Reading FANSAR RAI complete 1&2 BY SIS NERJA'ART Chapter 53 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nasiba tace dan Allah Jawhir wata 'yar alfarma ce muke nema a wajenki.
Alfarma kuma?,,, tatambaya cike da mamaki.
Janye kai Nasiba tayi gefe guda sannan tace dan Allah ina so ki auri Faruk.
Zumbur tamik'e tsaye tace ni kuma? Aunty Nasiba kinsan abinda kike fad'a kuwa?
'Daga kai tayi tace Eh na sani cewa nayi kitaimaka ki aureshi.
Jawahif juyawa tayi takalli Faruk da yajingine kanshi a jikin kujera idanuwanshi suna a lumshe yana saurarensu, d'auke kai tayi tace gaskiya ba zan iya auren mijinki ba ni kawai matsayin Yaya yake a wajena.
Saurin bud'e idanu Faruk yayi yakalleta.
K'walla ce ta cika ma Nasiba idanu tace kar kice haka Jawahir dan Allah kitaimaka ki aureshi na maki alk'awalin zamu zauna da ke lafiya, bazamu ta'ba cutar da rayuwarki ba, idan har baki auri Faruk ba hankalina bazai ta'ba kwanciya ba, dan Allah kitaimaka ki auri Faruk na tabbata zai kula da ke fiye da yadda Umar yakula da ke.
Zama Jawahir tayi tare da juyawa tana kallon gefe guda nan hawaye suka fara fita daga idanunta.
Faruk ganin yadda take hawaye yasa jikinshi yayi sanyi nan yayi ma Nasiba nuni alamun tabasu waje, mik'ewa Nasiba tayi tafita cikin sanyin jiki, Nan yamaida kallonshi ga Jawahir ahankali yakira sunanta tajuyo takalleshi cikin muryar kuka tace Yaya Faruk dan Allah kace min maganar da Aunty tayi da wasa take ba da gaske ba.
Murmushi yayi yace Jawahir dagaske take ina sonki kuma zan aureki idan har kin amince.
Saurin tarar numfashin shi tayi tace ban amince ba bazan ta'ba aurenka ba domin kai Yayana ne.

Wani irin haushi Faruk yaji ammah yadanne yace idan har kin d'aukeni a matsayin Umar zaki iya aurena Jawahir tunda shima kin aureshi ko kin mance lokacin da muke bankwana zaki dawo nan kikace infad'i duk abinda nake so kiyi min nace bana buk'atar komai sai abu guda, kikace menene nace zan sanar da ke ba yanzu ba, inzaki tuna cewa kikayi Allah yakaimu lokacin insha Allahu komenene zan nema zaki mallaka min shi, idan ko haka ne Jawahir aurenki nakeson yi dan Allah ki amince min.

Kallonshi tayi fuska sha'be sha'be da hawaye tace taya zan iya aurenka Yaya Faruk? Taya zan auri mijin Aunty Nasiba idan har nayi haka ban mata adalciba ga mahaifinta anrufe sanoda ni sai kuma in auri mijinta dan Allah kacanza wani abun ammah bazan iya aurenka ba.
'Dan guntun murmushi yayi yace wannan alfarmar ita kad'ai nake nema a wajenki idan kuma har baki amince ba shikenan zan hak'ura Jawahir saidai na san kisan girman alk'awali da hukincin rashin cikashi.

Cikin kuka tace ni ba wai alk'awalin bane bazan iya cikawa ba kawai dai aurenka ne bazan iyaba kai fa matsayin Yayana kake kuma Aunty Nasiba ban mata adalci ba idan na auri mijinta nidai kayi hak'uri bazan iyaba Barrister...tun kan tarufe baki sai jin muryar Inna Mairo sukayi ta ce Jawahir indai kika k'i amincewa da aurenshi tabbas kin zama butulu domin duk halarcin da mutanen nan sukayi maki baidace kice haka ba.
Cikin kuka tad'ago takalli Inna Mairo sai kuma tajuya cikin sauri tashige uwar d'aka tamaida k'ofa tarufe.

Inna Mairo kallon Faruk tayi tace kar kadamu Faruk zamu fahimtar da ita.
Nasiba ce tashigo ganin yadda sukayi cirko cirko yasa tagane Jawahir bata amince ba, dan haka tace Inna dan Allah kulallasheta ta amince da auren nan zamu zauna lafiya bazan ta'ba cutar da itaba insha Allahu zatayi alfahari da auren nan da zatayi.

Murmushi inna mairo tayi tace kubarta kawai Nasiba zata amince, muma ai abun farin cikine agaremu ko bakomai munsan zata rage yawan shiga damuwa da tunane tunanen da take.
Faruk dai baice komai ba dan ya san daman mawuyacine ta amince ta aureshi saidai shima a yanzu yana da burin aurenta dan yacanza mata rayuwa yamaido mata farin cikin da tarasa a rayuwarta.


Har sakayi sallar la'asar bata fitoba dan haka Baba Malam yaje yabuga mata k'ofa lokacin tana kwance har lokacin tana kuka dan jin abun take wani iri wai itace Nasiba take rok'o ta auri mijinta, jin muryar Baba Malam yasa tayi saurin tsaida kukan tare da tashi cikin sauri tabud'e k'ofar takoma tazauna tana sheshek'ar kuka.

Baba Malam ne da Inna Mairo suka shigo suka samu waje suka zauna nan Baba Malam yakalleta yace Jawahir idan har kikayi ma mutanen nan haka baki kyauta ba, kar kimance halarcin da Faruk yayi maki a rayuwa kar ki kasance me manta alkhairi, kar kisaka kanki cikin mutane marassa godiya, tunda su suka nemi ki aureshi ba ke ce kika nema ba Jawahir na tabbata idan har kika auri Faruk bazaki ta'ba yin da kin saniba dan shi d'in mutumin kirki ne.

Girgiza kai tayi cikin muryar kuka tace ni ba wai na k'i bane kawai dai hakan ba adalci bane in auri mijinta nidai sutaimaka subarni ink'are rayuwata a haka dan Allah na rok'eku.

Baba Malam ne yace shikenan Jawahir mu bazamuyi maki dole ba zamu hak'ura da abinda mukeso dan bamu muka haifekiba dole mubari kiyi abinda zai faranta maki rai.
Inna Mairo ce tace tabbas haka ne Alhaji domin mu mahaifiyarta muka haifa itace zata kasance me biyayya da duk abinda mukeso Allah sarki rayuwa mutuwa bata barin wani dan wani yaji dad'i, ina ma ace Khausar tana raye.

Jawahir tana jin haka k'ara sautin kukanta tayi tare da zamowa k'asa cikin kuka tace dan Allah Inna da Baba kuyi hak'uri wallahi nima mai biyayya ce zanyi maku biyayya ga duk abinda kukeso na amince zan auri Faruk dan Allah kusa ma rayuwata albarka.

Suna jin haka duk sai wani irin farin ciki yalullu'besu nan sukaita shimata albarka, gefe d'aya kuma tausayinta suke ji.
Jawahir kasa cewa komai tayi saidai cigaba da kukanta da tayi.



Fitowa sukayi suka samu su Baba Musa da su Faruk zaune sunyi shuru suna jira sufito suji yadda sukayi da ita dan Faruk tsintar kanshi yayi da jin wani iri akan nunawa da Jawahir tayi bata sonshi, yana ganin su Baba Malam sun fito saida gabanshi yafad'i wanda yarasa dalilin fad'uwar gaban, idanu yazuba masu yana kallonsu, Nasiba ce tayi k'arfin halin cewa Baba ya kukayi da ita ta amince?
Murmushi su Baba Malam sukayi sukace Eh ta amince.

Gabad'ayansu hamdala sukayi Faruk ko ajiyar zuciya yasafke yaji wani irin sanyi ya ziyarceshi.
Nan shi da Nasiba sukayi masu godiya.

Nasiba jikkarta tad'auko tafiddo dubu d'ari taje tatsugunna gaban Baba Malam tace Baba ga wannan kud'in neman aurene ni nad'auki nauyin biyansu, sannan insha Allahu su Dad zasu zo atsaida ranar aure mudai muna rok'on ataimaka mana kar asa rana dayawa dan munfiso ayi bikkin batare da anja lokaci ba.

Su dukansu mamaki yakamasu ganin yadda ko kad'an bata nuna damuwa ba saima murna da take.
Inna Mairo ce takasa daurewa tace tabbas wannan mata zuciyarki me kyau ce tunda nake a tarihin rayuwata da idanuna kece macen da nata'ba ganin ta yi hakan, Allah ubangiji yasaka da alkhairi, Allah yabiyaki da gidan aljanna.
Murmushi Nasiba tayi tace babu komai Inna ai Jawahir 'yar uwatace kuma duk musulmi na k'warai zaiso ma d'an uwanshi abinda yake so ma kanshi, ko bakomai Jawahir ta cancanci fiye da hakan a wajena dan itama ta taimaka mani a lokacin da nake buk'atar taimako taya zan kasance me manta alkhairi.

Maganar da tayi ta shigesu sosai nan sukaita mata godiya, Faruk ko saidai idanu yazuba mata cikin zuciyarshi yana gode ma ubangiji da yamallaka mashi Nasiba a matsayin mata dan tabbas ita d'in macece ta gari.


A chan 'bangaren Jawahir tana ganin su Baba Malam sun fita komawa tayi takwanta nan tafara rera sabon kuka, dan dole ta amince da za'bin su saboda a yanzu batada na sama da su suna k'ok'arin yi mata duk abinda take buk'ata, alk'awaline tayi ma kanta bazasu ta'ba kuka da itaba babu abinda zasu nema a wajenta surasa itace zata koma madadin mahaifiyarta a wajensu, wannan dalilin ne yasa tayi saurin amincewa da auren Faruk.



Har wajen k'arfe biyar Jawahir bata fitoba dan haka wajen biyar da rabi suka bar Kebbi sunso suyi bankwana da Jawahir ammah tak'i fitowa dan koda Inna Mairo tashiga dan tafad'a mata tafiyar da zasuyi samunta tayi tana bacci ko da ma ba baccin gaske takeba dan bataso tasake had'a idanu da mutanen ne saisa tatsiri baccin k'arya zuciyarta a tunkushe.



Nasiba Alk'awali tayi masu insha Allahu da sunje zasu sanar da su Dad azo ayi maganar auren, Faruk ko saidai yabita da idanu ta k'ara daraja sosai a cikin idanunshi.

K'aramin galan d'in kindirmo da man shanu aka basu da k'ananun tsarabobi suka tafi da su har airport su baba musa suka rakasu saida jirginsu yatashi sannan suka baro airport d'in.



Suna komawa gida Nasiba part d'inta tawuce Faruk kamar jira yake yabi bayanta fara cire kaya tayi sai gashi ya shigo kallonshi tayi tai murmushi tace ya dai ango bazaka d'an watsa ruwaba kafin magrib?.
Matsowa yayi kusa da ita yace yanzu saboda Allah Nasiba hakan da kikayi kin kyauta?.
Murmushi tayi tace me nayi, dan kawai na nema maka auren Jawahir sai yazama laifi, kaima fa kana sonta malam kafiddo farin cikinka a fili kawai ba sai ka 'boye min ba.
Rik'o ta yayi yana mata kallon mamaki yace Nasiba wa yafad'a maki ina son Jawahir?

Cikin idanunshi takalla tace soyayyarta nagani a cikin idanunka ko zaka iya rantsewa kace baka sonta.

Jan hancinta yayi yace ni bance ina sonta ba.
Janye hancinta tayi tace wash da zafi fa Lovely, ni dai nasan kana sonta kawai dai kana basarwa ne,,, tana fad'in haka tajuya tana k'ok'arin cire skirt d'inta, rik'o hannunta yayi yace ya akayi kikasan haka?.
Batare da ta juyo ba tayi murmushi tace tun daga yanayin yadda kake waya da ita da yadda kake yawan min labarinta kai tunma kafin nan zan iya cewa tun a kotu nafara ganin alamar hakan.

Faruk kasa cewa komai yayi nan yaja yai tsaye yana kallonta cike da mamaki.
Juyowa tayi takalleshi fuskarta d'auke da murmushi tace ko zakayi wanka muje muyi kar magrib yayi kaga na gaji sosai yau.
Batare da ya ce komai ba yafara cire kayanshi dan rasa abinda zaice mata yayi.




------*****-------
A daren Nasiba takira su Dad da Mom tafad'a masu yadda sukayi da su Baba Malam, washe gari Faruk yaje gida nan yasake fad'a masu komai har da irin k'ok'arin da Nasiba tayi wajen nema mashi auren Jawahir.
Daga Dad har Mom sun jinjina mata nan sukaji ta k'ara shiga ransu sukayi Allah yasa alkhairi.


Dad yasa mom takira Nasiba a waya tatambayeta wata nawa yadace asa bikkin nan Nasiba tace kar yawuce wata biyu kamar yadda akasa nata suka amince da haka.

A cikin satin ne su Dad da abokinshi sukaje Kebbi suka nema ma Faruk auren Jawahir wajen Baba Malam yace ai Nasiba ta nema mashi auren saidai ayi baiko, haka ko akayi akasa bikki wata biyu masu zuwa, dan a lokacin bikkinsu Khausar sati bakwai yarage nan aka ce za'a k'ara sati guda ayi tare da na su Jawahir jin haka yasa su Dad sukace a'a kar ak'ara kawai arage sati guda daga cikin wata biyun da akasa sai ayi bikkin tare nan da sati bakwai nan su Baba Malam suka amince su Dad dayake a mota sukazo suka fiddo kayan sa bikkin da suka ciko boot da su suka bada sannan suka juya saboda tafiyar mota ce basuso suyi dare dan ma driver yakawo su.




_________Jawahir ko tun ranar da su Faruk sukazo sukayi maganar aurenta tad'auki damuwa tasa a ranta saida Inna Mairo tadinga mata nasiha tare da bata shawara tabar ma ubangiji za'bi acikin rayuwarta sannan tarage sa damuwa tadinga tashi kullum cikin dare tana kaima ubangiji kukanta tare d neman za'binshi a cikin rayuwarta.

Su khausar ko murna suka dinga yi suna tsokanarta dan cewa suke daman chan sun ga alamar faruk yana sonta yanayin yadda yake kallonta, Rashida tace yoh itama d'in bakiga yadda take d'oki idan yazoba tana sonshi gulma ce kawai mudai munji dad'i.
Shuru jawahir tayi tak'yaleshi nan magana tazagaye gida akaita murna tare da yin Allah yasa alkhairi.

Lokacin da akasa bikki ko jawahir kasa fitowa tayi a d'aki ta'boye tadinga kuka.

Sauran mutanen gida aka dinga murna musamman da akaji tare da nasu Khausar za'a had'e ayi ......







_Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:22 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 26*

Tunda su Dad suka dawo suka fad'a masu Nasiba maganar baikon da akayi murna tadinga yi abun har yaba Faruk mamaki ganin yadda bata nuna damuwa ba,
lokacin suna zaune a parlor nan tafara tsara yadda bikkin zai kasance, batare da ya ce mata komai ba yamik'e yashige bedroom d'inshi.
Da idanu tabishi nan tayi d'an guntun murmushi wanda baikai zuci ba sannan tamik'e tabi bayanshi, tana shiga tasameshi kwance a saman gado kanshi yana kallon ceiling.
Zuwa tayi takwanta a k'irjinshi cikin shagwa'ba tace shine muna magana sai kataso katafowarka kabaroni ko?

Batare da ya kalletaba yace Nasiba wai anya kina sona?
Da mamaki take kallonshi tace me kagani? kaga wani abu ya canza ne daga soyayyar da nake nuna maka?
Kusan haka dan da ace kina sona da sai kinyi kishina.
K'wallah ce tanemi tafito daga idanunta tayi saurin maidata tace Faruk kaima ka san ina sonka soyayyar da nake makace yasa nakeson ka auri Jawahir dan Allah kadaina irin wannan tunanin indai ba so kake kad'aga min hankali ba.

Sai a lokacin yad'ago yakalleta murmushi yasakar mata yace shikenan hearty insha Allahu na daina, nagode sosai da irin k'aunar da kike nuna min.
Itama murmushin tayi tace kadaina godiya agareni Lovely, yauwa ammah dan Allah nan gidan Jawahir zata zauna ko? Dan wallahi nafiso muzauna tare kaga mun dinga hira tunda kai ficcewa kake wajen aiki kabarni ni kad'ai.
Toh Hearty duk yadda kikeso haka za'ayi tunda ga gudan part d'in chan sai tazauna a ciki.

Cikin jin dad'i tace nagode sosai Lovely, sai kuma tamarairaice tace dan Allah inaso idan kabani dama gobe inje ingano Mummy.
Shafa bayanta yayi yace toh Allah yakaimu goben idan nadawo wajen aiki sai inkaiki.
Godiya tayi mashi cikin jin dad'i.


_______**______
Nasiba ce zaune a gidansu tare da mahaifiyarta da 'yan uwanta da suka zo su ma, suna cikin hira ne take sanar da su maganar auren da Faruk zaiyi, su dukansu hucking sukayi sukace aure kuma? Wane Faruk d'in wai ma?,,, cike da mamaki suke tambayarta
Murmushi tayi tace nawa man.
Yaya Sadiya ce tace ban gane nakiba duka yaushe akayi bikkin naku da har zai k'ara aure?
Cikin nuna rashin damuwa tace Yaya Sadiya ai ba wani abu bane dan ya k'ara aure nice ma nanema mashi auren.
Daga Mummy har su Yaya Sadiya rik'e baki sukayi suna kallonta cike da mamaki.
Bata damu da irin kallon da suke mataba tace ba wani abun mamaki bane dan na ce haka.
Nasiba anya kina cikin hayyacinki kuwa? Ke ana gudun kishiya ke kuma kina jawo ma kanki ita.

K'walla ce tacika mata idanu tace toh ya zanyi wallahi ina tausayin Jawahir sosai kuduba kuga mahaifinmu ne yajefata halin da take ciki na rashin duk wani makusanci nata hatta mijinta, ya zanyi idan bance ta auri Faruk ba, bamusan halin da take ciki ba koda ace bata nuna a fili ba ansan akwai damuwa acikin ranta, sannan duk abinda mahaifinmu yayi mata hakan baisa tak'i mu ba dan tasan ba mu mukayi ba, wallahi duk irin k'aunar da nakeyi ma Faruk zan iya hak'ura ya auri Jawahir domin ita d'in mutuniyar kirki ce, nidai dan Allah kusa albarka a cikin auren nan kar kusakar min da gwiwata a lokacin da nake sanar da ku aikin ladan da zanyi.

Su dukansu jikinsu sanyi yayi nan sukayi masu Allah yasa alkhairi, Mummy ta jinjina ma halin d'iyartata dan bata ta'ba tunanin hakan ba saboda Nasiba tana da kishi sosai.

Nan tayi masu wuni sai dare Faruk yazo d'aukarta suka koma gida.





Bayan sati biyu da sa bikkin Nasiba ta amshi kud'ad'e wajen Faruk taje da kanta tafara had'a ma Jawahir lefe kaya na gani nafad'a masu tsada tahad'a mata komai da zuciya d'aya batare da tasa mugunta ba akwatuna takwas Faruk yace tahad'o mata, wasu kayan duk irin nata ne taza'bo mata hakan da tayi ya k'ara mata k'ima da daraja a idanun mijinta da surikkanta nan Faruk yabata kud'ad'e sosai yace tayi hidima da su itama.
Godiya tayi mashi sosai.



A chan 'bangaren su Jawahir ko duk wani shirye shirye da ake yi ma Khausar da Rashida yanzu anhad'a har da ita akeyi tun ana saura wata guda bikki aka fara masu gyara musamman ma ita da akasan ta ta'ba aure, yaunzu gabad'aya ta mik'a lamurranta ga Allah kullum addu'arta d'aya Allah yatabbatar mata da alkhairi a cikin rayuwarta, gefe guda kuma ta sha ta'boye kanta taci kuka batare da sanin kowaba, ga wata irin kunyar su Mom da takeji yanzu indai ba su suka kirata aka gaisaba bata kira shima bakamar da ba yanzu bata sakewa suyi hira.

Faruk ko ya kira bata d'agawa saidai idan message yaturo mata sannan tamaida mashi reply hakan yana ba Faruk mamaki sosai dan hakane yashirya yaje Kebbi a motarshi a waya yasanar da ita zai zo dan haka Jawahir tafara shirin tarbarshi, Baba Nura tafad'a mawa shi kuma yasanar da su Baba Malam sukace Allah yakawoshi lafiya.

Ranar asabar tun da safe da tatashi tashiga kitchen tafara girki Khausar ce tazo tana tayata fried rice suka shirya mashi wadda tasha had'i sannan sukayi mashi pep chicken da kunun aya .
Wajen k'arfe d'aya sun gama nan taje tayi wanka tun tana girkin hankalinta yana wajen Faruk tana so takirashi taji yanayin tafiyar tashi bare da yasanar da ita a mota zai zo, har waya tad'auko zata kirashi sai kuma tafasa.
Cikin kayan da yayi mata da zata dawo kebbi tad'auko wata shadda gown brown tasaka wadda tasha aiki da pink d'in zare, ita tazauna tayi kwalliyarta.

Tana zaune saman darduma bayan ta gama sallar azuhur sai ga kiran Faruk ya shigo.
Saurin d'auko wayar tayi tazuba mata idanu tana kallo har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama.
Amsa mata yayi sannan yace kifito ganinan na iso.
Har zatace mashi yashigo nan yakashe wayar dan haka tamik'e tad'auke darduma saida tak'ara gyara fuskarta tad'akko pink d'in gyale tayafa sannan tafito tanaso tashiga 'bangaren su Khaisar tace tafito tarakata sai tajiyo hayaniya a cikin gidan alamun kowa yana nan ita kuma ga kunya bataso tahad'u da 'yan cikin gida dan haka tasamu Inna Mairo tafad'a mata ya iso.
Inna Mairo tace toh taje tashigo da shi kanta sunkuye a k'asa tafita.
Faruk da ke zaune cikin mota ya zuba ma k'ofar gidan idanu dan ganin ta inda zata fito dan a lokacin su Baba Malam basu nan ba kowa a wajen, idanunshi a kanta tafito har ta iso wajen motar ta shi taja tatsaya tare da yin sallama.


Amsawa yayi tare da bud'e mata k'ofar gaba yace tazagayo tazauna.
Sai a lokacin tad'ago takalleshi sanye yake cikin manyan kaya ya yi kyau sosai da har zatace mashi a'a ganin yadda yatsareta da idanu yasa bata musaba tazagaya taje tashiga tabar k'ofar a bud'e, gaishe shi tayi maimakon ya amsa sai cewa yayi shine ko kikirani kiji yanayin tafiyar tunda natafo ko.

Shuru tayi dan ita kanta ta san bata da gaskiya.
Ta cikin mirror yake kallonta ganin batada niyar d'ago kanta bare tayi magana yasa yace Jawahir nuna rashin kulawar da kike min bana jin dad'inshi idan kina haka sai inga kamar baki sona, tilasta maki akayi sai kin aureni ko?
Shuru tayi nan ma tana wasa da yatsun hannunta.
Juyowa yayi yakalleta yace indai har baki sona kifad'a min Jawahir wallahi sai inhak'ura ba wani abu bane sai inbarki ki auri wanda kikeso dan nima kaina bazanso kiyi auren da bakiso ba.

Sai a lokacin tad'ago kai takalleshi idanu cike da k'walla tace Yaya Faruk ba wai bana sonka bane ka cancanci insoka ko dan saboda alkhairin da kayi min da taimaka man da kayi a lokacin da nake buk'atar taimako bazan ta'ba kasancewa butulu agareka ba ko da ace wanine na daban kakawo kace in aura ni me biyayya ce agareka bazan ta'ba baka kunya ba, kawai dai banason zama da Aunty Nasiba a matsayin kishiyarta ne sai inga kamar banyi mata adalciba kamar na so kaina dayawa, wannan dalilin ne yasa kaga na kasa sakewa hankalina ya k'i kwanciya.

Wani irin sanyi yaji a ranshi nan yasafke ajiyar zuciya sannan yace Jawahir idan dai har kina sona to dan Allah kidaina shareni kisaki jikinki da ni Nasiba kuma batada matsala wallahi itace ma tagoya min baya in aureki na tabbata zata zauna da ke lafiya domin ita d'in mutuniyar kirkice ba irin mahaifinta ba, ina sonki jawahir ina fatan kema zaki taimaka kisoni.

Murmushi ne yasu'buce mata ahankali tace nagode Yaya Faruk.
Idanu yazuba mata yace bakice komai ba zaki so ni ko?
Saurin fita tayi daga cikin motar tace kashigo kagaisa da Inna Mairo kafin su Baba Malam sudawo daga wajen jana'izar wani abokinshi da ke nan bayan layinmu sunce bazasu dad'eba.

Murmushi Faruk yayi batare da ya ce komai ba yabud'e motar yafito nan tawuce gaba yana biye da ita a baya suka shiga cikin gida.

Gaisawa sukayi da Inna Mairo cikin girmamawa daga nan Jawahir tawuce kitchen takawo mashi abinda tatanadar mashi, tana gama ajiyewa tazuba mashi yace saidai tazauna suci tare indai ba haka ba bazai ciba.
Marairaicewa tayi tace dan Allah Yaya Faruk kaci ni na k'oshi.
'Dauke kanshi yayi yace shima bazai ciba duk yunwar da yakeji zai hak'ura sai ya koma gida sannan zai ci.

Tana jin haka tazauna k'asa tare da jawo plate tana zubawa yana kallonta tana turo baki ahaka tad'an zuba rabin plate.
Murmushi yayi sannan yasafko k'asa shima nan yafara cin wanda tazuba mashi, lumshe idanu yayi yace ashe amaryar tawa itama ba bayaba wajen iya girki.
Murmushi tayi sannan tafara cin wanda tazuba ma kanta.

Suna cikin ci sukaji sallamar su Baba Malam Jawahir d'aukar plate d'inta tayi cikin sauri tanufi bedroom dan kar sushigo suganta.

Faruk dariya yayi nan suka shigo suka gaisa da shi sannan suka bashi waje yakimtsa cikinshi.

Bayan ya gama ne yafita suka sake gaisawa sannan yafiddo tsarabar da yazo da ita cikin boot yasa aka shiga da ita cikin gida.
Har sukayi sallar la'asar baiga fitowar Jawahir ba dan haka yakirata a waya yace tafito suyi bankwana tafiya zaiyi.

Kiran Khausar tayi a waya dan tafito sugaisa da shi dan ta san halin Khausar indai har yatafi basu gaisaba sai ta sha tsegumi wajenta.

Tare suka fito da Khausar suka sameshi tsaye wajen motarshi nan suka iso Khausar tagaisheshi.
Amsawa yayi cikin sakin fuska yace ya gida khausar?
Lafiya Lau Yaya Faruk, ya su Mom?
Duk suna lafiya lau, kallon Jawahir yayi sannan yace ina fata dai kina kula min da matata.
Saurin d'agowa Jawahir tayi takalleshi nan yad'aga mata gira.
Dariya Khausar tayi tace ina kula da ita sosai angonmu, dan bana barin kowa yakalleta bare yasamu damar yi mata magana.
Murmushi yayi yace gaskiya na ji dad'in jin haka daga gareki nagode sosai Khausar bari inbada tukuici, nan yasa hannu a aljihu yad'auko bandir d'in 'yan 500 yamik'a mata.
Amsa tayi cikin jin dad'i tayi godiya sannan takoma gida tabasu waje dan suyi bankwana.
Tana wucewa Faruk yace Jawahir ya kamata kisake kidaina wannan kunyar taki dan gaskiya tana cutar da ni kwatakwata baki bani kulawa ko waya baki bari muyi hakan baya min dad'i.
Batare da ta d'ago ta kalleshi ba tace toh zan gyara.

Yauwa kokefa, mota yabud'e yafiddo wata leda wadda duk kud'i ne a ciknta yamik'a mata yace ga wannan kinyi hidima da su.
Girgiza kai tayi tace a'a kabarsu akwai kud'i a account d'ina.
Ban damu da kud'inki ba wannan ni nabaki, kinsan dai bana son gardama.

Amsa tayi taimashi godiya.
Yace bakomai yanzu dai bari inwuce kar inyi dare.

Toh Yaya Faruk nagode agaishe da su Mom da Su Aunty Nasiba.
Insha Allahu zasuji idan na isa zan kiraki waya salan kik'i d'auka kamar yadda kika saba min, Allah had'aki zanyi da Baba Malam.
Ahankali tace kayi hak'uri zan d'auka.
Shiga motar yayi yace Allah yasa.

Bakuyi bankwana da su Baba Malam

Please Login or Register in order to submit comment