Reading FANSAR RAI complete 1&2 BY SIS NERJA'ART Chapter 31 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kad'ai bane Lovely dole mucanza,,, tana fad'in haka tazare jikinta tare da rik'o hannun Jawahir gudan hannun tarik'o nashi tace muje kuyi breakfast kar mubar amarya da yunwa.

Dining suka wuce tayi serving d'in kowa nan suka fara ci Jawahir ba wani ci take sosai ba Faruk yana lura da ita ji yake kamar yayi mata d'ure dan de kawai Nasiba da ke wajen.

Nasiba tana gama ci tatashi takoma d'akinta dan tabasu waje Faruk ko kamar jira yake nan yafara feeding d'in Jawahir saida yatabbatar ta k'oshi sannan yabarta.

Waya aka kirashi dan haka tatashi takoma part d'inta tagyara abunta sannan tazauna takira su Baba Malam a waya suka gaisa.


Tana cikin wayar Faruk yashigo daga gefenta yazauna har saida tagama sannan ya amshi wayar ya ajiye yace habibty shine kika gudo kika barni ko?
Murmushi tayi tace ba gudowa nayi ba.
Rungumeta yayi sannan yace toh me kikayi?.
Shuru tayi nan yasafke ajiyar zuciya sannan yace dan Allah Habibty ataimaka a ajiye kunyar nan dan ina buk'atar kulawarki sosai.
'Dagowa tayi takalleshi har ta bud'e baki zatayi magana sai kuma tafasa ganin haka yasa yakwantar da ita sannan shima yakwanta gefenta yadinga janta da hira tana d'an biye mashi.

Wajen azuhur sukayi wanka sannan yatafi masallaci ita kuma tayi sallarta a gida bayan ya dawo Nasiba tazo takirata sukayi lunch.


Da marece yafita dan haka suka samu damar zama ita da Nasiba suka sha hira sosai dayake Nasiba akwaita da son mutane nan da nan tasa Jawahir tasake da dare tare suka shiga kitchen sukayi girki duk yadda taso Jawahir tabarshi ammah tak'i saida takama mata sukayi.


Tun daga ranar tare suke girki breakfast ne kawai bata samun damar fitowa suhad'a tare saboda Faruk baya bari ahaka har suka cinye kwana ukkunsu a ranar da zai koma wajen Nasiba nan tace ta k'ara masu sucike sati guda dan a lokacin bata jin dad'in jikinta kawai dai bata nuna masu ba dan kar sutada hankalinsu, koda Faruk ya ji dad'in hakan ammah bai nuna mataba, a fili yanuna bai yarda ba saida tadinga lalla'bashi sannan ya amince yakoma suka ida sati gudansu yakoma hannun uwargidanshi inda yanuna ya yi missing d'inta sosai, ta ji dad'in ganin yadda yanuna mata ya yi missing d'inta.


*****
Zaman lafiya sukeyi sosai idan kaga Nasiba da Jawahir baka ta'ba cewa kishiyoyine dan suna k'aunar junansu suna mutunta juna, Faruk ko ya zage wajen kula da matanshi ko da sau d'aya baya yarda a fuska yanuna ga wadda yafi so saidai idan ya ke'be da matanshi ne yake nuna masu yadda yake k'aunarsu nan kowace hankalinta yakwanta ganin ta ciri tuta a wajen mijinta


*BAYAN WATA 'DAYA*

Kasancewar lokacin Hajji ne daman tuni ya biya masu batare da saninsu ba nan yad'auki matanshi sukaje aikin hajji.

Tunda sukaje Nasiba batada cikakkar lafiya ahaka tayi hajjinta saidai jawahir take kula da ita da mijinsu.

Sai da suka gama hajji sunje umrah sannan taga likita a chan ne yake sanar da su tana da shigar ciki na wata biyu nan su Faruk da Jawahir sukaita murna.

Bayan sun dawo ne suka cigaba da kula da ita dan Jawahir bata bari ko cokali tad'auke inda a 'bangaren goga Faruk ma haka duk motsin da zatayi sai sun tambayeta abinda yake damunta hatta abinci sai ta fad'i irin wanda za'a dafa.
Tana jin dad'in irin kulawar da suke bata da cikinta.


Watansu d'aya da dawowa suka shirya suka je kebbi lokacin cikin Nasiba yana wata ukku kwanansu biyu suka dawo gida.

Jawahir kanta ta samu nutsuwa sosai dan har k'iba ta yi koda su Baba Malam suka ga yadda take cikin kwanciyar hankali sai hankalinsu yakwanta, sunje gidan Khausar dan ita Rashida ta dawo gida saboda laulayin da takeyi.


Ranar wata litinin Jawahir tashigo parlor tasamu Nasiba zaune tana cin yalo gefenta Faruk ne zaune, zuwa tayi tazauna tana cewa Auntyna me kuma ake ci?
Murmushi Nasiba tayi tace kinganni nan wallahi yalo naji inaso shine oga yasiyo min.

'Daukar guda tayi tace bari inci wannan dan gaskiya ya biya raina.
Dariya Nasiba tayi tatura mata robar yalon tace kici iya cinki sister ni har ya fara isata tun d'azu nake ci.
Murmushi Jawahir tayi nan tace nagode Auntyna sannan tafara ci, kallon Faruk tayi tace Lovely (dayake itama sunan da take kiranshi da shi kenan) maimakon kasiyo har da d'ata ?
Murmushi shima yayi yace toh ai bakice asiyo makiba habibty Auntyn taki yalo kawai tace asiyo.

Ajiye yalon tayi tace ni d'ata nakeso Allah ban iya cin yalon.

Faruk kallon Nasiba yayi itama takalleshi sukai murmushi sannan tace 'yar k'anwata ko dai kin kamu ne kema?
Turo baki tayi tace ban kamu da komai ba Aunty kawai dai d'ata nakeso.

Murmushi Faruk yayi yace toh shikenan bari insa asamo maki ai duk zan iya da ku nan yad'akko wayarshi yakira megadi yafad'a mashi.

Mik'ewa tayi taje kitchen tad'aura masu girki daurewa kawai take dan kwana biyun nan itama ba isassar lafiya gareta ba......








_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:22 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 27*

Cikin Nasiba yana da wata hud'u lokacin aka fiddo da su Alhaji Sufyan daga gidan yari za'a ratayesu dan a lokacin shekararsu guda cif a gidan kaso, duk sunyi bak'i sun rame, a mota aka kaisu gidajensu dan suyi bankwana da iyalansu, Mummyn Nasiba a waya takirata dan taje ammah tace babu inda zata batason sake sakashi a cikin idanunta, nan tazauna tadinga kuka, Jawahir ganin yadda Nasiba take kuka yasa duk sai jikinta yayi sanyi duk'awa tayi gabanta tana hawaye tace dan Allah Aunty Nasiba kiyi hak'uri nasan ni najamaki da badan haka ba da duk haka bata faruba dan Allah kiyafe min.

'Dago kai Nasiba tayi takalleta cikin kuka tace wallahi ba laifinki bane Jawahir bakida laifin komai a ciki *SON ZUCIYA* ne da kwad'ayi suka ja ma Daddy ina nadamar kasancewarshi mahaifi agareni yanzu gashinan abinda yaja ma kanshi, ba wai ina kuka akan abinda za'ayi mashi bane kawai dai ina kuka akan mutuncinmu da yazubar mana yanzu shikenan kowa zai dinga kallonmu da abinda mahaifinmu ya aikata na tabbata yau dai ta kasance *RANAR NADAMA* agareshi ranar da bai ta'ba tunanin zata zo mashi ba saidai nadamar bazata ta'ba kasancewa mai amfani agareshi ba.

Jawahir ma fashewa tayi da kuka nan aka rasa me rarrashin wani saida sukayi me isarsu sannan sukayi shuru dan lokacin Faruk baya gida.


Su Alhaji Sufyan da Alhaji Mansur bayan ankaisu sunyi bankwana da iyalansu nan aka wuce da su wajen da za'a ratayesu su dukansu kuka suke sha'be sha'be kamar k'ananun yara, d'aura su akayi saman wani dogon gini aka rufe masu fuska sannan aka sa igiya aka rataye masu kai sasu akayi sukayi kalmar shahada sannan aka saki igiyar sukayo k'aya, ji kake k'yat alamun karyewar wuya nan sukaita wuntsila wuntsila da k'afafu har saida ransu yarabu da jikinsu.


________

Jawahir tunda tatashi yau dakyar tayi sallar asuba nan saman darduma tayi kwance dan ranar Faruk ba a d'akinta yakeba, wajen k'arfe shidda yashigo yasameta kwance ta k'udundune tana ta kwasar bacci wajen da take yanufo yana cewa Habibiti ba dai har yanzu bacci kike ba, ta'bata yayi yaji jikinta da zafi.
Rud'ewa yayi yace subhanallahi ba dai bakida lafiya ba.
Maganarshi ce tatasheta daga baccin da take nan tabud'e idanu dak'yar k'amshin turarenshi ne yadoki hancinta tayi saurin tureshi tamik'e tashiga toilet tafara kwarara amai.

Hankalin Faruk ya tashi sosai ganin yadda take amai kamar zata amaye 'yan hanjin cikinta gabad'aya ta galabaita tana gama aman taimaka mata yayi tai wanka tashirya sannan yafito da ita yace ma Nasiba zasuje asibiti Jawahir bata da lafiya hankalin Nasiba ya tashi sosai tace saidai suje tare.

Haka ko akayi atare sukaje wajen family doctor d'insu da yace susameshi a asibiti nan yadubata yaimata tambayoyi tabashi amsa sannan yarubuta mata tests yace taje ayi mata a lab.

Bayan sunyo sun kawo sakamako nan yake tabbatar masu da tana d'auke da ciki tsawon wata ukku, murna wajen Faruk da Nasiba ba'a magana dan ita ko uwar gayyar kunya ce takamata.

Haka suka dawo gida suna ta murna Faruk ko baki har kunne yana ta godiya ga ubangiji ganin matanshi dukansu ciki garesu Nasiba nata wata hud'u Jawahir kuma wata ukku.

Zuwa yayi yasanar da su Mom su ma sukaita murna nan tasamo masu wata mata tazo gidan tazauna tana masu girki da gyaran gida.
'Dakunansu da na mijinsune kawai basu bari agyara masu su suke abunsu.

Faruk ko indai yana gida toh yana manne da matanshi yana basu kulawa sosai duk abinda sukeso sai ya samo masu shi, kusan tare suke rainon cikin da shi.
Dan ma Jawahir nata ba mai laulayi bane sosai saisa take samun damar yin wasu ayyukan indai bai gida tare da ita ake girkin abinci.



Faruk d'aukarsu yayi yakaisu gidan Ummah suka ganta nan Ummah tayi ta kuka da taga jawahir tana rok'onta gafara Jawahir ta tausaya ma halin da taga ummah dan har lokacin 'barin jikinta d'aya shanye yake komai sai anyi mata har kuka jawahir tayi saboda tausayi tace ta yafe mata tad'auko kud'i masu yawa tabata.


*BAYAN WATA SHIDDA*


Cikinsu ya tsufa sosai dan a lokacin Nasiba nata yana cikin wata na goma ana sa ran haihuwa yau ko gobe inda Jawahir nata yake wata na tara.

Mummyn Nasiba ta so amaido mata Nasiba tahaihu a gida ganin abubuwan zasuyi mashi yawa mata biyu duk tsohon ciki garesu ammah Faruk yace a'a abarsu zai iya saidai Inna Mairo da tazo daga Kebbi tazauna tana kula da su gabad'aya dan cewa tayi da Nasiba da Jawahir dukansu d'aya ne a wajenta.

Yau tun da Nasiba tatashi take fama da ciwon mara haka suka fito zasuyi breakfast daurewa kawai takeyi bata bari sun ganeba kasa cin komai tayi chan da taji cikinta ya wani irin juya mata nan tafara cize le'be.

Ganin haka yasa duk hankalinsu yatashi Faruk yayi saurin yo inda take yana tambayarta lafiya.
Jawahir ma saurin mik'ewa tayi tanufi wajenta cikin tashin hankali tana cewa Aunty me yake damunki ko jikin ne?
Girgiza kai tafara yi cike da juriya tace wayyoo cikina.
Faruk rasa yadda zaiyi yayi nan yakwala ma Inna Mairo kira cikin sauri tazo ganin halin da Nasiba take ciki yasa tace haihuwa ce yayi maza yakaita asibiti.

'Daukarta yayi chak yafita da ita jawahir da take ta faman kuka zuwa tayi tad'akko jikkar kayan haihuwar da aka tanada lokacin da tafita Faruk har yasakata cikin mota nan ya amshi jakkar yace takoma gida.
Cikin kuka tace ita dai saidai suje tare bazata zauna ba.
Kallon inna Mairo yayi yace takula da ita bari suje nan yashiga mota yajata dagudu yanufi asibiti da Nsiba da take kwance tana ta salati.

Yana isa Hajiyar Nasiba ta isa a daidai lokacin nan aka wuce da ita labour room Nasiba duk ta fita hayyacinta sai zufa takeyi.
Nan su Faruk da Hajiyar Nasiba sukayi cirko cirko suna jira.



Jawahir ko tunda suka koma cikin gida kasa tsaye da zaune tayi dan hankalinta ya tashi sosai akan halin da taga Nasiba a ciki, inna mairo lalla'bata tadinga yi dan takwantar da hankalinta saboda tsohon cikinta ammah tak'i kiran Faruk tadinga yi a waya tana tambayarshi halin da Nasiba take ciki ko ta haihu saidai yace a'a sudai cigaba da mata addu'a.

Sai wajen k'arfe d'aya sannan Nasiba tahaifo shantalelen d'anta jajir da shi sak Faruk nan su Faruk da Mummyn Nasiba suka dinga murya har da su Yaya Sadiya da su ma sunzo asibitin.

Faruk kiran jawahir yayi a waya yafad'a mata nan tadinga murna sannan yakira su Mom yasanar da su.

Wajen k'arfe biyu aka sallamesu bayan antabbatar da lafiyar me jego da ta baby.

Mummyn Nasiba ta so tawuce da ita gida ammah Faruk yace a'a dan haka tayarda suka koma gidanshi.

Suna isa Jawahir ce tafara zuwa dagudu ta amshi yaron tarungume tana murna sannan tayi ma Auntynta ta barka.
Nasiba d'akinta tawuce takwanta kafin ruwan zafin da su Inna Mairo suka d'aura yadafu.

Duk wanda yazo saidai yakalli baby a hannun Jawahir dan kamashi tayi tarik'e yaron ya shiga ranta sosai, su Inna Mairo saidai suka dinga mata tsiya suna cewa itama ai sai takawo masu kamarshi tunda haihuwartata yau ko gobe ne.

Su Mom duk sunzo barka a ranar gidan cika yayi da jama'a.
Wajen k'arfe biyar Jawahir tazame kanta takoma d'akinta dan daman tun da aka tafi da Nasiba asibiti tafara jin ciwon mara kawai dai tana daurewane ammah a lokacin taji abun ya k'aru a k'asan kafe tazauna nan tafara murk'ususu tayi kusan minti talatin a nan Inna Mairo tashigo tasameta a wannan halin duk ta jik'e sharkaf da zufa, hankalin inna mairo ya tashi sosai tatambayeta abinda yake damunta ammah jawahir takasa cemata komai saidai gefen mararta da take nuna mata nan Inna Mairo tagane nak'uda ce takeyi cikin sauri tafita taje part d'un Faruk tasanar dashi.

Nan yafito a rud'e yazo yad'auketa da inna mairo sukaje asibiti duk wannan abun su Nasiba basu saniba suna chan part d'inta da jama'a 'yan zuwa barka.

Suna isa asibiti aka kar'beta aka shiga da ita labour room ana gama sallar magrib tahaifo shantalelen d'anta, nurses suka fito suka sanar da su Faruk nan yad'aga hannu yaita godiya ga ubangiji akan kyautar da yayi mashi ta 'ya'ya biyu a rana guda, kawo mashi d'an akayi shima kyakkyawa da shi yana kamashi da shi waya yad'akko yakira Nasiba yafad'a mata.

Da fari bata yarda ba saida yarantse mata nan ita da 'yan barka akaita mamakin haihuwar jawahir, su mom yakira basu d'au lokaci ba suka iso asibitin.

Faruk jin abun yake kamar a mafarki wai shine da yara biyu a rana guda.

Sai bayan sallar isha'i aka sallamesu suka koma gida nan ma aka kafa wata sabuwar murnar.
'Yan barka santin yaran suka dinga yi ganin kamanninsu guda da yanayin jikinsu duk na mahaifinsu ne idan ba amfad'a makaba sai kace 'yan biyu ne mutum d'aya yahaifesu.

Dad da Mom ma sunyi farin ciki sosai ganin rana guda sun samu jikoki har biyu.

Faruk ko da ka kalleshi kasan yana cikin farin ciki kasa zaune da tsaye yayi, Inna Mairo ce tagyara maijego sannan tasata taci tuwon da aka girka masu.



Gida kullum cike yake da mutane 'yan barka kowa yana farin cikin k'aruwar da aka samu, Dad kud'i yafitar sosai yaba Mom taje dubai tasiyo ma yara kaya duk iri d'aya sannan aka siya ma masu jego kaya kowa akwati biyu.

Ranar suna Faruk ya yi bajinta dan kud'i yafitar sosai akayi hidimar suna da su, inna mairo ita takeyi ma jarirrai da masu jego wanka, shiga iri d'aya Jawahr da Nasiba sukeyi a zaman barka hatta jarirran ma haka.

Ranar daren suna Faruk yakira matan nashi a part d'inshi yatambayesu sunan da suke so asa ma yaran, Nasiba ce tayi saurin cewa tana so asa ma nata sunan mahaifin Jawahir.
Jawahir saboda mamaki kasa cemata komai tayi saidai hawaye da suke fita daga idanunta daga k'arshe tasafko k'asa tadurk'usa tare da rik'o hannun Nasiba tana mata godiya.
Nasiba tace bakomai ta cancanci fiye da hakan a wajenta.
Shi kanshi Faruk ya ji dad'in hakan da Nasiba tayi nan yatambayi Jawahir sunan da ita takeso asa ma nata.
Itama tace sunan mahaifin Nasiba, nan Nasiba tace bata yarda da hakan ba bataso asa sunan mahaifinta dan bai cancanci hakan daga jawahir ba nan tanemi alfarma da jawahir tabarta taza'ba mashi suna
Jawahir amincewa tayi Nasiba taza'ba mashi sunan Dad.

Faruk ya ji dad'in haka yai masu godiya sannan yad'akko makullan mota yadamk'a masu kowa da tashi suma sukayi godiya.


Baba Malam shanu biyu ya aiko masu da su inda Dad yasiyo manyan raguna biyu ya aiko da su.

Ranar suna yara suka ci suna Muhammad da Sani inda Muhammad ake kiranshi da Affan, Sani kuma suna kiranshi da Ameer, anyi shagali sosai ankashe kud'i abun sai sambarka dan shiga iri d'aya masu jegon suka dinga yi yaran nasu ma haka mutane dadama sunyi sha'awar yadda kishiyoyin biyu suke tafiyar da rayuwarsu da k'aunar da suke nuna ma junansu.
Faruk ko ji yake kamar ya fi kowane namiji sa'ar samun mata.

Bayan angama hidimar suna anwatse nan Inna mairo tacigaba da kula da masu jego da yaransu, gyara tadinga yi masu na mutunci yadda zatayi ma Jawahir haka takeyi ma Nasiba bata barinsu suke'be da mijinsu har saida suka yi arba'in sannan tatattara takoma garinsu tare da sha tara na arzik'i da tasamu daga wajen Faruk da matanshi hatta mummyn Nasiba da su Mom saida sukayi mata kyauta me tsoka.


Faruk hankalinshi kwance yana kula da matanshi sosai gefe guda ga yaransu da suke ta girma sun taso da ka gansu ka ga tagwaye dan komai iri d'aya akeyi masu kamanninsu sai k'ara komawa take sak ta mahaifinsu.

**** ******

Dad yana kula da companynshi da na jawahir sosai nan sukaita k'ara ha'bbaka kud'ad'e suna shigowa yadda yakamata, tura ma jawahir kud'inta yake ta account d'inta baya cin ko naira d'aya ko da tana cewa yadinga d'ibar kasonshi ammah yace a'a baida kaso a ciki na companynshi ya isheshi dan haka tadinga tura ma su Baba Malam tatura ma Baba Musa kud'ad'e sosai yasa aka gyara masu gidansu.
Cikin kud'in tafidda wani kaso da fili tadamk'a ma Nasiba nan Nasiba tayita mata godiya har da kuka.

Sannan tasa aka gina masu wani k'aton boutique wanda akayo masu order kaya a chan dubai duk wasu kaya na gani na fad'a anzuba su a tantsamemen boutique d'in da yaci suna *FANAJ BOUTIQUE* wanda aikin Jawahir ne nan su Nasiba da Faruk sukaita jin dad'i.


*BAYAN SHEKARA 'DAYA DA WATA BIYU*

Nasiba ce zaune a babban parlornsu inda gefenta Ameer da Affan ne suna ta wasa da kayan wasan da aka baje masu, duba lokaci kawai take kasancewar darene, Jawahir ce tashigo parlorn babu ko sallama sanye da hijab da alama daga anguwa suke, zama tayi saman kujera batare da ta ce ma Nasiba komai ba ganin haka yasa Nasiba hankalinta yatashi tace lafiya Sis me yake faru tun d'azu ina nan ina jiranku kudawo daga asibitin ko jikin ne?
Hawaye ne suka gangaro ma Jawahir.
Mik'ewa Nasiba tayi takomo kusa da ita tana cewa lafiya Jawahir kifad'a min abinda yafaru kinga hankalina ya tashi.
Tun kan tayi magana su Ameer suka nufo wajen dagudu suka fad'a jikin Jawahir cikin maganarsu da bata fita sosai suka ce Ammi kin siyo mana chocolate d'in?
Nasiba ce tarik'osu ganin suna neman haye Jawahir tace kunga Ammi batada lafiya kubarta.
Affan ne yaturo baki yace uhm uhm Ummi.
Murmushi Nasiba tayi tace ni bari inbaku chocolate d'in, nan tajasu taje tad'akko masu a part d'inta sannan suka zauna suna sha suna wasa.
Kusa da Jawahir takoma tana cewa kiyi min bayanin abinda yafaru Sister.
Shigowar Faruk ne yasa duk suka juya suka kalleshi Nasiba tace yauwa gaka wai me yake faruwa ne dan Allah me likita yace yana damunta.
Murmushi Faruk yayi tare da mik'a mata takardar hannunshi yace k'aruwa muka samu.
Saurin amsa tayi tana dubawa tayi saurin rungume jawahir tana cewa Alhamdulilah Sis ashe mun samu baby har na tsawon wata biyu wayyo dad'i.
Fashewa da kuka Jawahir tayi cikin kuka tace wallahi ba'a kyauta min ba duka yaushe na haifi Affan ko yayeshi banyi ba sai ace ina da wani cikin.

Nasiba kallon Faruk tayi sukai murmushi sannan tace toh menene Sister ai ba wani abu bane.
Wallahi wani abune Aunty Nasiba duka nawa nake da za'a ce ina da ciki na biyu kuma kema ai da sai yayi maki inda ta tsakani ga Allah yabi.

Faruk da Nasiba dariya ce take cinsu, yadanne tashi yace toh ai itama yi mata zanyi kikwantar da hankalinki.
Mik'ewa tayi tana turo baki tace ai da yi mata zakayi kamar yadda muka haihu tare wannan karon ma sai kayi mata,,, tana fad'in haka tawuce fuuu tanufi part d'inta.

Nasiba da Faruk ko me zasuyi inba dariya ba Nasiba tace ina ruwan Jawahir da wauta.
Tsagaitawa yayi da dariyar da yake yace toh kin dai ji abinda tace kema inyi maki kusake haihuwa tare.

Zaro idanu Nasiba tayi waje tace karufa man asiri Lovely idan nima nayi cikin wa zai kular mana da su Affan? Juyawa tayi takallesu taga har sunyi bacci a saman carpet d'in tace kaga tashi muje katayani d'aukarsu inkaisu d'aki inyaso sai kaje chan kayi ta lallashi dan ka yi laifi.

Mik'ewa yayi yace kedai bari hearty akwai aiki agabana.
Dariya tayi tad'auki Affan shi kuma yad'auki Ameer suka nufi part d'inta, saida tawanke masu hannu sannan takwantar da su a saman gado dan dama tuni ta yi masu shirin bacci tazauna jiran dawowarsu Faruk, itama tahau takwanta, daga gefenta Faruk yazauna yace hearty ba dai bacci zakiyi tun yanzu ba duka fa yanzu tara tayi.
Hamma tayi tace wallahi Lovely yau d'in ne jina nake duk wata iri kamar banda lafiya.
Kwantar da kanshi yayi a saman k'irjinta yace Hearty ko dai kema kin kamu?
Zaro idanu tayi waje tace karufa min asiri ni banda komai.
Murmushi yayi yace toh inma akwai ya kuka iya tunda kuna tare da lafiyayyen miji ni ai abun farin ciki ne agareni kuyi ta haifa min 'yan tagwaye.
Turo baki tayi tace nidai a'a.
Bakinshi yasa yaciji le'benta ahankali yace kedai Eh Hearty,
Kallon agogo tayi tace dan Allah katashi kaje kaji da 'yar uwata ka barota ita kad'ai.
Tallabo fuskarta yayi yace wai da ingama ji da ke kafin inje,,yafad'a yana kashe mata ido guda.
Tureshi tayi daga jikinta tatashi zaune tace dan Allah lovely katafi ka ga ka barta ita kad'ai gashi batada lafiya.
Shafa cikinta yayi yace kema d'in ai bakida lafiya.
Uhm uhm ni lafiya ta lau,, tafad'a tana ture mashi hannu.
Tallabo fuskarta yayi yamanna mata kiss a baki, nan takoma takwanta, shafa kanta yayi yace zan tafi Hearty sai dasafe.
Murmushi tayi tace Allah yakaimu masoyina abun alfaharin mu,, tana fad'in haka tayi saurin juya mashi baya dan tasan idan ba haka tayiba bazai barta ba, tana jinshi yabata peck a kumatu tare da cewa ina sonki sosai matata kikular min da kanki.
Murmushi kawai tayi batare da ta ce komai ba nan yakalli yaran nashi da suke ta bacci sannan yakashe masu fitala yafita yabar d'akin.



Part d'inshi yawuce yafara yin wanka saida yashirya cikin shirin bacci sannan yafito yanufi part d'in Jawahir yana zuwa yasameta kwance saman gado ta lumshe idanunta ammah daga ganin yanayinta ba bacci take ba, zama yayi a gefen gadon yakai hannu yashafa fuskarta sannan yace taya masoyiya zatayi fushi da masoyinta dan kawai Allah ya basu kyautar da ba wanda zai iya basu ita idan ba shi ba,
Ahankali tabud'e idanunta takalleshi sai kuma tajanye fuskarta gefe.
Ajiyar zuciya yasafke yace Habibty kinsan dai banason ganinki a wannan yanayin dan Allah kifad'a min menene laifina a ciki.
Turo baki tayi cikin shagwa'ba tace toh ba kaine kayi min ciki ni kad'ai ba bayan wanchan karon tare da Aunty Nasiba muka haihu.
Dariya ce take cinshi ammah yadanne dan kar yayi wani laifin sannan yace toh ai kece kin fita zalama saisa kika rigata samun ciki.
Kallon rashin fahimtar inda maganarshi tadosa tayi mashi tace me kake nufi da hakan? Wane irin zalama nafita?.
Ganin bata ganeba yasa yace babu komai itama ai tana da nata cikin ba wai ke kad'ai nayi mawa ba.
Saurin tashi zaune tayi cike da jin dad'i tace dan Allah dagaske kake lovely.
'Daga mata gira yayi nan tafad'a jikinshi tare da rungumeshi tace na ji dad'i sosai Lovely.

Shima rungumeta yayi yace dan Allah Habibty kuyi hak'uri da yanayina ina son 'ya'ya sosai in son samune kuyi ta haifa min su dayawa.
Ajiyar zuciya tasafke tace kayi hak'uri lovely nasan ban kyauta maka ba da fushin da nayi akan kyautar da ubangiji yabamu dan Allah kayafe min
'Dago kanta yayi yakalli cikin idanunta sannan yace babu komai Habibty ai ku d'in baku laifi ina k'aunarku fiye da tunaninku nidai fatana kucigaba da nuna min k'auna da tarairaya.

Zaka samu fiye da hakan ma Lovely, ina sonka so na gaskiya wanda ni kaina bazan iya misulta shi ba bana ji zan iya son wani kamar yadda nake sonka.
Tun kan tarufe baki yace kina nufin har Umar?
Murmushi tayi tare da komawa takwanta tace tabbas nasan na so Yaya Umar saidai son

Please Login or Register in order to submit comment