Reading FANSAR RAI complete 1&2 BY SIS NERJA'ART Chapter 34 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda takashe itama akasheta.

Hakane Alhaji Allah dai yashige mana gaba.
Ameen.


*BAYAN SATI 'DAYA*

Jawahir tana zaune d'an kurkukun d'akinta ita kad'ai kanta sadde a k'asa hannunta rik'e da wani d'an tsinke tana rubutu a k'asa koda rubutun ba fitowa yakeba ammah ahaka takeyi tana zubar da hawaye, kawai sai ji tayi an bud'e k'ofa anshigo saurin runtse idanunta tayi tare da tsayawa da abinda takeyi.
Barr Faruk ne yatsaya yana kallonta sai kuma chan yatako ya iso inda take, saurin mik'ewa tsaye tayi tare da matsawa gaba tajuya mashi baya cikin dashewar murya tace menene dalilinka nadawo wa wajena shin ba na ce kadaina zuwa ba?

Wani irin haushi ne yakama Faruk yana ji kamar yajuya yai tafiyarshi sai kuma yadake yace ammah ai kinsan bamuda isashen lokaci ya kamata ki fahimci hakan jawahir.

Cikin muryar kuka tace ban damu da hakan ba.
Jinjina kai yayi yace hakane ammah dai ya kamata ki k'arashe min labarinki,,
Shuru tayi tak'yaleshi kamar bataji abinda yace ba dan hakane Faruk yamatso kusa da ita yace Jawahir shin wai ina mijinki Umar meyasa ban ta'ba ganinshi ya zo nan ba?
Tun kan yarufe baki tafashe da kuka, dafe k'irjinta tayi da hannunta cikin kuka tace Yaya Umar d'ina? Taya zaizo inda nake alhali kowa yana fushi da ni, ko kad'an banyi nadamar abinda na aikata ba,, juyowa tayi takalleshi fuska sha'be sha'be da hawaye tace shin zaka taimaka min in ida cika burina inyaso akashe ni daga baya?
Kallonta yake cike da mamaki, d'an guntun murmushi tayi tace ban damu da cigaba da rayuwa ba domin rayuwata batada sauran amfani saidai ina burin inje inda iyayena sukaje.

Saurin katseta yayi yace ba haka ba jawahir yakamata ki ida min labarinki domin musan ta yadda zamu 'bullo ma lamarin ko da ace kina so in taimaka maki ki cika burinki dole ne in ida sanin komai shin kina da hannu a cikin mutuwar su Barr Muhsin? Shin dagaske ku ne kuka kashe Alhaji Sa'idu Nepa?

Murmushi tayi cikin nuna rashin damuwa kamar ba itace take kuka ba tace ni kaina bansan abinda zan iya cewa ba, saidai abu guda nasani Alhaji Sa'idu nice nakasheshi da hannuna.
Saurin ja da baya yayi cike da mamakk yake kallonta yace kece kika kashe shi? Garin ya bayan muna tare a hotel kuma baki fitaba?
Girgiza kai tayi tace ba wai dole sai na fitaba sannan nake samun damar kisa na san ka karanta diary na yakamata ace ka fahimci komai akan haka, taya zan iya barin wanda yake da gurin rabani da rayuwata batare da na cika nawa gurin ba.
Matsowa yayi kusa da ita yace kenan jawahir kina nufin yana cikin mutanen da suka kashe iyayenki?
Girgiza kai tayi a karo na biyu sannan tace baya ciki kawai dai d'an uwanshi ne yaturoshi daga chan Europe yazo yaga bayana kafin yadawo k'asar nikuma naga idan nabarshi zai iya samun galaba akaina, shi d'in abokin Abba ne shima saidai d'an uwane na jini ga Alhaji Tanimu sunaso suga bayana ammah kuma bansan me yasa hakaba.

Jawahir wannan ba wani abu bane da ace zaki min cikakken bayani da na taimaka miki na maki alk'awali zan tura ma Alhaji Tanimu takardar gaiyata domin muzauna kotu da shi da ma sauran duk wanda yake da hannu akan kisan iyayenki yakamata ki fahimci bana da burin da yawuce inwanke ki daga zargin da ake maki.
Ahankali tace zargi kuma? Wanene yace maka zargi ne na fad'a maka gaskiya ne nice nake kisan da taimakon wadda takasance masoyiya a gareni.
Shuru Faruk yayi cikin ranshi yace yarinyar nan ta cika taurin kai dayawa,,, muryarta yaji tana cewa iyayena sun sha suce ina da taurin kai tun ina k'arama musamman ma Ammina a duk lokacin da tayi min wanka tad'auko min kaya zan saka sai in nuna bana son su duk yadda zata so insa bana yarda har sai ta canza min wasu wannan dalilin ne yasa take cemin jawahir kin cika taurin kai,, d'an guntun murmushi tayi tare da kallonshi tace ammah wannan ba shine dalilin da yasa nake da taurin kai ba wani lokacin ina duba ne da abinda yadace da rayuwata.
Mamakine yacika Faruk ganin a zuci yayi magana ammah har ta san abinda yace cikin ranshi yace anya itama ba aljanar bace, ajiyar zuciya yasafke sannan yace hakane jawahir kin faye taurin kai nima kaina kiduba tsawon lokacin da nad'auka ina bibiyarki akan kifad'a min komai game da rayuwarki ammah kin k'i...
Katseshi tayi tace ba wai haka ba kawai dai banaso had'arin da yake tare da ni yashafeka dan baka cancanci hakan ba.

Jawahir kar kiyi duba da hakan insha Allahu babu abinda zai sameni dan Allah na rok'eki ki ida sanar da ni komai a game da rayuwarki, shin a lokacin da Abba yazo da malamin nan me yafaru da lokacin da Umar yagano kina da hannu a cikin kisan da akeyi?

Dafe kanta tayi da yasara mata lokaci guda tayi tace a'a bazan ce ga abinda yafaru ba nima kaina kawai dai duk abinda yafaru yana cikin.....bata k'arasa fad'in abinda yake bakinta ba sai gani yayi kamar an fizgeta da k'arfin ta je ta bugi bango, wata irin razanannar k'ara tasaki tare da sulalewa k'asa a sume.










_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:10 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 4*

Mummyn Nasiba ce tashiga d'akin d'iyarta ta tasameta zaune ta buga tagumi girgiza kai tayi sannan taje gefenta tazauna cike da jin tausayinta tace Nasiba ya kamata kikwantar da hankalinki kidaina saka damuwa a ranki kiduba kiga a 'yan kwanakin nan yadda duk kika bi kika rame.

'Dago kai tayi takalli mahaifiyarta idanunta cike da hawaye tace bazan iyaba mummy bansan me yasa Faruk zaiyi min haka ba duk son da nake mashi ammah shine zai saka min da haka, shin wai ma wacece wannan yarinyar da yafifitata akan soyayyata.
Shafa kan d'iyartata tayi cike da jin tausayinta tace Nasiba saisa nace maki Faruk baida kirki kicire tunaninshi a ranki dan shi dama kike tunaninshi baisan kina yi ba da ace ya damu dake da bai fifita aikinshi akankiba.
Mik'ewa tayi tsaye tare da fashewa da kuka tace Mummy duk su Daddyne suka ja min hakan da ace sun barshi da aikinshi ai da bazai za'bi aikin akaina ba, koma menene yasamemu ai daga ubangiji ne ni inason faruk a hakan.
Yi shuru Nasiba kar insake jin haka kinsan dai kowane iyaye bazasu so 'ya'yansu susha wahala ba, taya kike tunani zamu amince ki auri Faruk a wannan yanayin ko ma ince akan wannan bala'in da yaratumo ma kanshi, ya kamata kigane cewa mahaifinki gatane yayi maki domin bayason duk abinda zai ta'ba lafiyarki.
Komawa tayi takwanta saman gadonta tajuma ma mahaifiyartata baya tare da fashewa da wani sabon kukan.
Hajiya Maijidda nan tadinga lallashinta tare da k'ok'arin kwatanta mata har tasamu tasafko daga fushin tadaina kukan.




Washe gari Faruk bai samu yakoma wajen jawahir ba saboda shara'ar da zasu shiga haka sukaje suna ta fafatawa har Allah yabasu nasara suka gama.


Bayan kwana biyu koda yaje gidan kaso bai samu ganawa da jawahir ba dan lokacin tana bacci koda yatambayi me gadi yashaida mashi tun baccin da takwanta shekaran jiya ne ammah tana yi tana d'an farkawa tayi sallah sai kuma idan ankawo mata abinci shine ake tashinta, haka yajuya yatafi batare da ya samu yadda yakeso ba abun ya d'aure mashi kai sosai dan bai ta'ba ganin irin haka ba.


A rana ta biyu ce da yakoma yasamu su DPO sunje wajenta sun tsareta da tambayoyi abun ya bashi mamaki sosai dan duk atunaninshi angama case d'in hakanan, DPO yana ganinshi yace Barr Faruk mun sake had'ewa kenan.
Murmushi Faruk yayi yace ai na d'auka tuni angama da wannan case d'in.
Taya za'a gama bayan ta k'i ta amsa laifinta, tana da taurin kai sosai.
Ta'be baki Faruk yayi yace bai zama dole mutum ya amsa laifin da bai aikata ba, yakamata ace ka gamsu da ba ita tayi kisan ba tunda bakada k'wak'warar shaidar da tanuna maka ita duk binciken da zakayi ka yi ammah baka samu ba, da ace ka yi wani tunanin watak'il zaka samu wani nadaban da yayi kisan.

Mik'ewa DPO yayi yamatso kusa da inda Barr Faruk yake tsaye yace har ni zaka fad'a ma haka bayan nasan itace tayi wannan kisan? Ni ko nake da k'wak'warar shaida ko da ace a yanzu nayi niyar kamata akan wannan laifin sai ta kamu saboda duk alamomi sun nuna itace, ya kamata kasan abinda kake fad'a musamman ga babban d'an sanda wanda yasan makamar aikinshi, juyawa yayi yakalli jawahir da kanta yake sadde k'asa yace tana da k'arancin shekaru sannan tana da fuska biyu zan iya amfani da damata insa ta amsa laifin nan ta k'arfin tsiya tunda ta k'i amsawa ta lalama.

'Dan guntun murmushi Barr Faruk yayi yace d'allabai tabbas kana da wannan damar a matsayinka na DPO sannan nima ina da tawa damar da zan iya kareta a matsayina na lauyanta, ba ma wannan ba idan naso zan iya shigar da k'arar duk wanda ya zargeta muyi zama na musamman da shi a kotu, kaga kai kana da damar kamata ni kuma ina da damar kareta.

'Daga mashi hannu DPO yayi yace ya isa haka ya kamata kadinga sanin abinda kake fad'a katsaya a matsayinka kawai na lauyanta mai bata kariya, idan har kace zaka shiga hurumina kai kanka zan iya sa a d'aureka ba lauya ba koda ace alk'ali ne, da sannu zan tabbatar maku da cewa itace tayi wannan kisan, kallon jawahir yayi yace kekuma kisaurare ni zan dawo a gareki,,, yana fad'in haka yajuya zai tafi sai jin muryar Faruk yayi ya ce ni kuma dasannu zan wanketa akan duk wani laifin da ake zarginta.
Jinjina kai yayi tare da yin murmushi sannan yawuce yafita, yana fita direct office d'in Alhaji Mahadi yawuce.

Bayan ya zauna ne yace wai wanene wanchan Barrister d'in.
Wane kenan d'alla'bai?
Shuru yad'anyi na d'an lokaci sannan yace lauyan da yake kare wannan yarinyar wadda tayi kisa.
Oh barister faruk kake nufi na gane shi.
DPO yace eh shi, ya cika zak'ale min akan aikina wai har ni yakece ma zaiyi k'arata akan wacchan yarinyar,

Da mamaki Alhaji Mahadi yake kallonshi yace Barr Faruk d'in? Ko dai baisan ko wanene kai ba?
Ta'be baki yayi yace me zai hanashi sani bayan kayan da nake sanye da su sun isa sununa bashi matsayina kuma ya je station ya gani kawai dai na lura kamar yanaso yanuna min shi wani ne, shin wai ma wanene mahaifinshi a garin nan?

Alhaji Sani Meshadda shine mahaifinshi,, cewar Alhji mahadu
Jinjina kai DPO yayi yace dakyau da wannan damar yake amfani yana d'aukar kanshi wanine saboda matsayin mahaifinshi koda shima d'in na ga ba k'aramin lauya bane ammah ya kamata yadaina shiga hurumina akan case d'ina da yarinyar chan.
Alhaji Mahadi yace kayi hak'uri d'alla'bai zan fahintar da shi domin Faruk abokina ne ba wai haka yakeba bansan dalilinshi na yin haka ba saboda ba mutum bane mai shiga sabgar da bata shafeshi ba.
A'a kabarshi kar kayi mashi magana kakyaleni da shi kawai dan bai sanni ba saisa yake min haka ammah dasannu zai sanni,,, yana fad'in haka yamik'e.




Faruk kallon jawahir yayi da take zaune ta zuba ma gefe d'aya idanunta da sukayi jajir, matsowa yayi gefenta yad'auko diary d'inta daga cikin suit d'inshi yamik'a mata yace gashi na maido maki.
Saurin juyowa tayi takalleshi sannan ta amsa muryarta tana rawa tace nagode.
'Daga kai yayi sannan yace duk abinda yake ciki na gani saidai babu inda zai kaini ga ha'bar zaren, shin ko zaki fad'a min inda zan had'u da su Umar domin mugana?
Wani irin kallo tayi mashi wanda shi kanshi baisan ma'anarshi ba saidai ya fi danganta shi da harara.
Ta'be baki yayi yace duk ba wannan ba yakamata kisan cewa bamuda wani isashen lokaci sannan kar wai kidamu da maganganun DPO bare har sutsorata ki, ammah yakamata kudaina kisan nan da kuke kumik'o min case d'in ni zan tsaya maki wajen ganin na k'wato maki hak'inki kamar yadda nayi maki alk'awali, sannan wannan matar meyasa take wahalar da ke alhali ta nuna taimakonki zatayi.

Cikin k'araji tace ya isa haka barrister ya isa! Maganganunka suna min yawa, taya zakace inmik'a case d'ina agareka bayan lokaci ya k'ure? Hawaye ne suka gangaro mata ahankali tace tun farko yakamata ace Ammina ta samu wanda zai iya tsaya mata yak'watar mata hak'inta ammah hakan ya gagara daga k'arshe ma aka ga bayanta, ni kaina wace hanya ce banbi ba dan ganin ank'wato min hak'ina ammah hakan bai samuba saboda azzalumai sunyi yawa,, shuru tayi nad'an lokaci sannan tacigaba da cewa sai yanzu da tadawo dan tad'auki fansa sai hakan yazama laifi? Ban damu da duk abinda zai faruba ni ina bayanta sannan zan cigaba da taimaka mata wajen ganin ta d'auki fansa, na tabbata kai ba irinsu Barr Muhsin bane dan haka ya kamata karabu da ni kar kajefa kanka acikin had'ari a dalilin son kataimaka ma wacce rayuwarta bata da sauran amfani, fashewa tayi da kuka tace duk wani farin ciki nawa anraba ni da shi hatta mijina da nake gani shine kad'ai nake jin dad'i ta 'bangarenshi ammah daga baya ya tsaneni yana ganin laifina akan abinda na aikata,, d'aga murya tayi dak'arfi tace meyasa haka yaya umar? Meyasa Ammi tayi min haka!!! cimimiyo gashinta tayi dak'arfi tare da fashewa da matsanancin kuka.

Barr Faruk mutuwar tsaye yayi yana kallonta duk sai yaji wani iri a ranshi ganin yadda take kuka bil hak'i.
Tsugunnawa yayi a gabanta yace jawahir kidaina cewa haka ni nayi maki alk'awali zan taimaka maki yakamata kifahimci hakan.

'Dago manyan idanunta tayi da suka rine saboda kuka tasafke su akan fuskarshi cikin sheshek'ar kuka tace katafi kawai barrister kadaina wahalar da kanka ban damu da duk abinda mutane zasu fad'a ba akaina saidai abu d'aya nasani duk abinda nasa a gaba sai na yi shi, shin ko zaka taimaka min akan d'aukar fansar da nake? Inhar zaka taimaka min akan haka shine kad'ai taimakon da nakeso daga gareka.

Shuru yayi yana kallonta yama rasa abinda zaice mata sai chan yabud'e baki zaiyi magana tayi saurin tarar numfashinshi tace nasan bazaka ta'ba taimaka min ba katafi kawai kabarni ni da Ammina zamu cigaba da ganin bayansu, ba kowane zaiso rayuwarsa takasance me had'ari irin tawa ba.

Barr Faruk girgiza kai yayi yace jawahir yakamata kifahimci abinda nake nufi.
Saurin mik'ewa tsaye tayi tace babu wanda zan fahimta kamar yadda nima babu me fahimtata, katashi katafi kawai.
Har ya bud'e baki zaiyi magana tai saurin tarar numfashinshi tace na rok'eka katashi katafi zanji da abinda yadameni,, hannu tasa tayi saurin dafe kanta da yasara mata tare da runtse idanunta dan duk lokacin da zaizo yayi mata maganar nan sai ta ji kanta kamar zai cire saboda tsananin ciwo.
Mik'ewa yayi tsaye yace lafiya jawahir me yake faruwa?
Ahankali tabud'e idanunta tace a'a babu komai katafi kawai.

Ammah kamar kanki yana ciwo.
Wucewa tayi takoma chan k'arshen bango tazauna tace babu abinda yake damuna na rok'eka katafi ina buk'atar hutawa.
Jinjina kai yayi tare da juyawa yatafi batare da ya sake cemata komai ba, da kallo tabishi har yafita sannan takife kanta da gwiwa tashiga rera kuka me shiga rai..


Koda yakoma gida kwanciya yayi jikinshi duk ya yi sanyi sosai, ga wani irin haushi da yakeji akan yadda jawahir take mashi dan de kawai yai alk'awalin tsaya mata da badan hakaba da tuni ya rabu da ita, saboda bai ta'ba ganin irin haka ace kwatakwata bata damu da rayuwarta ba, saidai ya fi tunanin haka akan rashin samun farin cikinta, ammah kuma me yafaru bayan a yadda yaga ta rubuta a diary d'inta tana samun kwanciyar hankali a wajen umar, ahankali a fili yace to wai ma ina umar?
Ajiyar zuciya yasafke tare da gyara kwanciyarshi yana me cigaba akan tunanin haka saidai gefe d'aya na zuciyarshi soyayyar masoyiyarshi abun k'aunarshi tana fizgarshi ammah baya iya nuna hakan saboda hali irin na faruk duk yadda yakeson abu daga lokacin da aka nemi aimashi iko da shi toh zai iya ja baya dashi komi irin k'aunar da yakeyi mashi kusan hakan ne yake tunani zai faru da soyayyarshi da Nasiba.

Daga k'arshe da yaga tunanin yana nema yadameshi yamik'e yad'auko laptop d'inshi yacigaba da aiki.





________washe gari Zaune yake wajen aiki yana tura wani sak'o ta laptop gabad'aya ya maida hankalinshi da aikin da yake, knocking d'in k'ofa akayi nan yabada izini ashigo, Barr junaid ne yaturo k'ofar yashigo.
Faruk yana ganinshi yai murmushi yace kamar ka san kana a raina.
Zuwa yayi yaja kujera yazauna yace wallahi kau barrister nima ganin kwana biyu bamu had'u bane yasa nace bari inshigo office d'in mutumin nawa inga ko yana nan.
Ture system d'in yayi gefe bayan sak'on da yake turawa ya gama shiga sannan yace ina nan abubuwa ne sunsha min kai.
Ga kuma case d'in jawahir,,, cewar Barr Junaid.
Murmushi Faruk yayi yace kusan haka ammah har yanzu na rasa samun k'wak'k'warar sheda.
Shima junaid murmushi yayi yace bana tunanin zaka samu indai akan case d'in yarinyar chan ne, yauwa Barrister wai intambayeka ya maganar baikon ka? Na ji kamar ance ba'ayi ba.
Kallonshi yayi da mamaki yace wanene yafad'a maka haka?
Kaga Faruk baidace ka'boye min komai ba ni abokinka ne sannan ina ganin kamar ba daidai bane kayi watsi da soyayyarka saboda kawai wannan case d'in ya kamata kafahimci haka.
Ta'be baki Barr Faruk yayi yace hakane saidai inaso kasani zan iya hak'ura da komai indai har za'a yi min wasa da hankali, ban damu da irin son da nake ma Nasiba ba koda ace zan rasa raina idan har mahaifinta bazai iya bani ita ahaka ba, bazan ta'ba janyewa daga case d'in jawahir ba har sai naga abinda zai ture ma buzu nad'i.
Haba Faruk wace irin magana ce haka kakeyi yakamata kagane cewa ita fa Jawahir mai laifi ce kar kayi wasa da damarka karasa soyayyarka.
Duba agogon hannunshi yayi cike da k'osawa da maganar Junaid kamar ba zai ce komai ba sai kuma chan yad'ago yakalleshi yace a yanzu ba kowa bane zai iya fahimta ammah inaso kasani da sannu zan wanke jawahir daga zargin da akeyi mata.
'Yar dariya Barr Junaid yayi yace ka jika da wata irin magana da sannu dai asirinta zai tonu, wallahi Faruk ina baka shawara kafita daga harkar case d'in yarinyar nan dan kar kaji kunya..
Katseshi yayi ta hanyar cewa Junaid idan ka gama abinda yakawoka zaka iya tafiya domin ina aiki me muhimmanci.
Mik'ewa tsaye junaid yayi yace yi hak'uri oga yanzun nan ko, atashi lafiya.
'Daga kai kawai Faruk yayi batare da ya ce komai ba yajawo syatem d'inshi ganin haka yasa Junaid yawuce yafita yabar office d'in.



Wajen k'arfe biyar Faruk yagama shiri yafito zai fita a parlor yacikaro da Momcy tana zaune ta buga uban tagumi, zuwa yayi daga gefenta yazauna tare da rik'o mata hannu.
'Dago kai tayi takalleshi saida tasafke ajiyar zuciya sannan tace Faruk.
Marairaicewa yayi yace dan Allah Momcy kidaina tagumi.
Murmushi tayi tace ai dole inyi Faruk d'azu Hajiya Maijidda takirani tana min maganar Nasiba tana chan ta tashi hankalinta sosai, Faruk ya kamata kagane cewa Nasiba tana sonka sosai koma menene bata cancanci irin haka daga gareka ba.
Kwantar da kanshi yayi saman kafad'arta yace Momcy laifin mahaifinta ne ni banda matsala ko da a yanzu zai janye k'udurinshi ni kuma zan auri Nasiba.
Girgiza kai tayi tace Faruk ka fiye taurin kai watau kana nufin kai bazaka iya janye naka ba.
'Dago kanshi yayi yakalleta cikin sanyin jiki yace a'a Mom nawa bazai ta'ba janyuwa ba idan har nace zan janye toh tabbas banyi adalci ba domin Jawahir tana buk'atar taimako taya za'a zalunci mutum sannan akamashi a rufe, ta rasa me tsaya mata yak'wato mata hak'inta na tabbata daga inda najanye za'a iya kasheta inko nayi haka ban kasance me adalci ba akan aikina.
Cike da tausayin d'an nata take kallonshi tace hakane Faruk Allah ubangii yataimaka insha Allahu zaka auri Nasiba dayardar Allah ita rabonka ce.
Cikin jin dad'in kalaman mahaifiyar tashi yace nagode sosai Momcy.
Shafa kanshi tayi tace bakomai Babana.
Mik'ewa yayi yace Momcy bari inje akwai wani aiki da zanyi yanzu.
Toh shikenan Allah ubangiji yataimaka sai ka dawo.
Ameen Momcy.



Wajen k'arfe biyar da rabi ya isa gidan kaso direct office d'in Alhaji Mahadi yafara zuwa kamar yadda yasaba bayan sun gaisa ne mahadi yakalleshi yace wai Faruk minene yahad'aka da DPO ne?
Ta'be baki Faruk yayi yace me fa? Wani abu yace maka ya faru?
A'a ba wai haka ba.
'Dan guntun murmushi Barr Faruk yayi yace kabarni da shi kawai yanzu dai bari inje inga jawahir wallahi yarinyar nan ta k'i tabani had'in kai yadda yakamata.
Jinjina kai Alhaji Mahadi yayi yace kama gode ma Allah da bata shek'aka lahira ba.
Uhm kaidai kasani malam ni bari intashi inje.
Dariya Alhaji Mahadi yayi yace toh shikenan ba damuwa abokina bari insa arakaka.


Lokacin da suka isa tsaye yasameta wajen 'yar k'aramar tagar nan idanunta suna ga d'an hasken da yake shigowa tsaye yayi daga bakin k'ofar yana kallonta inda ma'aikacin gidan yake tsaye a waje yana jiranshi takowa yayi yamatso kusa da ita bai ankara ba sai jiyo muryarta yayi ta ce shin zaka taimaka min in cika burina?
Ajiyar zuciya yasafke yace jawahir ya kamata kifahimta lokaci yana k'ure mana kidaure ki ida bani hujjojin da zasu taimaka wajen ganin na tseratar da ke daga gidan nan.
Cikin muryar kuka tace meyasa kafi damuwa da fitata akan d'aukar fansar abinda akayi min? Wa yafad'a maka na damu da incigaba da rayuwa? Nidai abu d'aya nakeso shine inga bayan duk wanda yarabani da iyayena.
Cikin sanyin jiki yace jawahir nasan haka kifahimceni idan har kika ban dama nayi aikina yadda yadace toh dole ne ingurfanar da su agaban hukuma ni zan taimaka maki da hakan.
Ahankali tace hukuma kuma? Ni bana buk'atar hukuma a ciki nafiso kowane d'a yad'and'ani irin rad'ad'in da naji a lokacin da narasa iyayena, nasan bazaka ta'ba taimaka min ba ammah ni zanyi komai dakaina.
Tsaye Barr Faruk yayi yana kallonta cikin ranshi yace meyasa jawahir take haka ko har yanzu bata yarda dani ba?
Juyowa tayi ahankali takalleshi idanun nan nata sunyi jajir kamar garwashin wuta duk sun k'ank'ance d'an guntun murmushi tayi tace kar kadamu ahakan ma nagode.
Amm jawahir ya kamata kifahimci kwana goma sha biyar fa yarage mana lokaci bazai ishemu ba kidaure muyi abinda yadace.
Dafe kanta tayi da hannu d'aya ahankali tace wannan shine abinda yadace Barrister a gobe zan kasance cikin farin ciki saboda akwai aikin da zan aiwatar wanda shine zai rage min rad'ad'in abinda nakeji.
Tun kan tarufe baki yace jawahir kisa zakiyi?
Takawa tayi dak'yar tana k'yangashi taje tazauna tare da jingine kai da bango sannan tace abinda yadace da rayuwata zanyi.
Matsowa yayi kusa da inda take zaune yatsaya yace jawahir na rok'eki ki taimaka kiban k'wak'warar hujja ni zan taimaka maki akan dukkan abinda yadace nayi maki wannan alk'awaline duk wanda yake da hannu akan mutuwar mahaifinki bazan ta'ba barinshi ba koma wanene shi.
Ahankali tamaimaita kalmar da yace koma wanene shi? sannan tad'anyi guntun murmushi tace kana nufin koda ace kana da dangantaka da shi idan har kagane yana da hannu a ciki zaka taimaka min?
Shuru Barr Faruk yayi sai chan yace ban damu da kusanci na da shi ba domin ina akan aikina ne zanyi k'ok'arin haka kiyarda da ni jawahir.
Hawaye ne suka gangaro mata tace bana so kajefa kanka acikin had'ari Barrister domin rayuwata babu komai a cikinta sai had'ari idan har kacigaba da bibiyata ahaka komai zai iya faruwa da kai wannan dalilin ne yasa nakeso kacire hannunka a ciki sannan saboda haka ne nakasa fad'a maka komai akan rayuwata.
Kidaina cewa haka jawahir ban damu da duk yanayin da zan shiga ba indai ina akan aikina nidai kawai taimako d'aya nakeso kiyi min.
Idanu tazuba mashi batare da tayi magana ba ganin haka yasa yace shin ina labarin su umar da d'an uwan mahaifinki? Ko zaki fad'a min inda suke saboda ina da tarin tambayoyi akansu sannan ya zama dole Abbanku yagurfana a

Please Login or Register in order to submit comment