Reading BUZU BOOK 2&3 BY Ayshercool Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a cikin murhu.
Ta dawo tsakar gida ta zauna, ta fara da Bismillah da karanta Suratul fatiha, sai Suratul falaƙi da nasi. Ta karanta ayoyi biyar ɗin farko na Suratul Baƙara, ta fara karanta Suratul mulk, a hankali sai ta fara gani dishi-dishi, ta fara daina ganewa. Ta busa ayoyin a cikin ruwan, Sai ta ajiye takardar. Ta ɗauki wata leda da ta zo da ita, ta fito da man habbatussauda da jan Almiski.
Saboda wauta sai ta buɗe miskin, ta kai hancinta, da sauri ta dungurar da shi a gurin, ta ja da baya, dan tuni ta ji jikinta ya fara tsuma.
Sai da ta ɗan samu nutsuwa, sannan ta zazzaga tazargaɗe a cikin bokitin, ta kawo ganyen magarya guda bakwai, ta saka a leda ta ɗan bubbuga musu muciya, ta haɗa a cikin ruwan. Ta yi shiru tana tunani a ranta ta ce "Allah ya sa ba mai magani na zama ba, Ƙaisar bai mayar da ni 'yar bori mai bayar da magani ba, larurar Sayyid ta saka na fara koyi da magungunan sarkin baka."
"Amma ai ayoyin Alkur'ani ki ka karanta, shi ma kuma Sarkin Bakar yana amfani da Alkur'ani" wata zuciyar ta tunatar da ita. Haka dai ta ci gaba da wasi-wasi.
Can yamma, bayan ta tabbatar da ganyen magarya da tazargaden sun tsumu, ta ɗumama ruwa ta tsiyayi ruwan tofin ta tace ta haɗa da ruwan ɗumin, ta kawo man habbatussauda ta tsiyaya a ciki, ta kawo jan miskin nan da ta saka kwalbar a ruwan ɗumi, ya narke ta tsiyaya a ciki, ta ɗebo garwashi a kasko ta shiga ɗakin. Yana ganin Nana ya tashi zaune yana kallon ta, ya ga ta samu ƙyalle ta ɗaure hancinta da bakinta.
Ta nufo shi ya ga ta hau tuɓe masa kaya, ya din ga bin ta da ido, ta bar shi daga shi sai gajeren wando. Hannunsa da yake maƙale take kallo cikin damuwa, ta shafa hannun.
Sai kuma ta yi Bismillah ta fara shafa masa wannan ruwan. Tun daga cikin kansa.
Girgiza kai ya fara yi, yana ture ta da lafiyayyen hannunsa, yana toshe hancinsa. Ya din ga girgiza kai jikinsa yana karkarwa bakinsa yana rawa, ya din ga wani irin gunji yana miƙa. Amma sai da Nana ta jiƙe shi da ruwan nan tsaf.
Ta kunna kiran salla a wayarta. Ta kawo tazargade, da habbatussauda da ganyen magarya ta zuba su a kan garwashin nan, hayaƙin ya turnuƙe ɗakin, ta ajiye shi a nesa da shi kaɗan. Ta fice daga ɗakin ta kulle shi a ciki. Ta tafi ta din ga wanke hannunta. Wani irin jiri ya din ga ɗaukar ta, ga matsanancin ciwon kai, ɓari ɗaya da ya sanya take jin, tamkar kan zai yi bindiga ya rabe.
Ta samu guri ta zauna a tsakar gida, ta dafe saitin zuciyarta da yake ta bugawa da sauri.

Bayan wasu mintuna, ta tashi ta je ta leƙa ta window, ta hango shi a kwance a ƙasa. A tsorace ta buɗe shi, ta nufe shi da sauri tana kiran sunansa.
Gaba ɗaya ƙwayar idonsa baƙar ta ɗauke sai farar, ta durƙusa a kansa kawai ya miƙo hannu zai shaƙe ta, amma ta riƙe hannunsa. Hannun ya din ga rawa, ya sauke shi a hankali.

"Sayyid" tana ambatar sunansa, ƙwayar idonsa ta dawo ya kalle ta.

"Sannu Shugaba" hararta ya yi ya juya mata baya. Dariya ta fara yi ƙasa-ƙasa.

Ta ce "Haba Shugaba, ya ka juya mini baya, juyo ka kalle ni" ya ƙi juyowa. Ta tashi ta buɗe labule saboda yadda warin ita ma ya fara damunta.
Ta ɗaukko tsumma, ta hau goge masa jikinsa, saboda ya daina warin miskin nan ita ma ba ta so.
Ya tashi zaune, tana goge masa. Ta ce "Ko a yi wanka?" Ya ɗaga idonsa yana hararta, jikinsa ya koma jawur kamar wanda ya ƙone.
Ta din ga ɓoye dariyarta, ta yi masa wanka, ya din ga sinsuna jikinsa yana yamutsa fuska.
Ya shafa fuskarsa ta ce "Ka yi haƙuri, magani ne, ina son ran Ubangiji Allah ya kawo mana afuwa" Ya ture ta daga jikinsa. Amma ta manne masa ta hau cinyarsa ta zauna tana dariya.

Ta juyo da fuskarsa suna kallon juna, ta lumshe ido ta buɗe ta ce "Sannu shugaba" Ya jinjina mata kai. "In zubo Abinci ne?" Ya girgiza kai.

"Sai an yi salla?" Ya gyaɗa mata kai.

Ya yi sallar magariba da isha'i, ta zubo masa Abinci.

Washegari ma da sassafe, ta kuma rutsa shi tana shafa masa ruwan nan. Yau ma ture ta ya din ga yi yana girgiza mata kai. Ta kunna masa hayaƙi, ta gudu ta rufe shi a ɗakin. Haka ta sake tarar da shi, ya koma ja ya haɗa uban gumi. Ta yi masa wanka. Ta ba shi Abinci ya karya.
Allah ya dafa wa Nana, ba su taɓa rasa abin da za su ci ba. Kuma haka take ta jujjuya kuɗin.

Sai da ta gama yi masa duk abin da zai buƙata, sannan ta tashi za ta yi wanka, tana tsaye daga ita sai bra da zani a ƙugunta, sai cika bakinta take da aya mai gishiri, ga cikinta ya ɗaga sosai.
Ta waiwayo suka haɗa ido. "Ya ake kallona haka?"

Ya yi mata alama da hannunsa mai lafiya ta zo.
Ta ƙaraso gabansa ta durƙusa ta ce "Gani" ya nuna mata cinyarsa.
Ta ce "Ina da nauyi fa, jiya ma dan na tsokane ka na zauna, ka ga baka da lafiya" ya saka hannu ya janyo ta, ta hau cinyar tasa tana dariya.
Yatsansa ya saka ya ɗan latsa cikinta, ya kalle ta yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi ta ce "Kullum sai ya ce ko ta ce tana gaishe ka" Da hannunsa yake tambayarta yaushe za ta haihu?

"Nima ban sani ba, amma dai bai fi wata  huɗu ba, saura wata biyar in Allah ya sa mu na raye. Idan ka samu lafiya sosai, za mu je mu ƙara dubawa idan su Habu sun dawo, idan ba su dawo ba sai mu tafi Nijar. Duk da na san da sun dawo zuwa yanzu za su neme mu" Ya yi shiru yana ci gaba da kallon cikinta, da lokaci lokaci yake dan harbawa.
"Zan je na yi wanka"

Da hannunsa ya yi mata alamar, su je ya yi mata.

"Kana fama da kanka za ka yi mini wankan? Wato a ramawa kura aniyarta ko? To na yafe idan Allah ya baka lafiya sai ka yi mini Rayuwata" Cikin murmushi ya sunkuyo da kanta ya sumbaci goshinta ta da laɓɓanta. Hira yake so ya yi da ita, amma ya kasa sai dai ya kalle ta yana murmushi ko kuma ya din ga yi mata nuni da hannunsa.

Ya ɗauki wayarta, ya kunna waƙar da take yi masa, yana yi mata nuni da ta yi masa. Ta ce "A'a karatu za mu ji ba waƙa ba, a wannan yanayin da muke ciki, ai ba mu ga ta waƙa ba Sayyid" Ya tsuke fuska yana hararta. Ta ce "To shikenan, bari a kashe waƙar, sai na raira maka da bakina ko?" Kawai ya tsare ta da ido yana wani lumshe ido.

Tana dariya ta ce "Wai Sayyid ni fa ban gane maka ba kwana biyun nan, rigima ka ke ji, amma Alhamdillah alamun sauƙi ne da nasara.

Aka shiga kwana na huɗu, tana shafa masa tofi tana kunna masa hayaƙi ta gudu ta bar shi a ɗaki. Yau sai dai ta gama shafa masa, za ta gudu ya riƙe ta gam. Duk yadda ta so guduwa ta kasa. Ya kalle ta yana murmushin mugunta. Aikuwa jikinta ya fara tsuma ta saka masa kuka, jin yadda gaba ɗaya duniyar take juya mata, tana shirin fita hayyacinta.
Har dare ya yi suka kwanta, ba ta kula shi ba, dan gaba ɗaya jikinta ya mutu murus, babu abin da yake yi mata daɗi.
Can cikin bacci ta ji ya yi magana"Ma viee"

"Sayyid"

"Na'am"

"Magana ka yi?"

"Eh, yanzu na ji ta zo"

Ta tashi zaune cikin murna tana taɓa shi ta ce "Alhamdillah Sayyid, Allah ya ƙara lafiya"

"Taɓa ni na ji, ko zan ji wani abu"

Ta ce "Ga shi ina taɓa ka"

Ya ce "Ba wannan ba" ya yi maganar yana rungumota da duk hannayen sa biyu.

"Sayyid hannunka ya warke?" Ta tambaye shi a kiɗime cikin farin ciki.

"Eh" ya amsa a taƙaice yana ƙoƙarin yin wani abin daban.

"Bari na lalubo waya na haska ka na gani"

"Kar ki haska ni"

"Me yasa ganinka fa zan yi, hannun zan gani"

"Kar ki haska ni" ya sake maimaitawa.

A ɗan tsorace ta ce "Anya kai ne?" Ya yi dariya ya ce "A'a Ƙaisar ne. Idan ma ba ni ba ne, ai kina ganewa"

Ta yi dariya ta ce "Wai Sayyid ya haka ne? Ka tsaya mu yi murnar ka samu sauƙi"
Ruf ya rufe bakin Nana, bayan ya tabattar da lafiyarsa ta dawo. Duk da ya yi farin ciki da miƙewar da hannunsa ya yi, wanda farkawa ya yi daga bacci kawai ya ji hannun ya saki, duk da ya yi masa wani iri babu daɗi.

Bayan wani lokaci, ya saka hannunsa ya ɗaukko fitila a gefen Nana, ya kunna ya haske ta. Rufe fuskar ta ta yi, ta juya bayan ta da sauri.
Ya kwanta a jikinta yana yi mata raɗa a kunnenta. "To tashi ki haska ni ki ganni, kin ga hannun" Nana ta ƙare rufe fuskarta a fulo, ta ƙi ɗagowa.
"Kin ga" ya yi maganar yana taɓa ta da hannun. Shi wannan abubuwan da take yi ma, ba ƙaramar dariya take ba shi ba.

Da ƙyar ta tashi, tana kallon hannun nasa da take ganin, tamkar almara ya miƙe.
Ta ja hannun ta ga ya miƙe, ta ce "Kuma ba ya ciwo?"
Ya girgiza kai yana taɓa hannun ya ce "Ba ya yi"

"Allah ya ƙara maka lafiya mai ɗorewa"

"Amin. Na gode. Na gode" ta rufe bakinsa ta ce "Ya isa haka. Allah za mu godewa"

"Alhamdillah. Amma ya zama dole na yi godiya, kuma na jinjina miki, saboda" bai ƙarasa maganar ba ta cije shi a kafaɗarsa, kamar yadda ya kan yi mata, idan yana jin raha.
Kamar ba su ne cikin zullumi da damuwa ba, suka koma shagalinsu. Dare ya tsala amma tamkar rana a gare su, ƙarshe ma zaman hira suka zauna. Da anjima sai ta tattaɓa hannun nasa, dan ta tabattar lafiya kalau yake bai kuma maƙalewa ba.
Haka suka kwana cikin nishaɗi, da kewar juna.
Da safe ta gama abin da take yi, ta shigo da maganin da take shafa masa, ya kalle ta ya ce "Wallahi ki ka zo kaina da wannan abun, sai na yi miki wanka da shi, ke ma na kulle ki a ɗakin, ki ji abin da nake ji" Ganin yadda ya haɗe rai ya sanya ta rabu da shi.
Wunin yau ma lafiya suka yi shi, babu damuwa, duk da jikinsa babu ƙarfi sosai.
Ya ci Abincinsa ya yi sallolinsa babu wata matsala. Sai dai yau ma Nana ba ta samu rintsawa yadda yakamata ba, sai da ta san ya warke. Wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita.
Wani mutum ta gani a tsaye a jikin bishiya, ya lulluɓe jikinsa da mayafi. Ta yi tsuru tana son ta ga waye haka.
Yana ɗaga mayafin ta ga fuskarsa, ta ja da baya, ta tsorata. Tsohon nan ta gani, jikinsa yana ta fitar da wani irin baƙin abu, fuskarsa ta yi baƙi ƙirin, ga hayaƙi na fitowa daga cikin bakinsa da hancinsa gaba ɗaya siffarsa ta yi muni babu kyawun gani.

Sai da Nana ta ja da baya, cikin tsoro da razani.

"Kin tafka kuskure yarinya, kuma za ki san kin taɓa Giyaz bin Jaddul Jinn. Babu wanda ya taɓa karya alkadarina, abu ya yi tasiri sosai haka a jikina. Dan a duk lokacin da aka yi yinƙurin illata ni, barin guri nake yi. Sai dai kash kina ɗauke da abin da aka yi mini tarko da shi a wancan karon." Ya jefo mata wani littafi jikinta ya ce "Ga shi nan, littafin da ki ke ta bibiya sai kin ji ƙwaƙwaf, ki ƙarasa karantawa kafin na je na yi jinya na dawo. Amma ki sani dawowata ba za ta haifar miki da ɗa mai ido ba. Domin illar da ki ka yi mini sai na ninka wa mijinki, wahalar da ki ka sha ba ki ga komai ba." Kawai ya ɓacewa ganin Nana.
Nana ta kalli littafin hannunta, na gurin Ƙaisar ne, da take ta bibiyar sai ta karanta hanata.
Da kansa littafin ya buɗe, a daidai shafin da tsaya da karantawa wancan karon.
Jiki na tsuma ta ci gaba da karantawa.

Jama'ar da suke gurin girkar, wasu suka watse a dalilin gakin sarkin Aska ya bayyana a gurin, kar ya gansu ya hukunta su. Bayan musayar yawu a tsakanin Duna da uban duƙusa, Sarkin Baka ya yi girgiza ya ɓace.
Uban duƙusa ya saka aka ɗauki kakan Lanti, a ka kai shi gida. Ita ma Lantin tana zuwa gida ta faɗi ƙasa.
Ba ta sake farfaɗowa ba sai washegari. Sai dai bayan farfaɗowarta, ta tarar da kakanta cikin mawuyacin hali, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba.
Cikin damuwa mijinta ya ce "Lanti sai da na gaya miki ina jin tsoron wannan abun, ki ka ce babu komai, ina tsoron kar rikici ya ɓarke a garin nan"

"Babu rikicin da zai ɓarke, ka kwantar da hankalinka, ni dai kawai fatana na kawo ƙarshen Sarkin Aska."

Kakan Lanti da ya yi tari, sai aman jini, dama ga jikin tsufa, ya zamana ko tashi baya iya yi saboda buguwar da ya yi. Kwanaki huɗu da faruwar lamarin, Lanti tana yi masa hayaƙi da ganyen ɓaure. Ya riƙo hannunta ya ce "Ya ke jikata, ki sani na yi miki Girka da babban Aminina, kuma ya ɗaukar mini alƙawarin ba ki duk wata kariya, da zama mai hidima a gare ki, kuma ya yi alƙawarin bawa zuriyarmu kariya daga cutarwar miyagun Aljanun cikin su. Dan haka a duk lokacin da ki ke buƙatar ganawa da shi, ki sanya kayan saƙin ki, ki ɗaura gurunki. Sai dai kar ki kira shi a guri mai ƙazanta, ba ya son zama a guri mai ƙazanta, kuma ba ya zama a guri mai najasa. Sannan 'yar ki Duna ne ya shafe ta, kuma ga wannan abu da ya faru, abu ne mawuyaci ta warke, sai dai idan uban duƙusa ne ya samo mata magani. Ni na san ba zan rayu ba, Duna ya riga ya yi mini illa, dan haka ki kula da mutanen Buda. Yana gama faɗin haka wuyansa ya karye. Lanti ta fashe da kuka, ya buɗe baki yana son ya yi mata magana amma ya kasa, har ya daina motsi ya mutu.
Nana ta yi kuka ba kaɗan ba, da mutuwar Kakanta.

Ƙaisar ne a tsaye a kan wani dogon tsauni, gabansa kuma Giyaz ne, da yake kamannin da shi sak, tamkar ya yi kaki ya ajiye.

"A kan me za ka je ka aikata wannan shirmen da ka yi? Ko har ka manta da cewar fansarmu za mu ɗauka a kan abin da mutanen nan suka yi mana?"

"A'a Giyaz, mutanen nan ba su ne ainihin waɗanda suka fara rigimar nan ba, kuma ɓarnar da aka yi musu ta yi yawa. Babu amfani rashin zaman lafiya da tashin hankali. Kuma ka duba irin cutarwar da abokinka Duna ya haɗa kai da sarkin Aska yake yi wa mutanen garin nan. Yakamata a zauna lafiya, haɗa kai da bil'adama ana cutar da jinsinsu ba zai haifar da ɗa mai ido ba."

"Rufe mini baki Ƙaisar" Ƙaisar ya kalli mahaifinsa jin ya kira shi da sunansa na yanka, saɓanin sunan da yake masa kara da shi, na uban duƙusa wanda da shi ake kiransa saboda kara ga mahaifinsa. Dan duk cikin bataliyar 'ya'yan da ya haifa, ya fi ƙaunar sa. Ya ɗora da cewa "Kar ka manta abin da suka yi wa Mahaifina Jaddul Jinn wanda yake kaka ga duk wani Aljani da yake nahiyar nan, da yadda ake girmama shi, sai mene ne dan a azabtar da su. Dan mene zaka hau kan bil'adama a matsayin bawa, duk da kasancewar ka ƙasaitaccen matashin aljani da ake ji da shi a jinsinmu" ya yi maganar cikin ɗaga murya, muryarsa na amsa kuwwa a ilahirin dajin.

"Zaman lafiya da kwanciyar hankali, mu rayu mu da su babu cuta babu cutarwa. Lalata musu amfanin gona, sanya musu rashin lafiya da makamantansu duk ba zai sanya ku huce ba, tun da waɗanda suka yi laifin na sun mutu basa nan"

"Uban duƙusa yanzu ka fifita bil'adama a kan ni mahaifinka?"

"Ko ɗaya, sai dai ka san muna mutunta yarjejeniya. Mun yi yarjejeniya da abokina, zan ci gaba da bawa zuriyarsa kariya, zan kula 'yar sa zan din ga kawo mata magunguna tana bayarwa. Kuma ya yarje mini ci gaba da yi wa zuriyarsa hidima, da bayar da magani ta hanyar waɗanda aka haifa da tauraron 'yar sa Lanti"

"Ƙarya ka ke yi Ƙaisar. Ɗana ba zai zama bawa ga gajiyayyun halittu kamar bil'adama ba, ka sani yadda suke yi mana kallon halittu maƙaryata, haka su ma ba su da cika alƙawari. Ka tuna kai makaranci ne, manazarci kuma marubuci. Ka karanta litattafai da ni kaina ban san adadinsu ba. A ɗakin karatun ka akwai litattafan da aka rubuta dubbanin shekaru kafin zuwanka Duniya. Ka yi yawace-yawace a Duniya domin neman abubuwan rubutawa, kuma ina da tabbacin ka karanta tarin kashedin da magabantanmu suka yi mana a kan bil'adama. Dan haka ba zan bari iliminka da soyayyar da nake yi maka, su ƙare a kan yi wa biladama hidima ba, ba ma su su yi maka ba. Sai dai ka zaɓa, zama da mu ko kuma hidima ga bil'adama!"

Ayshercool
08081012143
59

Ƙaisar ya ce "Haƙiƙa kai Babana ne, ka so ni mai sonka ma ya so ni. Kuma na san ni ne ruhi mafi soyuwa a gare ku. Ka tallafawa burikana da bani damarmaki a matsayina na ɗanka. Sai dai ka tuna, na kawo girman da zan iya yankewa rayuwata hukunci. Kamar yadda ka faɗa; na karanta kashedin da aka yi mana a litattafan magabata, na yi yawon neman labarai a duniya, amma babu inda na ga an ci riba da tashin hankali da yaƙar juna. Kuma Aljani bai taɓa nasara a kan bil'adama ba, komai tasirin cutarwar da ya yi masa.
Na yi abota da bil'adama, na karanci wasu abubuwa masu muhimmanci dangane da zamantakewar su. Kuma ina son na yi amfani da ilimina na sanin magunguna, na sanar da wasusn su, domin samun waraka daga wasu cututtukan da mu ne muke haddasa musu su.
Dan haka ina mai baka haƙuri, na riga na yi alƙawari ba zan iya warwarewa ba. Sannan ba a banza zan yi wa zuriyar sarkin baka wannan aiki ba. Kamar yadda na gaya maka, sun sadaukar mini da duk wani mai irin tauraron Lanti, domin gudanar da burina na son yaɗuwar ilimin bayar da magani"

Cike da ƙunar rai Giyaz ya numfasa ya ce "Shikenan, ka yi abin da ka ke so, amma ka je, na sallama ka daga cikin zuriyaramu, kar ka sake danganta kanka da mu" daga haka Giyaz ya ɓace.

Lanti ta damu da mutuwar kakanta, sai dai ba a rufa sati ba, 'yar ta ma mai larurar shan Inna ta mutu. Ta shiga tashin hankali sosai da sosai, tamkar za ta zauce.

Hankalin Sarkin Aska kuwa ya yi mummunan tashi, bayan da Duna ya sanar da shi cewar, da Uban duƙusa aka yi wa Lanti girka. Kuma cutar da Uban duƙusa ka iya kawo fitina da tashin hankali a tsakanin su kan su Aljanun. Duk da zafin bil'adama da Giyaz yake ji a kan abin da suka yi wa mahaifinsa, amma ba zai lamunci kowane Aljani ya taɓa masa ɗa ba.
Sarkin Aska ya ji baƙin ciki ba kaɗan ba,  da abin da Duna ya gaya masa, bayan tabattar da cewa ya samu abokiyar hamayya a garin.

Ƙaisar ya fara bawa Lanti magunguna, ta fara aikin bayar da magani a garin. Babu nasiha da rarrashin da ahalin Ƙaisar ba su yi masa ba, a kan ya janye daga harkar taimakon biladama, amma fafur ya ƙi ya ce ba zai daina ba. Akwai kyakykywar fahimta a tsakanin Lanti da kuma Ƙaisar.
Lanti ta kuma samun juna biyu, ta haihu sai dai ɗan da ta haifa, ba ta haife shi da irin taurarinta ba.
Aka shiga zazzafan takun saƙa, a tsakanin Lanti da Sarkin Aska, dan mutane suna tururuwar karɓar magani a gurinta. Domin ita ba ta tsauwwala wa mutane, kuma ba ta neman su kawo wani abu da ya fi ƙarfinsu. Duk da Giyaz ya sallama Ƙaisar, amma hakan bai bayar da damar, 'yan uwansa su iya cutar da shi ba.
A lokacin sai zuriyar Jaddul Jinn wasu suka goyi bayan zaman lafiya, kamar yadda Ƙaisar ya yi, wasu kuma suka zauna a kan bakar su na lallai sai an ci gaba da cutar da bil'adama da duk wanda ya fito daga wannan tushe na Buda.
Sarkin Aska ya ci gaba da jan Aljanu, yana sadaukar musu da jini, yana amfani da su ta hanyar tsafi, da kuma alwashin taimaka musu a duk lokacin da suke buƙatar hakan.
Cike da baƙin ciki, Giyaz ya zura wa Ƙaisar ido, babu yadda ya iya da shi.
Ganin abin da Sarkin Aska yake ci gaba da yi, duk a ƙoƙarin sa na mamaye garin a ci gaba da tsoron sa, ya sanya Lanti ta ƙara zage damtse a kan harkar bayar da magani da laƙantar hanyoyin da za ta kawo ƙarshen Sarkin Aska.

A haka ta haifi yara biyar maza, duk babu mai irin tauraronta, gaba ɗaya abin ya damu Ƙaisar, ganin babu wanda zai iya gadar ayyukan Lanti.
Sai dai a jininsin mutane ma, 'yan uwan Sarkin Aska ba sa ƙaunar abin da yake aikatawa na zaluntar mutane.
Wata jakar fatar damusa, Ƙaisar ya sanya Lanti ta fara haɗawa, wadda da ita take burin kawo ƙarshen Sarkin Aska, saboda babu irin mugun hari da yinƙurin da Sarkin Aska ba ya yi, dan ya kashe ta.
Sai da ta shekara biyar, tana aikin jakar nan, tare da jiƙata da magunguna daban-daban. Ban da zanen hatimai kala-kala da yake cikin jakar.
Ta haɗa kai da ɗan uwan Sarkin Aska, baya nan ya je ya ajiye masa jakar a ƙasan abin kwanciyar sa. Kuma ƙaisar ya ɓatar da sahun sa, ta yadda babu wanda ya gane a cikin aljanun da suke yi masa hidima. Tun da ya kwana a kan jakar, Aljanun da suke yi masa aiki, suka watse suka bar shi, ya kamu da matsananciyar rashin lafiya da sai da ta yi ajalinsa. Yana mutuwa kuma aljanun suka fantsama kan 'ya'yansa da jikokinsa, sai dai aka rasa wanda zai gaje shi gurin ci gaba da aikin zaluntar al'ummar da yake yi. Sosai mutanen gari suka yi murna da mutuwar sa. Babban ɗan sa da suke bokancin tare ma, cewa ya yi ba zai iya ba.
Ƙin samun wanda zai gaje shi, ya sanya aljanun fara sanya wa iyalansa cututtuka. Wasu kuturta wasu suka makance, har da waɗanda suka haukace. Aka din ga ɗauki ba daɗi da Lanti, a kan sai ta warkar da su. Ƙaisar ya gargaɗe ta a kan babu ruwanta ta rabu da su.
Lanti ta shafe shekaru Ashirin da bakwai, tana aiki tare da Ƙaisar tana harkokinta na bori da bayar da magani, haka zalika ita ma ta yi wa mutane da dama girka, masu sha'awar harkar bori. Akwai bikin 'yan bori da ake gudanarwa da nuna bajinta duk shekara, wanda a nan ake yi wa masu so girka, ake bikin bajekolin abubuwan ban mamaki, na gidaje daban-daban.
Maharba su yi na su, wanzamai, 'yan bori da dai sauran su.
Domin bayan mutuwar Sarkin Aska an ɗan samu zaman lafiya, tun da dama shi yake assasa duk wata fitina da rashin zaman lafiya. Sai dai aljanu ba su fasa cutar da su da razana su ba, duk da Lanti tana iya kokarinta. Sai dai ita ma bayan wannan shekarun ta koma ga Allah.
Sai dai kan ta mutu, a cikin jikokinta an samu guda ɗaya da take da irin tauraronta.
Dan haka bayan mutuwar Lanti, aka ci gaba da ba ta kashi tsakanin mutanen garin, da Aljanun da sarkin Aska ya yi aiki da su, har ma da waɗanda ba 'yan asalin garin ba ne.
Sai dai babu yadda Ƙaisar zai yi, a lokacin jikar Lanti ba ta kai lokacin da za ta iya bayar da magani ba. Kuma har a lokacin ba a fasa yi masa magiyar ya rabu da bil'adama ba. Gaba ɗaya ya nesan ta kansa da Ahalinsu.

Bayan jikar Lanti ta fara tasawa, Ƙaisar ya fara bijiro mata, domin yin gadon kakarta, sai ta kasa

Please Login or Register in order to submit comment