Reading TRIPLETS BOOK 1 and 2 COMPLT BY FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA Chapter 53 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan uban ki, ban son munafurcin banza" shiru Umaisha tayi bata amsa mata ba, kukan ta kawai take.

A fusace Ammie ta haye saman gadon tare da yaye bargon da Umaisha ke lulluɓe, ta riƙon ta, ta miƙar da ita tsaye tana faɗin "To wuce a kai kaya ma sauki" kasa tsayuwa Umaisha tayi, Ammie na sake ta, ta zube a kan gadon tare da kara sautin kukan nata, daidai lokacin Akila ta shigo ɗakin, kamar zatayi kuka tace

"Ammie dan Allah kiyi hakuri ki barta kinji?" Ammie bata kula taba, sai ma kara mikar da Umaisha tayi, ta jata, sai kokarin faɗuwa kasa Umaisha take saboda jikin ta ba kwari, kuma ba zata iya taka kafar ta ba, saboda azaban da take ji, sai kukan wahala take abun gwanin ban tausayi.

Kai tsaye waje Ammie ta nufa da ita, tana jan ta kamar wata rago, sai kuka Akila take tana addu'ar Allah ya kawo yaya Akil ko Abba.

Ammie tana zuwa bakin kofar Palo, ta tura Umaisha waje tana faɗin "Kar na sake ganin kafar ki a gidan nan" tana turata ta tafi sai saman kirjin Akil ta faɗa, yanzu ya dawo daga masallaci yana kokarin shigowa kenan

Umaisha na kokarin sulalewa kasa daga kirjin nasa, yayi saurin riƙota yana kallon Ammie dake tsaye a bakin kofa tana kallon sa

Kasa tsayuwa Umaisha tayi dan kafar ta babu kwari, sai kerma jikin ta keyi, dawo da kallon sa kan fuskar Umaisha ɗin yayi, kasa kasa yace "I'm so so sorry" ya kai karshen maganar tare da ɗaukan ta cak, ya juya ya bar wajen, ya nufi motar sa da ita ba tare da yace da Ammie ko uppan ba, dan baya son jan magana da ita a kan Umaisha, yasan halinta sarai zata iya yi masa baki a kan hakan, ta raba shi da Umaisha, shiyasa baya son maganar Umaisha ta haɗa su

juyawa ita ma Ammie tayi ta koma cikin Palo, tana jan guntun tsaki, a tunanin ta Akil zai mai da Umaisha gida ne. Ita kuma Akila tana ɗakin Akil tana kukan ta.

Kai tsaye asibiti Akil ya wuce da Umaisha dan yaji jikin ta da zafi sosai, yan gwaje gwaje aka mata, sannan aka basu bagunguna, ya ɗauko ta suka dawo gida.

A palo ya samu Ammie da Akila suna zaune, Abba bai dawo ba, bai yiwa kowa magana ba, ya wuce ya nufi ɗakin sa, "Akil kazo ka ci abinci" cewar Ammie, a takaice yace "Bana ci, na ƙoshi" yayi maganar ba tare da ya tsaya daga tafiyar da yake ba, "Ka fitar da yarinyar nan daga gidan nan nace ko?" Ammie ta sake yi masa magana, shiru yayi bai tanka ba, ya wuce bedroom nasa.

Saman gado ya kwantar da Umaisha, wadda take fitar da numfashi da kyar saboda wahala, bargo yaja ya rufa mata sanna ya fice ya dawo palon

Kusa da Ammie ya zauna yana faɗin "Ammie me yasa yanzu baki son farinciki nane ne? Me na miki? So kike na mutu ne eh Ammie na?" Zaro ido tayi kafin tace "Haba Akil kasan me kake faɗe kuwa? Nice bana son ka? Idan ni bana son farincikin ka waye kake tunanin zai so farincikin ka?" Kallon Akila dake zaune tayi shiru tana tunani, tasha kuka ta koshi, dan ita a tunanin ta Ammie ta kori Umaisha ɗin ce

"Heartbeat tashi kije ɗaki bari muyi magana" Akil ya faɗa yana tsare Akila da ido, tun bai kai karshen maganar ba ta miƙe ta wuce bedroom nasa wajen Umaisha, dan bata da burin da ya wuce ta gan ta tare da yan uwan ta.

Dawo da kallon sa yayi kan Ammie cikin nitsuwa yace "Ammie na faɗa miki ina son matata, kuma ita ce farinciki na, me yasa baki son hakan? Me ta miƙi? Na san bai wuce kice abun da ya faru tsakanin ku da baban ta, da kuma su bappa Husaini bane, to ita me nata a ciki, kinga ai ita bata san komai ba, kuma da wuya ma idan ta san labarin abun da ya faru kafin a haife mu, dan Allah Ammie ina son kiyi min wannan alfarma, ki yafe wa family'n Abbana komai ya wuce kinji ko?" Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun ta yana kallon cikin idon ta "Akil, Akil, Akil, sau nawa na kira sunan ka?" Shiru yayi yana kallon ta

"Ba zaka bani amsa ba, nace sau nawa na kira sunan ka?" "Sau uku kika kirani Ammie" ya bata amsa, "To wlh ka fita ido na, karka sake min maganar su Hussaini a gidan nan, ita kuma yarinyar tun da kace ita kake so, kaje kai kasani da ita can, in dai family'n Abban kane da kan ka ma zaka guje su ba sai wani yace ka barsu ba" murmushi yayi kafin yace "Shikenan Ammie in dai kin yarda na zauna da ita shikenan ba damuwa ai" kawar da zancen tayi da cewa "To ka tashi ka ɗauko abinci ka kaci" to kawai ya amsa da shi tare da miƙewa ya nufi saman table ya ɗauki abinci kula ɗaya da plate ɗaya tare da spoon shima ɗaya, ya wuce bedroom na sa, binshi da kallo Ammie tayi, kasa kasa tace "Ba zan taɓa bari ka zauna da yarinyar nan ba, dan bana son ta, kuma bana kaunar iyayen ta, dole ka rabu da ita"

Da sallama ɗauke a bakin sa ya shiga cikin bedroom na sa, Akila na zaune saman gado tana rarrashin Umaisha dake ta faman kuka har lokacin.

"Heartbeat ɗauko min Yoghurt a Palo" turo baki Akila tayi kafin tace "Yaya Akil ba haka zaka ce ba, kace Heartbeat tashi ki fita min a ɗaki" murmushin yayi kafin yace "Ni na isa in ce ki fita min a ɗaki ne? Yoghurt fa kawai nace ki ɗauko min" "Yaya Akil yaushe ka fara shan Yoghurt ban sani ba? Kai da ko tea da madara baka sha saboda karni shine yau zakace na ɗauko maka Yoghurt, na sani ba wani Yoghurt kawai korata kake yi" ɗaga mata gera ɗaya yayi yana faɗin "To tun da kin gane me kika tsaya yi ware da wuri" dariya tayi tana faɗin "Ba damuwa yaya Imran ya kusa dawowa ai, idan ya dawo ba zan sake zuwa nan ba, kuma shi nasan ko ya auri Aunty jelly ba zai koreni a ɗakin saba" "oho dai tashi ki tafi" yayi maganar yana kokarin hawa saman gadon, bayan ya ajiye musu abincin su saman table dake cikin ɗakin,
Da sauri Akila ta diro kasa daga saman gadon tana faɗin "Aunty Umaisha Amarya sai da safe, yaya Akil mun ɓata da kai" shiru ya mata, dan bai son biye mata, so yake ta fita ta basu waje.

Tana fita ya sanya hannun sa ya tallaɓo Umaisha yana faɗin "Sorry tashi kici abinci kisha magani" cikin kuka tace "Na koshi" girgiza kai yayi yana faɗin "a'a ban yarda ba ki tashi kici" ba dan taso ba, haka ya miƙar da ita zaune ya rinƙa ɗura mata abinci tana ci dan dole

Bayan ta gama ya bata ruwa ta sha, sannan ya mai da ita ya kwanta, ya sauƙo ya wuce toilet dan yayi wanka yazo ya gabatar da sallar issha da bai samu yayi ba, sakamakon kai ta asibiti da yayi.

Bayan yayi Sallah ne ya haye gadon kusa da ita ya kwanta, yana faɗin "I'm sorry kinji?" Shiru ta masa ba tayi magana ba na ɗan lokacin kafin tace "Ka mai dani gida kada Abbi ya neme ni" juyo da kallon sa yayi kan fuskar ta "Already na kira bappa a waya na sanar masa da nazo na ɗauke ki daga school kina tare dani" mamaki ne ya kamata tace "Abbi na fa wanda ya haifeni" ya gane me take yiwa mamaki, wato ya za'ayi Abbi ya yerda ya ɗauke ta su tafi su kwana, bayan ba aure sukayi ba, shine abun ya kulle mata kai

"Eh Abbin maki fa, bakin san cewa ke matata bace ko?" Shiru ta zuba masa ido tana kallon sa "To ki rufe idon ki ya isa haka kallon nawa, karki haifa mana baby mai kama dani, zai fi kyau ki haifi mai kama dake, kiyi barci da safe zamuyi magana" ya kai karshen maganar tare da sanya hannun sa ya rufe mata ido, mamaki ya hana ta magana ta kwanta shiru, da haka barci ya ɗauke ta.

Shima shiru y kwanta har barci ya ɗauke sa. Ammi kuma tana can palo tanan saka yadda za tayi da Akil dan ya rabu da Umaisha, Akila kuwa tana fita ɗakin Akil nata ɗakin ta wuce dan taje ta kira daddyn Jelly dasu Abbi, yayan Imran, haka take, kafin tayi barci sai ta kira kowa daga cikin yan uwan ta, har da Abla sun sha hira sannan take barci.

Muleƙo Washington DC mu dawo

Yau ban haɗa muku page biyu bane, sakamakon bana jin daɗin jikina, shiyasa ban samu damar yi muku editing 2 page ba, amma In Sha Allah gobe zan biya

Karku manta idan Allah ya kai mu ranar Jumma'a da rai da lafiya, zan ɗauki hutu na ɗan wani lokaci, dan in ɗan huta in samu kwakwalwata tayi fresh, in ji daɗin zubo muku zafafan page's masu tashin kai, ina godiya sosai da sosai Allah ya bar zumunci 🥰

Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu .
[11/11, 8:52 PM] +234 906 579 6460: 💞💞TRIPLET'S💞💞






# BOOK 2📚📙✍️


💔💔Episode 5-6💔💔


💔RIMSHA💔


💞💞Washington DC💞💞

09:30am

A hankali yake sako kafar sa a saman benen yana tafiya kafar baya son taka kasa, jikin sa gaba ɗaya a mace, sai wani cizan lallausan laɓɓan sa yake, jikin sa na sanye da Ripped Jeans black color, da white Round neck t-shirt, kayan sun masa kyau sosai da sosai, kamar dan shi akayi su, kyawawan fararen kafafunsa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal fari tas kalar rigan sa, ya ɗaure wannan kyakkyawan dark black curly hair nasa a bayan, ya bar wanna ɗan guntu a gaban goshin sa, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshi yake, kamar anyi ɓarin turare.

Palon kasa shiru babu kowa kasan cewar already sun riga sun breakfast kowa ya kama harkan gaban sa, masu barci sun koma barci, masu fita sun fice yawon party da sauran su, dan basu da aiki da ya wuce wannan.

Jiki na kerman tsoro bodyguard dake cikin palon suka fara ɗaga masa gaisuwa ta hanyar ɗaga hannayen su, suna sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba, ya sa kai ya fice daga palon.

Already an jera motocin da zasu fita, shi kawai suke jira. Yana fitowa jibga jibgan sojojin sa suka fara sara masa, wucewa yayi kai tsaye ya nufi motar sa kirar Bugatti La voiture, da sauri wani jibgegen soja yazo ya buɗe masa motar, ya shiga ya zauna. A guje sauran sojojin suka haye saman bayan nasu motoncin.

A jere motocin suka tashi, suka fice daga gidan, tare da sakin jiniya, tamkar yaki zasu tafi. Kai tsaye white house suka nufa.

Kun dai san yadda white house yake ba sai na tsaya dogon bayani ba, ko ta ina sojoji ne kewaye a cikin gidan, hannayen su riƙe da manya manyan bindigu masu rai da lafiya, ga yan sanda ma ba'a barsu a baya ba, suna tsai tsaiye.

His excellency mr president yana cikin fadan shugaban kasa, kai tsaye wajen sa Romeo ya nufa yana taku irin na manyan jarumai sadaukan yaki, duk in da ya wuce sai sojojin wajen sun sara masa, jibga jibgan sojojin sa huɗu ne suka take masa baya har zuwa bakin kofar shiga cikin fadan, a daidai wajen suka dakata, shi kuma ya shige ciki.

Fadan shugaban ƙasa waje ne mai girman gaske, duniya ne guda, cikin fadan ɓangarori ne daban daban, sannan akoi ofisoshin da dama a ciki, kaɗan daga ciki, akoi office ɗin shi kan shi His excellency mr president, sai office na vice president, sai na secretary sa, da dai sauran su, sannan akoi manya manyan kujeru masu rai da lafiya, launin ja set nasu daban, haka zalika launin blue suma set nasu daban, akoi abubuwa da dama wadda faɗen su da baki ba zai yiwu ba, sai dai ku kawata su a ran ku, a takaice dai fadan shugaban ƙasa ya haɗu iya haɗu, domin tsayawa zayyana muku yadda cikin fadan yake zamu jima bamu gama ba, dan fadan dunaya ce guda.

Kusa da His excellency lion ya wuce yaje ya zauna, kallon sa cike da so da kauna His excellency yayi yace "My dear what is happening, naga kamar ranka a ɓace?" Ba sai na faɗa muku ba, kun dai san da turanci suke magana.
_Shiru lion yayi na yan sakanni kafin yace "kasan komai uncle ba sai na sake faɗa maka ba, Ina son a matsayin ka na president kayi magana da president na Spain, ina son a bincika min bayan James ya sauƙa daga jirgi ina ya nufa, shin ya hau wani jirgin ne ko kuma ya shiga cikin kasar ne, idan ya shiga cikin kasar wani gari yaje, uncle ina da ayyuka dayawa, ba zan iya zuwa Spain yanzu ba, kuma ina da tabbacin duk in da James yake yana cikin damuwa da tashin hankali, na kasa samun nitsuwa, ina jin har cikin zuciya ta, James na neman taimako na, a halin da nake ciki yanzu, ba zan iya fita daga Washington DC ba, saboda matsawa ta zai iya sanya mu rasa jigo na rayuwar mu, wato daddy, a situation ɗin da daddy yake yanzu, yin nisa da shi babban haɗari ne, da gara idan Michael yana da lafiya ma, zai iya ɗebe masa wasu matsaloli da kuma damuwa na rashin mu ni da James, amma ace babu ko ɗaya daga cikin mu, abune mai wuya a gare shi ya iya zama, jiya nayi tunanin zanje Spain da kai na, zuwa wayen gari na sake wani tunanin kuma, hakan ba mai yiwuwa bane, jiya ne kaɗai daddy bai ga James ba, ya damu sosai, yau da safe tun karfe 6 yazo bedroom na, wai sai na kira masa James a waya dan yayi mafarkin sa, da kyar na lallaɓa shi ya hakura, idan aka ci-gaba a haka, tofa akoi babban matsala, ka sani kuma ba sai na sake maimai ta maka ba" shiru His excellency ya ɗan yi kafin yace "Yes you are right, but kana ganin wani abune ya faru da James?" "No uncle i don't know, ban sani ba, kuma bani da amsa a kan hakan, sai dai ina ji a jikina hakan ne" shafa dark black curly hair sa His excellency yayi yana faɗin "I really like William family so much" ya kai karshen maganar tare da mannawa lion kiss a kumatu "Same here uncle we like you" ya faɗa shima yana mannawa kakan nasa kiss a goshi, murmushi His excellency yayi kafin yace "My lion zanyi yadda kake so, fata na dai James yana cikin koshin lafiya, sanna kuma ka kula da William da Michael sosai, yanzu nauyin su na kan ka, kada ka bari William ya san abun da ya samu Michael, idan hakan ya faru zamu iya rasa shi, ba tare da mun shirya ba" miƙewa Romeo yayi yana faɗin "Maybe in dawo yau maybe kuma sai gobe, duk yadda kayi da president ɗin Spain zan kira ka zuwa dare" ya kai karshen maganar tare da wucewa, ya nufi hanyar fita daga fadan, sai fatan Alkhari His excellency ke masa, a zuciyar sa yake amsa fatan alkharin da kakan nasa ke masa.

Yana fitowa sojojin da suka take masa baya zuwa bakin kofar fadan, suna tsaye a wajen, yana fita suka bi bayan sa zuwa wajen mota.

Kamar yadda suka zo, haka jerin gwanon motocin suka tashi, suka bar white house, suka nufi *Madstar Washington hospital center*.

Alhamdulila ba laifi jikin Michael ya fara kyau, saboda kwararun likitoci da suka tsaya, tsayin daka wajen ganin sun bashi kulawa, ga kuma kayan aiki masu kyau, inganci, da kargo. Sun cire masa kayan jikin sa, sun sanya masa kayan asibiti na majinyata.

Kusa da shi lion yazo ya tsaya yana kallon yadda fuskar sa ta sauya kamar ba Michael Triplets ɗin sa ba, ko motsi baya yi, da alama har yanzu bai san in da kan shi yake ba.

Romeo ya ɗauki tsawon lokaci yana kallon sa kafin ya juyo yana kokarin fita daga ɗakin idon sa ya sauka kan diamond watch nasu na Triplets na Michael, ɗaure saman wani kyakkyawan plate irin na ajiye zobe abun hanu na majinyata, da likitocin suka cire masa ne, sai suka ajiye a wajen, hannu Romeo ya kai ya ɗauki watch ɗin, ya nufi hanyar fita daga ɗakin, yana yiwa Michael addu'ar samun lafiya.

Gida lion ya koma bayan ya bar hospital, dan baya son yin nisa da dad, kasan cewar ba Michael kuma ba James, idan shima yayi nisa da shi za'a iya samun matsala.

Babu kowa a palon kasa, sai daddaɗar kamshi air freshener da sanyin Ac dake tashi, ko'ina a palon a gyare yake tsab, kamar sabbin kaya aka zuba, wucewa yayi ya haura sama, kai tsaye bedroom ɗin dad ya nufa.

Daddy na kwance saman gado, yana kallon News a jikin makeken Tv plasma dake manne a bango a cikin ɗakin, kusa da shi Romeo yaje ya zauna yana faɗin "Good afternoon dad" murmushi dad yayi kafin yace "My lion how are you doing?" Shiru Romeo yayi bai amsa ba, dan shi ba hira yazo yi da dad ba, kawai yazo su zauna ne dan kar ya fara sa masa rigiman ya kira masa James ko Michael, dan dad idan ya fara rigiman shi kamar ƙaramin yaro haka yake zama saboda tsufa, sannan kuma ga ciwo dake damun sa.

Ganin Romeo yayi shiru ya zubawa Tv ido kamar mai kallo ne, amma kuma a zahirin gaskiya ba kallon yake ba, kawai dai yayi zubawa Tv dara daran idon sa ne, wani tunani daban yake yi "My lion wai up till now Michael bai dawo bane? Ko dai ya tare wajen His excellency ne" ba tare da ya kalli dad ba yace "in the evening zai dawo" "What about James?" Nan ma ba tare da ya kalli dad ba yace "Sai bayan two weeks ko three zai dawo" zaro ido dad yayi ya miƙe zaune yana faɗin "What? Wai me yaje yi a Spain ɗin ne daman?" Sai lokacin Romeo ya juyo da kallon sa kan dad "Ba wani aiki ne mai wuya ba" ya bawa dad amsa, dad na komarin sake yin magana yayi saurin cewa "No dad, please stop asking me these silly silly questions, don't worry they will come back soon" shiru dad yayi ba wai dan yaso hakan ba, sai dan kawai lion ya zauna tare da shi, yasan cewa idan ya cika yiwa lion tambayoyi da magana, yana sanya shi yin magana to zai tashi ta fice ne, kuma dad ba zai so hakan ba, dan Romeo baya zuwa ya zauna tare da shi haka, idan kaga Romeo yazo wajen dad to fa sai dai in drugs na shi zai bashi, haka kawai ba zaka taɓa ganin sa a wajen dad ba, yauma da dalilin zuwan nasa, bai son dad yazo yayi ta takura mashi a kan ina James ina Michael shiyasa yazo rufe wa dad baki.

Sun jima suna zaune shiru sun tsare Tv da ido, dad yana kallo da gaske, shi kuma Romeo yana duniyar tunani.

A gefe guda kuma, Musharraf ya kara samun lafiya sosai da sosai, sai dai ɗan kwana biyu da James baya nan, ya shiga damuwa sosai, saboda babu mai yi masa alwala, sai dai shi ya lallaɓa ya rarrafo yaje ya ɗauki ruwa yazo yayi alwalan da kan shi, haka zalika babu mai ɗaura shi saman kujera ya kai shi toilet, abun ya fara damun sa sosai, babu wanda zai iya tinkara ya sanar wa damuwan sa, dan shi gani yake duk yan gidan danja ne, babu mai saukin kai a cikin su.

To bari dai mu leƙo My Rimsha kuma muga wani wai na take toyawa.

💔💔RIMSHA💔💔

Makale Kausar take saman bishiyar gwaiva tana tsinko musu, ita kuwa Rimsha tana tsaye a kasa sai aukin cewa "Kausar ga wani nunanne ta can" bata san ya wuyar hawa bishiya yake ba, ci kawai ta sani, sai bakin iya magana, dan yanzu Rimsha ta kware wajen iya magana zaman ta da Ayla da Kausar, dan Ayla yarinyar akoi ta da surutu, amma mafiyawancin surutun nata mai amfani ne, ita kuwa Kausar akoi murya, kunsan dai yadda yarbawa suke, idan suna magana sai ka rantse da Allah faɗa suke, gata bata da jumiriyar yinwa, kundai san halin yarbawa da bala'i cin abinci basa wasa da ciki, shiyasa koda suka fito daular mutuwa ta kasa tafiya, sai da Rimsha ta goyata, saboda bata iya jurewa yinwa ko kaɗan, idan kuma taci ta koshi, tofa akoi iya magana, gata da karfi kamar doki, dan ko a gaɓɓai tafi su Rimsha, kuma tafi su ƙiba sosai, wahalar daular mutuwa ya mai da ta siriri ya, amma Kausar mace ce mai ƙiba, sak yarbawan haka take.

Tana makale saman bishiya tana ta faman gabzan gwaiva, daɗi da santi ya ɗebe ta sai surutu take hankalin kwance

"Meesha yau baki zana masoyin mu GAR ba" Kausar ta faɗa daga saman bishiya tana dariya, murmushi Rimsha tayi har sai da dimple nata ya lotsa, wani daɗi taji ya ziyarci cikin farfajiyar zuciyar ta, Kausar ta taɓo mata in da yake mata kai-kayi, ita ka ɗai sai murmushi take, tana cin gwaiva tace "Ke dai bari Kausar am, ina nan zuwa in zana shi, yanzu har jikin bishiya zan rinƙa bi ina zana shi, dan wannan daji tasan da zaman mu" dariya Kausar tayi kafin tace "Kai Meesha ina da shawara" cikin sauri Rimsha tace "Shawarar me? Faɗi ina jin ki" gefowa Rimsha gwaiva tayi kafin tace "Me zai hana mu tara kuɗi muje wajen wannan mutumi mu gan shi ido da ido" Rimsha bata san lokacin da dariya ya kubce mata ba, har da faɗuwa kasa, zuba mata ido Kausar tayi tana kallon ta da mamaki, bata taɓa kallon Rimsha na irin wannan dariya ba, sai dai murmushi kawai, amma yau Rimsha ce saboda dariya har da faɗuwa kasa

Da dai Kausar taga Rimsha fa bata da niyar dakatawa daga dariyar da take, sai tace "Haba Meesha menene kuma abun dariya?" Har wani dafe ciki Rimsha take saboda dariya, ga hawayen dariya nan wani na bin wani a kumatun ta, Kausar kuwa dataga Rimsha taki kulata sai ta saka kuka tana faɗin "Wlh idan baki dai na dariyar nan ba mun ɓata, haba dan Allah mahaukaciya kika mai danine?"

Sai da Rimsha taga Kausar ta ɓata rai da gaske tana kuka, sai ta dakata da dariyar nata, ta ɗago ta dubi kausar, murya ɗauke da dariya tace "Sorry Aunty yar lukuta, ai ke ɗin ce santin gwaiva ya ɗebeki sai faman sakin layi kike da zance, ke kwata kwata kin manta aina muke" A kule Kausar tace "sai dai sama da yar lukuta ba yar lukuta ba" guntse dariya Rimsha tayi dan tasan in tayi dariyar nan, bazasu wanye lafiya da Kausar ba, kuma tana sane da gangan ta kira ta da yar lukuta, tasan ba abun da Kausar ta tsana biyun wannan suna Aunty yar lukuta, baba da Mustapha suka sa mata sunan, suma dan ba yadda zatayi da sune yasa take amsa wannan suna idan sun gaya mata.

"Me ya baki dariya to?" Kausar ta tambaya tana kara haurawa saman bishiyar da kyau, dan ta hango wani gwaiva nunanne a can sama, sake kwashewa da dariya Rimsha tayi dan Kausar ta tuna mata da abun da ya saka ta dariya ɗazun

Saboda haushin dariyar da Rimsha take, tsinko gwaiva ɗanye Kausar tayi ta sai ta tsakiyar kan Rimsha ta kwala mata, ihu Rimsha tasa tayi baya tana faɗin "muguwa Aunty yar lukuta" sake tsinko ɗanyen gwaiva Kausar tayi ta jefo mata, a sukwane ta matsa a wajen tana faɗin "kin dai yi na farko kinci

Please Login or Register in order to submit comment