Reading IG AJEEMAL complete part 2 by Oum amreesh Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng AJEEMAL🌬

STORY AND WRITING
By

Oum amreesh❤

DAGA ALKALAMIN

Khaleeseart Raeeys💦💦
...........
....
.........Free book😍

............


Page 4⃣8⃣..............................

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

.......
..Gyara tsayuwa heelah tayi baki bude heelah kebin ajmal da nisha da kallo yayinda nisha ke serving dinshi tashaka abinci a plate tatura masa plate din gabanshi, jikake dadda dan kamshin abincin gabaya daya ya gauraye tsakar parlourn duk wani abunda nisha tasan ajmal zai bukata seda ta tanadar masa, heelah takaici yacikata kamar ta hadiye ranta jitayi tamkar ta isa garesu tarufesu da duka tadauki plate din abincin tajuyewa nisha atsakiyar kanta ,

dakarfi raheelah ta ciza lips dinta daga bisani cikin sauri tahaura upstairs tabar arean parlour , tsit kakeji parlourn kamar bakowa , nisha tunda ta gama serving din ajmal taja baya tatsaya tana bin aheel da kallo gwanin ban tausayi ya shige jikin papansa tamkar maishirin komawa ciki, se ajiyar zuciya yake saboda tsawar dayasha gurin mommynsa dazu , itade kullum tausayin aheel da kaunarsa sake karuwa yake kullum sake tasiri yake cikin zuciyarta , jitake inama ace aheel daga cikinta yafito dayasha tarairaya kulawa tareda shagwabashi , wacce baisamu daga mom dinsa ,

ajmal kuwa hankali kwance yakecin abincin yana latsa phone dinsa, yau wajan cin abincin nasa harwani lumlumshe ido yake da alama yana amsar sakon girkin yanda yakamata , kamar wanda akace yadago kai , karaf idonsa yasauka akan nisha wacce ta zura masa ido yuwa zata lasheshi se zuba murmushi take , ganin yanda taga ajmal keta lumlumshi ido kamar maijin bacci , harkullum face dinsa kara kyau da kwarjini take ga kyakykyawan dimple dinsa dake lotsawa yayinda yake cin abincin , duk wanda yasanya ido kansa bazaiso yajanye idonsa daga kansaba"

He! are you okay ajmal yatambaya yana hade gira , "

I'm okay nisha tafadi adan razane because yakamata tana masa kallon kwaf, jin haka yasa yacigaba da cin abincin , yana kammalawa , yajuya gefe yakalli kyakykyawan dan nashi aheel wanda tuni yasuma gyangyadawa jikin papanshi , ajmal hanu yasa yasun kuci aheel yadaura saman cinyarshi aheel tar idonsa akan papanshi yashiga zuba murmushi, ajmal shima kallon dan nasa yake tareda fadin,"

My little boss aje ayiwasu hajia gaisuwan safe ajmal yafadi yana masa alamar yabi nisha sutafi aheel kamar jira yake dama cikin hanzari yazame daga cinyar papansa ya isa gun nisha yana washe mata baki, itama se murmushi take zubawa, nan tamatsa tashiga tattare saman table din tareda daukan tray din tana shirin barin parlour,"

As from now bana bukatan breakfast lunch ko dinner daga side din su daddy , duk wani abun bukata na tanadesu cikin store dina , kululu yan hanjin nisha yakada meyake nufi ?kitchen dinsu zata shiga tanamasa girki ? "

Bakiji bane? ajmal yatambaya jin shiru bata amsashiba, nisha murya asanyaye tace "
To naji ,

daga haka tadauki hanyar fita tareda aheel dake biye da ita , ajmal tunda tajuya yakurawa bayanta ido hartafice ,karun farko daya tsaya yasanya ido akan yarinyar yau shigar da nisha tayi skirt and blouses yayi matukar yimata kyau gashi yafitar mata da shape sosai ajmal baisamu daman kallonta da kyauba har seda tajuya baya sannan yasamu daman yimata kallon tsaf yanda take tafiya slowly kamar wata macijiya gwanin daukan hankalin mai kallonta ba laifi yarinyar akwai tsari da yanayi maikyau duk da ba tsayawa wani kallonta yake da kyauba, balle yasan sauran baiwar da Allah yamata

wani gauron numfashi yasake daga bisani yamike yanufi upstairs yashiga bedroom dinshi tunda yashigo dakin yafahimci kamar ankimtsa bedroom din ba kamar yanda yafita yabariba , koda yashiga toilet ma haka angyarashi an wanke duk dadai gyaran bawai dari bisa dari bane yasan bazai wuce aikin heelah ba. tadaiyi kokari because bawani iya aiki tayiba just kinibibine irin nata, koda yashiga toilet din bakinsa ya wanke tareda face dinshi sannan yafito yanemi sofa yazauna , laptop dinshi yashiga dannawa yafada wani aikin jim kadan heelah taturo kafa tashigo kallo daya ajmal yamata yakai dakai yacigaba da abunda yake,

tana karisowa tanemiguri kusa dashi tazauna ,"

sannu da hutawa honey heelah tafadi tana dan murmusawa, batareda yakalletaba yagyada mata kai batareda yace komai ba, dan silent heelah tayi daga bisani tadaura head dinta a shoulder dinsa tashiga raira masa kuka, mamakine yakama ajmal jin sautin kukan heelah ya doki kunnuwansa , rantsa ido yayi tareda zame shoulder dinsa yajuyo suna fiskantan juna ,"

what are you cry yatambaya yana kallon heelah dake matsar kwalla, head dinta tamayar saman cinyarshi cikin kuka take fadin,"

Pls honey meyasa duk abunda zanyi naburgeka bakaso ? why? inwani laifi nayi aiseka sanar dani nabaka hakuri pls heelah tafadi gamida tasowa tarike hand din ajmal, "
niba abunda kikamin, kuma niban hana kiyi abunda zaiburgeniba duk da burgeni abune mai walaha kema kin sani yafadi yana dan zame hand dinshi, "

But meyasa kazabi waccan yarinyar amatsayin mai hidama dakai bayan gani amatsayin matarka , "

ba zabanta nayiba tananuna miki abunda yakamata kiyine amatsayinki nayadda kikafada , koba komai tafara maido dake cikin sense dinki, ajmal yafadi tareda mikewa yadauki phone dinshi yana kokarin barin dakin, takaici duk yacika heelah jin abunda ajmal yafadi mai yake nufi da ita tadawo da ita hankalinta, dasauri heelah tawuce gabanshi tana fadin, "

to daga yau banason sake ganin kafarta cikin side dinnan idan ba hakaba sena karyata gida uku.., ihu heelah tasake sakamakon damko gashin head dinta da ajmal yayi , rai amatukar bace yake magana,"

baki fiska danayi bashi yake nufin kimin rashin kunya ba , sake murda gashin nata yayi yanacigaba da fadin "

yarinyar dakike magana akanta kuma she is my staff nitakeyiwa aiki bakeba barunki da ita , yana gama fadin haka yasaketa yajuya yafita abunsa , dagan heelah tafadi kan gwiwowinta tasaki sabon kuka tamkar wacce tayi sabon hauka ,....

dariya suke sunashewa gwani shaawa ana breakfast anatafa hira kamar yanda aka saba , su hajia Goggo rabi ammi ga daddy wanada aheel kecinyarsa yanashan fruit salad , gefe su yan matan ammi reeda da fadeelah sekuma nisha dake gefen hajiarta ,"

Niko nace ya maganar komawar takine , ko kincanza ra ayine bayanzuba Daddy ke tambayan Goggo rabi , tambayetade ya kama tasamu takoma tabar bar gdnta tamakale anan, hajia takarbi zancen tana kallon Goggo rabi, dan zumbura baki Goggo rabi tayi kamar wata karamar yarinyar tana fadin,"

ba fasawa nayiba jira nake atsai da bikin yaranan nan saboda nasamu daman dawowa bikinsu nan kusa , "


Hhh wasu yaran wai? Daddy yatambaya yana yar dariya , "

gasu agefenka kana kallonsu Goggo rabi tanuna su reeda dasuke zazzare ido , "

yo banda abunki yaranda suke karatu basu tsaida samariba balle asa ranar auraddasu gwarama ita fareeda yar gd za ayi ba matsala but ita hajia karama ( fadeelah ) babu saurayin ma balle ayi tunanin hadasu Daddy yafadi yana dan kurban ruwan tea dariya duka suka bushe dashi suna kallon fadeelah wacce taturabaki tashagwabe fiska,"

To albishirunku , itama fadeela anyi mata miji lokaci kawai mukejira, gabaki daya hankalinsu suka mayar kan ammi wacce takemagana, "

ina mijin yake akawo manashi mugansa Goggo rabi tafadi suna koma dariya, ,"

seriously last week MODIBBO yasameni da maganar cewa yayiwa fadeelah miji nasanarwa Daddynsu atsaida ranar bikinsu, "
Amma ai ba asanar danidinba , amma waye yayi babban saa haka Daddy ya tambaya gaba daya suka koma maida kallonsu ga ammi suna jiran amsa harda fadeelah dayi tsuri tsuri da ita tana jiran tajiwaye akayiwa sadakanta haka , murmushi ammi tayi tana dan juya ido takalli fadeelah miji nagari zabi mai kyau aboki ga yayansu kuma doctor gida da waje doctor fu' ad Allah yasa zamin yayi miki ammi tafadi tana kallon fadeelah data zaro ido waje , tsan tsan farin ciki batasan sanda tafurta,"

Alhamdulillah abaiyabe wanda yasa tayi hanzarin mikewa dasauri tabar gurin tanufi bedroom da gudu , nan fa su nisha da reeda suka rufa mata baya , daga nan fa dukansu suka shigayin hamdallah lallai yayansu yayiwa kanwarsu zabi nagari sede fatan dacewa , "

Masha allah komai yayi kyau yanda akeso , duk da tafiya tasameni cikin week dinan ammade zanje muzauna da dan uwana (abu)muga abunda yadace se musamu mutsaida bikin ko nan da 1 month tunda bawani abunda zamu tsaya jiraba, sede muyi fatan Allah ya aramana tsawun rai da lokaci, nan su ammi suka shiga amsawa "Ameen ,

yau kowa farinciki fal zuciyarshi , fadeelah kamar tazuba ruwa akasa tasha saboda tsan tsan murna da farinciki , haka suka wuni suka kwana cikin nishadi , washe gari da safe karfe 8 nisha tayi wanka tafito takimtsa jikinta tashirya tsaf cikin duguwar gown tareda yafa mayafi bisa kanta tanufi fita side ajmal ,

kamar yanda ya fada baya bukatan wani abu daga bangaransu , tana isa part dinshi kamar kullum seda suka gaisa da securityn dake wajan sanan tasamu daman shigewa ciki, koda nisha tashiga ciki hamdallah tayi ganin bakowa cikin parlourn

sidi sidi , tashiga kitchen, seda tafara gyara kitchen din takimtsa komai daga bisani tashiga duba kayayyakin da zatayi amfani dasu bada wani bata lokaciba tashiga hada masa dadda dan delicious data saba , cikin dan kankanin lokaci ta kammala komai tafito tajerashi komai slowly takenyinshi gudun kar wanan masifaffiyar matar tajiyuta, nan tasuma kokarin komawa kitchen din but kankace kwabo heelah tabaiyana a parlourn kaikace kamar jiratake, "

Mayya dama nasan kece mai mini buruntu a kitchen, tundaga sama nakejin motsi akasa mai kikazo dauka? heelah ta tambaya yayinda take kokarin karisawa ga nisha wacce tayi tsayowar soja batare da tawaiwayoba , "

Tambayarki nake kibani amsa kinyi ajiya a kitchen dinne da kikazo dauka , heelah takuma tambaya tareda juyo da nisha suna fuskantar juna, "

Uhm breakfast nazo na hadawa papan aheel, nisha tace tana zare ido,"

Uhm yayi kyau dakinbar wannan muzuran dakikeyi ba koranki zanyiba , because ke yar aikin mijinane Mai mana hidima , Bakomai kicigaba da aikinki , sede warning dina dake shine banason wadanan kazamun kafafuwan naki yasake taka bedroom din mijina da sunan gyara , wannan nikeda hurumi da hakki akanshi inafatan kin gane,? but babu laifi kigyaramin nawa bedroom din , dan matsawa heelah tayi dining table area tashiga duba girkin da nisha tashiryawa ajmal, dan tabe baki tayi sannan tace,"

Inada bukatan abinda zanci yanzu wadannan abubuwan DA kika shirya banida ra ayinsu, ko zaki iya shiga kitchen kigirkamin abinda nakeda bukata ,"

kiyi hakuri aunty niba yar aiki bane bazan iya sake girkawani abin yanzuba because inada abunyi yanzu, nisha tafadi tana mai kokarin barin parlourn ,"

ke tsaya heelah tafadi gami da janyota baya, mekike nufi dake ba yarki bane bayan aikatau kekawoki side dina kuma akarkashin mijina kike , dole kikasance akarkashin matar shi, dan haka kiwuce kije kiyi abunda nasaki , cike da takaici nisha tadubi heelah tana fadin"

Eh akarkashin mijinki nake but kekuma ban kasance akarkashinki kiba because ni yar hidiman mijinkinkine bakeba , dan uwa kuma yayana nadauki mijinki ba uban gida ba,, incede kima macece kamarni , zaifi kyau kishiga kitchen kiyiwa kanki abunda zakici , ni inada abunyi nisha tana fadin haka tajuya zatafice , aiko cikin takaici da bakin ciki heelah batayi wata wataba tasha gaban nisha tadauketa dawani gigitaccen mari wanda yasa nisha zubewa kasa ta tallafe gefen face dinta tasaki kuka wuiwui kamar karamar baby , "

tas nisha taji andauke heelah damari itama wanda yasa nisha mikewa daga durkuson datayi tana kallonsu, ajmal ne tsaye jikinsa sanye da white jallabiya wanda yake tsaya tundazo daga sama yana hango rikicinda heelah keyi, ganin marinda heelah tayiwa nisha yasa yayi saurin sakkowa cikin bacin rai yadauki heelah DA mari seda taga wasu taurari, "

nikamara? heelah ta tambaya tana kallon ajmal wanda shima Itan yake kallo cikeda takaici,"

saboda namari wannan mara kunyar yarinyar shine kasa ahanu afiskana da sunan mari , abunda bantaba fiskanta daga garekaba wlh azim yau kajawo mata kwanan kabari heelah tafadi akidime tayi wajan dining tazari wata yar karamar wuka zatayi kan nisha dashi,

nisha kamar wacce aka dasa agurin gaba daya tatsorata takasa yin gaba ko baya , ganin abunda heelah ke kokarin aikatawa yasa ajmal yashiga gaban nisha yatare heelah daga abunda takeson aiwatarwa rike hand din heelah yayi tareda fisge dan karamin wukar dake hanunta yacillashi gefe , daganan yasa hanu h
Yasunkuci heelah saman shoulder dinsa ya haura da ita sama, direct bedroom dinta ya nufa da ita , seda yakata harsaman bed ya wullar da ita daga bisani cikin hanzari yabar dakin tareda baida kofar yarufeta tabaya da key, heelah kamar wanda hauka yasuma taba kwakwalwarta haka take dukan kofar da karfi tana fadin ajmal yazu ya bude yau seta kashe nisha,

ajmal ko ajikinsa haka yanufi downstairs cikin sauri , amma kafin isowarshi ,nisha najin motsin sakkowanshi ahanzarce tasamu daman watsawa dagu tayi waje, ajmal naganin fitar hakan yasa yakoma yazauna kan sofa , yadau mintuna yana zaune agurin daga bisani yamike yahaura sama yanufi bedroom din aheel, koda yashiga yasamu dan nasa se bacci yake tasha hankali kwance , hakan yasa ajmal ya fice daga bedroom din aheel yanufi nashi dakin ,

yana shigowa yadauki phone dinsa domin duba time karfe9 dawasu yan mintuna gakuma miss call dayasamu cikin wayarsa jikin screen din wayar anrubuta "

My blood bro, phone din ya ajiye yanufi toilet yayi wanka yafito yashirya cikin shiri maikyau daga bisani yanufi kasa, kotakan breakfast din biyeba yawuce yafita abunsa ,

Aban garan nisha kuwa tana barin side din ajmal tanufi part dinsu direct bedroom dinsu tawuce tasamu su reeda se bacci suke basuda niyan farkawa yanzu, itama kwanciyar tayi tana share hawayenta tareda maida ajitar zuciya , bakaramin takaici tajiba da marin da heelah tayimata, amma ko bakomai taji radadin da takeji yarago tunda agabanta ajmal yasa hanu yawanke matansa da mari saboda ita , bakaramin jindadin hakan tayiba ,

ko bakomai da lamamun tana da dan mutunci aidonsa tunda ya iya marin matarsa akanta abunda baitabayiba kuma yanuna baccin ransa sosai afili, to kuwa itama yanzu takejin takudiri damaran farantawa mijinta tareda yimasa hidima yanda yakamata tunda ita tagaz



a, daha bacci mai nauyi yadauketa because dama tagaji gashi jiya batayiwani bacci sosaiba saboda kwana tayi tana karantu exam dazatayi na jam gobe gashi dasafe ta tashi dawani aikin kuma,

Misalin karfe11pm nisha bacci mai nauyi take , cikin baccin taji anataba mata tafin yan kafafuwanta, but takasa bude idanunta because baccine sosai acikinsu haka cikin muryan bacci Nisha kefadin ,"

Banaso!

cankuma sejitay ankoma anakokarin jan pillown data kwanta Kai ahankali, jin head dinta nakokarin barin saman pillow yasa tabude ido ahankali , tar tabude idonta gamida tashitsaye tsakiyar gadon tana zazzare idanu , farkon bude idonta ganitayi kamar ajmal tagani yana tsaye kanta, daga bisani kuma data murza idon dakyau kamal tagani tsaye yana washe mata baki yana fadin,"

Surprise!

da mamaki take binshi da kallo sekuma tamaida kallonta ga dakin ita kadai su fadeelah basanan sekuma takalli kamal wanda keta zubamata murmushi kamar gonar auduga, "

Ya kamal! Kaine? nisha tafadi ahankali, dariya yakwashe dashi kafin yace,"

Year I'm nacanza mikine? yafadi yana mata kayataccen murmushi, sakkowa nisha tayi daga bedroom din tana fadin, "

saukan yaushe? Ina aunty nabilah? dan matsowa yayi kusa da ita yana fad'in "

Nayi surprising din kune because
duk gidan nan bawanda yasan da zan dawo ya ajmal ne kaide yasani in fact ma shiya daukomu daga airport, kallonshi kawai nisha keyi tana murmushi,"

Ina aunty nabilah nisha tasake tambaya karo nabiyu, kamar bazaiyi magana ba sekuma taji yace,"

tana sashin hajia a can muka sauka duk family anacan kekuma kinanan kina bacci, cikin hanzari nisha tashiga fadi'n, "
Muje can musameso to tafad'i tana kokarin yin gaba , ga mamakinta setaga kamal yanuke, bakin bed yanema yazauna tareda hade raii, "

Zomuje mana! Nisha tafadi gamida jiyowa tana kallonshi, amma kamal senukewa yakumayi yaki tashi, dariya nisha tasaki ganin yanda kamal yayi tamkar wani baby harda wani nuke shoulder, "
Please meyasa? Nisha tafadi tana d'an shagwab'e fiska "

Naki d'in da murna da d'auki nataho gareki but ko tambayan yanake bakiyiba balle. adanyi hugging dina amatsayina na brother dinki, dariya nisha takumayi tana fad'in, "

I'm sorry bro ya kake let me shaking hands nisha tafadi gamida mika masa hanu , haka kamal yadauki hanu yamika mata amma ga mamakinta setaga kamal gam yarike mata hanu tareda janyo hanunta tafado jikinsa tsam yarungumeta akirjinsa kamar wata baby, cikin hanzari nisha tajanye jikinta akunyace tafice da gudu tana murmushi, shima mikewa yayi cike da farin ciki da nishade yana murmusawa yabi bayanta,

Nisha bata tsaya da gudunba harseda ta iso door din hajia taja tatsaya ganin ajmal dake kokarin fitowa wanda harsuna kokarin karo da juna , kallonta ajmal ya tsayayi da mamakin hanzarin metake gashi harwani haki take kamar wacce tayi tsere , daga kanda zaiyine ya hange kamal dake biye da ita wanda ganin yayansu yasa yarage saurin yashiga tafiya slowly yana sosa keya irinta marasa gaskiya "

wato shiyasa akane meshi cikin family aka rasa ashe gun wannan yarinyar yaje yatare ajmal yashiga maganar zuci , baitsaya jiran isowar kamal ba yasamu daman barin wajan yanufi side dinshi, wanda hakan yabawa nisha daman shigewa part din hajia cikin hanzari kamal shima yasamu daman biye mata baya, ajmal yana isa cikin parlour ya hangi aheel da mom dinsa wacce tayi amfani da extra key wajan bude kanta tazuba musu abincin da nisha ta girka sunaci , aheel naganin papanshi yashiga washe baki yataso da gudu ya rungumeshi , cidak ajmal yadaga aheel suka karisa dining table suka zauna, "

Your welcome dear heelah tafadi kamar ba ita tagama daru dazuba, shiru yayi baice mata kala ba sema kallonta dayake idonta sunyi subul subul dasu saboda kukan datasha dazu , mikewa tsaye tayi tashiga yin serving din ajmal ba tareda yanemi taimakon taba , shikuwa baiyi kokarin dakatar da itaba hartagama tatura masa plate din abincin gabanshi tareda duk wani abun bukatu , bamusu yasuma cin abincin , yana tsaka da cin abincin kamar wanda aka tsikareshi idanunshi suka shiga hasko masa nisha dake tafe cikin hanzari kamal nabiye da ita,

Nan kuma ya kauda wannan tunanin daga ransa, lokaci d'aya kuma yaji abincin yafita daga ransa ma' ana yakoshi , haka yasoma kokarin mikewa , "

Papa ina zakaje ? Aheel ke tambayan papanshi ganin yamike"

I'm going to the rest kazauna kusa da mom dinka ,gyada kai aheel yayi tareda cigaba dashan cornflakes dake gabanshi , heelah bayan ajmal tabi da kallo tana tab'e baki harya kurewa ganinta ,..
,
Ab'an garansu nisha kuwa tunda suka shiga sashin hajia , a parlour suka tararda sauran familyn anatashan fira cikin raha Daddy ammi hajia da Goggo rabi sesu fadeelah da reeda wanda suka sanya nabilah a tsakiya sunata zuba mata surutu da tambayoyi, itakuwa nabilah duk hankalinta nakan kamal da nisha wanda sukashigo yanzu atare ,

duk yanda nabilah tayi iya kokarinta wajan mantarda kamal soyayyan nisha amma abun yaci tura , yanzu gashi daga saukanso zuwa gida ita yafara cigiya , koyanzuma da ake tsaka da hira tafahimci yanda suke jefawa junansu wani kallo suna murmushi, shiyasa koda sukashigo cikin parlour nisha data dagawa nabilah gaisuwa ba harzuci ta amsa mataba saboda yanda kishi ke d'awai niya da ita, itakuwa nisha kallon nabilah take ganin yanda takara canzawa tayi kyau taciko kuma takara haske ,da alama hutu yakarbeta

Masha allah wasa yayi kyau kamal kundawo cikin SAA sede kuma kasam mashemu because bawanda kafadawa , yanzu yakamata mubarku kuje kuhuta kaida matarka dan nasan baza arasa gajiya atareda kuba, Daddy yafadi yana kallon kamal daga bisani kuma yamaida kallonsa ga ammi yacigaba da fadin,"

yakamata kiyiwa barka magana ta tanadar musu da abuntabawa , daga bisani kuma munada bukatar ahadamana kayataccen dinner in the night saboda farinciki wannan ranar , "

Insha allah yanzu kuwa ammi tafadi cikin farinciki tareda mikewa tafice , sundan taba hira sosai yayinda kamal yaciga ba dabasu labarin yanda wasansu ta kwallon kafa takasance, seguraran azahar tagabato kai suka suma watsewa domin gabatar da bautan ubangiji, koda suka fadeelah suka shigo bedroom dinsu reedane kadai tashiga toilet tagabato alwalanta sukuwa nisha da fadeelah suna fashin sallah ya bakon nasu kusan atare yaziyarcesu,

cikin nisha da yamurda matane nayunwa yasa tatuna tunsafe ba abunda tasawa cikinta , hakan yasa tamike tafice tabar fadeelah dake kwance saman bed tana latsa wayarta , nisha direct kitchen tanufa ta tadda barka tana tsaka da aikin da ammi tasata , barka naganin nisha tasaki murmushi, "

yar nan yau koma inakika shiga kolekoni bakiba inata cikiyarki ,murmushi nisha itama tayi tana fadin"

kinsan yanzu papan aheel yace nadaina kawo masa breakfast daga nan sede naje can part dinsa nayimasa girki dana dawo kuma bacci nakomayi shiyasa yau bakijiniba ai , "
.
Kai amma yayankun nan yana wahalar mana dake amma ko bakomai zaki samu lada ai, amma koya kikeji da wannan masifaffiyan matar tashi mai bala'in kishin tsaya duk ita take kore masu mata aiki saboda rashin hankali irin nata , barka tafadi gamida jimami, ,"

Uhm baba barka taimakeni da a binda zansawa acikina because yunwa nakeji sosai tunsafe namance banci komai ba nisha tafadi gamida kaiwar da zancen barka,"

laa ai ammi tafadamin bake a breakfast din dazu sabida bacci kike baki tashiba shiyasama nakillace miki naki breakfast din amma inda wani abunda kikeso kifadi yanzu sena miki shi,"

aa basekin wahalar da kankiba iya wannan dinma yayi ,"

To shikenan kede jekizauna a dining table yanzunan zanfito barka tafadi, bamusu nisha tayi abunda barka tace ba dadewa barka tafito daga kitchen tajerawa nisha plate agabanta plate din Irish and chicken dawani hadin salad agefe se dan madaidaicin kyakykyawan bowl mai daukeda fruit salad wanda yaji madara Yakuma sha sanyi ,bawani tsayawa jira nisha tasoma ci seda taci takoshi takauda yunwar dake tareda ita daga nan tadauki plates din tanufi kitchen, tana shiga ta ajiyesu daga bisani tashiga taya Barka da aikace aikacen da take ,sannu ahankali sunayi suna fira hatsuka kammala daga nan suka shiga jera kayan lunch bisa dining table daga nan Barka takoma kitchen tadauko try din abincin data tanadarwa kamal da matarsa masu lunch din tasuma kokarin ficewa,"

Baba Barka ina kuma zaki bayan gani ? nasan lunch din su ya kamal ne da aunty nabilah please

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment