Reading FANSAR RAI complete 1&2 BY SIS NERJA'ART Chapter 32 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da nakeyi maka ya lunka wanda nayi mashi saboda kai da gabad'aya rayuwata nake k'aunarka shi kuma da zuciyata, na mallaka maka gabad'aya soyayyata.

Wani irin farin cikine yalullu'be Faruk yai saurin rungumeta yace nagode sosai Jawahir da irin wannan matsayin da nasamu awajenki, nagode ma Allah da yamallaka min ke amatsayin mata na soki tun lokacin da banyi tunanin zan sameki ba ashe ke d'in rabona ce.
Lumshe idanunta tayi tare da tura hannuwanta cikin sumar kanshi tana shafawa tana jin sonshi yana k'ara mamaye mata duk ga'b'ban jiki.
Lamo yayi a jikinta sai kuma chan yad'ago yakalleta itama bud'e idanunta tayi suka sakar ma juna lallausan murmushi tace ya dai Lovely?
Mik'a yayi sannan yace ya kamata aji da ni yanzun nan gaskiya.
Hararshi tayi cikin wasa sannan tace bayan cikin da kayi min sai kuma kace wani inji da kai.

Toh ya kika iya tunda kina auren lafiyayyen miji ko ana nufin baza'a baniba.
Saurin jawoshi tayi yafad'o jikinta tace ni wacece da zan hana mijina shi da kayanshi akoda yaushe ashirye nake domin kar'barka.
Murmushi Faruk yayi yakai hannu yakashe masu fitila tare da jawo bargo yalullu'besu.


_Ina ganin haka nayi saurin tattaro takarduna da alk'alamina nafito daga d'akin tare da jawo masu k'ofa nace asuba tagari Mr nd Mrs *FANAJ*_


*BISSALAM*

_Alhamdulillah anan muka kawo k'arshen wannan littafin me suna *FANSAR RAI* kurakuren da suke ciki Allah yayafe mana_

_*Nagode sosai da irin k'aunar da kuka nunamin da lokacinku da kuka bani Allah ubangiji yabar zumunci Allah yak'ara dank'on zumunci*_



_Ina maku albishir da sabon novel d'ina me suna *KUWWA DA KUWWA* (bata korar buzu)_

_Labari ne wanda yak'unshi abubuwa da dama wanda sai mutum ya karanta sannan zai fahimci hakan ga kad'an daga cikin labarin_
~~~~~~
_*KUWWA DA KUWWA.....*_
_(Bata korar buzu)_


Kwance take saman makeken gadonta tana bacci inda dogon gashinta yabaje mata a fuska, yanayin yadda take baccin kawai zaka kalla kagane cewa a nutse takeyin shi, lokaci guda tatashi zaune zumbur tare da saurin sa hannunta takare fuskarta, wani irin farin haskene yadaki tafin hannunta ji kake wata irin k'ara k'attt.

Janye hannunta tayi tare da sa gudan hannun tagyara gashinta da yake baje a fuskarta nan kyakkyawar fuskarta tabayyana, ajiyar zuciya tasafke tare da mik'ewa tsaye tanufi wajen makeken mirror da yake manne a bangon d'akin tatsaya tana duba fuskarta, komawa tayi tazauna tare da dafe kanta da hannu biyu cikin siririyar muryarta me dad'in saurare tace *Najma* meyasa kike kai ma fuskata hari meyasa kikeso ki'bata min fuska? sauri janye hannunta tayi takalli zobenta da yake manne a dogon yatsan hannunta na tsaka sai kuma tamik'e tanufo k'ofa tun kan ta iso k'ofar dakanta ta bud'e, tana fita parlor nan wasu mata kusan su goma da suke sanye da kaya iri d'aya suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa, batare da ta amsa masuba taje bisa lumtsumemiyar kujerarta tazauna sannan da hannu tayi masu nuni da subar wajen.
Cikin sauri duk suka tashi suka fita tare da jawo mata k'ofa.



Duk wannan abun da yake faruwa tana gani a cikin wani d'an k'aramin madubi dake hannunta, wurgi tayi da madubin ganin batayi nasara ba tamik'e cikin fushi tana cewa ko da ba yau ba *Najla* sai na cika burina, sai na 'bata maki wannan kyakkyawar fuskar da kike tak'ama da ita bazan ta'ba barinki ba....



** ** ** **

Tunda suka shigo cikin garin kallon mutane kawai suke abun yana burgesu ganin yadda suke ta rayuwarsu, itako shugabar tasu yatsina fuska kawai take dan abun sam bai burgeta ba, suna tafiya a wajen titi wata mata tagifta ta gabansu nan d'aya daga cikinsu tafara lasar baki saurin shak'o wuyanta gimbiya najma tayi tace kar kikuskura kilashi wani a cikin garin nan domin garin nan yana da had'ari sosai duk mayen da suka kama basu barinshi a raye,,, tana fad'in haka tatureta gefe nan tayi saurin duk'awa cike da girmamawa tace kigafarceni ya shugabata.
Batare da ta amsa mataba tawuce gaba suna biye da ita a baya suna cikin tafiya a wajen kasuwa tana kallon wani shago da yad'auke mata hankali saboda cikowar mutanen da suke cikinsh nan wani tsoho yatafo da 'yar sandarshi yana dogarawa bai kulaba yad'an bugeta.
A fusace tajuyo takalleshi tare da shak'oshi cikin fushi tace kai wane irin dabba ne da zaka bugeni, bakasan wacece ni ba?.
Jikin tsohon yana karkarwa yace kiyi hak'uri bana gani sosai ne.
Batare da ta sakeshi ba tace bana yafiya a duk lokacin da akayi man laifi sai na d'auki fansa dan haka bazan ta'ba barinka ba, dogon harshenta tafara fiddowa daga cikin bakinta tana shirin lashe fuskar tsohon, daga bayanta taji andaka mata tsawa saurin maida harshen tayi tasaki tsohon tajuyo dan ganin wanda yayi tsawar

Wasu mutane ne tagani tsaye a bayan wani kyakkyawan saurayi yana sanye da kaya na sarauta duk sun fito daga cikin motocinsu, saurayin ne cikin 'bacin rai yace ke wace irin macece bakida hankali zaki shak'e tsoho ko iyayenki basuyi maki tarbiya ba?.
Tsayawa tayi tana kallonshi cike da mamaki jin kalaman da yake fad'a mata wanda tunda take a rayuwarta ba'a ta'ba fad'a mata irinsu ba sai yau da tashigo k'asar nan yawon bud'e ido.
Kallon tsohon saurayin yayi yaga yana ta kyarma sannan yakalli nakusa da shi yace aje arakashi gida.
'Dan russunawa yayi yace angama ranka yadad'e nan biyu daga cikin mutanen suka yi saurin nufar inda tsohon yake suka ruk'oshi suka sa cikin mota suka tafi da shi.

Kallon kallo suka dinga yi shi da Gimbiya Najma yana mata kallon tsana, inda ita kuma take jifanshi da mugun kallo, sai kuma chan yajuya aka bud'e mashi mota cikin k'asaita yashiga aka rufe nan sauran mutanen nashi kowa yashiga mota suka bad'a ma su Najma k'ura suka tafi.

Cikin 'bacin rai tace wanene wannan? Wanene shi da har zai d'aga min murya? Ya zama dole kubishi kugano min inda yake da kuma matsayinshi a garin nan dan bazan ta'ba barinshi ba!!!
Mata ukku ne suka 'bace lokaci guda.
Nan Najma takalli sauran tana hucci sai kuma tarufe idanunta tana motsa baki ahankali nan ita da sauran matan suka 'bace 'bat.


___kuyanginta ne zaune kusa da ita suna ta mata hidima inda ita kuma take ta murza zoben da yake hannunta, k'wank'wasa k'ofa akayi nan masu tsaron k'ofar sukayi saurin bud'ewa.
Wata farar macece tashigo fuskarnan fara fat.
'Dago kai Najla tayi takalleta tace Hasisa ina kika shiga yau tun d'azu ina ta nemanki.
Saurin duk'awa tayi tace kigafarceni ya shugabata hak'ik'a na zo maki da wani labari da zai sakaki cikin farin ciki.
Idanu Gimbiya Najla tazuba mata hakan yaba Kuyangar damar cigaba da maganarta dan tasan shugabar tasu ba me yawan hayaniya bace...
Yau 'yar uwarki tafita da bak'ak'en kuyanginta yawon bud'e ido inda ni kuma nayi amfani da tsafina nabisu batare da na bari ta ganni ba, wata k'asa ce me suna Miraj mukaje inda mutane ne suke rayuwa a k'asar suna rayuwa ta 'yanci sannan suna da arzik'i sosai k'asar tana cikin k'asashe da ake ji da su wajen dukiya sannan sarkinsu ya kasance me adalci saidai abinda zai baki mamaki su d'in suna bin wani addini sannan su mutane ne ba irin muba, kowane maye yana tsoron zuwa k'asar miraj saboda basu yarda da maita ba duk lokacin da suka kama maye basu barinshi suna had'a wuta me zafi suk'oneshi wannan dalilin ne yasa muke tsoron tunkarar k'asar tun shekaru d'ari biyu a chan baya, saidai wasu daga cikinmu sunsha suyi k'ok'arin zuwa k'asar sukama mutanen ciki wasu suna samun nasarar dawowa da ransu wasu kuma ana kamasu akashe.

Gimbiya Najla idanu tazuba mata tana saurarenta, cigaba tayi da cewa saidai abun mamaki da ban tsoro a yau d'innan wani mutum me shiga ta alfarma yanayinshi kawai zaki kalla kigane shi d'in jinin sarauta ne ya harzuk'a Gimbiya Najma da kalamanshi da yayi mata wanda taci alwashin d'aukar fansa bazata ta'ba barinshi ba dan a yanzu haka ta tura bak'ak'en kuyanginta dan sugano mata asalin mutumin......


____*****_____

....A yanzu nice shugabarku nice shugaba a k'asar Nairan ya zama dole kowane mahaluk'i yayi min mubaya'a fararen mayu da bak'ak'en mayu duk wanda yak'i haka zan kasheshi a yanzun nan,,, tana fad'in haka tazauna saman kujerar mulki...




Tsugunne take a gaban gawar tana ta rusa kuka nan wata kuyanga tashigo cikin sauri tamaida k'ofar tarufe cike da girmamawa tace ya shugabata ya kamata kitashi kibar masarautar nan dan a yanzu 'yar uwarki ta aiko azo akawo mata ke, jama'arta suna nan dayawa sun nufo d'akinki.
'Dago fuskarta tayi da tayi jajir saboda tsananin kuka takalli kuyangartata har ta bud'e baki zatayi magana sukaji anfara buga k'ofa dak'arfi, kuyangarce cikin sauri tanufo inda take tataimaka mata tamik'e tsaye..........

+++++++++++

...Ranka yadad'e ya kamata kaduba maganata baidace ace kamar kai ba a matsayinka na babban sarki ace d'anka yarima yana zaune babu aure bayan duk wata dukiya yana da ita shin idan baiyi aure yanzu ba sai yaushe zaiyi ko sai bayan mutuwarmu kaduba kaga 'yar uwarshi yadda take k'aunarshi tana binshi ammah ko kad'an baya kulata shin hakan da yakeyi ya dace kenan.....bud'e k'ofar da akayi aka shigone yasa taja bakinta tayi shuru saboda yanayin takun tafiyar da tajiyo yasa tagane Yarima ne, sai a lokacin sarki yad'ago kai yakalleta sannan yamaida kallonshi ga yarima d'an da yad'auki son duniya yad'aura mashi.....


_____
..Ya kamata ace Gimbiya ta fito a wannan ranar anyi girkin masarautar nan da ita kar kumance hakan shine al'adar masaraurar nan duk amaryar da aka auro acikinta dole ne bayan sati biyu tafito tashiga kitchen dakanta tagirka abincin da Yarima, sarki da sarauniya zasu ci a ranar nan wannan sak'one aje afad'a ma gimbiya!!!

Wata kuyanga ce cikin sauri tamik'e tafita dan ta isar da sak'on uwargijiyarta.
Wadda tagama bayanin juyawa tayi takalli Sarauniya mahaifiyar yarima da itama take kallonta nan tasakar mata murmushi mai cike da ma'anoni sannan tawuce gaba inda sauran kuyanginta suka take mata baya.


A lokacin da sak'on ya iso agareta tsaye tayi tarasa ta inda zata fara, k'arar k'araurawa tajiyo daga waje nan tafara jiyo muryar jakadiya tana cewa a yau ranar murnar ce agaremu auren yarima da gimbiyarshi ya cika sati biyu a yanzu haka muna jiran fitowar gimbiya zatazo tagirka ma yarima da iyayenshi abinci me dad'i wanda zasuci dan nuna farin cikin wannan ranar.
Kallon agogo tayi da daidai lokacin k'arfe sha d'aya daidai tabuga saurin matsawa tayi tad'age labule nan taga yanayin gidan ko akwai rana sosai.
Ja tafara yi da baya cike da tashin hankali tana tunanin ta yadda zata iya fita a wannan lokacin dan ta san ba irin wannan lokacin bane lokacin fitarta.....


*_KUWWA DA KUWWA....._*
(Bata korar buzu)
Labarin ya sha banban da wanda kuka saba karantawa.
shima ga duk me buk'ata zai sameshi akan farashi naira d'ari biyu (200), saidai bazan fara sakinshi ba har sai na gama typing d'in part 1.
Kar kubari abaku labari


Kukasance da ni acikin sabon free novel d'ina wanda yake tafe gajeren labari me suna *NADAMAR RAI*


_Taku har kullum sis Nerja'art✍🏻_












[7/24, 11:09 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]


_Follow me on Wattpad: *Sis-Nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_



PART TWO

_~GORON SALLAH~_

*PAGE 1*


Kwance yake saman makeken gadonshi yad'age kanshi sama yana kallon Ceiling tare da lumshe idanunshi kamar me bacci ammah azahiri tunani yake rayuwar jawahir kawai yake tunani akan irin gwagwarmayar da tasha, tambayar kanshi yafara yi daman ashe tana da aure? Toh ina mijin nata? Meyasa bai ta'ba ganinshi ya je wajenta ba??tambayoyin da suka dinga mashi yawo kenan a k'walwa saidai me a gefe d'aya Allah Allah yake yi gari ya ida wayewa yayi wanka yatafi gidan kaso na mata dan yagana da ita dan ya fi so ya ida samun full details kafin yafara aikinshi,,,, yana cikin wannan tunani bacci 'barawo yasace shi.


Wajen k'arfe bakwai kiran da yashigo wayarshi ne yatashe shi dakyar yabud'e idanunshi da sukayi mashi nauyi saboda rashin samun isashen bacci, d'auko wayar yayi yaduba yana ganin me kiranshi sai ma yamaida ta silent sannan yamik'e yashiga wanka.

Bayan ya fito ya shirya cikin shirinshi na tafiya aiki jikkar laptop d'inshi da wayoyinshi yad'auko yafito parlor daidai da Momcy ta shigo parlorn d'auke da plask tsayawa tayi tana kallonshi.
Murmishi Faruk yasakar mata tare da gaisheta.
Amsawa tayi sannan tace Son ka dai san babu inda zakaje sai ka yi breakfast ko?
'Bata fuska yayi yace Momcy bana jin yunwa.
Batace mashi komai ba tawuce dining area.
Ajiye kayan da suke hannunshi yayi yabi bayanta yana zuwa yaja kujera yazauna, fara serving d'inshi tayi sannan tace d'azu Nasiba ta kirani a waya ta ce tana ta kiran wayarka baka d'auka ba.
Yi yayi kamar baiji ba yafara breakfast d'inshi.
Kallonshi Momcy tayi tace Faruk magana fa nake maka ka min shuru.
'Dagowa yayi yakalleta yasakar mata murmushi sannan yace momcy time d'in bacci nake kuma ko da natashi ban bi ta kan wayarba saboda naga zanyi late ban tafi aiki ba.
Momcy kallonshi kawai tayi tawuce tatafi cikin ranta tana mamakin halin d'an nata.

Sama sama yayi breakfast d'in yamik'e yad'auki kayanshi yaficce yabar gidan.

Yana cikin mota yana tuk'inshi a nutse nan wayarshi tafara ringing kallon wayar yayi ganin sunan da yabayyana a jikin screen d'in wayar yasa yai saurin yin picking tare da yin sallama,,, yanayin yadda yake maganar kawai zaka gani kagane cewa akan wajen aiki ne suke tattaunawa sun dad'e suna wayar kafin daga bisani suyi sallama.

Suna gama wayar d'an guntun tsaki yaja tare da canza hanya yanufi wajen aikinsu.

Yana isa yai parking a daidai inda yasaba yin parking yad'auko bakin space d'inshi yadad'e fuskarshi sannan yafito daga cikin motar yazagaya yabud'e mazaunin me zaman banza yad'auko jakkar laptop d'inshi.

Tafiya yake cikin takunshi me burgewa duk inda yagifta sai mutane sun mashi barka da safiya saidai kawai yad'aga masu hannu, wad'anda suka yi mashi farin sani ne kawai zasuce daman haka yake dan Barr Faruk ba mutum bane me yawan son hayani.


Yana zaune a office d'inshi akayi mashi knocking izini yabada ashigo nan aka turo k'ofa.
'Daga kai yayi yakalli me shigowa sai kuma yamaida kallonshi ga system d'in shi.
Sacratery takowa yayi ya iso wajen Barr Faruk daga gaban table d'inshi yatsaya yace Barrister barka da aiki.
Batare da ya d'agoba yace yauwa barka.
File d'in da yake hannunshi yamik'a mashi yace gashi oga yace akawo maka.
Ohk ajiye nan.
Ajiyewa yayi saman table d'in yace atashi lafiya sannan yajuya yafita.
Barr Faruk d'auko file d'in yayi yabud'e yafara dubawa chan sai yamik'e tare da d'aukar file d'in da key d'in motarshi yafita.
Saida yafara biyawa a office d'in ogansu suka tattauna sannan yatafi.


Yana barin nan direct gidan yari yawuce yana isa kamar yadda yasaba office d'in abokin nashi yafara safka bayan sun gaisa ne yanuna yanaso yaje yagana da jawahir.
Alhaji Nasibi yanuna ba matsala nan yakira wani ma'aikacin gidan kamar yadda yasaba yahad'a shi da Barr Faruk suka je.




Suna zuwa suka sameta zaune ta had'e kai da gwiwa, daga bakin k'ofa ma'aikacin yatsaya inda shi kuma Barr Faruk yashiga ciki ko kad'an bata motsa ba daga inda take da alama kamar bata ma san da shigowarshi ba.

Barr Faruk matsawa yayi yatsugunna a gabanta tare da kiran sunanta ahankali.
Bud'e rinannun idanuwanta tayi tare da d'ago kanta tasafke idanunta a fuskarshi inda fuskarta take a d'aure.
Cike da jin tausayinta yake binta da kallo inda itama take kallonshi babu ko k'yaftawa.
Ajiyar zuciya yasafke yace jawahir insha Allahu zan taimaka maki zan wanke ki daga zargin da akeyi maki.
Lokaci guda tamik'e tsaye tare da sakar mashi murmushi sannan tawuce tafara taku d'aya biyu sai taja tatsaya batare da ta juyo ta kalleshi ba cikin dashewar murya tace zargi kuma? Wanene yafad'a maka zargina akeyi? Duk abinda kaji ance na aikata to dagaske ne.
Mik'ewa yayi daga inda yake yatsaya yace idan har abinda kika rubuta a kan labarinki gaskiya ne toh tabbas zanyi k'ok'ari wajen wanke ki.
Murmushi tayi a karo na biyu tare da sake jefa mashi tambaya tace labarina kuma?
'Dan matsowa yayi kad'an yace Eh saidai inaso insan k'arshen shi dan samun cikakkar hujja.
Shuru tayi kamar bataji abinda yaceba ganin haka yasa Barr Faruk yace shin ina Umar?
Lokaci guda tajuyo takalleshi cikin sauri tatako ta iso wajen da yake tsaye tare da cacimo wuyar rigarshi muryarta tana rawa tace wanene yafad'a maka shi? Ina kasan yaya umar d'ina?,, tafad'a tare da fashewa da kuka.
K'wacewa yayi daga rik'on da tayi mashi yad'an ja baya kad'an yace ban san umar ba saidai na karanta acikin labarin da kika rubuta.
Hannu tamik'a mashi muryarta tana rawa tace ina diary na.
Cikin nuna rashin damuwa yace yana wajena zanyi wani aiki ne akanshi ammah jawahir ya kamata kisanar da ni ina umar da su Abba shin suna raye?
Sulalewa tayi a lokaci guda tazauna k'asa tare da rushewa da kuka tace nima ban saniba bansan me yasa babu wani wanda yazo gareniba meyasa zasuyi min haka?
Takowa yayi yamatso wajen da take yace kenan suna a raye jawahir?
Wani irin kallo tayi mashi har ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tafasa.
Ganin haka yasa yacigaba da cewa jawahir dole sai kin daure kin sanar da ni komai domin ta haka ne zamu samu mafita wad'annan mutanen da suka kashe maki iyaye, sannan ita wannan aljanar ta wace hanya takebi tana d'aukar maki fansa akansu, kuma idan har itace take yin kisan ai inaga bai dace ace ankama ki akan laifin da bake kika aikata ba ammah me yasa tun lokacin da akayi abun baki sanar da hukuma ba? Inaga da ace kin sanar da......wata irin k'ara jawahir tayi tare da toshe kunnuwanta cikin d'aga murya tace ya isa haka barrister! ya isaaa!!!

Hawaye ne suka cigaba da fita daga idanunta tace taya kake tunanin hukuma zata taimaka min bayan Ammina ita kanta ta je ma hukuma ammah babu wanda yakulata bare har yataimaka mata, wannan dalilin ne yasa nad'auki fansa dakaina ban damu da abinda zai faru da niba bana buk'atar cigaba da rayuwata ina so akasheni saidai kafin nan nafiso incika burina a rayuwa sai na ida kashe wad'anda suke da hannu a mutuwar iyayena daga nan nima zanyi farin ciki sosai idan na mutu dan daman mutuwar itace nafi buk'ata,,,,, juyawa tayi takalli gefe guda sannan tace rayuwata batada sauran amfani ban ta'ba bak'in ciki ba akan zaman da nayi a nan na tsawon wata goma zanyi farin ciki ace daga nan gidan sai k'abarina zan shiga.....





Katseta Barr Faruk yayi yace jawahir wannan wace irin magana ce kikeyi kidaina cewa haka insha Allahu zaki rayu ni zan taimaka maki kifita daga gidan nan saidai ta ina zan fara bi, shin ya za'ayi in iya sanar da kotu cewa aljanah ce take wannan kisan?
"Wannan ba gaskiya bane nice nan nayi kisan Barrister kar kasaka kanka acikin lamurra na domin gudun kar kajefa rayuwarka acikin had'ari, duk wanda yanemi yajawo jikinshi agareni yana shiga matsala yakamata kafahimci hakan.
Kallonta yake gabad'aya ta hargitse yace ban damu da wannan ba jawahir kawai dai akwai wasu tambayoyi da nakeso inyi maki shin ina lauyan mahaifinki wanene shi? Sannan dagaske kina da hannu acikin mutuwar Alhaji....
Bata bari yak'arasaba takatseshi tace ya isa haka barrister na fad'a maka babu abinda zaka samu daga gareni wannan duk ba gaskiya bane,,,, tana fad'in haka tamik'e taje chan wajen 'yar k'aramar tagar nan da tasaba tsayawa wajenta tatsaya tajuya mashi baya ahankali tace wannan duk shirina ne ya kamata katashi katafi.
Idanu Faruk yazuba mata yana kallonta har ya bud'e baki zaiyi magana tatari numfashinshi tace banason jin komai daga gareka dan Allah kabarni haka bansan ya zanyi ba tambayoyinka sun min yawa!.
Mik'ewa Barr Faruk yayi yace shikenan jawahir zan tafi ammah inaso kisani zan dawo agareki bamuda isashen lokaci ya kamata kisan haka sai anjima,,,, yana fad'in haka yajuya zai tafi sai jin muryarta yayi ta ce katabbatar ka maido min diary d'ina.
'Dan guntun murmushi yayi yajuya yafita.

yana fita yajiyota ta fashe da kuka d'an ja yayi yatsaya sai kuma chan yawuce yatafi.

Saida yabiya ta office d'in Alhaji Mahadi sukayi sallama sannan yawuce yatafi yana a mota DPO yakira shi a waya yace suna son ganinshi yanzu, amsa masu yayi da toh gashinan zuwa sannan yakashe wayar.

Lokacin da ya isa station d'in direct office d'in DPO yawuce lokacin yana ciki suna ganawa da wani dan haka yajira sugama.

Kusan minti shidda sai ga mutumin ya fito juyowar da Barr Faruk zaiyi nan sukayi ido hud'u da Alhaji Mansur wani shu'umin murmushi Alhaji Mansur yasakar mashi tare da cewa Barr Faruk barka da rana.
Kallo d'aya Barr Faruk yayi mashi batare da ya tanka shi ba yawuce zai shige sai jiyo muryarshi yayi daga baya yana cewa har yanzu kana da damar da zaka mallaki Nasiba but in kana da buk'atar hakan.
Ja yayi yatsaya har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa yawuce yashige.
Dariya Alhaji Mansur yayi yace nasan dai zaka amince da hakan.

Yana shiga hannu yamik'a ma DPO suka gaisa nan yanuna mashi kujera yazauna, tambayarshi yayi ya aiki ya amsa da Alhamdulillah.
DPO jujjuyawa yayi a kujerar da yake zaune sannan yace Barrister Faruk ba komai yasa na kiraka ba sai akan case d'in jawahir akan kisan Alhaji Sa'idu wanda a yanzu mun k'ara samun k'wak'k'warar hujjar da tanuna mana tana da hannu a cikin kisan shi zamu mik'a case d'in a kotu dan ya kamata kotu tayi gaugawar d'aukar mataki saboda abu sai k'ara cigaba yake.
Shuru Faruk yayi yazuba mashi idanu yana kallonshi har yakai aya sannan yace DPO na ji bayaninka saidai inaso kasan cewa wannan zancen duk ba gaskiya bane jawahir bata da hannu acikin mutuwar Alhaji Sa'idu Nepa yakamata kudaina zarginta saboda kun duba CCTV Camera a daidai lokacin da akayi kisan muna a hotel kaga babu hujjar da zatasa ace itace takasheshi.
'Dan guntun murmushi DPO yayi yace Eh munga haka ammah wannan bai isa yazama k'wak'warar shaida ba, inaso kasan wani abu duk mutuwar wad'anda ake zarginta akansu kusan haka yafaru kuma muna tunani tana amfani da layar zana ne tana 'bacewa taje takashesu sannan su kansu lauyoyinta bata barsu ba tana acikin gidan yari takashesu.

Na ji wannan saidai ban gamsu da hujjarka ba.

Cikin d'aga murya DPO yace Barrister nasan aikina sannan ina k'ok'ari wajen ganin na kawo cikakkun hujjoji da dole za'a yadda cewa itace takashesu kamar yadda tun yanzu na fara samu dan mun samu hoto kamar yadda muka samu an aje a mutuwar sauran mutanen shin wannan ba hujja bane?
Murmushi Barr Faruk yayi yace kusan haka saidai inaso kasani nima zanyi bakin k'ok'arina a matsayina na lauyanta.

Jinjina kai DPO yayi yace dakyau Barr Faruk.
Mik'ewa yayi tare da mik'a mashi hannu sukayi musabaha sannan yace na barka lafiya.
Ta'be baki DPO yayi yace ba damuwa a duk lokacin da buk'atar nemanka yataso zakaji kirana.
Ohk ba damuwa inspector sai na ji ka.

Tunda yakama hanya ba abinda yatsaya mashi a rai sai maganganun da jawahir tafad'a mashi kenan har hukuma sun sanar da su akan kisan da akayi ma mahaifinta ammah ba'a d'au wani mataki ba? Indai hakane to da wannan damar sukayi amfani wajen d'aukar fansar kisan da akayi ma iyayenta saidai taya zan samu cikakkun hujjojin da zan iya kareta da su? taya zan wanketa gaban kotu? A fili yace ya zama dole jawahir kiyi min magana indai har kinason barin gidan kason nan ammah ita fa wannan aljanar...bai rufe bakiba sai gani yayi ta mirrir d'in motarshi kamar wannan tsohuwar ce zaune tana kallonshi da k'walak'walan idanunta saurin jan burki yayi yatsaya tare da waiwayawa baya ammah baiga kowa ba, ajiyar zuciya yasafke tare da jingine kanshi a jikin kujera kusan minti ukku sannan yatada motarshi yanufi gida.


Yana isa wanka yayi yashirya sannan yafito parlor yasamu iyayenshi Momcy tazubo mashi lunch yazauna yayi suka d'an ta'ba hira yatashi yakoma d'akinshi wayoyinshi gabad'aya yakashe dan kar atakura mashi yad'auko laptop d'inshi tare da diary d'in jawahir yazauna yana aiki saida yaji k'walwarshi ta d'auki caji tana buk'atar hutu sannan ya

Please Login or Register in order to submit comment