Reading YAR SADAKA BOOK 2 COMPLETE by MOMN SULTAN Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan da magananta saita sa Kuka tana cewa' aidai auntynace Ko daddyn Ayman?

Dariya daddyn Ayman yayi Yana cewa' ke dama shikenan abinda tayi Miki kike wannan kukan?
Dasauri nijlah ta daga masa kai tana turo baki.
Be iya Magana ba Saima kallanta dayake can Kuma yace to shikenan kiyi hakuri Zan gayama auntyn kada taqara cewa keba kanwanta bace' to nijlah tace tana murmushi.

Aunty husna dake tsaye jikin window tana jinsu ta tabe baki tana mamakin shagwaba da rigima irin Na nijlah' ita mamaki take da yadda yarinya ke Abu kama me wayo Amma idan tayi wani Abu saikaga kama Bata wani wayo tabe zuge labule tayi Dan batasan daddyn Ayman ya ganta,,nan ta kwanta tana latsa wayan hannunta.


Hanya ya Bata Yana cewa' zoki Shiga cikin kafin Mujaheed ya dawo yasa mutane gaba da tambaya' batayi Magana ba ta Shiga cikin dakinta tana Shiga ta fada toilet.


Girgiza kai daddyn Ayman yayi Yana cewa' kai gaskiya ni bazan iya auren karamar yarinya ba' to tayayama Zan iya da rigimarsu yafada Yana Shiga dakin husna' husna najin taba qofan tasan shine,dasauri ta juyamasa Baya tare da aje wayan a gefe' cikin takunsa Na qasaita ya qaraso bakin gadon' Yana zuwa yasa hannu ya janyota jikinsa Yana dariya' husna batayi Magana ba Saima qoqarin kwace jikinta take nan yay saurin hade bakinsu Seda yaga jikinta yayi sanyi kafin ya saketa Yana me cigaba da kallanta.
Kiyi hakuri babynah bansan meyasa nake kasa controlling kaina Akan Dan uwana ba' Na roqeki ki yafemin.

Janye jikinta husna tayi kafin ta gyara riganta daya Gama batawa tana cewa' nagaji wallahi nagaji daddyn Ayman Nima mutumce Kuma inada zuciya yakamata ka riqa Bina a hankali' dasauri Shima ya dawo inda take Yana cewa' nasani baby nah ina takura Miki Akan Dan uwana sedai inaso kiyi hakuri bazan qaraba.

Kama qara wallahi Duk ranar daka qara Zan tafi ne' nabar muku gidan inyaso saika zauna da Dan uwan Naka da wacce kukeso' Naga Dai Nina kawo nijlah gidan nan Ko Dan haka aiya kamata Ku tausayamin.

Shikenan shikenan husna ya wuce tinda nace bazan qara ba kiyi hakuri yafada Yana hade hannunsa alaman roqo" kasancewan husna nada sauqin kai Bata ce komai ba Saima murmushi datayi tana cewa' yakamata kayi wanka Kaci abinci nasan ka kwaso gajiyan office.

Wuraren karfe 8 Mujaheed yay parking motarsa a waje'Yana sauri ya shigo gidan Yana sallama beji an amsa masa ba kai tsaye ya Shiga dakin nijlah.

Nijlah Na zaune kan bed tayi shiru zuciyanta tayi nisa cikin tunanin mashkur tare da tuno irin soyayya da rayuwar da sukayi kafin ta bar gidan zuwa yanzu' ajiyar zuciya ta safke tare da juyi tana qara rungume pillow dake hannunta' Takai minti ashirin tana nazari' jitake yay Mata halaccin dabe kamata ta manta dashi Adan wannan lokacin ba sedai Bata iya tinanin komawa inda yake Dan bazata iya rayuwar wulaqanci ba.
Ta rasa wanne irin muhalli zata ajiyeshi lokaci guda kaka da Malam suka fado Mata tare da wasu hawaye masu zafin gaske,,Jin motsin ana shigowa dakin yasa tayi qoqarin goge hawayen fuskanta'ta Maida kanta kan pillow ta kwanta tare da rufe idonta.

Ahankali Mujaheed ya shigo dakin Yana tafiya cikin Sanda harya qaraso kan gadon yasa qafansa daya a Sama daya a qasa ya janyota jikinsa tare da Hura Mata iskar bakinsa Yana cewa'hello sweety?

Zumbur nijlah ta miqe tana San janye jikinta ta kasa' Ido ya qura Mata Yana cewa' yada bacci keda mukayi dake Zaki rakani anguwa?
Turo baki nijlah tayi tana cewa toka sakeni saina gayama' Babu yadda Mujaheed ya iya haka ya saketa ya Kuma zuba Mata mayatattun idanunsa Yana kallanta..

Dan matsawa nijlah tayi tace' Yaya kaina ke ciwo bazan iya zuwa ba!
What bazaki iya zuwa ba Ko Dai aunty husna ta hanaki zuwa?
Hannu nijlah tasa ta rufe bakinta tana cewa ah ah niba ita ta hanani zuwa ba' to naji zoki gayamin abinda yasaki fasa zuwa yafada Yana nuna Mata kan cinyarsa' Bata Musa ba ta zauna tana cewa' Yaya Mujaheed kaina fa ke ciwo taba Kaji tafada tana Dora hannunsa Akan goshinta.
Sakamakon tinanin mashkur datayi seya samu kan nata yaya zafi Duk da zafin bame yawa bane' dasauri ya janyeta Yana cewa' Tashi kisa mayafinki muje hospital baki da lafiya kina kwance a daki bazaki fada ba.

Uhmn uhmn nifa banaji yanzu ya Dan saki kabari kawai' ah ah baki isaba' banaso kina tabamin lafiyanki Tashi Maza Maza muje''
Tashi nijlah tayi ta dauka mayafi ta yafa suka fito a tare daidai lokacin da aunty husna da daddyn Ayman ke fitowa a nasu dakin hannunsu sarke da juna.

Sakin baki sukayi Suna kallansu husna tayi saurin cewa' kai Kuma yaushe ka dawo gidan bamu sani ba ?
Yanzu nadawo aunty gashi Na samu sweety ba lafiya'murmushi husna tayi tana kallan nijlah data Boye Bayan Mujaheed tace zo muji jikin naki meke damunki haka.

Mujaheed ne yatari numfashinta'Aunty ina zaku sani kun tafi daki Kuna hutawa kunbarmin ita' murmushi husna tayi tace' oh gadima ka ajiyemu Ko Shima dariya yayi Yana cewa' ah ah nibance ba ya fada Yana riqe hannun nijlah tare da cewa' aunty munje hospital.

Cikin dabara aunty husna tace Aida ka kawota Nina kaita da kaina kaje ka huta ko' kaga yanzu kadawo nasan agajiye kake Ko Dan kanina?

Dasauri Mujaheed yace no aunty kibari Kawai muje ai gwara Na Saba tin yanzu kafin gobe nauyi ya hau kaina' Magana husna zatayi daddyn Ayman yace toke dazaki tafi hospital kinbani abinci?
Girgiza kai husna tayi yace to kibarsu su tafi abinsu kema ki kula da naki mijin' Babu yadda ta iya haka tayi shiru tana ji tana kallo Mujaheed yakama hannun nijlah suka fita.

Ganin yadda husna ta bisu da kallo yasa daddyn Ayman kama hannunta Yana cewa' ah ah hubby wannan kallanfa? Sun dace da juna Ko?
Murmushi yaqe tayi tana daga masa kai tare da bashi amsa da sosaima.
Nan suka zauna kan dinning ta zuba masa abinci' cokali daya ya kai bakinsa itama yasa Mata abaki Yana cewa' kema ci zaki husna tayi murmushi tana cewa'nifa naci nawa daddyn Ayman kaima Kaci wannan Naka ne'ture plate din yayi yace Nima nakoshi indai bazakici ba.
Murmushi tayi tana cewa' kai daddyn Ayman Naga alama sokake kafi Ayman rigima' eh naji ya fada Yana cewa lah kinga Zan manta.

Cikin alamun mamaki husna ta dage masa gira tana cewa' dame ka manta?

Beyi Magana ba Seda ya cinye abincin bakinsa kafin yace' mun raba invitation na daurin auren nijlah da Mujaheed..

Ikon Allah Wai har an raba kace Abu yazo' to yaushene?
Gobe insha Allah harna Gaya Limamin babban masallaci,, za'a daura auren misalin karfe 10:30 Na safe.
Murmushi husna tayi batace komai ba sabida gudun abinda zeje ya dawo tana cewa' Allah ya nunamana ya sanya alkairi' da ameen ya amsa ya cigaba dacin abincinsa husna Ko Bata iya zama ba ta Tashi da sauri gabanta Na faduwa ta koma dakin Harda sa key ta kwanta tana mejin faduwar gaba' Wanda batasan dalilin faruwan Hakan ba.




____________



Tinda mashkur ya kwanta bacci ya gagara zuwa masa daya rufe ido nijlah yake gani tana masa murmushi gefe guda Yana tinanin yadda yake hutawa tare dajin dadin kasancewansa da ita Duk da iya wasanni abin nasu ya tsaya" haka ya zurfafa cikin tunani wani yay dariya wani kewanta ya lullubeshi ahaka Har bacci barawo yayi nasaran daukanshi..

Da asuban fari ya farka nan ya Tashi da kyar ya Shiga toilet' wanka yayi ya dauro alwala' Bayan ya fito ya saka jallabiya ya tada Sallah' nafillah ya gabatar raka'ah biyu Yana roqon Allah daya bayyana masa nijlah tare da fatan samun Zaman lafiya da sabuwar amaryarsa Yasmeen'' Yana idarwa ya tafi masallaci yayi sallar asuba acan' be dawo gida ba seda yay wasu addu'oin tare da karatun alqur'ani, Yana idarwa ya dawo gida' a falo ya Sami 'yan uwansa da suka zo biki Har sun fara hayaniya nan ya Shiga gaishesu daya Bayan daya Suna amsawa kafin ya Shiga dakin mummy' mummy dake zaune da waya riqe a hannunta tayi saurin miqa masa wayar tana cewa'Nasir kagama ya dawo amsa mashkur yayi Yana murmushi yasa wayan a kunne Yana cewa' babban abokin ango katashi lafiya?
Daga daya bangaren Nasir yace lafiya qalau ango ina ka Shiga inata Kiran wayan shiru Se daga Baya mummy ta dauka?
Eh naje masallaci bandawo ba Se yanzu' eh haka mummy take gayamin itama dakin ta shiga nemanka ta samu wayan Na ringing ok to ya akayi mashkur ya tambaya Yana murmushi.

Kaima ka sani batin kudine ba wani abu ba' kai Nasir Wai meyasa kake haka Nafa Baka ATM nakuma ce Duk abinda ya kama Kacira Kawai ba Seka kirani ba.

Ah ah abokina ba haka akeba Na yadda zancira kudi Amma dole saina gayama' abinda za'ayi dashi Da Kuma adadin yadda muke bugata' to naji tinda kai bazaka chanza ba mashkur yafada cike da qosawa' sun Jima Suna waya kafin suyi sallama ya rungume mummy Yana cewa'
Barka da safiya mummy nah' yauwa auta katashi lafiya' lfy qlau mummy yabata amsa' toya fama ya jama'a?

Ina fama mummy Nasir bashida aiki Sai damuna Kuma fa mungama shirya komai' dariya mummy tayi tana cewa ai gwara ayi Shiri me kyau sabida kaga mun gayyaci manya manyan mutane bazamu so Aji kunya ba kasanfa Nima sainaje gurin.

Dariya mashkur yayi ya Tashi tsaye Yana cewa' eh haka nakeji itama Yasmeen tace mama da kawayen Duk zasu zo shiyasa ma muka kama qatan holl Wanda ze isa kowa da kowa..

To kadai shirya da wuri karfe 3 zamu fara' Allah ya kaimu mashkur fada Ya fita a dakin.

Yana komawa daki ya Kira Yasmeen a waya..




Karku Manta mesan cigaba da wannan labari ze sa 200 naira ta wannan number 09038049272,, saina jiku....


A qarshe inaso kusani ba yanzu za'a fara siyan wannan labarin ba Sai next week sabida ina wani aiki nafiso saina Gama yadda zan riqa posting kullum.





Momn sultan ce💘💘 *'YAR SADAKA 2.*💘💘



*BOOK 2.*



*STORY & WRITING...*
*BY*
*MOMN SULTAN*



*WANNAN LABARIN NA KUDI*

*Ga mai so zata biya 200 naira kachal ta karanta ta hanya mafi sauqi' yadda Zaki siya Zaki turo MTN ta wannan number 09038049272,,ko kuma ta account number 0089110527, suwaiba Hussaini zakirai, access bank.*

*'yan Niger su tuntubeni ta wannan number 09038049272,Zan baku number 'yar garinku da zaku turamata kudin insha Allah*



*Free page*



4️⃣


Suna fita ya bude Mata mota Yana cewa' sauri kishiga muje likita ya dubamin lafiyanki' kallansa nijlah tayi fuskanta da alamun damuwa'' dasauri mujaheed ya gyadamata Kai yana murmushi' soyayyanta me karfi ke qaraji a cikin zuciyarsa' lokaci guda ya lumshe ido yaqara budesu akanta Yana cewa' shiga Mana sweety me kike kallo haka' ko nidin na chanza Miki?
Shiga motan tayi a hankali tana kallanshi tana zama tace wayyo Allah ni tsoran asibiti nakeji ko a kauye magani kaka ke jiqawa tana bani.
Dasauri mujaheed yace what kauye' baby kauye fa kikace? Inane can waye naki acan.
Ganin yadda duk ya rikice Mata Yana tambayanta yasa nijlah girgiza masa Kai tana murmushi tare da cewa'bafa haka nace ba tana fada tana turamasa Baki.
Oh'to naji Amma me kikace ya tambayeta cike dasanjin amsa'
Tari me qarfi nijlah ta riqayi ba kakkawata beyi magana ba ya shiga motan yaja da mugun gudu Yana mejin haushin tambayan daya tsaya yimata yasan badan ya tsaya hakan ba da wannan tarin me ciwo be kamata ba' tafiya yake Yana mata sannu nijlah kam Bata amsa Shiba ahaka har suka Isa wani babban hospital'' suna zuwa ya bude motan ya fito tare da zagayawa itama ya bude Mata.
Tinda ta fito take kallan asibitin sedai batace komai ba tabi bayanshi'
Basu Bata lokacin wurin ganin likita ba sabida suba baqi bane asibitin' sosai likita ya dubata ya rubutamata magani suka fito' tinda suka fito mujaheed ke jeramata sannu har abin yafara ba nijlah haushi' tafiya kawai take Yana binta ahaka suka qarasa jikin motan' nijlah na zuwa ta tsaya tare da rungume hannunta a qirji tana kallansa.

Da murmushi a fuskansa yace' yadai sweety? Wani abune yafara Yana gyara tsayuwansa' turo Baki nijlah tayi tana cewa Yaya mujaheed bacci nake Nika kaini gida' to to yanzu kuwa shiga muje kinji baby na' tana shiga yaja motan.


Basu dawo gida ba sai qarfi 10 na dare lokacin aunty husna na tsaye a falon sai zagayashi take tana adda'u dawowansu lafiya gashi tana tsoran Kiran mujaheed sabida kada ya dauka Bata yadda dashi ba' tana nan tsaye taji tsayuwan motansu,, dasauri ta fita tana Kiran sunan nijlah''
Nijlah sannu badai jikin bane ko? Ta fada tana bude motan' murmushi nijlah tayi ta rungume husna tana cewa la aunty nafa Samu sauqi dama kaina ne kuma ya Dena.
To alhmdllh Allah ya kiyaye gaba' nijlah ta amsa da ameen aunty.

A tare suka shiga cikin falon daidai lokacin da daddyn Ayman ke fitowa a dakin Shima sannu da zuwa ya musu tare da tambayan jikin nata' wannan Karan mujaheed ne ya amsa nijlah ko harta fara tafiya' dasauqi mujaheed yasa hannunsa ya riqeta Yana cewa' sweety Ina kuma Zaki kokin manta bakisha maganinki ba?
Rau rau nijlah tayi da ido kafin tace' Allah banisha kaika shanye kayan ka.

Nannauyen ajiyar zuciya mujaheed ya sauke Yana cewa' Kinga sweety hakuri Zaki Kisha maganin nan banaso adaura aurenmu kina fama da ciwan Kai koke bakiso muci amarci a ranar? Safke Kai qasa nijlah tayi tana mejin kunya.
Husna tayi saurin cewa' to Mara kunya matsa kabani guri dariya mujaheed yayi ya sake hannun nijlah' aunty husna ta shiga dubanta a tsanake kafin tace' ah ah fa kanwata kefa amaryace bekamata kina wasa da lafiyanki ba'' ki amsa magani kisha Naga duk kin fada''
Murmushi nijlah tayi Wanda ya bayyanar da kyawun fuskarta sannan tace'aunty Babu abinda ke damuna na warke.

Kallan mujaheed husna tayi tace'to baban soyayya shikenan kaji tasamu sauqi?
Dasauri daddyn Ayman yace' ah ah hubbyna Kinga zo muje daki kibarshi shiyasan yadda zemata dabara Tasha maganin' dasauri husna ta maida kallanta gareshi tana cewa' hubby bafa a daura auren ba Dan Allah ka.....!
Kinga hubby nah ya Isa haka kwana nawa ya rage gobene fa Dan Allah shiga muje yafada fuskanshi Babu alamun wasa''
Yawu me daci husna ta hadiye ta shiga cikin dakin tana waiwayen nijlah data daskare tana kallan mujaheed shi kuma ya tsareta da ido.

Husna na shiga dakin ta dauka wayanta tayi dealing wani number' zagaye dakin take tana fatan a amsa seda takira so wurin 3 kafin a dauka' dasauri tace' hello kawata kinajina?
Daga daya bangaren tace eh kawalli inajinki' yauwa lateefah akwai matsala fa Dan Allah inasan taimakinki' dasauri lateefa tace taimako kuma?to inajinki'' Kinga kibari sai zuwa safe banaso daddyn Ayman yaji'' shikenan kawata goben zanzo da wuri kafin mufara komai '' yauwa kawata nagode husna ta fada tare da surin katse kiran.
Tana aje wayan daddyn Ayman ya shigo tare da rufe dakin Yana cewa' ki saki ranki hubby Babu abinda ze faru' to kawai husna tace ta hau kan gadon tare da rintse idonta tana jin wani irin bacin Rai na taso mata' ahaka daddyn Ayman ya hau kan gadon Yana Mata cakulkuli' nan da nan tafara zillo tanasan kwacewa' be saketaba seda ya tabbata sakonsa ya shiga jikinta kafin yaja musu bargo.

Suna tafiya mujaheed yasa hannu ya daga nijlah sama Yana juyi da ita a falon' tare da yimata waqa irin na saban masoya' dariya nijlah ta riqa yi tana jin dadin hakan' seda yagaji da kansa kafin ya shiga dakinsa da ita' akan gadon sa yamata masauki Yana cewa' wash sweety haka kike da nauyi?
Dariya nijlah tayi tana cewa Allah ah' ah nibani da nauyi Kaine dai qato' pillow ya cillamata Yana cewa' ah ah kece yafada Yana Mata gwalo itama pillow ta dayka suka fara zagaye dakin tana dukanshi da pillow tana kukan shagwaba' seda yaga kukan nata na niyyan zama na gaske ya fara Bata hakuri' shikenan naji nine qatan me nauyi' sweetyna Yar shilace yadda zanji dadin sarrafa kayana ko? Yaqare maganar Yana Kai hannu kan fuskanta.

Shiru tayi ta zauna kusa dashi tana sauke ajiyar zuciya'' sakin fuskanta mujaheed yayi ya dauko ledan maganin nan ya ballo iya adadin yadda Dr yace abata ya riqe a hannunsa tare da dauko Goran ruwa ya bude' Yana cewa' yauwa sweetheart bude baki nasamiki yanzu zakiji ya tafi.
Ni ah ah nijlah tafada kama zatayi kuka' Babu irin rarrashin da mujaheed bema nijlah ba akan Tasha maganin' Amma taqi hakan yasa mujaheed zama kan kujera ya janyota jikinsa'
Wayyo Allah kaka Dan Allah ya mujaheed kayi hakuri niban taba Shan wannan maganin ba' a hankali mujaheed ya bude bakinsa yace'amsa Kisha Dan Allah Kinga jikina yafara amsar wannan salon naki' nidai Kisha mu rabu lafiya' qin amsa nijlah tayi ahaka har saida ya matseta ya dura Mata maganin duk da Bata shanye duka ba' kuka me sauti ta sakar masa tana yarfe hannu. Cike da tashin hankali yace"
Kiyi hakuri Kinga abinda banaso ni kuma bazan iya hakura ba har saikin Sha gani hankalina ze kwanta Dan a gaskiya ba daga qafa yafada Yana bin boobs dinta da kallo.
Tureshi nijlah tariqayi tana kuka' Allah ya Isa takesan yimasa sedai bakinta yakasa furtawa' be saketaba saima qara rungumeta da yayi Yana dariya' to ya Isa haka Yi baccin abinki bazan qaraba yafada Yana shafa bayanta.
Ahaka bacci me nauyi ya dauketa.


__________________



Yasmeen na daukan wayan ta sakar masa kukan wasa tana cewa' shine yau gaba daya baka kirani ba kuma ni na Kira baka amsani ba' murmushin kasaita mashkur yay Yana cewa' tuba nake amarya ran ango' angon nakine ya shiga rububi.
Gyara kwanciya Yasmeen tayi tana cewa' Amma duk da haka aiya kamata najika Koda ba yawa zuciyana zatabi samun sauqi?
To ayi hakuri nasan nayi laifi kinji amarsu' dariya Yasmeen tayi tana cewa' baka laifi mijina yanzu kana ina?
Kinganni a daki yanzu nagama shiryawa nakesan zuwa ganinki kafin anjima afara shirye shiryen party ko?
Wani irin dadine ya lullube Yasmeen Wanda yasata tashi zaune tana cewa' Kai ammako danaji dadi idan nazama ta farko gurin ganin wankan angon nawa.

Dariya mashkur yayi ya katse Kiran tare da daukan makullun motansa ya fita' ko Nasir dasu Ahmad be kiraba ya ya dauka hanyar gidansu Yasmeen' a kan layi suka hadu da Daddy nan mashkur ya tsaya ya fito a hankali kansa a qasa ya qaraso kusa da Daddy ya sunkuya har qasa ya gaisheshi' cike dajin dadi daddy ya amsa Yana samasa albarka' bayan sun gama gaisawa daddy yace' tashi Mana Dana kashiga ciki kaima gidankune' murmushi mashkur yayi Yace' daddy Naga da mutane ciki data fito saimu gaisa nabata sakon..

No kashiga kawai mutannan danwa suka zo' Ina sabida daurin aurenkune? Daga Kai mashkur yayi Yana mejin kunya' Babu yadda ya iya yashiga ciki' sedai be qarasa shigaba ya Kira wayanta' Yasmeen na dauka tace hello angona?
Murmushi mashkur yay yace' baby ki fito gani a get.

Wani irin tsalle Yasmeen tayi Wanda yasa kawayenta binta da kallo suna dariya'mubeena tace' ji banza Naga dai yau za'a kaiki ku kwana tare qarewan doki' murguda Baki Yasmeen tayi tana cewa' aidai ba'a kainin ba gwara Naga abina kafin lokacin tana fada ta koma jikin mirror ta gyaran kwalliyanta da daurin dankwalinta ta fita a dakin tana musu dariya.

Tsaye ta sameshi ta qarasa jikin wani kofa a hankali ta bude tana cewa' Bismillah baby zo muje' kasa magana mashkur yayi sabida chanzawan dayaga Yasmeen tayi masa har saida ta shiga ciki be dawo daga dogon tinanin daya tafi ba' tana shiga ta duba taga be shigova' da sauri ta koma tana dariya tana cewa' baby muje Mana bafa kowa a ciki bakaga yanzu na bude dakin ba.

Beyi magana ba yabita a baya Yana murmushin jin dadi' suna shiga ta Sami guri ta zauna Amma me' mashkur Yana zama ya miqa Mata hannu Yana cewa' come to me dasauri Yasmeen ta tashi ta qarasa inda yake zaune kanta a qasa' jikinsa na karkarwa yasa hannunsa biyu ya zaunar da ita akan hannun kujeran dayake Kai gani yayi hakan be masa ba ya qara dawo da ita kan cinyarsa Yana kallanta tindaga fuskanta har zuwa qafanta' yawu ya hadiye yasa hannu ya dago fuskanta ' dakyar ya iya bude Baki yace' baby kinyi kyau kafin tayi magana yakai hannunsa kan boobs dinsa Yana shafawa tare da matsasu .
Uhmn uhmn Yasmeen tafada tana riqe hannunsa' be iya Bari ba danba a cikin hayyacinsa yake ba!
Hannu yasa Yana qoqarin zuge zip din rigarta tayi saurin riqesa tana cewa' wayyo baby da zafi' kumani' ni'!
dakyar mashkur ya iya bude bakinsa dayamasa nauyi Yana magana' kiyi hakuri nijlah kibari nasha ko kadan ne wallahi a buqace nake ganinki ya tadamin da tsumin daya Dade be motsaba taba kiji taba nan kinji nijlah tah....

A firgice Yasmeen ta dago idonta Wanda jajur tana kallansa dashi.






Number da zaku Samu cigaban wannan labari 09038049272 karku siya wannan labari a gurin kowa indai Bata wannan number ba' saina jiku






*Momn sultan ce*💘💘 *'YAR SADAKA 2.*💘💘



*BOOK 2.*



*STORY & WRITING...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*NA KUDI NE*

*Wannan labarin na kudi ne' ga mai so zata Biya 200 naira kachal ta karanta' Zaki Tura katin MTN ta wannan number 09038049272,,Ko ta account number, 0089110527, suwaiba Hussaini zakirai, access bank.*

*'yan Niger su tuntubi wannan number,, +22789520047.*

*Garabasa ga duk Wanda yasan 'yar sadaka ze karanta wayafi sonta na mmn fareesah akan 200 naira'Wanda bai siya 'yar sadaka ba zai karanta shi 300*


*Free page*


5️⃣



Kwance nijlah take jikin mujaheed tayi lamo da ita tana bacci yasa hannu ya zageye bayanta Kai kace kwace masa ita za'ayi'sosai ya zuba Mata Ido yana kallanta,, zuciyarsa na qara zurfafa cikin soyayyan nijlah' ya rasa wanne irin so yake mata' ya tabbata idan za'abashi zabi a duniya babu abinda ze zaba sama nijlah' a hankali mujaheed ya janyeta daga jikinsa ya kwantar da ita a kan pillow Yana murmushi' da sauri ya daga kansa ya kalli qatan agogon dake manne a dakin' cike da mamaki ya zaro Ido ganin yadda lokaci yaja' a hankali ya maida kallansa gareta Yana cewa' bangaji da kallan wannan kyankyawar fuskar taki ba nijlah sedai Zan tafi sabida kema ki Samu kiyi bacci cikin nutsuwa.

Kamar tanajin abinda yake fada tafara juyi akan makeken gadon rigar jikinta na dagawa take boobs dinta suka bayyana Wanda zuwa yanzu sun fara cikowa daga qirgan dangi sabida jin dadi da chanjin abinci data Samu' zuba Mata Ido yayi zuciyarsa na dokawa tare da yimasa zillo akan abinda idonunsa ke nuna masa' sedai bashida yadda zeyi nan yaja qafarsa datayi masa nauyi ya fita a dakin zuciyarsa na dokawa tare da azalzakashi akan shauqi da begenta' Allah' Allah yake gari ya waye a daura masa aure da ita koya Dena jin wannan azababben abin daya tokare masa qirji'

Yana fita ya zagaya ta kofan baya ya shiga cikin dakinsa' da kyar yayi wanka ya kwanta' daren ranar kasa bacci mujaheed yayi sai faman juyi yake gabadaya ya rasa abinda ke damunsa' zuciyarsa Banda harbawa babu abinda take 'bacci yake sanyi Amma daya runtse Ido nijlah' yake gani tana masa murmushi tare da shagwabanta Mai tsayawa a rai' har qarfe 3 bacci be iya daukasaba saida kyar yasamu bacci barawo yayi nasaran daukanshi.


Tin asuba husna ta tashi tana tinanin yadda zata kubutar da nijlah'daga wannan aure' duk da tasan nijlah na kaunar mujaheed sedai haka kawai takeji Bata San ayi auren batare da sani ko amincewar iyayen yarinyar ba' tashi tsaye tayi tana zagaye dakin tare da qara duba agogon hannunta a Karo na barkatai zuciyarta na qara dokawa tare da yimata lugude Wanda yasata ta kasa zaune ta kasa tsaye' bude Ido daddyn Ayman yayi dake kwance kan gado yayi juyi tare da addu'a ya tashi zaune Yana kallanta' ya jima Yana binta da kallo Bata sani ba' girgiza Kai yayi ya tashi zaune tare da Kiran sunanta acikin nutsuwa gami da zuba Mata shanyenyun idanunshi?

A firgice husna ta amsa tanasan boye damuwar dake kwance a fuskanta'sosai daddyn Ayman ya lura da yanayin datake ciki Dan haka yayi shiru Yana binta da kallo Mai dauke da tambayoyi iri iri?

Cike da qarfin Hali husna tace' daddy Ayman ka tashi' ga ruwan wanka na hadama

Please Login or Register in order to submit comment