Reading FANSAR RAI complete 1&2 BY SIS NERJA'ART Chapter 30 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita.

K'walla ce tacika mata idanu tace toh ya zanyi wallahi ina tausayin Jawahir sosai kuduba kuga mahaifinmu ne yajefata halin da take ciki na rashin duk wani makusanci nata hatta mijinta, ya zanyi idan bance ta auri Faruk ba, bamusan halin da take ciki ba koda ace bata nuna a fili ba ansan akwai damuwa acikin ranta, sannan duk abinda mahaifinmu yayi mata hakan baisa tak'i mu ba dan tasan ba mu mukayi ba, wallahi duk irin k'aunar da nakeyi ma Faruk zan iya hak'ura ya auri Jawahir domin ita d'in mutuniyar kirki ce, nidai dan Allah kusa albarka a cikin auren nan kar kusakar min da gwiwata a lokacin da nake sanar da ku aikin ladan da zanyi.

Su dukansu jikinsu sanyi yayi nan sukayi masu Allah yasa alkhairi, Mummy ta jinjina ma halin d'iyartata dan bata ta'ba tunanin hakan ba saboda Nasiba tana da kishi sosai.

Nan tayi masu wuni sai dare Faruk yazo d'aukarta suka koma gida.





Bayan sati biyu da sa bikkin Nasiba ta amshi kud'ad'e wajen Faruk taje da kanta tafara had'a ma Jawahir lefe kaya na gani nafad'a masu tsada tahad'a mata komai da zuciya d'aya batare da tasa mugunta ba akwatuna takwas Faruk yace tahad'o mata, wasu kayan duk irin nata ne taza'bo mata hakan da tayi ya k'ara mata k'ima da daraja a idanun mijinta da surikkanta nan Faruk yabata kud'ad'e sosai yace tayi hidima da su itama.
Godiya tayi mashi sosai.



A chan 'bangaren su Jawahir ko duk wani shirye shirye da ake yi ma Khausar da Rashida yanzu anhad'a har da ita akeyi tun ana saura wata guda bikki aka fara masu gyara musamman ma ita da akasan ta ta'ba aure, yaunzu gabad'aya ta mik'a lamurranta ga Allah kullum addu'arta d'aya Allah yatabbatar mata da alkhairi a cikin rayuwarta, gefe guda kuma ta sha ta'boye kanta taci kuka batare da sanin kowaba, ga wata irin kunyar su Mom da takeji yanzu indai ba su suka kirata aka gaisaba bata kira shima bakamar da ba yanzu bata sakewa suyi hira.

Faruk ko ya kira bata d'agawa saidai idan message yaturo mata sannan tamaida mashi reply hakan yana ba Faruk mamaki sosai dan hakane yashirya yaje Kebbi a motarshi a waya yasanar da ita zai zo dan haka Jawahir tafara shirin tarbarshi, Baba Nura tafad'a mawa shi kuma yasanar da su Baba Malam sukace Allah yakawoshi lafiya.

Ranar asabar tun da safe da tatashi tashiga kitchen tafara girki Khausar ce tazo tana tayata fried rice suka shirya mashi wadda tasha had'i sannan sukayi mashi pep chicken da kunun aya .
Wajen k'arfe d'aya sun gama nan taje tayi wanka tun tana girkin hankalinta yana wajen Faruk tana so takirashi taji yanayin tafiyar tashi bare da yasanar da ita a mota zai zo, har waya tad'auko zata kirashi sai kuma tafasa.
Cikin kayan da yayi mata da zata dawo kebbi tad'auko wata shadda gown brown tasaka wadda tasha aiki da pink d'in zare, ita tazauna tayi kwalliyarta.

Tana zaune saman darduma bayan ta gama sallar azuhur sai ga kiran Faruk ya shigo.
Saurin d'auko wayar tayi tazuba mata idanu tana kallo har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama.
Amsa mata yayi sannan yace kifito ganinan na iso.
Har zatace mashi yashigo nan yakashe wayar dan haka tamik'e tad'auke darduma saida tak'ara gyara fuskarta tad'akko pink d'in gyale tayafa sannan tafito tanaso tashiga 'bangaren su Khaisar tace tafito tarakata sai tajiyo hayaniya a cikin gidan alamun kowa yana nan ita kuma ga kunya bataso tahad'u da 'yan cikin gida dan haka tasamu Inna Mairo tafad'a mata ya iso.
Inna Mairo tace toh taje tashigo da shi kanta sunkuye a k'asa tafita.
Faruk da ke zaune cikin mota ya zuba ma k'ofar gidan idanu dan ganin ta inda zata fito dan a lokacin su Baba Malam basu nan ba kowa a wajen, idanunshi a kanta tafito har ta iso wajen motar ta shi taja tatsaya tare da yin sallama.


Amsawa yayi tare da bud'e mata k'ofar gaba yace tazagayo tazauna.
Sai a lokacin tad'ago takalleshi sanye yake cikin manyan kaya ya yi kyau sosai da har zatace mashi a'a ganin yadda yatsareta da idanu yasa bata musaba tazagaya taje tashiga tabar k'ofar a bud'e, gaishe shi tayi maimakon ya amsa sai cewa yayi shine ko kikirani kiji yanayin tafiyar tunda natafo ko.

Shuru tayi dan ita kanta ta san bata da gaskiya.
Ta cikin mirror yake kallonta ganin batada niyar d'ago kanta bare tayi magana yasa yace Jawahir nuna rashin kulawar da kike min bana jin dad'inshi idan kina haka sai inga kamar baki sona, tilasta maki akayi sai kin aureni ko?
Shuru tayi nan ma tana wasa da yatsun hannunta.
Juyowa yayi yakalleta yace indai har baki sona kifad'a min Jawahir wallahi sai inhak'ura ba wani abu bane sai inbarki ki auri wanda kikeso dan nima kaina bazanso kiyi auren da bakiso ba.

Sai a lokacin tad'ago kai takalleshi idanu cike da k'walla tace Yaya Faruk ba wai bana sonka bane ka cancanci insoka ko dan saboda alkhairin da kayi min da taimaka man da kayi a lokacin da nake buk'atar taimako bazan ta'ba kasancewa butulu agareka ba ko da ace wanine na daban kakawo kace in aura ni me biyayya ce agareka bazan ta'ba baka kunya ba, kawai dai banason zama da Aunty Nasiba a matsayin kishiyarta ne sai inga kamar banyi mata adalciba kamar na so kaina dayawa, wannan dalilin ne yasa kaga na kasa sakewa hankalina ya k'i kwanciya.

Wani irin sanyi yaji a ranshi nan yasafke ajiyar zuciya sannan yace Jawahir idan dai har kina sona to dan Allah kidaina shareni kisaki jikinki da ni Nasiba kuma batada matsala wallahi itace ma tagoya min baya in aureki na tabbata zata zauna da ke lafiya domin ita d'in mutuniyar kirkice ba irin mahaifinta ba, ina sonki jawahir ina fatan kema zaki taimaka kisoni.

Murmushi ne yasu'buce mata ahankali tace nagode Yaya Faruk.
Idanu yazuba mata yace bakice komai ba zaki so ni ko?
Saurin fita tayi daga cikin motar tace kashigo kagaisa da Inna Mairo kafin su Baba Malam sudawo daga wajen jana'izar wani abokinshi da ke nan bayan layinmu sunce bazasu dad'eba.

Murmushi Faruk yayi batare da ya ce komai ba yabud'e motar yafito nan tawuce gaba yana biye da ita a baya suka shiga cikin gida.

Gaisawa sukayi da Inna Mairo cikin girmamawa daga nan Jawahir tawuce kitchen takawo mashi abinda tatanadar mashi, tana gama ajiyewa tazuba mashi yace saidai tazauna suci tare indai ba haka ba bazai ciba.
Marairaicewa tayi tace dan Allah Yaya Faruk kaci ni na k'oshi.
'Dauke kanshi yayi yace shima bazai ciba duk yunwar da yakeji zai hak'ura sai ya koma gida sannan zai ci.

Tana jin haka tazauna k'asa tare da jawo plate tana zubawa yana kallonta tana turo baki ahaka tad'an zuba rabin plate.
Murmushi yayi sannan yasafko k'asa shima nan yafara cin wanda tazuba mashi, lumshe idanu yayi yace ashe amaryar tawa itama ba bayaba wajen iya girki.
Murmushi tayi sannan tafara cin wanda tazuba ma kanta.

Suna cikin ci sukaji sallamar su Baba Malam Jawahir d'aukar plate d'inta tayi cikin sauri tanufi bedroom dan kar sushigo suganta.

Faruk dariya yayi nan suka shigo suka gaisa da shi sannan suka bashi waje yakimtsa cikinshi.

Bayan ya gama ne yafita suka sake gaisawa sannan yafiddo tsarabar da yazo da ita cikin boot yasa aka shiga da ita cikin gida.
Har sukayi sallar la'asar baiga fitowar Jawahir ba dan haka yakirata a waya yace tafito suyi bankwana tafiya zaiyi.

Kiran Khausar tayi a waya dan tafito sugaisa da shi dan ta san halin Khausar indai har yatafi basu gaisaba sai ta sha tsegumi wajenta.

Tare suka fito da Khausar suka sameshi tsaye wajen motarshi nan suka iso Khausar tagaisheshi.
Amsawa yayi cikin sakin fuska yace ya gida khausar?
Lafiya Lau Yaya Faruk, ya su Mom?
Duk suna lafiya lau, kallon Jawahir yayi sannan yace ina fata dai kina kula min da matata.
Saurin d'agowa Jawahir tayi takalleshi nan yad'aga mata gira.
Dariya Khausar tayi tace ina kula da ita sosai angonmu, dan bana barin kowa yakalleta bare yasamu damar yi mata magana.
Murmushi yayi yace gaskiya na ji dad'in jin haka daga gareki nagode sosai Khausar bari inbada tukuici, nan yasa hannu a aljihu yad'auko bandir d'in 'yan 500 yamik'a mata.
Amsa tayi cikin jin dad'i tayi godiya sannan takoma gida tabasu waje dan suyi bankwana.
Tana wucewa Faruk yace Jawahir ya kamata kisake kidaina wannan kunyar taki dan gaskiya tana cutar da ni kwatakwata baki bani kulawa ko waya baki bari muyi hakan baya min dad'i.
Batare da ta d'ago ta kalleshi ba tace toh zan gyara.

Yauwa kokefa, mota yabud'e yafiddo wata leda wadda duk kud'i ne a ciknta yamik'a mata yace ga wannan kinyi hidima da su.
Girgiza kai tayi tace a'a kabarsu akwai kud'i a account d'ina.
Ban damu da kud'inki ba wannan ni nabaki, kinsan dai bana son gardama.

Amsa tayi taimashi godiya.
Yace bakomai yanzu dai bari inwuce kar inyi dare.

Toh Yaya Faruk nagode agaishe da su Mom da Su Aunty Nasiba.
Insha Allahu zasuji idan na isa zan kiraki waya salan kik'i d'auka kamar yadda kika saba min, Allah had'aki zanyi da Baba Malam.
Ahankali tace kayi hak'uri zan d'auka.
Shiga motar yayi yace Allah yasa.

Bakuyi bankwana da su Baba Malam ba,,, cewar jawahir da take kallonshi.
Duba agogo yayi yace munyi bankwana suna tafiya ma kika fito daga cikin gida, yauwa ban tambayeki Event d'in da zakiyi ba dan idan za'a kawo lefe nakeso in aiko maki da Invitation Card d'inki saboda zan d'anyi tafiya workshop kwana biyu.

Girgiza kai tayi tace babu abinda zanyi walima ce kawai zanyi itama a makaranta.
Murmushi yayi cikin ranshi ya ji dad'in hakan dan shi daman ba mutum bane meson party saisa koda Nasiba ma batayi ba ya ji dad'i, yace shikenan zan sa abugo maki ko inturo kud'i Baba Nura yabugo a nan garin.

Amsawa tayi da toh nan tayi mashi godiya.
Kallon cikin idanunta yayi yace baza'a fad'a min magana me dad'i ba wadda zata tayani hira acikin mota tunda ni kad'ai ne.

Janye idanunta tayi cikin jin kunya tace Allah yakiyaye hanya Allah yamaida mana kai gida lafiya.
Amsawa yayi da Ameen sannan yace baki fad'a min kina sona ba.
Saurin juyawa tayi cikin jin kunya tashige gida.

Dariya yayi sannan yatada mota yakama hanyar Katsina.


Gudu yadinga yi da motar sosai ba shi ya isa ba sai dare.

________


Tun daga lokacin yake samun damar yin waya da Jawahir dan yanzu tana d'aga wayarshi idan yakirata cikin dabara yasamu tasake suka dinga hira sosai dan a kullum sai yakirata kusan sau ukku a rana ammah baya kira agaban Nasiba, a gefe guda kuma yana ba matarshi kulawa sosai babu abinda zata nema tarasa a wajen mijinta wannan dalilin ne yasa Nasiba tak'ra kwantar da hankalinta.


Ana saura sati ukku bikki aka kai lefen Jawahir inda Dad yad'auki nauyin kayan d'akinta yace shi zaiyi dan alk'awali yayi ma kanshi ko da ace ba Faruk zata aura ba shi zaiyi mata kayan d'aki saboda zaman mutuci da amana da yayi da mahaifinta zai iya cewa shine silar d'aukakar kamfaninshi, ya dai barsu da kayan kitchen d'inta.

Nan su Baba Malam sukaita mashi godiya tare da addu'a itama Jawahir ta ji dad'in hakan sosai nan tasake saka ma ranta zata zauna da d'ansu da matarshi lafiya ko dan irin soyayyar da mutanen nan suke nuna mata.


Barr Faruk ya je workshop a Abuja saida sukayi sati biyu sannan suka dawo tare da matarshi yaje suka safka a hotel.


Ana saura sati d'aya bikki suka dawo lokacin Dad har ya zuba ma Jawahir kayan d'akinta a part d'inta da zata zauna, set biyu yayi mata na bedroom sai na parlor set d'aya ya kashe kud'i sosai kamar yadda zaiyi ma 'yar cikinshi.


*BAYAN SATI 'DAYA*

Su Baba Malam sunyi k'ok'ari sosai wajen saya ma su Khausar da Rashida kayan d'aki set guda guda sai kayan kitchen.

Inda ita kuma Jawahir akayi mata kayan kitchen nagani na fad'a saboda ita ba'a siya mata kayan d'akiba saisa nata duk sukafi kyau da tsada.

Baba Nura ne yabugo masu invitation card me d'auke da sunayen amaren su duka ukku wanda suka dinga gayya da shi walima ne kawai zasuyi a islamiyyarsu sai kuma yinin bikki da za'ayi daga nan kowace amarya atafi da ita gidanta.


'Yan uwa da abokan arzik'i duk sunzo dan gudanar da bikki nan Baba Malam yaware shanu biyu aka yanka dan ayi hidima da su, amare suna shan gyara sosai nan da nan suka canza dan ita kanta Inna Mairo ba'a barta a bayaba wajen gyara 'yan jikokin nata gyara tayi masu irin nasu na 'yan zamfara.

Yau ma bayan ta gama tsuma Jawahir tana kwance saman gado inda tabar su Khausar suka fita dan suje suyo masu abubuwan da zasu raba wajen walima gobe, wayartace a hannunta tana chart da Faruk nan Inna Mairo tashigo da wata leda tazauna bisa gadon sannan tad'akko wata gumba a ciki tamik'a mata tace tashi kici wannan.
Kallon gumbar tayi ta'bata rai tace ni fa Inna na gaji da 'yan ciye ciyen nan.
Rik'e baki inna tayi tace yau Allah ya had'ani da shashashar yarinya ke ana so agyaraki miji yajiki zam ammah ke bakiso ko mancewa kike da gidan kishiya zakije?
Tashi Jawahir tayi ta amshi gumbar tana turo baki nan tafara ci, ji tayi da dad'i dan haka tacigaba da ci saida taci kusan rabi sannan Inna Mairo ta amsa tace tabarta haka.
Komawa tayi takwanta tana cigaba da chart d'inta.

A account d'inta Faruk yaturo mata kud'i yace tak'ara dan yasan wad'anda yaturo mata bazasu isheta ba godiya tayi mashi.



A chan Katsina ko ba wata hidima akeyi sosai ba dan wannan karan ba sosai sukayi gayya ba saboda a ganinsu kamar za'a takura mutane tunda duka yanzu baifi wata shidda da yin wanchan bikkin ba, Malam ne yabada shawarar hakan saisa.

Mummyn Nasiba da su Yaya Sadiya sunje har gida sunyi ma su Mom Allah yasa alkhairi.

Itako uwar gayyar ba'a magana dan ita tabugo IV taba Barr Nass yagayyaci abokansu, gefe guda kuma tabada aka d'inka ma ango kayan da zaisa na d'aurin aure.

Ran asabar wajen k'arfe goma su Dad da abokanshi biyar sai Faruk da abokanshi da Malam suka shiga jirgi suka je Kebbi dan da k'arfe sha d'aya za'a d'aura aure.


Amare sun sha kyau sosai su dukansu da ka kalli fuskarsu zakaga a kumbure duk sun sha kuka Khausar ce me d'an dama dama daga cikinsu.

Wajen k'arfe sha d'aya aka d'aura auren Faruk Sani Maishadda da amaryarshi Jawahir Muhammad Maikud'i, Sai Khausar Musa Maisalati da Mansur Abba sannan Rashida Jamilu Maisalati da angonta Aminu Umar.

Jama'a da dama sun samu halartar d'aurin auren tun daga mutanen Kebbi da ma wad'anda ba na kebbi ba.

Ana d'aura aure su Faruk suka koma masaukin da aka safkesu shi da abokanshi biyu inda su Dad da sauran abokan suka koma Katsina.



Jawahir ganin yadda gidan yacika yasa tasulale takoma cikin bedroom d'in Inna tayi zamanta ita kad'ai dan hayaniyar taji bata so.

Tana zaune ta buga tagumi nan Faruk yakirata waya, kallon wayar tayi kamar bazata d'auka ba sai kuma chan tad'auka batare da ta ce komai ba.
Daga chan 'bangaren Faruk yayi sallama yace ya dai amaryata ina fatan kina lafiya?.
Cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace lafiya lau.
Runtse idanunshi yayi cikin nuna damuwa yace oh my god jawahir ba dai kuka kike ba?
Shuru tayi nan yasafke ajiyar zuciya yace dan Allah kidaina 'bannatar min da hawayenki My Jawa kinga yau ranar murna ce agaremu kicire kowace damuwa acikin ranki kinga and'aura aure yanzu andamk'a min amanarki insha Allahu zan baki duk wata kulawa da tadace dan zan nuna maki ni d'in me k'aunarki ne zan mantar da ke duk wata damuwa da kike cikinta dan Allah Jawahir kisama min gurbi acikin zuciyarki ko yayane.
Runtse idanunta tayi nan hawaye suka fara gangaro mata tana jin maganganunshi har cikin kwanyar kanta.
Jin ta yi shuru yasa yace shikenan Jawahir bari inbarki kar incika ki da surutu ni zan nema ma kaina matsugunni a cikin zuciyarki da sannu zan koya maki sona, kihuta lafiya.

Tana ji ya kashe wayar janye wayarta tayi tad'aura saman k'irjinta batare da ta bud'e idanunta ba nan hawaye suka cigaba da fita.

Tana cikin haka Inna Mairo tashigo tasameta a gefenta tazauna tafara lallashinta har tasamu tayi shuru sannan tad'auko wani tsumi tabata tace ga wannan kisha
Wani irin haushi Jawahir taji dan har ta fara gajiya da abubuwan da Inna Mairo take d'irka mata babu yadda ta iya ta amshi tsumin tafara sha jinshi tayi da dad'i ba kamar sauran ba dan haka tad'age kai tashanye shi tas.
Nan inna tabata wata gumba ta amsa tafara ci wani irin gard'i taji ba kamar ta jiyaba wannan tafi dad'i dan kwakwa da zuma ne a jikinta haka tacita sosai.


Wajen k'arfe ukku aka had'a mata ruwan wanka tayi bayan ta gama aka shiryata cikin lace me tsada saida sukayi sallar la'asar sannan su Baba Malam suka shigo haka aka fito da amare aka kaisu d'akinshi yayi masu nasiha sosai.
Nan sukaita kuka.

Su Khausar aka d'auka a motoci aka tafi da su gidajen mazajensu inda Jawahir kuma sai k'arfe biyar sannan aka rakata filin jirgi ita da mijinta da abokanshi suka shiga jirgin.
Dakyar aka 'bam'bareta daga jikin Inna Mairo da zasu tafi.

Tunda suka shiga jirgin tahad'e kanta da gwiwa tadinga rusa kuka.
Duk yadda Faruk yaso yalallasheta kasawa yayi dan kuka tadinga yi sosai.

Suna isa Katsina suka tarar da motoci biyu su Aunty Kilima k'anwar Malam sunzo tararsu nan Aunty Kilima da wata k'awar Mom suka shiga mota d'aya da amarya inda gudar motar da driver yazo da ita su Faruk da Barr Nas suka shigeta.


Jawahir tana k'udundune cikin gyale har lokacin hawaye take ahaka suka isa gidan iyayen Faruk, d'akin Mom aka wuce da ita ganin har lokacin da sauran mutane a gidan.

Aunty kilima ce tazauna da ita a d'akin saboda kunya Jawahir takasa bud'e lullu'bin haka su Mom suka shigo suka gaisa suka sake mata nasiha bayan sallar isha'i aka tattarata aka kaita gidan mijinta Aunty Kilima da Hajiya Maimuna k'awar Mom ne kad'ai suka kaita direct part d'in Nasiba suka wuce da ita lokacin gidan ba kowa sai ita kad'ai tana ganinsu cikin sauri tazo tataresu tarungume Jawahir da ke lullu'be tana mata sannu da zuwa.

Su Hajiya Kilima sunji dad'in yadda Nasiba tanuna kulawa nan suka zaunar da su suka yi masu nasiha daga nan aka wuce da Jawahir part d'inta da yasha gyara sosai.

A saman gado suka zaunar da ita suka sake mata nasiha sannan sukai mata bankwana suka tafi.

Saida taji ba motsin kowa sannan tayaye mayafinta tana bin d'akin da kallo.


Wajen k'arfe tara Faruk yadawo gidan Nasiba ce tatareshi tarakashi part d'inshi yayi wanka yashirya ledojin da yashigo da su guda biyu tad'auki guda tace mashi suje.
Da mamaki yake kallonta yace ina zamuje?
Murmushi tayi tace wajen amarya man.
Cikin wasa yaharareta yace kamar irin kin gaji da ni kike nema kibada ni.
Dariya tayi tace eh d'in na ji bakomai nidai muje malam inrakaka dan bacci nakeji.

Haka suka fito tare sukaje part d'in Jawahir a parlor Nasiba tazauna yashiga ciki yasameta zaune dan tunda taji shigowarsu tamaida lullu'binta daga gefenta yazauna yana murmushi yace amarya ta ango kinsha k'amshi.
Shuru tayi nan yakai hannu zai yaye lullu'bin tayi saurin fad'awa jikinshi
Murmushi yayi a karo na biyu tare da rungumeta yace hanani ganin kyakkyawar fuskar za'ayi? Ko sai na siya?.
Shuru tayi nan yajanyeta tare da mik'ewa yace bakomai zan siya yanzu muje ga Nasiba chan a parlor tana jiranmu.
Mik'ewa tayi tabi bayanshi ta cikin gyalenta me shara shara take ganin hanya har suka fito parlor inda Nasiba take, a kujerar da take zaune yazauna inda Jawahir tazauna a 1 seater nan yayi masu nasiha.

Nasiba yafara tambaya ko tana da abinda zatace saidai tayi murmushi tace babu saidai abu guda shine yayi adalci atsakaninsu yarik'esu amana.
Murmushi Faruk yayi yace insha Allahu zanyi bakin k'ok'arina wajen ganin na yi adalci, kallon Jawahir yayi yace kefa akwai abinda zakice?
Girgiza kai tayi alamun a'a.
Nan yayi masu addu'ar zaman lafiya.

Mik'ewa Nasiba tayi tace toh Amarya da Ango sai ince mukwana lafiya.
Kallonta Faruk yayi yace Hearty tun yanzun?
Murmushi tayi tace wallahi na gaji sosai ga bacci ina ji.

Mik'ewa yayi yace toh bari inrakaki.
Saurin wucewa tayi gaba tana cewa a'a kabarshi nagode amaryarmu ga amanar miji nan na damk'a maki mukwana lafiya.

Tana fita taja masu k'ofa cikin sauri takoma part d'inta tana shiga tafashe da kuka tare da fad'awa saman gado wani irin kishine tadinga ji ganin yau mijinta ne zai kwana da wata ba itaba, kuka tadinga yi sosai kamar k'irjinta zai fito duk yadda taso tayi controlling d'in kukanta kasawa tayi saida tayi me isarta, har wajen k'arfe d'aya tana kwance zugum zuciyarta tadinga ayyana mata wasu abubuwa akan Faruk da Jawahir daga k'arshe takori shaid'an tamik'e taje tad'auro alwallah, sallah tayi raka'a biyu sannan tazauna karatun alk'ur'ani dan ji tayi kwatakwata bata ma jin baccin.

Sai wajen k'arfe ukku sannan tasamu taruntsa.


A chan 'bangaren su Faruk bayan fitar Nasiba komawa yayi gefen Jawahir yazauna tare da yaye mata malullu'binta saurin sadda kanta tayi k'asa.
Idanu yazuba mata yana k'are mata kallo duk sai taji ta tsargu nan gabanta yafara fad'uwa.
Saida yayi kusan minti biyar yana kallonta sannan yasa taje tad'auro alwallah sukayi sallah a nan parlor bayan sun gama ne yakama kanta yayi mata addu'a sannan yad'akko masu ledar da Nasiba ta ajiye masu dakanshi yatashi yaje kitchen yad'akko plate da cups.

Kaza yafara bata da fari ta k'i amsa saida yafara lalla'bata sannan tayarda taci cike da jin kunya take amsa, saida yatabbatar ta k'oshi sannan shima yafara cin nashi.

Mik'ewa jawahir tayi tashige bedroom d'inta toilet tafad'a tawanke hannu da bakinta sannan tazo tahaye gadonta ko kaya bata cireba gabanta yana dukan ukku ukku ita abun har mamaki yake bata ganin wannan ba shine aurenta na farko ba ammah duk tsoro ya kamata.

Tana nan kwance Faruk yashigo hawa yayi saman gadon tare da kallonta ganin yadda take wuk'i wuk'i da idanu yace Rabin ran ya kamata kicire kayan nan bazakiji dad'in bacci da su ba.
Cikin rawar murya tace a'a zan iya.
Murmushi yayi yace toh ai ni zasu takura man ammah bakomai tunda kince haka bari inrage maki su dakaina

Saurin tashi tayi zaune cike da tsoro tace bari inje incanza dakaina.
Rik'ota yayi yamatsa gab da ita nan yazuba mata manyan idanunshi saurin sadda kanta tayi k'asa tare da cewa bari inje incire....bata rufe bakiba taji hannunshi a bayanta yana neman yazage mata zip d'in riga saurin d'ago kai tayi takalleshi wanda hakan ya yi daidai da zage Zip d'in da yayi.
Tureshi tanemi tayi saima yarungumeta jikinshi tare da zame mata doguwar rigar nan hannunshi yafara yawo acikin jikinta.
Yadda gabanta yake fad'uwa Faruk yana ji dan har lokacin tana manne a jikinshi, cike da tsoro tace dan Allah Yaya Faruk kadaina.
Cikin kunnenta yarad'a mata Habibti yau fa ranar farin ciki ce agaremu dan Allah kibarni inyi.
Runtse idanunta tayi jin ya kirata da sunan da Umar yake kiranta da shi, jin ta yi shuru yasa yakwantar da ita ahankali nan yazuba mata idanu yana k'are mata kallo, ahankali tabud'e idanunta takalleshi ganin yadda yatsareta da mayun idanunshi sai a lokacin yakashe masu fitila.



Jawahir koda take ba sabuwar shiga ba ammah ta gurzu a hannun Faruk dan har kuka saida tayi saboda wahalar da tasha, Faruk ko za'a iya cewa fita yayi hayyacinshi, saida yasamu nutsuwa sannan yabarta.
'Daukarta yayi sukayi wanka tare sannan suka dawo suka kwanta yana manne da ita a jikinshi.


Washe gari bayan sunyi sallar asuba komawa sukayi bacci ba sune suka tashi ba sai wajen k'arfe tara da rabi, Faruk nema yayi suyi wanka tare da Jawahir tak'i dan kasa had'a idanu tayi da shi saboda kunya daga k'arshe yad'auketa yashiga da ita toilet tana ta nuk'u nuk'u da jiki yashareta yawanketa tas sannan shima yayi wanka.

Bayan sun fito ne suka shirya sannan yajata suka nufi babban parlor.
Suna zuwa suka samu Nasiba zaune ta sha gayu tana jira sufito.

Tana ganinsu murmushi tasaki tare da tashi cikin sauri tanufi inda suke tana zuwa tarik'e Jawahir da kanta yake sadde k'asa tace amarya sannunku da fitowa.
Maimakon ta amsa saima duk'awa da tayi tagaisheta amsawa tayi tare da rik'o hannunta tamik'e tace ina fata dai kina lafiya.
'Daga Kai tayi cike da jin kunya.
Kallon Faruk tayi da yake ta faman murmushi nan itama tayi murmushi sannan tagaisheshi, jawota yayi yarungume ahankali cikin kunnenta yarad'a mata kin mance irin gaisuwar da kikeyi min?.
Murmushi tayi itama ahankali tace yanzu ai bamu

Please Login or Register in order to submit comment