Reading FANSAR RAI complete 1&2 BY SIS NERJA'ART Chapter 23 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yad'an firgita, muryarce yaji tana cewa wannan aikina ne Barrister.
Dakewa yayi yace wanene nan? Ko ma wanene yabayyana min kanshi!! Shuru yaji nan yasake maimaitawa nan ma shuru dan haka yatabbatar da babu kowa d'akin.
Runtse idanunshi yayi tare da safke ajiyar zuciya.




**** *****

Barr MB kallonta yayi yace Malama Jawahir a iya binciken da mukayi mun gane cewa kin kashe Alhaji Mu'azu da 'ya'yanshi biyu wanda d'aya daga cikinsu mijine a gareki kinyi kisan ba dan komai ba sai dan kawai kina so kigaje dukiyar da ke gareshi.
Da mamaki tajuyo takalli Barr MB, bai damu da mamaki da yagani a fuskarta ba yacigaba da cewa, a lokacin da aka tuntu'bi Megadin ku ya bada shedar cewa daman kin dad'e kina yunk'urin kashe yayan mahaifin naki da shi da iyalanshi wannan dalilin ne yasa itama me aikin gidanku tagudu takoma garinsu saboda tsoron gargad'in da kika ta'ba yi masu a lokacin da suka ta'ba ganinki kin nufi d'akin kawun naki da wuk'a a hannunki lokacin yana bacci zaki kasheshi sai gashi 'yar aikin ta shigo ta ganki, a dalilin haka tatsorata takoma gidansu sannan shima megadinku bayan ankamaki da muka samu wannan bayanin daga wajenshi mun sake nemanshi dan musamu k'arin bayani ammah ya tsorata ya gudu ya koma garinsu chan Marad'i, shin ko zaki k'aryata wannan?

Baki tasaki tana kallonshi ganin yadda yake ta zubo mata k'arya.
Ganin batace komai ba yasa yacigaba da cewa sannan su kuma abokan mahaifinki kin kashesu ne saboda dalilin kun siyar masu da companynku wanda saboda karayar arzik'i yasa kuka rabu da shi shine daga baya kika dinga kashesu saboda kisamu kimaido companyn a hannunki, wannan bayanin mun sameshi a wajen sauran wad'anda suke da hannu wajen sayen companyn.....


Wata irin k'ara jawahir tasaki takai hannu cikin zafin nama tashak'e mashi wuya tace wallahi k'arya kake min, meyasa zakayi min k'arya.

Idanuwanshi waje sukayi saboda zafin mak'ara nan yafara neman yak'wace kanshi, police ne suka 'ban'bareshi daga hannunta alk'ali yace yakamata kisan a inda kike nan kotu ne ya zama dole kidinga ladabi.
Barr MB mik'a ma alk'ali takardun hannunshi yayi nan ya amsa yaduba sannan yad'ago yakalleta yace ga shaidar siyar da company da kukayi wanda a yanzu yake mallakin mutum biyu sannan ga duk bayani akan kisan da kikayi ko zaki iya kare kanki a gaban kotu me adalci?
Wasu sabbin hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin runtse idanunta, Alk'ali sake maimaita mata yayi, ahankali tagirgiza kai alamun a'a.
Buga table Alk'ali yayi yace tunda bakida shedar da zaki kare kanki kotu ta yanke maki hukuncin.....tun kan alk'ali ya ida fad'a Jawahir tasulale tazauna k'asa d'irshen tare da fashewa da kuka dan ta san kisane kawai zai biyo baya gashi bata cika burinta ba.......







_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:15 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 20*

K'ofar Kotun ce aka turo da k'arfi aka shigo wanda hakan yaja hankalin duk mutanen da suke cikin kotun suka juya dan ganin wanda zai shigo, shima kanshi Alk'ali bai ida fad'in hukuncin da yayanke ma Jawhir ba, wanda yabud'e k'ofar ne yashigo inda daga bayanshi sukaji murya ana cewa Ya Megirma me shara'a kar ayanke mata hukunci na zo da hujjoji masu k'arfi da zan bayyana ma kotu wanda zaisa agane batada laifi acikin kisan da akayi.


Jawahir na jin muryarshi saurin d'ago kai tayi tana kallonshi cike da mamaki, sanye yake cikin kayan aiki shi da nakusa da shi watau Barr Nas.

Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan saurin mik'ewa sukayi tsaye mamaki duk ya bayyana a fuskarsu k'arara sukace kai daga ina kake ya akayi kazo nan?

Kallonsu Barr Faruk yayi yai murmushi sannan yataka yanufi wajen alk'ali yana cewa agafarceni ya me girma me shari'a.
Alk'ali gyara zaman farin glass d'inshi yayi sannan yace watau sai yanzu kaga damar zuwa, kotu zakayi ma wasa da hankali bayan a farko baka zo ba saida kotu zata zartas da hukunci sannan.

Matsowa yayi yace agafarceni ya me girma me shara'a babban daliline yahanani zuwa wanda idan kabani dama nagabatar da hujjata zan sanar da kotu dalilin.

Jinjina kai Alk'ali yayi yace kotu ta baka dama, kowa yakoma yazauna.

Nan duk aka zauna, Jawahir mik'ewa tayi tsaye daga duk'en da take tana kallonshi, shima kallonta yayi sannan yamaida kallonshi ga Alk'ali yace Allah yagafarta malam nagode sosai, a yau zan gabatar da shedun da natattara akan zargin da akeyi ma Jawahir ammah kafin nan inaso kotu tafara bani dama infara tattaunawa da wadda ake k'ara.
Alk'ali yace ta baka dama.
Juyawa yayi ga jawahir sannan yace shin malama jawahir ko zaki taimaka kifad'a ma kotu yadda kike da Alhaji Mu'azu da su Alhaji Tanimu?
Shuru tayi tana kallonshi, nuni yayi mata alamun tayi magana sannan tace Eh Alhaji Mu'azu yayan mahaifina ne su kuma abokan mahaifina ne bayan rasuwarshi suka koma tare da yayan mahaifin nawa.
Jinjina kai yayi yace dakyau sannan yajuya ga alk'ali yace Allah yagafarta malam hujjata ta farko da zan fara gabatarwa itace Marigayi Alhaji Mu'azu da Abokan mahaifinta su takwas kenan sunyi amfani da damarsu sun kashe mahaifinta da mahaifiyarta dan sugaje dukiyarshi ban fad'i hakan ba saida natabbatar da shedata.
Kotun ce tafara kacamewa da hayaniya jin abinda yafito daga bakin Barr Faruk, saida aka nutsar da mutane sukayi shuru.
Juyawa Faruk yayi yakalli k'ofa yace kushigo.
Wani buzu ne yashigo nad'e da rawani a kanshi sai wata dattijuwa tana tura wata mata a saman wheelchair, jawahir idanu tazuba ma matar ahankali tace Ummah, matar ma kallonta tayi nan hawaye suka gangaro mata.

Barr Faruk ne yanuna buzun yace wannan shine megadin gidan Alhaji Mu'azu wannan kuma uwar d'akinshi ce.

Alk'ali d'agowa yayi yakallesu sannan yace ma megadin kotu tanaso kafad'a mata gaskiya akan abinda kasani a game da gidan Alhaji Mu'azu.

'Dage kanshi sama yayi yace eh zan fad'i gaskiya ni nine megadin shi kuma wannan yarinya tun bayan mutuwar iyayenta Alhaji yake azabtar da ita yana cin dukiyarta shi da abokanshi, akwai wata rana ina zaune a wajen gate ina sauraren radio Alhaji yafito zai shiga mota yafita nan naji yana waya yana cewa zai san hanyar da zaibi yafito da ita suje banki yasa taciro mashi kud'i daga account d'in mahaifinta, toh bayan nan na ta'ba jin suna magana da wani abokinshi yana cewa zai siyar mashi da wani gida da yagano k'anen nashi yana da shi baisan da gidan ba sai bayan mutuwar d'an uwan nashi, sannan a game da mutuwar d'an uwan nashi a ranar da aka shigo aka kasheshi Alhaji Mu'azu najiyo yana magana da wasu a waje ban dai ji abinda yake cewa ba saidai na ji ya ce masu ga makullin gidan nan, toh kuma da makullin aka bud'e gidan aka shigo aka kasheshi, d'aga hannunshi yayi sama yace wallahi wannan shine abinda nasani banyi maku k'arya ba.
Alk'ali jinjina kai yayi sannan yaduk'a yacigaba da rubuce rubucenshi yace Barrister muna saurarenka.
Faruk juyawa yayi ga Ummah yace Hajiya munaso kifad'a ma kotu matsayinki a wajen Alhaji Mu'azu da duk abinda kika sani akan kisanshi.

Goge hawayen fuskarta tayi tare da motsa 'bari d'ayan jikinta da yake da lafiya sannan murya chan k'asa tafara magana ganin haka yasa aka d'auko mata lasifika aka kanga wajen bakinta fara jawabi tayi tace nice matar Alhaji Mu'azu kamar yadda kotu taso zan fad'a mata gaskiya maganar gaskiya tabbas ni da mijina mun cutawa yarinyar nan kuma ya ci dukiyarta wannan shine abinda nasani sannan itace takasheshi da 'ya'yana biyuuuuu, kyarma tafara yi tana jijjiga nan wasu nurse guda biyu sukayo saurin zuwa wajenta dan dama tare da su sukazo, alk'ali yabada izini afita da ita amaidata asibiti nan suka tafi da ita.

Barr MB me yamik'e a fusace yace ya megirma me shari'a ya kamata kotu tagaggauta hukunta lauyan wadda ake k'ara akan zuwa da yayi har asibiti yazo da marar lafiya wanda a halin yanzu ya ja ta shiga wani hali, wannan ba daidai bane.
Alk'ali d'agowa yayi yace Barr MB yace koma kazauna, komawa yayi cikin sanyin jiki yazauna


Barr Faruk cigaba yayi da cewa shedata ta gaba da zan bada itace Marigayi Alhaji Mu'azu da Abokan mahaifinta su takwas sunyi amfani da damarsu sun kashe mahaifinta da mahaifiyarta dan sugaje dukiyarshi ban fad'i hakan ba saida natabbatar da shedata, wayarshi yad'auko yakunno recording d'in duk maganganun da yatura na wayar da su Alhaji Mu'azu yayi da abokanshi d'aya bayan d'aya yakunna ma alk'ali yasaurara, gabad'aya kotun tayi tsit ana saurare, akan lokacin da suke had'a plan zasu kashe Alhaji muhammad da kuma kisan da sukayi ma mahaifiyar jawahir sannan wajen ciro kud'i dan su mallaki dukiyarta duk ya saurara

Alhaji Mansur ne yayi saurin mik'ewa yace wannan k'arya ne sharrinshi ne kawai.

Kallonshi alk'ali yayi yace kotu tana gargad'inka kar kasake sa mana baki in ba hakaba zaka fuskanci hukunci.
Komawa yayi cikin sanyin jiki yazauna sannan alk'ali yaduk'a yafara 'yan rubuce rubuce, nan Barr Faruk yacigaba da cewa wannan bayanin duk na sameshi a cikin wayar Alhaji Mu'azu saboda wayarshi tana saving d'in call recording, ga ma wayar ta shi nan yamik'a ma alk'ali yadudduba cikin wayar nan yajinjina kai, yace cigaba da bayaninka.
Cigaba yayi da cewa sannan duk ga bayanai nan akan dukiyarta da suka mallaka da takardun jabu da suka dinga bugowa shaidar sun sayi fili da gidaje daga hannun mahaifinta, ita kuma ta shigar da k'ara kotu ammah anyi watsi da k'arar wannan dalilin ne yasa tadinga d'aukar mataki da hannuwanta saidai batayi niyar kashe d'an uwan mahaifin nataba shine yafara neman kasheta sannan ita kuma dan takare kanta takasheshi, kamar dai yadda matarshi tayi bayani.
Alk'ali yace shin ko zamu iya samun bayanai agame da dukiyar Alhaji Muhammad d'in?

Eh Allah yagafarta malam ammah kafin nan inaso kotu taban dama inyi ma mutane biyu wasu tambayoyi wad'anda tambayoyin ne zasu taimaka wajen samun cikakkar sheda.

Alk'ali kotu ta baka dama su wanene mutane biyun?

Juyawa yayi yakalli Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan da suke zaune suna zare idanu sunyi sharkaf da zufa,
Sannan yace Alhaji Mansur Maiharka da dollar sai Alhaji Sufyan me nasara.

Alk'ali ne yasake maimaita sunan yace kotu tana son ganinsu sun hallara a gabanta.
Su dukansu kusan tare suka mik'e cikin sanyin jiki suka fito suka tsaya.
Barr Faruk matsawa yayi kusa da su yace Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan wasu 'yan tambayoyine zanyi maku ammah kafin nan ya kamata kufara sanar da kotu matsayinku a wajen Alhaji Muhammad.
Su dukansu sukace Na'am
Yace eh kar dai kumanta a kotu kuke ya kamata duk abinda zaku fad'a kufad'i gaskiya.
Gyaran murya Alhaji Mansur yayi sannan yakalli Alk'ali yace ni abokin kasuwancin Alhaji Muhammad ne a lokacin da yake raye bayan rasuwarshi ne muka koma kasuwanci da d'an uwanshi, wannan shine dalilin sanin da nayi mashi.

Murmushi Barr Faruk yayi sannan yakalli Alhaji Sufyan yace kaikuma fa me zakace?

Eh toh nima dai kamar yadda Alhaji Mansur yace nima haka nake da su.

Kana nufin kaima abokan kasuwancinka ne?
Eh haka.

Dakyau ammah a iya binciken da nayi na gane cewa ba wai abokin kasuwanci kawai bane akwai aminta a tsakaninku da su, ammah ba ma wannan ba na san kun san komai a game da mutuwar Alhaji Muhammad da me d'akinshi Khausar ko akwai abinda zaku iya cewa?

Alhaji Mansur ne cikin 'bacin rai yace kai banason zancen banza me kake nufi? Sharri zaka ja mana?

Barr MB mik'ewa yayi yace ya megirma me shara'a ya kamata kotu tagargad'i lauyan wadda ake k'ara akan irin tambayoyin da yakeyi ma su Alhaji Mansur domin suna muni agaresu.

Alk'ali kallon Barr Faruk yayi yace kagyara yanayin tambayarka.
'Dan rissina kai yayi yace nagode sannan yajuya garesu yace, kafin mutuwar Alhaji Muhammad kun ta'ba taruwa ku takwas a chan wani d'aki kukayi magana inda kowa yafurta abinda yakeso yamallaka na Alhaji Muhammad a k'ark'ashin jagorancin d'an uwanshi, ko zaku iya tuna haka?

Su dukansu shuru sukayi suna kallon kallo sai chan Alhaji Mansur yagirgiza kai yace bansan anyi haka ba.

Shuru faruk yayi sai kuma yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a tabbas su Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan suna cikin mutanen da suke da hannu akan mutuwar Alhaji Muhammad dan a nan cikin wayar da namik'o duk akwai muryoyinsu da maganganun sirrin da sukayi a tsakaninsu sannan ga k'arin shedar da ke gareni ta k'arshe, juyawa yayi yakallesu sannan yabud'e file d'in da yake hannunshi yad'ago masu yace shin cikinku akwai wanda yagane takardun da suke cikin file d'innan?

Zaro idanu sukayi gabad'aya nan take cikin Alhaji Sufyan yakad'a yace ina kasamo wad'annan?.

Murmushi yayi sannan yace takardar farko original ce ta companyn Alhaji Muhammad inda ta biyu takasance jabu ce kun bugotane dan ku samu ku mallake companyn ga signing d'inku nan da komai.

Mai gabatar da k'ara ne yazo ya amsa yakai ma alk'ali, wasu takardun yafiddo yanuna masu yace wannan fa me zakuce akanta?
Shuru sukayi suna kallonshi sai Alhaji Mansur yayi k'arfin halin cewa wannan ai kai za'a tambaya dan kai kasan sharrin da kake shirin k'ullawa.
Girgiza kai yayi yace wannan ba sharri bane sannan yajuya yakalli Alk'ali yace ya megirma me shara'a wannan takardun motocin Alhaji Muhammad ne da suka samo a cikin gidanshi bayan mutuwarshi sunyi amfani da wani ya yi masu yarjejeniya akan kowane d'aya daga cikinsu Alhaji Muhammad ya siyar mashi da motocinshi biyu ga signing nan irin nashi anje anyi, zuwa yayi yamik'a ma Alk'ali nan yaduba, sannan yace ya megirma me shara'a na tabbata da za'a tuhumesu da zasu fad'i gaskiyar cewa suna da hannu a cikin mutuwarshi da kuma irin k'ulle k'ullen da suka dinga shiryawa akan dukiyarshi wadda sunci fiye da rabin dukiyar dan Alhaji Sufyan shi yashirya masu yadda zasuyi susamo dukiyar da take cikin account d'in jawahir inda su Alhaji Mansur da Alhaji Tanimu sukaje suka shirya ma kawunta k'arya a matsayinshi na bagidaje sukace yasamo masu kud'in zasu yi kasuwanci wanda zai dinga kawo masu kud'i sosai shine yayi amfani da damarshi yatafi da jawahir a banki yasa tayi mashi signing d'in rabin dukiyarta aka fiddo daga acount d'in koda yakawo masu ba wai business sukayi ba sunje sun raba kud'in a tsakaninsu ne.

Alhaji Sufyan ne yayi saurin katseshi yace ya megirma me shara'a wannan k'arya ne sharri kawai yake son ja mana dan ya'bata mana suna bamusan komai ba akan abinda ake zarginmu da shi ba dan bamu aikata ba kawai dai yana da wani nufi akanmu ne dan kawai na hanashi auren d'iyata saisa yakeso ya'bata mana suna.


Faruk kallon Alk'ali yayi yace ko d'aya ba sharri bane Allah yagafarta malam duk sun aikata dan ga shedu nan na tara ga muryoyinsu nan a cikin wayata.

sake kunno recording d'aya daga cikin su yayi nan murya tafara tashi ana cewa "Hello kana jina ya kamata kayi k'ok'ari wajen ganin ka samo mana file d'in filin nan dan da alama zaiyi kud'i sosai ni na san yadda za'ayi asiyar da shi batare da kowa ya ganeba dan nima kaga wannan filin da kabarmin gwamnati nasiyar mawa kuma ta siya da kud'ad'e masu tsoka.
Toh shikenan Alhaji koma me kenan nasan hanyar da zanbi insamo dan dama maganar da muka gama yi da Alhaji tanimu kenan dan shine jagoran komai, da ace akwai hanyar da zanbi da a yau d'innan sai naga bayan yarinyar nan kowa yahuta dan na san idan har tamutu dole abarmin gadonta gabad'aya tunda ni kad'ai ne d'an uwan mahaifinta,,, Cewar Alhaji Mu'azu.

Daga chan 'bangaren dariya akayi akace kaidai kabi komai a hankali ko da baka kasheta ba zaka iya yin amfani da damarka wajen ganin mun samo dukiyar Alhaji Muhammad, inyaso idan har mun gama samun yadda mukeso zaka iya kasheta saidai kuma idan har zaka rufe ma mutane baki dan kar ayi zargin wani abu kamar yadda mukayi bayan munsa ankashe Alhaji Muhammad da matarshi.

Dariya Alhaji Mu'azu yayi yace ai fiye da hakan ma zan iya sa wa ayi mata dan ni ban had'a komai da kud'iba abokina, yanzu dai zuwa anjima zan kiraka idan har nagama tattara bayanan filin inyaso sai muje musiyar da shi.

Yauwa mutumina kayi k'ok'arin haka sai na ji daga gareka".



Yana k'arewa wani kuma yasake kunnowa me irin muryar sukaji yana cewa, Hello Alhaji Mu'azu ina jinka d'azu ka kirani bana kusa.
Eh Wallahi abokina cewa nayi ta samu fa a yanzu ga wani gida nan na Alhaji Muhammad da nagano yana da shi batare da sanin kowaba sai yanzu naga takardun gidan na je na ganshi kuma antabbatar min da nashine.
Daga chan 'bangaren dariya akayi akace lallai Alhaji Muhammadu wayonshi ya yi yawa watau yana da gida batare da sanin ka ba, toh bari zan zo inje muga gidan idan har yana da girma sosai ni zan sayeshi dan dama inaso mutashi da iyalina daga nan, kace abu ya zo gidan sauk'i ai wallahi mutuwar nan tashi dad'i tayi min dan ko bakomai munsan muma mun mori dukiyarshi.
Alhaji Mu'azu ma dariya yayi yace kaidai bari a yanzu gashinan ina ta facaka da kud'i yadda nakeso ba kamar lokacin da yake raye ba, ka san mutuwarshi ko kad'an bata d'aga min hankali ba sai waje d'aya lokacin da kabani layarnan insaka mashi a baki toh a nan ne nad'an tsorata dan ko da su Alhaji Mannir suka shigo gidan zasu kasheshi ban wani d'aga hankaliba dan na san zamuyi nasara.

Katseshi yayi yace a'a Alhaji Mu'azu kayi shuru kar ajiyo ka asirinmu yatonu agane mune muka kasheshi abar maganar kawai zan zo yanzun nan muje inga gidan dan ka san bana wasa da kud'i,,, su dukansu dariya sukayi....



Suna gama saurare yace shin wannan ba muryarka bace Alhaji Sufyan ko itama sharri akayi maka?
Fara raba idanu yayi yakalli Alk'ali cikin alamar rashin gaskiya yace ni bansan komai ba akai sharri yake son ja min wallahi.

Alk'ali baice komai ba yana dai cigaba da kallonshi sai kuma yad'auko takardun gidan yasake dubawa.

Barr Faruk cigaba yayi da cewa sannan akwai lokacin da Alhaji Mansur yakirani muka had'u yagargad'eni akan injaye daga shari'ar Jawahir har yad'auko mak'udan kud'i yabani ammah ban amsaba dan haka ne yasa aka kamani aka rufe a wani gida dan kar inzo inbada sheda a kotu wannan ne dalilin da yasa ban halarci kotu da wuri ba yau dan sai a yau nasamu natsero daga gidan


Cikin d'aga murya Alhaji Mansur yace k'arya yake wallahi sharri kawai yake ja min ba ni bane.

Kallonshi Faruk yayi yace ina da sheda da zata bayyanar da haka dan lokacin da muka had'u na yi recording d'in duk maganar da mukayi batare da ka saniba, nan yakunno recording d'in yakunna ma Alk'ali sannan yace bayan wannan akwai wata shedar, kallon Barr Nas yayi yace kace sushigo, nan yamik'e yafita duka mutanen cikin kotun juyawa sukayi dan ganin wanda zai shigo, police ne suka shigo da wasu mutane biyar a d'aure , Alhaji Mansur yana ganinsu zabura yayi nan yafara kalle kalle yana neman hanyar gudu yarasa, Barr Faruk kallon Alk'ali yayi yace wad'annan sune mutanen da yasa suka satoni suka tsareni

Alk'ali kallonsu yayi yace kufad'a ma kotu tsakaninku ga Allah abinda kuka sani inkukayi k'arya kotu zata hukuntaku.


Babban sune yayi k'arfin halin cewa wallahi wad'annan mutanen sune suka kiramu suka bamu kud'i sukace musato Barrister mutsareshi shine suka bamu gidan da muka zauna da shi, wallahi sune suka sa mu.

Alk'ali kallonsu Alhaji Mansur yayi da gabad'ayansu idanu sun raina fata yace toh kunji duk shaidar da aka samu akanku ya kamata kufad'a ma kotu gaskiya inko ba hakaba kotu zatasa atambayeku.

Shuru sukayi suna mazurai chan alk'ali yad'akko waya yakira ba'a yi minti biyar ba sai ga wasu k'atti su hud'u sun fito kowane d'aya hannunshi rik'e da shar'be'biyar bulala, Alhaji Sufyan yana ganinsu yayi saurin cewa wallahi zan fad'i gaskiya duk abinda yafaru mun aikata tabbas mu takwas ne muka shirya komai shidda daga ciki duk sun mutu, munci dukiyar Alhaji Muhammad sannan duk takardun nan mu mukasa aka had'a mana jabu muka siyar ma da gwamnati filayenshi guda biyu ko Alhaji Mansur?
Fashewa da kuka Alhaji Mansur yayi yace tabbas hakane mun aikata kuma sharrin shaid'anne dan Allah munaso kotu ta yafe mana insha Allahu bazamu sake aikata irin haka ba.

Alk'ali ajiyar zuciya yasafke yace Alhamdulillah kun amsa laifinku da kanku dan haka kotu zata yanke maku hukunci daidai da yadda shari'a tace, dan haka za'a yi maku hukunci guda biyu na farko dai bayan kun biya wannan baiwar Allahr dukiyarta da kukaci ku da kuke raye zakuyi zaman shekara guda a gidan kaso, na biyu kuma wannafsi binafsi dan haka ya zama dole za'a kasheku kamar yadda kuka kashe wasu.

Sannan kotu ta wanke Jawahir muhammad mekud'i daga zargin da akeyi mata dan haka kotu ta saketa zata koma tacigaba da rayuwarta sannan za'a damk'a mata dukkan dukiyarta da wad'annan 'barayin sukaci.

Su Alhaji Mansur duk'awa sukayi k'asa suna kuka suna cewa dan Allah Alk'ali ataimaka mana wallahi hukuncin nan ya yi mana tsauri ataimaka a safsafta mana tunda mun amsa laifinmu sannan kud'in da suka rage hannunmu basu kai wanda muka ci mata ba.

Girgiza kai Alk'ali yayi yace wannan ne kuma bazai yuwu ba dole ayi maku hukunci daidai da na kowa, kubar ma ta wannan sai kun biyata kud'in da kukaja aka rufeta tsawon shekara guda batare da hak'k'inta ba.


Mutanen da ke zaune cikin kotun salati suka farayi suna Allah wadai da halin su Alhaji Mansur.



Jawahir da take tsaye tun d'azu inba hawaye ba babu abinda take, hannu tad'aga tafara yi ma Allah godiya sai kuma chan cikin kuka tace tunda dai har gaskiya ta bayyana na ji dad'i bana buk'atar komai daga wajensu subar kud'in na yafe kawai dai akashesu su ma shine zan fi jin dad'i.

Alk'ali yace ba maganar yafewa a cikin hukuncin da kotu tazartas ya zama dole subiya wad'annan kud'in, kallon police yayi yace atafi da su subiya kud'in ga list nan na kud'inta da sukaci idan kud'ad'ensu basu isaba kusiyar da duk wata k'addara da suka mallaka.
Su kuma wad'annan (yanuna wad'anda suka sace Faruf yace) atafi da su gidan yari zasuyi bauta tsawon shekara guda sannan asakesu, yana fad'in haka yabuga table d'in gabanshi.


Nan take aka saka ma su Alhaji Sufyan da Alhaji Mansur ankwa aka fita da su.

Nasiba da take tsaye wajen motarta ita da mahaifiyarta suna kuka nan suka nufi wajen da mahaifin nata yake kafin su isa 'yan jarida har sun rufeshi sun fara mashi tambayoyi a matsayinshi na d'an siyasa, kutsawa sukayi suka isa wajen, yana ganinsu yayi saurin sadda kanshi k'asa......






_Sis Nerja'art✍🏻_[7/24, 11:21 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 21*

Nasiba cikin sheshek'ar kuka tace Daddy kalli abun kunyar da kajawo mana yanzu hakan da kayi daidai ne? Kaduba kaga halin da kajefa kanka da mu a ciki a idanun duniya, meyasa kabi son zuciya ka aikata hakan? Ba ka tunanin yadda rayuwarmu zata kasance, taya kake tunanin laifin nan da ka aikata zai goge a idanun mutane? Ya kakeso muyi da rashin ka? Meyasa haka Daddy, meyasa?,,, kukan da yaci k'arfinta ne yasa tayi saurin juyawa, har lokacin kan Alhaji Sufyan yana sadde a k'asa ji yake kamar a mafarki abin yafaru hawaye ne suka fara fita daga idanunshi, muryar matarshi yaji cikin muryar kuka tana cewa Alhaji ban ta'ba tunanin haka daga garekaba wallahi ka

Please Login or Register in order to submit comment