Reading Zumuntar kenan 2 Hausa Novels by Takori Kabara Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kazama dakikiya ‘yar Maimuna? Uhm! Ko don yanzu na yi idon gani na zamo abar kwatance cikin mata? Da da nake a ‘yar’uwarsa kankanuwar yarinya mai rauni da bukatar kulawar yayyu irin sa me ya hana ya kauna ce ni?
Ta ya ya yake tunanin ni Fa’izah zan mance kiyayyar da Fa’iz ya nuna mini tun ina ficiciyata har na kawo yanzu? Sanda yake aikowa su Ummi kayayyaki BAN DA NI. Ya tambayi lafiyar kowa BAN DA NI. Ya nuna banbaci kiri-kiri da fifiko tsakanina da sauran ‘yan’uwana...... Ya yabesu ni ya kushe ni..... ya zagi uwata a duk sanda ya so, ya dauko Ummi daga makaranta ni ya barni a jeji ko in mutu ko in yi rai ba damuwarshi ba ce. Ba don komai ba sai don saboda tsabagen tsana da kiyayya! Shin meye dalilin auren yanzu?
Don na yi girma na yi kyau na zama kyakkyawa..... Don na yi kwakwalwar karatu wadda a da bani da ita..... Don na yi kyawun da duk cikin A.B babu kwatankwacina balle tsarana! Kaico da masu halin son zuciya irin Fa’iz Giwa.
Wani da shan wahalar raino, ilmantarwa tare da real kauna ga Fa’izah shekara da shekaru bai samu ba sai shi. Wani da kwashe shekaru yana hidimtawa Fa’izah da inganta rayuwarta positively ba a bashi ba sai shi.
Ga masoyi na gaskiya irin Dr. N mai wuyar samu a wannan lokacin, mai sadaukarwa so da kauna dukkan hakkokin da Allah ya ce a basu bai samu ba sai shi. Tabbas muddin na yarda na zauna da Fa’iz ko na saurari wata kalma daga gare shi ko da guda daya ce na tabbata wadda ba ta san ciwon kanta ba, ba ta san darajar kanta ba, ba ta san darajar wadda ta dauki cikinta wata tara ta haife ta shayar cikin wahala da kakani-kayi. Muddin ban auri Dr. N ba na cika butulu duba da tarin kauna da soyayyar da ya mallaka mani, na zama mayaudariya.
Ya zama dole kenan in kaskantar da kaina ga Fa’izu ya warware igiyar da aka zarga a tsakaninmu? Juyawar da barin kaina yake yi ya tsananta cikin ‘yan dakiku, a yayin da zuciyata ta halarto min da cewa, rokon Fa’iz a bisa abin da bani da iko a kansa wannan dole ne! Kaskantar da kai ya zama dole gare ni, tunda durkusawa wada ba gajiyawa bane. Amma ba don ni ba illa don farin cikin Dr. Nazir Sani Galadanci.

****
A washe garin ranar idanuwana na bisa kofa, yinin ranar zungur ban ko leko falo ba, illa kunnuwana da na kasa suna zuko min duk mai shigowa da mai fita a gidan Hajjah ko zan ji muryar Fa’izun? Shiru! Har yamma. Kafin in ji Aliyu na ce da Hajjah “Fa’iz ya je Kano dauko Yaya Bashir”.
Hajja ta shigo dakin da nake kwance hannunta rike da kwano shake da gasasshen nama da ruwa-ruwan shi, an kuma barbade shi da yajin daddawa wanda ya ji kayan kamshin gargajiya mai dadi, ta zauna gefena a hankali da gani a darare take.
Allah sarki Hajjah! Duk zagin da ta sha bai sa ta yi fushi dani ba don ina ji da safe tana gayawa bakinta ‘yan taya murna da suka zo mata daga Zaria, kada wanda ya shigo ya ta dani barci nake a barni na huta.
Ita kanta ta fada fiyat! Kamar wadda ta tashi daga zazzabin kwana biyu. Ta ce, “Fa’izah ki yiwa Allah ki bude ido ki ci naman nan, na san kina jina ba barci kike ba, tun asuba nake aikin gasa miki don na san shi akdai za ki iya ci tunda kin ki cin komi tun jiya, shin baki tsoron irin ciwon Aliyu ne?”
Na yi mata banza na kara cusa kaina cikin filo na bude sabon kuka. Hajjah ta yi zugum da kwano a cinya, daga bisani ta aje shi a kasa ta ce, “In kin kin cin abinci wanka fa Fa’izah? Rabonki da wanka yau kwana hudu. Shin Fa’izu ya san wainar da kike toyawa ma, in don shi kike yiwa kanki wannan ukubar?”
Ban san sanda na zaro kai daga cikin filo ba na yi kutubal da shi na mike zauna, na ce, “Hajjah don na yi kyau, don na yi haske na daina kazanta na zama abin gani har a so ayi sha’awa Fa’iz ya ce miki yana son aure na ko? To daga yau duk wani abu da ya shafi gyaran jiki zuwa wanka na barshi har abada! Na koma Fa’izar da ya sanni a baya, kazama ‘yar Maimuna!!! In ce dai in na shiga warin hammata da warin baki ya ce baya so, ya je ya auro ‘yar Rasha ni kuma a barni da mai sona tsakani da Allah ba don wani abu da na mallaka ba....” Na ci gaba da kuka na gasken-gaske.
Hajjah ta ce, “Ayya Fa’izah, kin yi kuskure babba, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya. Daga ranar da Hafizi ya bar Najeriya bai kara ganinki ba ko a hoto sai ranar da ya dawo bayan an daura muku aure”.
Da hanzari na tari numfashinta, “Tunda haka ne ki kwance auren mana ko dole ne? Na ji ko da ban auri Dr. Nazir ba na yarda na amince ki hada ni aure da Malam Hassan maigadin gidan Baban Kaduna, ko Isa direban gidan nann....”
Hajjah kam ta koma yi min dariya, ta ce, “Yo ai shi kenan, wannan abu mai dan karen sauki. Sai ki je wurin Hafizin ki amso takarda ki kawowa Ahmadu da ya kulla auren ku, ni kuma na yarda ayi aure da Malam Hassan maigadi tunda ai mutumin kirki ne bawan Allah, ko ba jinina bane na san asalinsa da tushensa, na zauna da shi tun ba a haifeku ba, babu cuta ba cutarwa”. Ta mike ta fice ta bar kwanon naman a wurin yana ta turiri da kamshi.
Na dade ina juya maganar Hajjah bayan fitar ta. Don me kowa na ce ya rabani aure da FA’IZU ABUBAKAR sai ya bude baki ya ce in amso takarda wurin sa? Bayan suna da masaniyar cewa ba zan taba iya rokon Fa’iz wani abu ba, ko kalma ta hadani da shi a kafatanin rayuwata?
Ni na kai masa auren da zan je na karbo ba su suka kai ba? Don me su ba za su je su karbo ba in har da gaske suke suna son gyara kuskure da laifin da suka yi mini wanda ba zan iya taba yafe shi ba ko in amince da shi? Don me sai na karbo takardar aure zai warware ina ce in an maidawa Fa’iz sadakinshi shi kenan aure ya warware?
Cikin kuka na fitar rai mai soya zuciya na ce da Hajjah, a lokacin da na mike na bita har uwar dakin barcinta tana shirin ta da sallar walha.
“To ki bani sadakin mana ki gani in ban mayar mishi ba?”
Tana kokawar sanya hijabin sallarta ta ce cikin alamun nuna gajiyawa da magana daya, “Shin ni Hadiza meye nawa ne cikin lamarin nan Fa’izah? Sadaki dai Barau ya karba, bayan daurin aure kuma ya dankawa ubanki na Zaria. Saboda haka su za ki je ki yiwa wannan tijarar da kike yi mini amma ni in kika sa min hawan jini Allah zai saka mini....”
Ta soma kokarin fashewa da kuka. Na juya na fice da gudu na bar mata dakin tun Allah bai jeho wani cikin ‘ya’yanta ya aika dani lahira ba tare da na kara sanya N.S a idanuna ba.

****

BIKI-BIDIRI
Ga al’adar mutanen Giwa da yammacin Laraba ne muke kamu, washe gari alhamis kuma ayi budar kai. Don haka ban yi mamakin jin hargowar jama’armu ba daga ko ina cikin garin Giwa, Zaria, Kaduna da makotansu sun cika A.B Estate. Masu kidan kwarya sun soma wasa korai da gyaran murya cikin lasifaka, masu guda na yi, maroka na ma Hajjah kirari duk inda ta gifta.
Na tabbatar dai al’amarin nan da nake dauka almara nema yake ya tabbata, za su hadani rayuwa da Ya Fa’iz ne ko babbaka su zan yi. Lallashin ma babu mai lokacin yi min shi, shima Yaya Aliyun tun ranar da yasa kafa ya bar gidan ban kara jin ko tashin muryarsa ba.
Ummi da Zanirah babu wacce ta kara shiga sabgata, na kan ga dai Fa’iza ‘yar Zanirah ta rarrafo dakin da nake tana wasanta, ta yi ta gaji ta fita ko sanin da halittar dan Adam bana yi a dakin, domin ruhina da kulliyar tunanina baya wannan duniyar tamu, yana cikin wata duniya ta kunci, azaba da tafasar zuciya da zabalbalar kwallah.
A yau na yi amanna da cewa, zan zama matar Fa’iz in na bari tsofaffin nan suka shafa min lalle. Na yi tunani iyaka tunani bani da mafita, bani da mai mara min baya, babu mai duban hujjata da idanun basira in dai a kan Fa’izu Abubakar ne. Wani yaro cikin ‘ya’ya da jikoki da suke matukar so duk da tarin aibobinsa. Don haka na yakewa kaina mafita ta karshe.
Na janyo (travelling bag) dina na shiga shirya kayana da ba za suyi min wahalar dauka ba a gurguje.
Adda Hanne kanwar Maman Kaduna da tawagarsu suka yane labule suka shigo da guda da sallama, duk suka cika dakin taf! Tsokanar duniya babu irin wacce basu yi min ba, in gadon dakin ya daga ido ya dube su to nima hakan. Kaya nake ninkewa daga sif ina dannawa a jaka.
Adda Hannatu ta yi kwafa ta ce, “Ke ‘yar tawaye, mun zo kama ki ne kinyi kamar baki ganmu ba saboda kin isa”.
A yayin da ta bincire hancin kwalbar turare “intimately beckham” suna ta raha suna darawa cike da unexpressable nishadi da farin ciki bayyananne a zuciyar su da fuskokinsu.
Na dago jajayen kumburarrun idanuna na yi musu wani kallo a kaikace ta kasa-kasan ido a hankali na ce, “Ku kama uwarku dai”. A yayin da na sunto dankwalin kaina na yi damara a kugu gashina dake daure cikin (bound) ya sunce gaba daya ya cika fuskata da wuyana baki daya, ban damu ba, ban kula ba, jikina har tsuma yake ina jiran mai kwarin kashin da za ta fara matsowa gare ni.
Adda Hannatu ta ce, “Eye! Dambe za ki yi damu Fa’izah! Lallai da aka ce kin haukace ashe ba ayi kuskure ba. To bismillah ma ga mai kwarin kashi tsakanin ni da ke”.
Zaneerah cikin zafin cewa da na yi su kama uwarsu ta ce, “Eh, uwarmu zamu kama mana, tunda dai babban Yaya uba ne kamar yadda matar babban Yaya ta zama UWA...... wadda za ta cika mana gida da ‘ya’ya ta sauke tukunya ta dora mana abinci...... ta sa mana kula ta sabe mana babbar riga ta yiwa ‘ya’yanmu tarbiyyah irin ta gidanmu ba irin tata ta rashin neman albarkar iyaye da son gamawa da duniya lafiya ba.......”
Daga haka suka shiga kwararo min turaruka ta ko’ina gaba da bayana har tsakar kaina zuwa yatsan kafata, har kuma cikin idanuna.
Ashe dama kowaccensu da guzurin abinta cikin mayafi, ba Adda Hanne kadai ba. Azabar turare cikin kwayar idona ta rudani ta gigita ni na soma kara ina murza idanun da dukkan hannuwana, ina fadin “Idona.... idona..... wayyo Hajjah sun fasa min ido”.
In sun fasa to ke da baki nan kin fasa karatun nan, sai dariyarsu suke. Kasa na sulale na kwanta ina birgima ina murzar ido dake neman tsiyayewa.
Sai da suka kusa karar da kwalabensu kana na sha duka kitif-kitif-kitif daga hannun kowaccensu, wai ban yi wanka da kwalliyar tarbarsu ba sai zagin da na yi musu guzuri da shi.
Kai wannan rana na ga wulakancin duniya da takaici da bakin ciki wanda ke kokarin fin karfin juriya da karfin halin da nake tinkaho da su. Nake amfani dasu ko yaya ne wajen ganin na kwato hakkina daga iyaye da dangina na A.B baki daya.
Sai da idanuna suka lafa daga zugin da suke yi min na kuma tabbatar da basu tsiyaye din ba kamar yadda nake tsammani. Na shiga toilet dinmu wanda dama like yake da dakin barcinmu na wanko fuska da ruwan famfo mai sanyi, tuni zuwa lokacin an kece da kidan kwarya mai dadin amo da dadin sauraro.
Wanda sautinsa ke amsa kuwwa cikin kwakwalwata yana zabalbalar min da ita. Ji nake shine amo mafi rashin dadin sauti da na taba ji a rayuwata tunda uwata ta haife ni.
Mawakiyar waka take yi cikin lasifika tana kiran sunana tana hadawa da na Fa’izu Abubakar-Hafizin Hajjah, angon Fa’izah sanyin idaniyar Hajiya Hadiza Giwa..... Kin isar, kuma kin cika, baki taba gazawa ba uwar zuri’ar Abubakar Bamalli.... Allah ya ja kwananki ya kara miki lafiya ki ci gaba da kulle tsintsiyar Abubakar Bamalli. Takawarki lafiya uwar maza uwar Muntari, uwar Na’ibi uwa ga Ahmadu, uwar Ibrahim, Sani, Salisu da Sadi. Ki bani mota ki kaini Makkah Hajjah Giwar mata, Giwar mutanen Giwa.....
Da gudu na fito daga bandakin ba don komi ba sai don tagarsa tana tsakar gidan dai-dai inda tsohuwar ke zaune tana wakar mai kama da banbadanci tana rawa daga zaune, saboda ba ta iya mikewa saboda kibar da ta yi mata katutu.
Sai na ji kamar tana amfani da wakar tata ne da karin (tune) ko kuwa (melody) mai gaya min cikin tsakiyar kaina cewa, abin da Hajjah ta yi dai-dai ta yi, ina so ko bana so kuma ba zan taba yin nasara a kan A.B ba, sune suka riga suka yi a kaina.
Wannan tunanin kamar anyi min wata irin allura mai kashe lakar jikin dan Adam ta karar da kuzarinsa, ta raba shi da BURIN sa da duk wani buri da ya ciwa rayuwarsa.
Hawaye na malala ta kowacce mabubbuga ta idanuna yana kwarara a kan fuskata na tube kayan jikina dake kamshi na fita hankali ma zan ce ba na tashin hankali ba na canza wasu. Sai da na saurara na tabbatar su Adda Hanne da iyalanta su Zaneera da ‘yan kanzaginsu sun shige gidan Baba Na’ibi dukkaninsu don su kama Ummi, na sulale ta gareji ina jan trolley dina wadda ban cika da kayan da za su wahalar dani ba na bi ta baskwata inda babu ‘yan biki, mazan kuma duk basa nan, na bi ta hanyar da suke bi zuwa masallaci na fice daga gidan. Maigadin yana can yana baiwa tantabaru abinci.
Tafiya nake bana ko waiwaye da wata irin sassarfa mai hade da gudu-gudu kamar zan tashi sama, bana ko ganin abin da yake gabana, ban kuma damu ba wai don mota ko babur sun buge ni ba, gara su buge nin in mutun in huta da nufin A.B a kaina.
Don dai ba zan iya kashe kaina bane tunda na san abin da zan tarar idan na aikata hakan, babu mai kamasho ciki da za a raba bana mutuwar kafirici tare ni kadai zan dauki dakon abuna. Amma shiga ta duniya ba ni kadai zai yiwa illa ba, zai yi laga-laga ne da zuciyar duk wani da ya kwana ya tashi cikin zuri’ar Abubakar Bamalli, su rasa kwanciyar hankali da nutsuwarsu irin wanda na rasa tunda kowannensu cikin farin ciki yake da yankan kauna da kisan mummuken da suka yi mini, ni kadai ce cikin halin kaka-nikayi.
Nema na su rasa alhalin sun san ba mutuwa na yi ba shine kadai kokari na karshe da zan iya, tunda kalmar fatar bakina da duk wani bore na ya gaza, abin dariya ne ma abin a zauna ayi ta dariya. Tunda su dai burin su ya cika, gara in mutu da su tausaya mani, su dubi al’amarina da zuciyar hankali da tunani.
Da wannan tunane-tunane da zancen zuci da tafiya a kan hanya da kan titi bayan horn da zagi iri-iri da ga motoci da babura na bude ido na ganni cikin tashar motar garin Giwa. Ni da kaina na tabbatarwa kaina bani da wurin zuwa cikin danginmu kaf din su a karbe ni, in ka dauke gidan Baban Kaduna.
Sai dai kuma ai abin da kunya da nauyi, gudun auren dansu nake yi da suka tsuguna suka haifa, kiyayyarsa ke neman kashe ni da raina. Kuma su zamo sune mafakata idan ina da kunya?
Bugu da kari wanda ake bata kashin domin sa ba zai wuce can din ba, tunda baya Giwa wanda na rantse da in ga azzalumar fuskarsa na gwammace in yi arba da (arm robbers) cikin talatainin dare zai fiye min alheri da kwanciyar hankali fiye da sake arba da Fa’iz a sabuwar duniya da nake rayuwa bayan ta kuruciya ta shude da shi a ciki da duk wani al’amarinsa da na sani.
Duk da na san babu jituwa ko kankanuwa tsakanin Hafizin Hajjah, Fa’izu Abubakar da iyayensa da suka haife shi, Baba Muntari da Maman Kaduna, wani sako na kololu zuciya da kwakwalwata ya tuna mini da cewa DA har gobe sunansa DA a zuciyar iyayensa, ko da kuwa Hitler ne mai daukan rayukan al’umma babu dalili.
Da wannan tunanin sai na fada motar garin Zaria, wadda za ta kai ni har ABU in har DA shine DA a zuciyar iyayensa komin muninsa ko munin halinsa da munin ayyukansa, to kar in nemi gidan Baban Kaduna gara in koma ga tawa uwar wadda bana baiwa muhimmanci cikin rayuwata da hujjata ta banza mai cewa, ita ma ba ta bani kulawar da Allah ya ce ta bani.
Na tabbata idan duk duniya ta taru ta ki ni ta juya min baya a lokacin da bani da kowa, bani da gata, uwar da ta haife ni ko ba za ta kulani ba, ba za ta kore ni ba. Wadda ta sunkuya ta kawo ni duniya Fa’izun ke kamo sunanta yana zagi a duk lokacin da ya so, a dalilin ta haife ni kuma bare ce ba ta hada jini da iyayensa ba.
Bayan wannan ba ta yi masa laifin komai ba. Babban abin da ke damuna a wannan duniyar hujjar Fa’iz ta aure na? Har ya iya bude baki ya furta hakan bai ji kunyar kowa nawa ba? Duk da ba a auren na gani ina so cikin zuri’armu shi ya furta kuma an ba shi saboda fifikon da yake da shi a zuciyar Hajjah! Ko da zan mutu, zan so kafin isowarta (mutuwar) in samu amsar wannan tambayar, mene ne dalilin Fa’iz na aure na? Tunda na amince an halicce shi ne da kiyayyata ya girma ya rayu cikinta, ya bar kasar Nigeria cikin rainonta (kiyayyar), ya kuma yi gammon abarsa ya tafi da ita Rasha, ya kare shekarun da ya yi baya gida cikin soyayya da Ummi..... da kiyayya gare ni.
Na ce, kyawun da na yi ne wanda a da bani da shi, da tsabtar da na yi a yanzu wadda yake goranta min bani da ita a baya, yake kyara da hantara da wulakanta ni a kanta, su suka sa ya zo yanzu ya ce zai aure nin.
Hajjah ta ce ba su bane, ta kuma kafa hujjar ta da cewa, tunda Fa’iz ya tafi har ya dawo tsayin shekarun nan ko hotona bai taba gani ba, balle ya ga canzawar da ni nake ikirari.
To mene ne? Mene ne hujjarsa? Yana nufin alkhairi gare ni? Yana yi min tanadin alkhairi? Yana nufina da alheri da wannan auren ko ko ya yi shi ne don karasa cimma mummunar manufarsa a kaina ta ganin ya raba ni da duk wani farin cikin rayuwata? Na wulakanta na tozarta na tagayyara a rayuwa? Ina ruwan Fa’iz da duniya ta da burinsa kawai ya raba ni da jin dadina dake cikinta?
Tunaninnikan da nake ta yi kenan suna ci gaba da soya min zuciya, fuskata jage-jage da hawaye, domin iyaka tsinkaye da dan tunanin da Allah ya hore mini sun kasa bani amsar tambayoyina ko da guda daya daga ciki, har mai tasin da nake ciki ya hau kan titi dodar ya kama hanyar Zaria.
Mu karasa a
A littafi na 3
Takorin ku ce.
[6/3, 4:13 pm] Takori: ZUMUNTAR KENAN?-3
Mai taxin ya gaji da gaya min gamu cikin Zaria, ina zamu dosa? Na zama kamar mutum-mutuma, kurma, makauniya don tunani, saida ya bubbuga kujerar danake zaune nace masa gida mai lamba tamanin cikin gidajen malamai na jami'ar Ahmadu Bello. Gidan da ya zamto mahaifata, dandalin quruciyar rarrafe da tata-ta ta, kafin in gujeshi zuwa inda nake ganin ya fishi farin ciki da walwala, a yau gani na dawo da qafafuna, na kuma gwammace in qarashe sauran rayuwata cikinsa ko da ace yafi kurkuku rashin Dadi da taqaita farin ciki.
Wata irin doguwar ajiyar zuciya na saki, na ciro kudin da suka rage min kaf ko qirgawa banyi ba na baiwa mai tasi, ya fitar min da jakata daga bayan motar sa, ya yi min godiya mai yawa ya ja motarsa ya bar harabar wajen.
Zan iya kimanta lokacin da qarfe takwas na dare sanda nake tsaye qofar gidanmu, domin ina iya hangen tanqareren agogon falonmu wanda hasken qwan lantarki ya wadata, kuma an dage labulen wawakekiyar tagar falon. Rashin motar Baba ya tabbatar mini bai shigo cikin gida ba, ya shiga cikin (city) kamar yadda ya saba duk bayan sallar isha'i. Don haka naji dan sanyi da qwarin gwiwar cira qafa da tura jakata.
Sai dai a take wani irin tsoro da shakka suka lulluve ni, idan Momi ta yarda ta qyaleni in zauna Baban ABU zai qyaleni ne bai gayawa iyaye da 'yan uwansa ba? Kuma wane mataki zai dauka a kaina tunda ga dukkan alamu bai dauki al'amarin nan da sauqi ba?
Hakan dai nayi shahadar quda da yin qarfin halin danna qararrawar qofar shiga falon (door-bell), sai da na danna sau uku kafin a buxe.
Walida ce, zata yi magana nayi hanzarin kai hannu na rufe bakinta, muryata na rawa na ce.
"Ki rufa min asiri Walida, shin Baba na gida?"
Ta girgiza kai.
"Momi fa?"
Ta nuna min (kitchen).
Na ce, "To don Allah Walida kar ki gayawa kowa ina cikin gidan nan, zan zauna xakin Abdallah, ai yana makarantar kwana ko?"
Ta gyada kai tare da leqawa ciki ta tabbatar momi firar doya take, tayi min alamar in shiga.
A hankali ta murda qofar dakin Abdallah na shige wanda ke daga can gefen tafkeken falon, ta mayar ta rufe kenan Momi ta qwala mata kira.
"Walidaa!".
Ta ruga a guje tana faxin.
"Yes Momi".
Momi ta ce, "Ke da wane a waje ku ke magana?"
Ta dan diririce na rashin sabo da yin qarya, kafin ta ce.
"Joseph ne yake neman Cinyere na ce bata zo ba".
Ba tare da ta juyo ta dubeta ba ta ce.
"Ga abincin ku can kan leda ki ta da Walid ku ci, ya yi bacci ko?"
Ta ce, "Kai Momi, ki qyale shi ya fa sha kunun tsamiya mai yawa kafin ya yi baccin".
Ta juya don ta kira Kausar ta tarar tayi bacci akan litattafanta itama, ta gayawa Momi kana ta dauki plate din ta bude qofar a hankali ta shigo.
Nayi tagumi ne a gefen gadon Abdallah na zubawa kayana ido, da 'yar muryarta mai sanyi ta ce.
"Yaya Fa'izah". Tare da zama a kusa dani, ta dora hannunta bisa cinyoyina.
"Wai shin me ke faruwa ne? Duk akan auren ki da Ya Fa'iz ne?"
Na share hawayen da suka cika mini ido, na ce.
"Shin Walida kin mance sanda Fa'iz ke azabtar dani ne? Sharri kala-kala da azabobi iri-iri wanne ne Fa'iz bai min ba, bai kuma gana min ba? Qiyayyar duniya wacce iri ce Fa'iz bai min ba? Amma ki ga don zalinci ya zo ya kalallame Hajja da su Baba suka xaura mana aure...".
Wasu azababbun hawaye suka mirgino akan kundukukina.
"Don haka ni kam Walida anan zan ci gaba da voyewa har zuwa sanda suka gaji da nemana suka warware auren nan, ko kuma su kai gawata idan baqin ciki ya qarasa ni, da dai in zauna ayi bikin nan jibi...".
Na ci gaba da share hawaye ina fyace majinar dake ambaliya daga hanci na.
Walida tayi zuru tana kallona. Da alamun tayi nisa a tunani. Ni na san Walida yarinya ce mai kaifin basira duk da kasancewarta mai qarancin shekaru, kwata-kwata bana ji ta cika shekaru goma sha huxu. Wala'Allah abinda take saqawa ya zam mai amfani a gareni.
Ta ce, "Yaya Fa'izah, ban zauna a Giwa ba ko kaxan balle in san halin Ya Fa'iz a da can, ko rayuwar da ku ka yi tare, bana ma kuma marmarin zaman, sai dai nakan ji ana labarin a cikin 'yan uwa ko in munje gidan Baban Kaduna ko yaro ne ya takurawa xaya sai kiji manya na faxin, "Kada ku zama Fa'iz da Fa'izah mana, kuyi riqo da ZUMUNTAR ku". Sai dai wallahi a yadda Baba

Please Login or Register in order to submit comment