Reading Zumuntar kenan 2 Hausa Novels by Takori Kabara Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mufty ya je Giwa, matar gidan kuma tana fama da kanta ba ta (driving).
Don haka da Abdoul ya shigo ya ce, “Wai wadanda Haulatu ta turo a dauka su fito”.
Sai na zuba mishi rankwashi aka, muka zari mayafi muka yiwa Aunty Rabi sallama muka fita.
Ni dai na ga mota ‘Vauxhall’ (one door) ba Honda din gidan su Haulatu ba. Kofar direba a bude ya zuro kafafunshi waje, sautin Abdurrahaman Sudaith na tashi a hankali a motar, ya sanya (ear piece) yana bi idanunshi a rufe ya jingina bayansa da kujerar kamar mai barci.
Kamshin turaren ‘oud’ na mota na tashi kadan-kadan. Ganin bai da niyyar bude idon, bai kuma san da tsayuwar mu a wurin ba sai na yi masa sallama a hankali. Tare da cewa, “Mun fito”.
Duk idanun ya bude wal! A kanmu. Hasken lantarkin farin bulb din da ya haskake harabar gidan ya haska mishi fuskokinmu. A sannu a hankali ya dauke ido a kanmu ya yi dan murmushi yana yiwa motar key yana fadin “Bismillah ku shiga muje, kamar ma na taba ganin daya daga cikinku”.
Tuni zuciya da ruhi suka shiga aikin da suka saba a duk lokacin da suka yi arba da wannan bawan Allah. Lecturer dinmu ne (Mr. No name), don ban san sunan shi ba, mai kora ta a bainar jama’a in na yi latti. Meye hadin sa da Khaulatu?
Ganin na tsaya na kasa shiga motar saboda mamaki sai ya dago ya dube ni muka hada ido na yi hanzarin russunar da nawa domin sun zama masu rauni kwarai a cikin nasa.
Ya ce, “Ki shigo mu tafi, tana jiranku, o.k?’
Na bude bayan mota na zube. Ummi ta shiga gaba. Ya rufo kofar side dinsa cikin taushin murya ya ce, “FA’IZAH NAKE SO TA DAWO GABA BA UMMIN AUNTY RABI BA!”
Wani sauti kululuuuu! Da cikina ya bayar kenan na mamaki, tsoro da tu’ajjabi. Ummi na dariya ta bude kofar gaba ta fito ta dawo baya ta zauna tana min alamar in fita ina girgiza mata kai alamar a’a.
Ya ce, “Bana sayar da kai Fa’izah, ni aminin Barister Abdullahi Turaki ne. Shi ya turoni in taho daku an aiki Malam Saleh, ina fatan Fa’izah ta gamsu?”
Ni da Ummi duka sai da muka murmusa. Na bude mota na fito na koma gaban. Ya ja motar a hankali muka bar harabar gidan, ya hau titi dodar.
Daga ni har Ummi mun yi tsit kamar a ce kyat! Mu bude murfin mota mu arce. Sunayenmu da ya ambata wai har ma da Aunty Rabi. Na yi murmushi kadan daga aikin ( talkative ) Haulatu.
Mun yi nisa da Gadon Kaya mun hau titin Audu Bako, jefi-jefi yana karkata mudubin shi don hango motocin dake bayan shi. Da danja ta tsai damu sai ya juyo sosai ya dube ni ,”Are you o.k?”
Daga mishi kai na yi. Har muka zo ‘Yankaba bai kara magana ba, sai ni da Ummi kan yi magana na abin da ya shafe mu.
Haulatu da Abdullahi ke zaune a harabar gidan bisa fararen kujerun roba suna hirar su hakora na shining (dariya). Kai da ganin wadannan ma’aurata ka ga masoyan da ke ji da juna. Har dai-dai inda suke ya yi parking, ya yin da duk suka mike suka nufo motar suna dariya. Ya zagaya ya budewa abokinsa, Haulatu ta bude mana ni da Ummi.
“Mr. and Mrs”. In ji lecturer. “Na cika uzurinku, kyawun alkawari cika shi”.
Abdullahi ya ce, “Wannan lazim ne Sadiqy (aboki)”.
Haulatu ta ce, “Ni dai ba ruwana, kada ku shafa min kashin kaji, daman ta ce Dan iska ne”.
Na dafe kirji da hannuwa biyu na ce, “Ke Haulatu!”
Yadda na yi din da irin fiddo idon da na yi cikin razana ta gaske ya sa gaba daya har Ummi suka tuntsire da dariya.
Abdullahi ya ce, “Kada ki jawo mata ‘carry over’ Sweetie”.
Ya ce, “Ko spill over’ ba ta karasa a gidan mijinta”.
Da wadannan hirarrakin muka rankaya dakin saukar bakin su Haulatu.
“It’s a get together dinner of five....”
Haulatu ta fada tana wara yatsunta biyar tare da janyo warmers guda biyar Arabian cuisines, kabsa, kebabs, manakees cikin biredin (pita), sai mankees, shawarmah da burger.
Ta bubbude kowanne tana serving a plate, cewa take “I did it to you with my naked hands my dear Abdullahi! Congratulation on becoming a Lawyer”.
Gaba dayanmu bamu san sanda muka zuba tafi ba, ni Ummi, da Mr. Lecturer. Shi kuwa Abdullahi murmushi yake bakin kamar ya tsage.
Na kasa sakin jiki ko kadan abubuwan duk sun daure min kai. Sanda Mr. Lecturer ya bude wata foil paper ya turo gabana saura kadan in saki fitsari don mamaki.
Gasasshen naman saniya ne mai romo da ya ji tumatir da albasa, har da cabeji sai turiri yake. Ya kuma dakatar da Haulatu daga serving dina shi ya yi serving dina da kansa, wannan gasasshen naman da ‘kebabs’ (tsire) plate dina wato har appetite dina ya sani, wa ya gaya masa ina son gasasshen nama?
A yadda ya saki jiki a gidan na fahimci ba bakon zuwansa bane. Har wajen su Hajiyar Haulatu tare da shi muka je muka gaishe su muka dawo falon.
Ya dauki tambulan ya cika da lemun matsattsun kayan itatuwa (tropical juice) ya miko min cikin lumshe ido da bude shi duka a lokaci guda.
Ban iya na yi musu ba na karba, amma kurba daya na kasa saukewa saboda gardin lemon, ko ko in ce gardin hannun da ya fito daga gare shi. Cikin duka (Arabian Dishes) din nan gasasshen naman da ‘kebabs’ kawai na iya ci saboda na zama bakuwar zuciyata. This is the exact stranger I’m dreaming of. Sannan actions and emotions dinsa sun nuna abin da ke karkashin zuciyarsa, tun kafin ya furta, he care too much, sai shisshigi yake yi mun. Shishshigin da ba zan iya tankwabewa ba.
Zuciya da gangar jiki duka sunyi amanna, sun karbi shisshigin sun dora a kan kujera mai matsayin da baya kwatantuwa. Watakila da zai iya lashe ni zai yi saboda kulawa. Hakan yasa duk na bi na takura na kasa sakin jikina daga sanya baki cikin hirar shi da Ummi, wanda duka tambayoyi ne a kan abin da ya kawo mu Kano.
Haulatu ta ce, “Fa’izah fa ta bi ta takurawa kanta saboda malaminta”.
Gaba daya suka maido hankalinsu gareni suna murmushi. Ta ce, “Dama kin saki ranki, kin saki jikinki wannan malamin....”
Ya yi hanzarin cewa, “Abdullahi killace bakin matarka kafin in bubbuge shi”.
Abdullahi ya miko hannu ya rungumo kwibin matar shi yana fadin “Kada ki kara magana Honey. A yiwa Yaya Malam biyayya don tare zan tafi in barku. Sai dai ban goyi da bayan a buge min bakin amarya ba tun ban biya farashinsa ba (siyen baki)”.
Ban san sanda na yi dariya ba, ni dai haka nan soyayyar Haulatu da Abdullahi ta ke burge ni. A gaban kowa basa iya boye su masu begen junansu ne, sai dai in ba za ka iya gani ba ka kau da kanka.
Haka yake yi in ya je wajenta a makaranta ya yi ta bamu kunya, wani zubin su bamu sha’awa, wani zubin su bamu dariya. Tattalin Haulatu yake kamar kwan da aka nasa yanzu-yanzu. Haka ita ma.
Ganin dariyata sai Abdullahi ya ce, “Ko ke fa? In ya sake ce miki ‘get out’ ki zo nan ki gaya mun ni dashi ne kin ji Fa’izarmu”.
Cikin dariya na ce, “Ai ban ga laifin shi ba Yaya Abdullahi. Ni ya dace in nemi afuwar shi a bisa lattin da nake mishi, wallahi ba halina bane yin latti akasi da uzuri aka samu. I’m sorry Malam”.
Wani irin lumshe ido ya yi bai ce komai ba. Ya kara kwanciya a cikin kujerarsa. Wannan karon wayar hannunshi yake latsawa kamar bai san bikin da muke yi ba.
Haulatu ta cika baki da shawarma cikin tsokana, “Wallahi Ummi wulakancin dan iskan malamin nan fa ya soma isata? Ko kin san asarar lecture biyu ya yi min? Oho! Ina na san shi? Yana nan wani baki dan kakkaura mai in-ina”.
Na kai tafukana da suka sha adon jan lalle na rufe fuskata suna ta dariya. Shi kuwa murmushi kawai ya yi. Ya ce, “Haulatu ba a sirri dake?”
Na ce, “Daman kin san shi ai kika rufemu a bai-bai?”
Ta ce, “Ah toh! Ba ga shi yanzu na baku mamaki ba”.
Abdullahi ya ce, “Lallai dan iska, yau kuma ‘yan iskan idanun bisa aminiyata suka fada?”
Ya dago kai daga kan wayarshi ya ce, “Ya ishe ka haka nan Abdullahi! Kai ka tashi ma ka tafi lokacin tafiyar ya yi ko a nan za ka kwana yau?”
Ya ce, “In na kwana na yi laifi ne?”
Bai kula shi ba, suka ci gaba da kwasar girkin Haulatu sai da kowa ya yi kat. Shi da kansa ya yi serving dina. A yadda yake sarrafa hannayensa wajen serving din za ka fahimci lallai namiji ne wanda zai tattala matarshi matuka, wanda zai lallaba matarshi fiye da Abdullahin Haulatu.
Abdullahi ya mike yana fadin “Haulatu zan wuce, zo ki ji mana”.
Ummi ma ta mike ta ce, “Ni toilet za ki nuna mani a cikin gida”.
Gaba daya suka fice. Daga ni sai malamina Mr. no name. A sannan ne na fahimci sun fita ne duka don su barmu mu biyu.
Ya dan motsa a cikin kujerarshi sannan ya ce, “Fa’izah!”
Wannan kira ya dade yana amsa kuwwa a sassan jikina. Ban iya na amsa ba sai kara dukar da kai ina murza zoben hannuna.
“Har yanzu ban yi abin da zai sa a sake dani ba? Ko sai na kai ga durkuso bisa gwiwoyi na? Domin wannan afuwar Fa’izah?”
Na dan fiddo ido, “Ta ya ya malami zai durkusawa dalibinsa?’
“Ta dalilin yana SON dalibar soyayya mai yawa.....”
Ya fadi cikin kwaikwayar muryata. Da a ce ban ga yadda yake ciccijewa yana cin magani a aji ba, sai na rantse cewa ba shi bane. Lallai so ba dama ne.
Jin na yi shiru ina tauna maganarsa sai ya katseni da cewa, “Shin Fa’izah ta tsai da gwani ne tsakanin Giwa, Zaria, ko Kaduna?”
Sai na yi dariya cikin jin kunya, “Don me ka yi tunanin wannan? Mu ‘yan Giwa bama hada taura biyu a baka”.
Murmushi ya yi tare da girgiza kai, “Mu ‘yan Kano muna hadawa, kenan rabon kanawa ne ya hana?”
Murmushi na yi cikin jin shauki.
“Fa’izah I’m serious. I’ve interest on you. Shin za ki iya auren malamin makaranta?”
Dagowa na yi na dube shi da dukkan idanu, “Babana ma malamin makaranta ne”.
“But you are born with a silver spoon in your mouth (kin fito daga gidan masu hannu da shuni), kaman hakan zai zama takura”. Ya fadi cikin murmushi.
“A’a, ban fito daga (silver spoon) ba, na fito daga BABBAN GIDA (point of correction) mai babban suna”.
Tafi ya yi min sau uku, “Mene ne bambancin guda biyun?”
“Akwai bambanci da yawa. Babban gida kudi bai yi yawa ba, amma babu yunwa babu rashin suttura a cikinsa. Sannan masu shi dattijan kwarai ne masu magana daya. Idan kuma ka ce tajirin gida kana nufin gidan hutu”.
Wannan karon dariya yake yi sosai wadda ta sanya ni shagaltuwa a kallon sa, kyawunsa na kara kayatar da zuciyata.
“Na yarda dake Fa’izah, to amma fa sai kin ki ji kin ki gani a tafiyarmu. Abin da na gani ina so da zuciya guda ba zan iya munafuntar shi ba, ina da tabo Fa’izah, wanda na san as soon as an fara ganinmu tare za a kawo sukar sa. Duk da an ce waka a bakin mai ita ta fi daxi, ina jin kunyar kaifin idanunki....”
Ya yi dan murmushi.... “Ina son mata Fa’izah, ina son su da yawa..... na yi amanna da cewa har gida za a biyo ki a gaya miki wannan, sai in ba a ganmu tare ba. Amma na yi miki alkawari Fa’izah tsakanina da mahaliccina from you it will cease to exist (son matan) na yi miki alkawarin bari har abada in har kin amince ki zamo uwar iyalina.
Daga ganina dake na farko zuciyata ta gaya min ke ce (life-companion) dina mafi cancanta. Kaunarki ta fara ne daga ganina dake na farko (love at first sight) na rasa nutsuwar zuciyata a tsayin wunin ranar da daren baki daya.
Da nake kwatantawa Haulatu kamanninki da level din karatunki take ce min ke best friend dinta ce tun a secondary, da take yawan bani labari. Shine ta hada mana wannan dabarar ta dinner (to dine here together) ta kuma turani in dauko ku. Gaba daya tarihinki na jishi wurin Haulatu, na kuma kara tabbatarwa kaina INA SON FA’IZAH! Shin Am I accepted Fa’izah?”
Kaina na sunkuyar ina murmushi. Abin nan da masu iya magana ke cewa, labarin zuciya a tambayi fuska, don zuciyata ta yi na’am tun ma kafin ya furta. Har nake jin cewa, ba son mata ba ko mata dari gare shi zan iya zama ta casa’in da tara in har nice uwar ‘ya’yanshi. Domin yanada duk abubuwan da za a so shin a kansu. Ga dai ilimi, ga kuruciya, ga kyau na a manna a jarida, ban ga makusarsa ba.
“Ko da ban furta ba, kallo daya za a yi min a tabbatar da na fada a matsananciyar kaunar ka. Daga lokacin da idanuwana suka fada a kanka Malam”.
Magana nake a zuci, ban san cewa a fili nake yi ba.
Ganin ya lumshe idonsa ya bude ya ce, “Na gode”. Ya tabbatar min ya ji abin da na ce. Wannan sai ya tuna min da lokacin da na karbi tayin soyayyar Yaya Aliyu a Zaria, ga shi ban ci ribar waccan ba, na amsa ta biyu, kada Allah ya kara dandana min dacin ta.
Cikin dan lokacin nan mun tattauna abubuwa da dama mun kara fahimtar juna. Har zuwa lokacin na kasa tambayar shi sunan shi. Sai wurin karfe goma Haulatu ta fargar damu, da kyar muka katse hirar muka fito zuwa mota.
Ina ganin Ummi da Haulatu na gulma suna rada da dariyar shegantaka ko kula su ban yi ba. Don na san da ni suke. A kan hanya ma hirar muke yi. Ya gaya min ya yi dukkan karatunshi ne a Taiwan inda ya karanta harshen Larabci ziryan. Shi da Abdullahi ‘ya’yan family friends ne, haifaffun garin Dambatta.
Da kyar muka iya yin sallama don sai da Ummi ta shige ta barmu. Sai shigowar hancin motar Yaya Mufty ne yasa muka yi sallama ya jira fitowar shi da yin parking din shi suka yi hannu, sannan ya shiga motarsa ya tafi. Har zai fita get ya dawo ya yi min horn na juyo “Phone no na manta Fa’izah”.
“Ni da Ummi bamu da waya”.
“Saboda me?”
“An hana mu rikewa ne”.
Hannu yasa ya dauko tashi a gefe, “Ki rike wannan saboda ni Fa’izah. Na yi alkawari ba zan zamo mai hana ki karatu ba!”
Ya cire layin ya miko min (Sony experia) sabuwa dal. Na rasa abin da ya hanani kin karba, na kuma rasa wanda ya sani yin godiya. Wala’alla soyayyar kenan?

****
Fada na duniya babu irin wanda Aunty Rabi ba ta yi min ba a wannan daren. Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har sai da na saka kuka. Na farko daren da muka yi, na biyu tsayawa a waje da namiji tsayin karfe sha dayan dare. Na uku wayar da ta ganni da ita, da izinin wa na karbo ta?
Don bakwa gaban iyayenmu ba zan ci amanarsu ba. Abin da ya zaunar daku gidana shine karatu ba (flirting) ba. Wannan wayar dole ki mai da masa abarsa gobe. Gaskiya ba dani ba, ba a gidana za a karya dokar A.B House ba, gara ma ku sake tsari. Gobe abu na farko da za ki fara da zarar kun shiga makaranta shine mayar da wannan wayar.
Yaya Muftahu bai ce komai ba. Haka na kwanta zuciyata ba dadi da haushin Aunty Rabi. Duk kula mazan da Ummi ke yi ba ta taba yi mata fada ba sai ni da na yi sau daya, ni da nake da niyyar aure ma ba flirt irin na Ummi ba. Da zuciyata daya nake son malamina, da gaske auren shi zan yi in Allah ya yarda.

I love you. If you hate it, kill with an arrow. But please not in the heart because that’s where you are. Gud night.

Sakon da ya fara shigowa cikin wayar kenan da na saka layin da ya bani cikin kwalinsa.
“Why will I hate it?”
Na tambayi kaina cikin murmushi.
“I do love it too!”
Na baiwa kaina amsa. Don haka na baiwa Malami na amsa.

“You inspire in me a love so deep and powerful that cannot be destroyed by any arrow! How I wish there is a way you could see into my soul. My love on you is far to strong Mallam!”

Daga wannan na kashe wayar gaba daya.

****
Washe gari tun asuba nice farkon yin wanka a gidan. Ban jira Ummi ba balle Yaya Muftahun dake sauke mu ya wuce office, na yi tafiya ta ni kadai saboda fushin da nake yi da Aunty Rabi, ban yi ko tunanin wani abu wai shi kalaci ba.
Babban burina in dora idona a kan lecturer. Kusan nice farkon shiga laccarsa ta karfe goma ta safe. Kai! Ni Fa’izah na shiga uku!!! Don I become infatuated to him fiye da kima. Akwai wani sirri dake cikin kwayar idanunsa da ba duk maza Allah ya mallakawa ba.
Sai dai kuma cikin rashin sa’a bayan ajin ya cika (class-representer) din ya ce ya mai da ita (fixed) karfe biyu na rana. Kamar na fashe da kuka dai-dai lokacin da wayar da na jefa a jaka ta kama tsuwwa. Cikin rashin kuzari na amsa da tunanin yadda zan yi in mayar da ita din kamar yadda Aunty Rabi ta yi umarni.
Muryar mace ke tambaya, “Dacta ne?”
“A’a, ba shi bane, wace ce?”
“Ke me maganar wace ce?”
“Matarshi ce!”
Sai ta kyalkyale da dariya ta ce, “Ki ce Haulatu Sani Galadanci na gaishe shi, kuma inda hali yana jiranki a office dinsa. Saboda ke ya dage laccar ku zuwa anjima. He can’t wait to see you.... cross sword....!”
Kunyar Haulatu ta kama ni ainun yadda ta yi ta canza murya ta shammace ni na yi tabargaza, na yi shuka a idon makwarwa.
Jiki babu nauyi na nufi inda Haulatu ta kwatanta min cewa nan ne ofishin nasa. A ofishin akwai hoton gwamna mai ci a lokacin da na shugaban kasa, sai na Alh. Dr. Ado Bayero. Sanda na yi sallama rubutu yake yi amma bai kasa amsa min ba.
Na samu kujera na zauna har ya kare, sai ya turo min folder din da yake rubutun nasa hannu biyu na amsa. Ko da na duba (note) dinsa ne da na yi missing har guda biyu cikin hand-writing dinsa mai kayatarwa da ban sha’awa.
Idona ya kai ga dan karfen dake like saman kofar shigowa ofishin da ban rufe ba. Sunansa ne radau DR. NAZIRU SANI GALADANCI. Wato Dr. Yayan Haulatu ne uwa daya uba daya ta yi min irin wannan ninkewar? Kai abin da mamaki.
Har mun yi sallama na kai bakin kofa sai na juyo na ce, “Na yi mantuwa ne”.
“Ta me Fa’izah?”
Na dawo a nutse na ciro wayarsa daga jakata na mika masa, yasa hannu ya karba yana fadin “Ya kika dawo min da ita?”
“Aunty Rabi tana ta fada ne, ita ce ta ce na dawo maka da ita, ba za a barni na rike waya ba sai na yi aure”.
Ya yi kasake cikin kallona da murmushi, “Sai na ji na kara son ki, na kuma kara yarda da cewa da ki kai ke din ‘yar babban gida ce. Abin da ban taba ji ba a wannan zamanin ‘yammata kamar ku a jami’a iyayenku sun hanaku rike waya, kuma kun bi, anyway. Ki ce ma Aunty Rabi ta yi hakuri, ba za ki sake rike waya ba sai kin zama matar Dr. Nazir insha Allahu”
[6/3, 4:13 pm] Takori: Da sassarfa na karasa ficewa daga ofishin ina murmushi.
Yinin ranar zungur na kare shi ne cikin tunanin Dr. Nazir da maimaita ambaton sunansa cikin zuciyata sakan bayan sakan, minti bayan minti, awa bayan awa son Dr. Nazir karuwa yake yi a raina. Yana kara habaka a birnin zuciyata.

****
Soyayyarmu da Dr. Nazir ta yi nisa da karfin da ta zama sananniya a tsangayarmu. Tsegumi kam iri-iri an kawo min a kan yawan ‘yammatan da Nazir ke dasu cikin makarantar. Na kan toshe kunnuwana ne kamar yadda ya ce, ko in yi hannun riga da duk wanda ya kawo min tsegumin.
Dr. Nazir ya ware muhimmin lokacinsa wurin yi min (extra class) bayan kowacce laccarsa. Nazir ya iya koyarwa. A dalilin koyarwar da yake yi min ‘points’ dina a jarrabawa ya kara karfi fiye da na baya. Nazir ba shi da karfin idanu (short sight), a dalilin hakan yake amfani da farin gilashi mai kara karfin gani (lenses) ya yin rubutu ko karatu, ko ba da lacca. Amma in ba fadi aka yi ba za ka yi zaton na kwalisa ne. Don yana mai kyau sosai.
Nazir mutum ne da ya iya tsara magana da hafizin harshen da Ubangiji ya hore masa. Iya maganarsa da kirkinsa ya taka rawa mai yawa wajen sanya zuciyata ta zamo kangararra, bana ji bana gani.
Da kaina in ban ganshi ba sai na bishi office, har sayayya mu kan fita wasu lokutan. Tun Ummi na hana ni har ta gaji ta rabu dani. Wai ni Fa’izah tsatso daga A.B House nice mai bin saurayi har office, nice mai fita da saurayi. Wannan ba karamin kona ran Ummi yake ba. Har ta gaji ta tseguntawa Aunty Rabi.
Aunty Rabi ta samu Yaya Mufty take sanar da shi, inda ya ce, “A kawo mishi sunan Nazir cikakke zai yi bincike a kansa. In mutumin kirki ne a kyale ni, kwana nawa ne zamu gama karatun mu koma gaban iyayenmu? Domin Hajjah ta soma fadan mu dawo gida haka karatun ya ishe ta. Abu ya ki ci ya ki cinyewa tamkar cin kwan makauniya”.
Aunty Rabi ta ce, “In kuma ba mutumin kirkin bane ba fa Mufty?”
Ya ce, “Zan san abin yi a kai”.
Ni kam duk surutunsu da harare hararen su basa damuna, na yi nisa a son Naziru.
Wani irin so nake dandana mai wuyar fassarawa, wanda ya zarta na Yaya Aliyu fintinkau! Idona ya rufe a son Naziru, lokutana baki daya na Dr. Nazir ne.
Tambayar da jama’ar dake tare damu ke wa Ummi shin Fa’izah ta san Dr. Naziru (use and dump) ne? Ta ya ya yarinyar ‘yar gidan mutumci wadda ta san ciwon kanta irin Fa’izah ta yarda cewa Dr. Nazir auren ta zai yi? Shin Fa’izah ta san yawan ‘yammatan da Dr. Nazir ya yaudara ya watsar a Kano? Shi fa dama duk inda kyakkyawar mace take nan idonsa yake, zai nuna mata so ya yi ta yi mata facaka, amma da an ce ya fito ayi aure ba kya kara ganin keyarsa”.
Ummi ta kan girgiza kai, don bakin ciki ta rasa me za ta ce, sai dai ta ce, “Fa’izah kam ta yi nisa ba za ta ji kiran ba”.
A yammacin wata talata mun dawo daga Ado Bayero Mall (Shoprite) ni da Nazir ya sauke ni dai-dai inda ya ga su Ummi a zaune a (seaters) na dalibai karkashin wata bishiyar dalbejiya mai inuwa, bai ko tsaya sun gaisa da su Ummi ba don ya san Ummi ba ta goyon bayan tarayyarmu daga ita har shakikiyarshi Haulatu, ita ma ta bi sahu don tsoronta na kar mutuncinta ya zube idon su Aunty Rabi dake matukar ganin mutuncinta, ranar da Nazir ya yi (dumping) dina.
Ko ba don wannan ba Nazir baya sakar ma dalibanshi fuskar da raini zai shiga tsakani. Ko mata da yake nema tamkar bunsuru ba dai cikin tsangayarmu ba can a wasu tsangayoyin ko waje yake neman abinshi.
Na yi musu sallama duka suka amsa min a sanyaye, na aje ledar hannuna gefen Haulatu ina fadin “Wash Allah! Na gaji da yawa. Dr. N (sunan da nake kiransa) ba dai yawo ba, shi dai a je shopping burinsa kenan”.
Suka dubi juna suka kau da kai. Cikin nutsuwar da ban san tana da ita ba Ummi ta ce, “Fa’izah rayuwar da kika zabawa kanki kenan? Tarayya da maza irin su Dr. Naziru? Yau da Hajjah za ta ji wannan mummunan labari ina kike tunanin za ta tsoma ranta? Da kin sa zuciyarta ta yi bugawar farat daya.
Wallahi-wallahi tun wuri ki sake hanya tun dare bai yi miki ba. Nazir ba dai-dai yake da tsarin rayuwarki ba, kuma aurenku ba zai taba yiwuwa ba. In kin manta kin fito daga zuri’ar A.B ne

Please Login or Register in order to submit comment