Reading MANSURAT by Daga Alƙalamin Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

arish tanama soyawa ne tareda egg tana hadawa da toasted bread tanayi tana tilawanta cikin zazzaqan muryanta tana fidda tajwid tanaba ko wani harafi haqqinsa kamshi duk ya bid'e gidan, ijiye cup din yayi ya fice.


































































Shap shap ya shirya cikin jean da light long sleeved t-shirt,
Ya dauki car key dinshi da phones dinshi ya fice, parking lot ya nufa tunkan ya karisa ya danna remote motan shi kirar jeep na cherokee ta bude yana karisawa ya shiga ya mata key yayi horn da gudu me gadi ya bude ya fice ya nufi asibiti.




Mansu kam bayan tagama soye soyenta ta fito dasu ta koma daki tayi wanka tabar Ayya na nata kumallon, shiryawa tayi cikin lingeris cloth tayi kyau sosai ta saka glass dinta ta fito.


Ayya dake zaune tace. "Yar albarka maza kiyi kumallon kizo kimin tausa in kika koma makaranta zanyi kewanki. "
Murmushi tayi. "Kuma gashi gobe zamu koma amma ai bazamu dadeba zamu fara exam muna gamawa kuma shikenan nagama boarding...."
"Hummmm zanko yi kewanki sosai. "
Murmushi tayi. "Anjima zamu fita da Ya Farhan daddy yace ya kaini shopping. "
"Allah kaimu. " Ayya ta fada, Mansu ta amsa da. "Amin. "


Karisawa tayi tazauna kan dinning tafara kumallonta cikin kwanciyar hankali,




























































Bayan ta gama ta kwashe abubuwan da suka 'bata takai kitchen danta wanke a kyamace tasa hannu ta dauki cup din da Aryan yasha tea da spoon ta ijiye acan gefe tafara wanke wankenta ko kallon cup din bata sake yiba dan shike wanke abubuwanshi inya dawo,


Bata jimaba ta gama tafice falo tafara yiwa Ayya massage suna fira sama sama.




................


Around four sukaji sallaman Farhan dago kai tayi tana kallon shi tareda d'an jan tsaki. "Ya Farhan se yanzu kazo.....? "
Wani kallo ya mata. "To tun asbah kikeso inzo kinsan nifa ba irinki bane inada aikinyi..."
Baki ta ta'be. "Nima ba aikin banza nake yiba kabani nanda four years zan fito maka a cikakkiyar yar jarida na....."
Murmushin gefen fuska yayi. "Yarinya kenan ashema sena baki four years...."
"Naso kazo da wuri har gun saloon naso ka kaini amma duk da haka bata 'baciba zamu iya zuwa ai yamma bataiba...."


Wani kallon kin rainani ya mata. "Tunda ke kike zubamin mai a motan ko ko kin maidani driver dinki ko.....? "
Tsaki taja. "Ya Farhan bawaifa bamuda driver bane dan kai daddy yace ka kaini shiyasa na dage dan kuma kaga ATM din daddy nagun kane shiyasa kake min haka...."


"Ni let go jor inada abinda zanyi.."
Ayya ce ta fito. "Muryan wa nakeji kaman na Farhan...? "
















































Shafa kanshi yayi. "Nine tsohuwa..."
Tadubi Mansu. "To sekuyi maza ku tafi ki dawo da wuri..."


Duban Ayya yayi da kyau. "Kaga tsohuwa da tsoron tsiya se kace in batanan yankaki akeyi......"


Kanshi ta nufa yayi waje da gudu yana dariya, hijabi Mansu ta dauka tayi waje.


A cikin moto ta sameshi ta shiga ta zauna, tana shiga ya tada motan, dubanshi tayi. "Ka cika tsokana wallahi Ya Farhan sena fadawa daddy ince kana tsokanan mishi mama...."


Murmushi yayi . "ai garani kufa keda Ya Aryan kullum cikin fada kaman kaji...."


Kai ta juyar tana kallon hanya jin ya ta'bo zancen Aryan, bata sake kallon shiba har suka isa makeken katon shopping mall din dake unguwan rimi,


























































mika mata ATM din yayi. "Shiga ki fito. "
Baki ta riqe. "Lallai wato bazaka raka niba..."
"Ni saurayin kine...? "
Da sauri tace. "Allah kyauta ni bani ka jirani in fito.."


Ta fizgi ATM din ta fice, wayanshi ya dauko ya hau daddanawa.


Seda tai shopping duk abubuwan da tasan zata buqata kama daga kan su cornflakes, quaker oaks dan ita batashan madara bata san born vita haka garin rogo duk da kasance wanta er boarding ba abinda ya dameta dashi itadai tasha cornflake, goldenmone, da quaker oats ko abincin makaranta bata damu ta amsaba,


Bayan tayi shopping duk abinda tasan tana bukata har always da su chocolate da sauransu ta bada ATM sukasa a POS machine suka bata tasa pin suka cire kud'ad'ansu duka akasa mata komai a bag,
Boy help din gurin yayi gaba dankai mata kayan mota tana biye dashi, tazo daidai zata fita santsin tiles din gurin ya d'beta ta tafi ziiii zata fadi daidai lokacin Aryan ya shigo shopping mall din batareda ya luraba dan kanshi nakan dankareren iPhone 13 dinshi, yaji mutum ya fada kanshi


Dagashi har ita sukayi kasa
Mansu ta fada kan Aryan wani mayen turarene me tsananin kamshi taji ya bugi hancinta se taji kaman ta dawwama tanajin wannan kamshin har karshen rayuwarta, da sauri Aryan ya tureta daga jikinshi a firgice ta dago ido hudu sukayi gaban tane ya fadi, se yanzu taga tsantsan tsanan da Aryan yake mata dan bata ta'ba kallon idanshi hakaba se yau, kallo yake mata cikeda tsana bangaren Mansu kam lokaci daya taji wannan kamshin ya koma mata wari batasan shi dan ganin daga jikin Aryan ya fito,




































































Da sauri ma'aikaciyar gurin tace. "We apologize for the inconvenience we had an issue da cleaners din mune saisa yau basu zo ba......"


dogon tsaki yaja ji yake kaman ya cire kayan jikinshi da Mansu tafada kansu a gurin da sauri ya fice daga mall din, kwafa Mansu tayi tareda gyara glass din idanunta. "Na tsaneka Aryan....." taja tsaki ta fice,


Lokacin har ansa musu kayan a mota dan Farhan yafito da yaga Aryan ne yakoma motan ya buya,


Shiga motan tayi Farhan yace. "Se Ina..? "
"Saloon. "
Ta bashi amsa, be sake maganaba harya karisa da ita inda take zuwa gyaran kai,
Dubanta yayi. "Inkin fito ki sami taxi ni zanwuce zanje in hadu da auntynki.. "
Murmushi tayi. "Allah sarki auntyna Laila kace Ina gaidata. "














































































Dubanshi tayi ciki sigan shagwaba tace. "Ya Farhan ka bani na taxi wallahi ban fito da kudiba. "
Wallet ya ciro, ya bude dari biyar ya zaro cikin uban kudin dake wallet din ya miqa mata,


"Hummm wallahi matsalata dakai mugun san kudin tsiya yanzu dari biyar kawai zaka bani bayan kasan daga nan zuwa barnawa bazasu daukeni dari biyarba.."
"Yarinya kenan ke kyafadawa ma'aikacin banki san kudi. "


. "naji nidai karamin yamin kadan." ta fada.


"Banza mayyar kudi."
Ya furta yana bude wallet, "eh naji ko meye nidai kacemin amma seka karamin. "


Dubu biyu ya ciro. "Bani dari biyar dina mayya." Murmushi tayi
". Eh koma meye sena amsa. "
Miqamai tayi ya amsa amshe kudin tayi tana fadin. "Please driver na u should drop my kaya in house kaji...."
















































Tafada cikin dariya da sauri ta shige saloon din dan tasan tsaf ze iya sauke mata kayanta a gurin, murmushi yayi yaja motan ya wuce.


Seda suka mata tsifa sannan aka fara mata gyaran kan.




Mimi queen ✍.
2022-09-15, 4:03 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._








































































_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


9&10.






































































Washe gari.


Mansu se haushi takeji domin zata koma school da sassafe ta tashi tayi dambun naman da zata tafi dashi tayi Pepe chicken ta zuba a cooler bayan tagama hada breakfast ta koma ciki danta shirya.




Around 8am Aryan ya dawo daga jogging morning, yanada guest daga America kuma gashi sunmai waya sun iso suna airport kuma be shirya fita da sassafeba balle yaje ya daukosu, hakan yasa ya karisa gaban dakin bala driver,


Da karfi yace. "Driver...."
Da sauri ya fito,


Cikin dakewa yace. "I have a guest suna airport so kaje yanzu airport din ka daukosu ka kaisu hospital dina dake rigasa akwai wa'inda zanyi waya dasu zasu tarbesu daganan zakaje rigacikum zaka amsomin sako gun Atif...."


























































Shiru bala yayi kafin yace. "Amma...."
"Amma what....? "


Bala yace. "Dama yau Mansurat zata koma school kuma tace da wuri zamu wuce......"


Wani kallo Aryan yamai sama da kasa, kafin yasa kai ya wuce ba yanda bala ya iya dole ya fito dan zuwa cika umarnin Dr Aryan.




Shiryawa tayi cikin school uniform dinsu, dark blue trouser da sky blue riga se hijab white dan karami da kadan ya wuce kirji da head,


Fitowa tayi tana jan trolley dinta, daidai lokacin kiran wayan Nadeeya ya shigo wayanta, picking tayi tana fadin. "Yar halak yanzu nake tunaninki...."
"Ke yanzu ina hanya kefa.? "


"Yanzu zan fito."
"Okey se mun hadu. " Nadiya ta fada tareda katse wayan.


























Falo ta fito inda Ayya ke zaune, zama tayi gefenta tareda daura kanta kan cinyan Ayya daidai lokacin kiran mommy ya shigo wayanta da sauri tayi picking.


"Hello mommyna...."
A bangaren mommy murmushi tayi. "Yar albarka kin tafi...."
"Aa mommy yanzu na shirya se 10 zan wuce mommy amana addu'a muna komawa Monday zamu fara zana waec bayan mun gama muyi neco se mun gama neco zan dawo mommy dan zan tsaya inyi karatu...."


"Shikenan zan fadawa daddynku, addu'a ananan kullum cikin muku Allah bada sa'a ya miki albarka. "


Cikin jin dadin maganan mommy tace. "Amin mommyna"


Nan sukaci gaba da waya,
sun dade sunayi kafin sukai sallama ta katse wayan,


Ganin 10 ya wuce, yasa Mansu duban Ayya kaman zatai kuka.


"Ayya wai ina bala yaje since baya nan kuma yasan yau zamu resuming school gashi sunce 12 zasu rufe gate bari in kirashi."


























Bala ta kira nan yake sheda mata aiken da Aryan ya mishi, ran Mansu a 'bace ta kira Farhan nan yake sheda mata da sassafe yabi flight ya tafi seminar Abuja.


Daidai lokacin Aryan ya shigo, da sauri Ayya tace. "Dikko maza dauko key ka maida MANSURAT makarantar su tunda kai ka aiki bala dan haka dole ka kaita....."


Wani kallon miskilanci ya musu daga ita har Mansu ya watsar yasakai ya fice daki ya koma,


Salati Ayya tasa tace. "Ni dikko zema haka Mansu kiramin ubanshi in fada mishi inni ban isa dashiba aina isa da ubanshi....."


Kiran daddy Mansu tayi taba Ayya nan tasa kuka tana fadamai karya da gaskiya, Mansu harda dariya.


Aryan ya gama shiri tsaf ya fito yana shirin shiga mota wayanshi yahau ruri ganin daddy yasa yayi picking.
Tunkan ya gaida daddy, daddy yafara masifa ta inda yake shiga daban ta inda yake fita daban, jingina da moto Aryan yayi ya runtse ido yanajin yanda daddy ke mishi masifa wanda da baya mishi fada seda Mansu ta shigo rayuwarsu shiyasa ya tsani yarinyar domin da ba wanda daddy keso da nunawa kulawa sama dashi amma tunda Mansu tazo se kowa ya koma kanta.


Karshe daddy yace, yaba Aryan umarni yamaida Mansu school indai ya isa dashi.




























Daddy nagama fadin haka ya katse wayan, Shiru yayi yana huci kafin a hankali ya nufi cikin gidan.


Suna zaune batareda ya ko kallesuba yace. "Am in car...."


Yana fadin haka ya fice, murmushi Ayya tayi. "Ja'iri na dauka ko shima uban naka be isa dakai bane, maza tashi kije yana jiranki Allah bada sa'a. "


Tashi tayi taje dakinta tayi switching wayanta tasa a cikin drower ta fito ta goya jakan bayanta tanajan katuwar trolley din, har gaban mota Ayya ta rakata tana mata addu'a,


Bude boot din motan yayi da remote domin yana kallon su ta glass ta saka trolley din da katuwar jakan bayanta,


Bayan motan ta bude tashiga bece da ita qalaba, yaja motan tanayiwa Ayya waving ta cikin tinted glass din domin Ayya bata ganinta ta waje ya buga wani uban horn da sauri me gadi ya bude musu yayi waje,


Yana gaba tana baya kaman driver dinta,
Juyar dakai tayi tana kallon waje domin kallon shima haushi yake bata,


































Seda suka kusan barin layin, sannan yaja belt din motan yadaure jikinshi ya saka earphone a kunninshi, da gudu ya figi motan yayi gaba da gudu seda yakusan buga da wani gida sannan yayi baya da gudu, hakan yasa Mansu tayi gaba ta bugi da kujeran gaba takoma baya ta bugi da kujera da karfi,
Ko numfashi bata kumaba taji ya kara figen motan da karfi ya koma yayi baya hakan yasa Mansu kara buguwa da kujera, seda ya tabbatar Mansu ta jigatu dan har glass din idanunta seda ya cire sannan ya figi motan da mugun gudu yafara tafiya,


Numfashi Mansu tafara maidawa, ji tayi yayi parking dago kai tayi taga yayi parking a asibitinshi na rigasa, cire belt din yayi ya cire earphone din kunninshi ya bude motan yasa remote ya danna ma gaba daya door din motan key ya jefa remote din a aljihunshi yayi gaba ido ta bishi dashi to me yake nufi harya shige ciki,


Yana shiga nan aka fara gaidashi nurses da ma'aikatan asibitin kona mutum daya be amsaba yayi office dinshi ko gaisuwan sectery dinshi be amsaba ya shige, yana shiga yayi amfani da telephone ya kira secretary din da sauri tazo.


Nan yace ta kira mishi guest dinshi da suke gidan ma'aikata dake asibitin.


























Komawa tayi ta daga waya ta kira me kula dasu,


Basu jimaba sabbin doctors din da sukazo daga America suka iso nan suka shiga meeting,


Sunfi awa sannan suka daidaita nan yasa a nunnuna musu tsarin asibitin nan ya shiga cancer ward dan duba patient.


Mansu kam na zaune cikin mota tayi tayi ta bude ta kasa hakan yasa ta koma ta zauna Kaman zatai kuka ga lokaci na tafiya gashi glass din motan tinted ne bame ganinta sedai ta zubawa premises din hospital din ido tana kallon flower da masu zirga zirga kaman zatai kuka,
































Shikam hankalinshi kwance se kusan 1 ya gama duba patient ya fito ya nufi mosque din hospital din yayi sallah, Mansu najin an kira sallah tasa kuka yanzu abinda Aryan ze mata kenan tasan an rufe gate kuma ba wanda zasu bude mawa indai suka rufe,


Seda yayi sallah ya aika aka mishi orda sannan ya nufi motan, ya dannan remote ya bude ya shiga kota mirrow be kalletaba yafigi motan yafita daga asibitin,




























Wani hatred look take wurga mishi bata gama tantance inda yake yiba taji ya taka wata uwar burki da seda tayi baya da sauri, ijiyan zuciya tahau saukewa a zuciya tana mai Allah ya isa.


Kanshi ya juyo dashi kanta dukkansu suna sakinma juna wani kallo dake nuna tsantsar tsana,


A dake yace. "Ke uban wa kikewa wannan kallon....? "


Batace dashi komaiba, "dauke idanki cikin nawa fitsararriya....."






































Ko gezau bataiba balle ta nuna alaman zatai abinda yace, hakan yasa yasa hannu yayi fuskarta ko kyafta idanun batabai a tunaninta marinta zeyi se taga yazare glass din idanunta yawurga waje ta glass, sitiyari ya murza yasa tayan motan ya take glass din ya fashe.


Ficewa yayi ya bude boot ya fito mata da kayanta duka kafin ya koma ya bude inda take cikin tsawa yace. "Out......"


Shiru tayi ya kara daga murya. "I said out from my car......"


Kafanta ta fito dashi bata gama fitowaba ya rufe kofan da karfi cikin jin ciwan abun tayi gaba inda kayanta suke shikuma ya shiga motanshi yaja ya wuce yafigi motan da karfi har yana tada 'kura.


























Kukane kawai Mansu bata sakiba gashi ya fasa mata glass gashi bazata iya rubuta exam ba glass ba,


Jakan bayanta ta goya tanajan trolley din domin babu kudi a hannunta kuma gashi da nisa kafin takai makarantan,




Tazo tsallaka babban titin yayinda take gani dishi dishi dan in motoci a kusa suke ita a nesa take ganinsu,


Batareda data masan wata katuwar daff na kusanto taba ita a nesa take ganinta ta shiga titin ,
Unexpected drivern daff din yaga tashigo titin aiko da sauri yaso ya taka burkin motan sedai ta kwace mishi da gudu daff din tayi kan Mansu........






Mimi queen.
2022-09-15, 7:46 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._


https://www.facebook.com/107980080946102?=whatsa


_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


11&12.


Karan horn din da drivern daff din yake dannawane yayi bala'in firgita Mansu ji tayi an wani fizgeta da bala'in karfi an wurgata gefen titin daga ita har trolley dinta da jakan bayan sukai gefe daya, dagowa tayi jin hayaniyar mutane gani tayi daff din ta buga da wata mota ta sabo sabo amma da alama ba wanda yaji rauni me yawa se motan data bugu, wannan bawan Allah daya fizgota se masifa yake mata bata ganine,


Miqewa tayi tana kallon yanda school uniform dinta yayi bud'u bud'u daidai lokacin wani yace. "Ai duk laifin wancan mahaukaciyar yar makarantarne ta shigo titi kaman bata gani kaman wani gidan ubanta.........."


Da sauri ta karisa ta dauki jakanta da trolley din tayi gaba wani kukane ya taho mata wanda batasan lokacin data fashe dashiba haka taci gaba da tafiya tana kuka,


Seda takusa karisawa makarantarsu sannan wata zuciya tace mata "Yanzu Aryan kikewa kuka kome.? "


Da sauri tahau girgiza kai a fili tana fadin. "Allah ya kyauta inma banzan aladen nan mara amfani kuka mtssww. "
Taja tsaki tana goge hawayen dake idonta, ita abinda ya mata ciwo har tayi kuka maganan da mutumin nan ya fad'a wai tashiga titi kaman gidan ubanta, ambatan Abbanta da yayine shiya sataji wani iri, kuma tasan yanzu an kulle gate dan 4pm ta kusa gashi gobe 8am zasu fara exam.


Da sauri taci gaba da tafiya,
Harta karisa makarantar wanda taga gate din a rufe, tsaye tayi ta rasa ya zatayi a sanyaye ta karisa bakin gate din a sanyaye ta daura hannunta akan gate din zatai knocking daidai lokacin motan Aunty Ayna'u VP (vice principal) na school din tanufo gate din,


Tsaye Mansu tayi har aunty Ayna'u ta kariso qasa tayi da glass din motan. "La Head girl wot are yhu doing here...."


A sanyaye Mansu tace. "Am just coming and......" kuma se tayi shiru


Murmushi aunty Ayna'u tayi. "Okey come in lemme reach you in......"


Bude mata bayan motan tayi Mansu ta saka kayanta ta shiga, Aunty Ayna'u tayi horn da sauri me gadi ya bude mata ta shiga tayi parking,


Fitowa sukayi dukkansu Nadeeya dake tsaye tun d'azu idanta a gate hankalinta ya tashi ganin bataga Mansu ba,


Principal office sukayi nan Aunty Ayna'u taba principal hakuri wanda bata jaba ta amince domin the hole school loves her , warning tayiwa senior girl sosai (domin sunan da suke kiranta kenan head girl ko senior girl the hole school domin itace head girl ana bata respect dan tanada bala'in kwakwalwa).


Bayan sun fito daga office din dubanta Aunty Ayna'u tayi. "What happen to ur uniform Mansurat....? "
Murmushi tayi me ciwo batareda ta bata amsaba. "Please aunty can you help me with your phone I wanna call my brother..."


Ba musu ta ciro wayan danta yarda da Mansu sosai ta bata, numban Farhan tasa danta haddace,


Yana dauka cikin shagwaba tace. "Ya Farhan it's me ur tiny beb....."
Gimtse dariyar daya urkusa kufce mishi yayi jin abinda tace, yace. "Ehen am with yhu baby gurl wot d worry it seems u at school right.....? "


"Please Ya Farhan did yhu back to kaduna....? "
"Yep...." Ya bata amsa.
Da sauri tace. "Please ya Farhan I need ur helps inaso ka kawomin medicated glass yau dan gobe da sassafe zamu fara exam....."


Cikin gajiya yace. "What about ur own.....? "
cikin basarwa dan Mansu ta iya basar da abu tace. "Akwai wani a room dina please ask Ayya she will check it for you...."


Katse wayan yayi, godiya Mansu tayi ta miqawa Aunty Ayna'u wayan, murmushi ta mata yayinda tayi gaba.


Rungumeta Nadiya tayi sosai kaman zatai kuka tana tambayanta inda ta tsaya da abinda ya samu uniform dinta, bata bata amsaba ta nufi room dinsu.


Murna school ya dauka na zuwan head girl, room dinsu ta wuce bayan ta barsu suna en wake wakensu na murnar zuwanta tako ci sa'a ba kowa dan haka tana shiga ta rufe kofan ta karisa ta ijeya kayanta, tabar Nadiya na buga kofa tana cewa ta bude,


Seda ta cire uniform din t dauko wasu ta saka sannan ta bude tana fadin. "Kin dameni Nadeeya. "
Tsaye Nadiya tayi. "Okey nidai fadamin meya faru wallahi naji a jikina something is happen. "
Lumshe ido Mansu tayi.


Nan ta korawa Nadiya duk abunda ya faru ta karishe da fadin. "Wallahi wallahi Nadiya I promise my self senama Dikko abinda be ta'ba tunaniba sena mai abinda harya mutu baze ta'ba mantawa dashiba sena samai ciwo a rayuwarshi sena.......... "


Nadiya ne ta katseta da fadin. "Gara ki hakura Mansu domin kinsan dai Aryan namijine bakida wani abu dazaki mai da baze mantaba gara ma ki hakura. "
Bude idonta tayi ta zubawa Nadiya su. "Yanzu zaunawa zaki ki bani shawara ko kashemin gwiwwa zakiyi..... "


Zama Nadiya tayi tana fadin. "Gaskiya ni a ganina abu daya zakimai wanda zaki samai ciwo babba a rayuwarshi kuma shizai zama daukan fasa akanshi..... "
Da sauri Mansu ta riqo hannunta. "Tell me Nadee inajinki please. "


Nan Nadiya ta fad'a mata yanda take gani, shiru Mansu tayi riqo hannunta Nadee tayi. "U can do Mansu nasan zaki iya amma sekin daure wannan ne kadai abinda nake gani wanda zakimai da baze ta'ba mantawa ba....." wani murmushin mugunta Mansu ta saki. "Allah sa mugama exam lafiya mu koma gida u be surprise Dikko...."


Se lokacin data samu solution ta tuna tanajin bala'in yunwa domin tun breakfast din safe batasa komai a bakin taba, tashi tayi ta had'a cornflakes da ruwan sanyi.

(Allah sarki rayuwar boarding
Besty did yhu remember 😁 innalillah cin jiqaqqen indomie da shan cornflakes da ruwan sanyi innalillah I don't forget wooo, zaman boarding da dad'i I missed shan garin kwaki more wlh 😁)




Se around 6 Farhan yazo security yazo ya fad'a mata, da kyar aka barta taje ta ganshi shima 5mnt aka bata,


Amsan glass din tayi a box dinshi tana fadin. "Ya Farhan I love you more..."
"Humm nikin bani aiki wallahi am so tired sosai....."
Baki ta turo. "am sorry my lazy Nigeria youth.... "


Da gudu ta shige tana dariya shima dariyan yayi yana fadin. "Zan kama kine yarinya. "




*****
Aryan kam nacan yau har zama yayi a falo yana kallon network news dan Mansu batanan yayinda House help din Ayya tayi musu girki shida Ayya ya zauna yaci kuma ta gyara mishi daki tayi komai na gidan, har wani natsuwa yakeji da Mansu bata gida.








Sukam yan boarding tsawon daren ranan kwana akai ana kid'e kid'e da wake wakensu kasancewar ranan weekend ne Mansu kam nacan na karatu.




######
Washe gari 8am suka shiga exam dan ranar paper biyu garesu.




Se around 10 suka fito zasu shiga na 2pm kuma kai tsaye Mansu room dinsu ta nufa,


Tazo wucewa ta gaban room dinsu labor prefect tafara jiyo nishi sama sama, da kaman zata wuce se kuma wata zuciya tace tashiga ta gani.




Turus tayi takasa kwakwkwaran motsi abinda ta gani Farida class mate dinsu wacce tayi tayi su zama friends da Mansu amma taqi tana kwance da alama ko exam ma bata jeba dan bata damu da karatu sosaiba,


Ta bude qafa ba pant a jikinta tanasa hannunta a farjinta tana fitowa dashi tana nishi da alama she is enjoying the moment, ta matse nonuwanta da dayan hannunta,


. "Subhanallah..... "
Shine abinda Mansu ta fad'a da karfi ganin qazantar yayi muni, a firgice Farida ta bud'e ido tana jan riganta sama,


Da kyar Mansu ta tattaro natsuwarta tafara yiwa Farida wa'azi da nuna haramcin abinda take aikatawa.




CUTAR DA ISTIMNA'I YAKE YIWA ZAKARIN DA NAMIJI DA LALATA FARJIN MACE YAFI CUTAR DA CUTAR CIWON SANYI (INFECTION) DA BASUR DANKANOMA SUKE YIWA FARJIN MAZA DA MATA


Akwai Bukatar Duk Wanda ya san yana aikata Istimna'i wato Masturbation ko (Zinar Hanu) ya tsaya ya karanta wannan Rubutun domin ya kubutar da kansa daga bala'in da ya tsinci kansa ko ya saka kansa da kansa.


``
*WAI SHIN MA MENENE ISTIMNA'I*
Abinda ake Nufi da istimna'i da hausa shine Biyawa kai bukata ta hanyar wasa da Farji ko Al'aura da tafin hannu a turance ana kiransa da Masturbation,

Please Login or Register in order to submit comment