiqa ganin kuxin dake rubuce.
“Yaya Ubangiji ya qara maka arzikinka”.
Ya sake miqa mata envelop guda uku, “Ki kawai Bilkisu xaya, Hamida xaya, kema xaya, na san in za su sayayyar bikin za ki raka su”.
“Mun gode Ubangiji ya dawo da kai lafiya”.
Ya ce, “Ameen”.
Da yamma Mus’ab yana gidan Abu, hirarsu suke yi irin wacce suka saba, yana kuma cin dambun zogalen da ta yi mishi.
Saddiqa ta yi sallama ta shigo cikin kwalliya sosai mai ban sha’awa, ga yafen lafayan da ta yiwa jikinta ya yi matuqar karvarta. Rungume take da leda a hannunta, tana ganin Mus’ab ta qara fara’arta.
“Ashe har ka dawo?”
Ya ce, “Eh, tun la’asar nake nan gidan”.
Ta tsuguna ta gaisheshi shi da Abu. Ta miqawa Abu ledar dake hannunta ta karva tare da faxin “Tsaraba aka kawo min?”
Ta ciro ta, atamfar Diamond ce mai kyau, tare da kwalbar turare.
“Atamfa na samu? To Allah ya yi albarka, hala yau ma zannuwan kika saya?”
“Ka ji Abu, me zan saya? Su Yaya Hamida ne suka yi sayayyar kayan xaki, ni kuwa na sayi kayan ado. Yaya Kuluwa kuwa…. Ta qyalqyale da dariya kan ta yi bayani.
Tsakin da Abu ta ja ya katseta. Abu ta ce, “Sakarya, ‘yammata suna tari ran bikinsu ka ga sun fito da kaya gwanin sha’awa amma ke kullum kuxinki a zannuwa kina tsoma su a ruwa shi kenan kin wanke kuxinki”.
Ta yi dariya ta ce, “Amma ai kuma kwalliyar tawa tana burge ki ko. Tunda na sha jinki kina cewa daxin ki dani akwai ni da kwalliya, shi yasa ma duk tsiyata ba ta dame ki ba”.
Mus’ab ya yi murmushi ya ce, “Aisha wani iya tsiya ne dake?”
Abu ta yi maza ta riqe baki ta ce,”Wuuu! Ai ko sarkin fawa ya san da ita”.
Mus’ab ya yi dariya ya ce, “Mahauta su ji abin da kike gayawa sarkinsu”. Ya yi dariya yana kallon Saddiqa ya ce, “Bani ruwa mai sanyi a randar

Please Login or Register in order to submit comment